Terms Dictionary

Kitse - Tana nufin maiƙon da ke jikin nama. Misali; Ragon yana da kitse ainun, maiƙon jikinsa ya isa a soya shi. ENG; Fat On Meat (A turance tana nufin kitse)
Kitso - Tana nufin salon tufke gashi don ado da kwalliya. Misali; Mata su ne ke yin ado da kitso da ƙunshi. ENG; Plaiting Of Hair (A turance tana nufin kitso)
Kiwata - Tana nufin ciyarwa ta tsahon lokaci. Misali; Zan kiwata Saniyar da aka ba ni har ta hayayyafa. ENG; Feed Animal (A turance tana nufin kiwata)
Kiwo - Tana nufin ciyar da dabbobi kamar awaki da shanu da kaji da sauransu. Misali; Sana'ar kiwo ta karɓi Malam Iro, garkensa sai haɓaka yake kullum. ENG; Tending animal at pasture (A turance tana nufin kiwo)
Kiyama - Tana nufin ranar tsayuwa, wato ranar da za a tashi ababen halitta a yi musu hisabi. Misali; Allah SWT shi ya san ranar da kiyama za ta tashi. ENG; Day Of Resurrection (A turance tana nufin kiyama)
Kiyashi - Tana nufin ɗan ƙaramin ƙwaro mara cizo. Misali; Kiyashi ya lulluɓe naman da na ɓoye a cikin ƙwarya. ENG; Small Ant (A turance tana nufin kiyashi)
Kiɗa - Tana nufin rauji ko sauti mai daɗi. Misali; Matasan sun kunna kiɗa suna cashewa don murnar bikin abokinsu. ENG; Music (A turance tana nufin kiɗa)
Kiɗime - Tana nufin gigicewa ko shiga wani hali. Misali; Duk sun kiɗime saboda tashin hankali. ENG; Confused/Flustered (A turance tana nufin kiɗime)  
Knee - A turance tana nufin gwiwa. Misali; Ciwon gwiwa yake yi tunda shekarunsa suka ja. HAU; Gwiwa (Tana nufin sashen jiki da ke tsakanin ƙafa da cinya)
Kneel with front elbows on ground - A turance tana nufin gurfana. Misali; Masu laifin sun gurfana a gaban alƙali. HAU; Gurfana (Tana nufin durƙusawa a kan gwuiwa biyu)
1 186 187 188 189 190 300