Terms Dictionary

Kankana - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan maramari mai ɗauke da ruwa sosai a ciki. Misali; Kankana ta fi yawa a cikin kayan marmarin da muka siyo. ENG; Watermelon (A turance tana nufin kankana)
Kanti - Tana nufin gurin siyar da kayayyaki. Misali; An buɗe sabon kanti a unguwarmu. ENG; Shop (A turance tana nufin kanti)
Kantoma - Tana nufin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙaramar hukuma. Misali; An naɗa baban su Sharif kantoma a ƙaramar hukumar Dala. ENG; Local Authority Administrator (A turance tana nufin kantoma)
Kanumfari - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ƙamshi. Misali; Shayi idan an sa kanumfari ya fi daɗi. ENG; Clove (A turance tana nufin kanumfari)
Kanwa - Tana nufin wani nau'in gishirin tabki mai ƙunshe da sinadarin sodium a ciki. Misali; Ki ɗan jefa kanwa a waken don ya yi laushi da wuri. ENG; Potash (A turance tana nufin kanwa)
Karaf - Tana nufin ba zato ba tsammani. Misali; Ta yi karaf ta kamo shi kafin ya gudu. ENG; Suddenly (A turance tana nufin karaf)
Karaga - Tana nufin kujerar mulki ko sarauta. Misali; Sarki yana zaune a kan karaga tun safe. ENG; Throne (A turance tana nufin karaga)
Karantar - Tana nufin koyarwa. Misali; Ya karantar da mu darussa masu yawa. ENG; Teach (A turance tana nufin karantar)
Karate Fedaration of Nigeria (KFN) - Hukumar Wasan Kareti Ta Najeriya
Karatu - Tana nufin ambaton abinda aka rubuta. Misali; Tun safe ɗaliban suke karatu ba ƙaƙƙautawa. ENG; Reading (A turance tana nufin karatu)
1 177 178 179 180 181 300