Terms Dictionary

Kaki - Tana nufin kayan sojoji. Misali; Dole ne ka ji tsoron mai kaki don ka san soja ba abin wasa ba ne. ENG; Khaki Cloth (A turance tana nufin kaki)
Kaki - Tana nufin majinar da ake fitarwa daga maƙogwaro. Misali; Mura ta sa yana ta kaki. ENG; Phlegm From Throat (A turance tana nufin kaki)
Kaki - Tana nufin saƙar zuma. Misali; Zumar mai kyau ce don a cikin kaki take. ENG; Bees-wax (A turance tana nufin kaki)
Kakide - Tana nufin kitsen da ake samu a jikin nama musamman bayan an soya. Misali; Ina son babbar sallah ta zo don in samu kakide bayan an soya nama. ENG; Meat Fat (A turance tana nufin kakide)
Kakkarai - Tana nufin ciwon Yatsa. Misali; Kakkarai yana hana bacci saboda tsananin ciwo. ENG; Disease of Fingers (A turance tana nufin kakkarai)
Kakkaɓe - Tana nufin goge datti ko ƙura. Misali; Sai da na kakkaɓe ƙura a kan kujerar kafin na zauna. ENG; Shake dust off something (A turance tana nufin kakkaɓe)
Kalaci - Tana nufin abinci, na safe ko na rana ko na dare. Misali; Idan na gama kalaci za mu je dubiya. ENG; Any Meal (A turance tana nufin kalaci)
Kalami - Tana nufin zance ko magana. Misali; Ya iya kalami mai daɗi shi yasa mutane ke son shi. ENG; Words/Speech (A turance tana nufin kalami)
Kalanda - Tana nufin jadawalin da ke ƙunshe da watanni goma sha biyu na shekara. Misali; Sabuwar kalandar muslunci ta fito. ENG; Calendar (A turance tana nufin kalanda)
Kalangu - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya. Misali; 'Yan mata na son kiɗan kalangu matuƙa. ENG; Variable-tone Drum (A turance tana nufin kalangu)
1 174 175 176 177 178 300