Guduma - Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen buga katako ko ƙusa da sauransu.
Misali; Ya buge hannu da guduma a lokacin da yake gyaran kujerar.
ENG; Hammer (A turance tana nufin guduma)
Gudunmawa - Tana nufin tallafi ko agaji.
Misali; Gwamnati ta kawo gudunmawa ga waɗanda ibtila'in gobara ya afkawa.
ENG; Help (A turance tana nufin gudunmawa)
Guguwa - Tana nufin iska mai ƙarfi.
Misali; Bishiyar ta faɗo ne yayin da ake guguwa.
ENG; Whirlwind (A turance tana nufin guguwa)
Guild - Kadaura, Ƙungiya, Majalisa
Guinea Corn - A turance tana nufin dawa.
Misali; Tuwon dawa na ƙara lafiya saboda tana ƙunshe da sinadarai masu inganta lafiya.
HAU: Dawa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in hatsi)
Guinea-worm - A turance tana nufin kurkunu.
Misali; An yi nasarar kawar da cutar kurkunu a Najeriya.
HAU; Kurkunu (Tana nufin cutar fata mai sanya ƙuraje)
Gujjiya - Tana nufin nau'in abin ci mai kama da wake amma ta fi wake girma, kuma a cikin kwanso take, sai an ɓare.
Misali; Ina son gujjiya sosai, na ji an ce har tuwonta ake yi.
ENG; Bambara Groundnut (A turance tana nufin gujjiya)
Gulbi - Tana nufin kwari da ruwa yake taruwa.
Misali; Indo da ƙawayenta sun tafi gulbi yin wanki.
ENG; River (A turance tana nufin gulbi)
Gulma - Tana nan nufin ɗaukar zancen wani a kai wa wani da zimmar haɗa su faɗa.
Misali; Musulunci ya haramta gulma.
ENG; Setting one person against another through gossip (A turance tana nufin gulma)
Gum - A turance tana nufin danƙo.
Misali; Hannayensa danƙo suke saboda ya sha alawa.
HAU; Danƙo (Tana nufin abu mai mannewa)