Terms Dictionary

Gizo - Tana nufin ƙwaro mai yin yana a bango, yana da ƙafafu guda takwas. Misali; Gizo-gizo ya yi yawa a ɗakin. ENG; Spider (A turance tana nufin gizo)
Giɓi - Tana nufin gurbin mai faɗi da ke tsakanin haƙora. Misali; Ta samu giɓi sakamakon haƙorinta ɗaya da ya fita. ENG; Gap from loss of tooth (A turance tana nufin giɓi)
Gladden - A turance tana nufin faranta. Misali; Matar ta faranta ran mijinta ta hanyar yi masa girki. HAU; Faranta (Tana nufin sanya farin ciki)
Glare At - A trurance tana nufin harara. Misali; Harara ta yake don na dake shi. HAU; Harara (Tana nufin kallon raini ko wulaƙanci)
Goat or sheep skin used as prayer mat - A turance tana nufin buzu Misali; Malam yana sallah akan buzu a lokacin da na je. HAU; Buzu (Tana nufin abin da ake salla a kai wanda aka yi shi da fatar akuya ko tinkiya)
Goat Skin Bag - A turance tana nufin burgami. Misali; Malam Yahaya ya ratayo burgami a gurin bikin maharba. HAU; Burgami (Tana nufin jakar da aka yi ta fatar akuya, wadda yawanci masu ba da maganin gargajiya ke amfani da ita)
Goats - A turance tana nufin jam'in akuya. Misali; Kaka yana kiwon awaki. HAU; Awaki (Jam'in akuya)
Goba - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari tana da ƙananan ƙwallaye a cikinta. Misali; Goba tana da sinadarai masu inganta lafiya a cikinta. ENG; Guava (A turance tana nufin goba)
Gobe - Tana nufin bayan kwana guda ma'ana ranar da za biyo bayan wacce ake ciki. Misali; Gobe babu karatu saboda hutun ƙarshen mako. ENG; Tomorrow (A turance tana nufin gobe) Kishiyarta; Yau
God - A turance tana nufin jalla. Misali; Allah jalla wa azza ne ya nufa za a yi ruwa mai yawa yau. HAU; Jalla (Tana nufin Allah maɗaukakin sarki)
1 118 119 120 121 122 300