Food/Meal - A turance yana nufin abinci.
Misali; Muna cin abinci sau uku a rana.
HAU; Abinci (Yana nufin duk abinda za a ci ya kawar da yunwa)
Fool - A turance tana nufin dolo.
Misali; Yaron dolo ne, ya samu matsalar ne tun daga haihuwa.
HAU; Dolo (Tana nufin wanda yake da ƙarancin hankali da fahimta)
Football Writers Association (FWA) - Ƙungiyar Marubuta Wasan Ƙwallon Ƙafa
Fore-arm - A turance tana nufin damtse.
Misali; Masu manyan damtse yawancin su ƙarfafa ne.
HAU; Damtse (Tana nufin gaɓar da take saman hannu)
Forehead - A turance tana nufin goshi.
Misali; Ya fasa goshi garin wasan banza.
HAU; Goshi (Tana nufin gaɓar da ke saman gira)
Forestry Research Institute of Nigeria (FRIN) - Cibiyar Nazarin Gandun Daji Ta Najeriya
Forum - Ƙungiya, Kadaura
Foundation - A turance tana nufin harsashi.
Misali; An dasa harsashin gina makarantar islamiyya a yankin mu.
HAU; Harsashi (Tana nufin tushe)
Foundation - Gidauniya
Four - A turance tana nufin huɗu.
Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu.
HAU; Huɗu (Tana nufin lambar da ke bin bayan uku)