Servant - A turance tana nufin bara.
Misali; Idris bara ne a gidan Alhaji Sani.
HAU; Bara (Tana nufin mai yin hidima a cikin gida)
Service - Hukuma, Ma'aikata
Serving God - A turance tana nufin ibada.
Misali; Idan mutum ya kasance mai ibada rayuwarsa tana albaraka.
HAU; Ibada (Tana nufin bautawa Allah)
Setting one person against another through gossip - A turance tana nufin gulma.
Misali; Musulunci ya haramta gulma.
HAU; Gulma (Tana nan nufin ɗaukar zancen wani a kai wa wani da zimmar haɗa su faɗa)
Sexual Intercourse - A turance tana nufin jima'i.
Misali; Cututtukan sanyi na da nasaba da jima'i a lokuta da dama.
HAU; Jima'i (Tana nufin saduwa tsakanin mace da namiji)
Shake - A turance tana nufin jijjiga.
Misali; Sai an jijjiga maganin sannan ake sha.
HAU; Jijjiga (Tana nufin girgizawa)
Shameless/Disrespectful Person - A turance tana nufin ja'iri.
Misali; Babu mai yin rawar Gala sai ja'iri.
HAU; Ja'iri (Tana nufin mara kunya)
Sharpen - A turance tana nufin feƙe.
Misali; An feƙe wuƙaƙen kafin a yanka naman.
HAU; Feƙe (Tana nufin saka abu ya yi kaifi)
Sharpness - A turance tana nufin kaifi.
Misali; Wuƙar tana da kaifi sosai don ta yanke ni.
HAU; Kaifi (Tana nufin ƙarfin da zai iya yanka)
Shaving - A turance yana nufin kwashe gashi.
Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa.
HAU; Aski (Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban)