Sayings of prophet Muhammad SAW - A turance tana nufin Hadisi.
Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta.
HAU: Hadisi (Tana nufin maganganun manzon Allah SAW)
Scheme - Shiri, Tsari
Science Teachers Association of Nigeria (STAN) - Ƙungiyar Malaman Kimiyya Ta Najeriya
Seal - A turance tana nufin hatimi.
Misali; Wasiƙar tana ɗauke da hatimin sarki.
HAU; Hatimi (Tana nufin wata shaida ko alama)
Search - A turance yana nufin biɗa.
Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi.
HAU; Biɗa (Tana nufin nema ko lalube)
Search - A turance tana nufin caje.
Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba.
HAU; Caje (Tana nufin duba ko ina)
Second (of time) - A turance tana nufin daƙiƙa.
Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga.
HAU; Daƙiƙa (Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi)
Secret - A turance tana nufin asiri.
Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana satar kayan mutane.
HAU; Asiri (Tana nufin abinda yake a ɓoye)
Securities & Exchange Commission (SEC) - Hukumar Kadarori da Hada-hadar Hannun Jari
See something from afar - A turance tana nufin hanga.
Misali; Kamar Talatu na hanga tana shiga gidan maigari.
HAU; Hanga (Tana nufin gano abu daga nesa)