Terms Dictionary

Sweat - A turance tana nufin jiɓi. Misali; Mara gaskiya ko a ruwa sai ya yi jiɓi. HAU; Jiɓi (Tana nufin gumi ko zufa)
Sweet made from ground tigernuts and groundnut - A turance tana nufin daƙuwa. Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su. HAU; Daƙuwa (Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari)
Sweet pounded millet mixed with water - A turance tana nufin gumba. Misali; An raba gumba a gidan mutuwar. HAU; Gumba (Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa)
Swollen - A turance tana nufin hulu-hulu. Misali; Idonsa ya yi hulu-hulu tun jiya saboda ciwo yake masa,. HAU; Hulu-hulu (Tana nufin kumburi sosai)
Sympathy - A turance tana nufin jaje. Misali; Shugaban ƙasa ya yi wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa jaje. HAU; Jaje (Tana nufin taya alhini da tausayawa wanda wani abu mara daɗi ya same shi)
Sympathy/Pity - A turance tana nufin juyayi. Misali; Muna cikin juyayi sakamakon rashin da muka yi. HAU; Juyayi (Tana nufin alhini ko tausayi)
1 11 12 13