Terms Dictionary

Kwaleji - Tana nufin makaranta musamman ta gaba da sakandire. Misali; Idan matasa suka shiga kwaleji suna jin kansu. ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwalekwale - Tana nufin ƙaramin jirgin ruwa. Misali; Ba a zuwa ƙauyen sai an hau kwalekwale. ENG; Canoe (A turance tana nufin kwalekwale)
Kwalli - Tana nufin nau'in abin ado da ake sa wa ido don ƙara masa kyau da ƙwari. Misali: Kwaliiya ta ba ta cika sai na sa kwalli a idona. ENG: Antimony (A turance tana nufin kwalli)  
Kwaɓa - Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya. Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin. ENG; Mix Something (A turance tana nufin kwaɓa)
Kwaɗayi - Tana nufin tsananin son cin abu ko yin abu. Misali; Tun da ta fara kwaɗayi na san tana da juna biyu. ENG; Craving/ Yearning (A turance tana nufin kwaɗayi)
Kwaɗo - Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa. Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu. ENG; Frog (A turance tana nufin kwaɗo)
1 25 26 27