Gajiya - Tana nufin mutuwar jiki da jin rashin ƙarfi.
Misali; Gudu na sa gajiya sosai.
ENG; Tiredness (A turance tana nufin gajiya)
Galadima - Tana nufin muƙamin sarauta.
Misali; An naɗa malam Sani galadima jiya da safe.
ENG; A traditional title (A turance tana nufin galadima)
Galibi - Tana nufin mafi yawa.
Misali; Galibi akan yi ruwa mai yawa a watan Agusta.
ENG; Majority (A turance tana nufin galibi)
Gamayyar Ƙungiyar ‘Ƴankasuwa Ta Afirka - Organization of Afirican Trade Union Unity (OATUU)
Gamayyar Ƙungiyoyin Ma’aikatan Masana’antu da Kamfanonin Gwamnati da Wuraren Shaƙatawa Ta Ƙasa - Amalgamated Union of Public Corporations, Civil Service Technical & Recreational services Employees (AUPCTRE)
Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa - Coalition of Northern Youth Groups (CNYG)
Gamayyar Ƙungiyoyin Sa-Kai - Civil Society Organizations (CSO)
Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago - United Labour Congress (ULC)
Gambling - A turance tana nufin caca.
Misali; A hanyar akwai dandalin da 'yan caca suke zama.
HAU; Caca (Tana nufin wasan kati ne da ake sa kuɗi ko wani abu da zimmar wanda ya yi nasara ya ci wannan kuɗin ko abinda aka sa)
Game like draughts - A turance tana nufin dara.
Misali; Da yamma ake wasan dara a majalisar.
HAU; Dara (Tana nufin wasa da ake yi a kan katako mai faɗi, yana kama da wasan ludo)