Terms Dictionary

Husks of Rice - A turance tana nufin ɓuntu. Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai. HAU; Ɓuntu (Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki)
Hut - A turance tana nufin bukka. Misali; Fulani na gina bukka a rugagensu domin su zauna. HAU; Bukka (Tana nufin ƙaramin ɗakin da ake ginawa da busasshiyar ciyawar da ake kira da zana)
Hutu - Tana nufin zama guri ɗaya ba tare da aikin komai ba ko rashin zuwa gurin aiki ko makaranta ko gyurin sana'a na wani lokaci don a tsahirta kafin a ɗora. Misali; Yara ba sa zuwa makaranta saboda an ba su hutu. ENG; Rest/Holiday (A turance tana nufin hutu)
Huɗu - Tana nufin lambar da ke bin bayan uku. Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu. ENG; Four (A turance tana nufin huɗu)
Huɗuba - Tana nufin jawabai na hikima da jan hankali don faɗakarwa ko kwaɗaitarwa a kan binn Allah da kuma gujewa saɓa masa. Misali; Muna sauraron huɗuba daga masallaci mai alfarma a rediyo. ENG; Sermon (A turance tana nufin huɗuba)
1 21 22 23