Hair - A turance tana nufin gashi.
Misali; Mata sun fi maza yawan gashi.
HAU; Gashi (Tana nufin tsiron da ke fitowa a saman fatar ɗan Adam ko dabba)
Hajijiya - Tana nufin jujjuyawa.
Misali; Maganin da na sha ya sa ni jin hajijiya.
ENG; Dizziness (A turance tana nufin hajijiya)
Hajj - A turance tana nufin hajji.
Misali; Maniyyata aikin hajji na zuwa bita a kowane mako don sanin yanda za su gudanar da aikin.
HAU; Hajji (Tana nufin ɗaya daga cikin shikashikan musulunci)
Hajji - Tana nufin ɗaya daga cikin shikashikan musulunci.
Misali; Maniyyata aikin hajji na zuwa bita a kowane mako don sanin yanda za su gudanar da aikin.
ENG; Hajj (A turance tana nufin hajji)
Haki - Tana nufin yin numfashi sama-sama da sauri.
Misali; Gudun da na yi ya sa ni haki.
ENG; Panting, Gasping (A turance tana nufin haki)
Haki - Tana nufin ciyawa.
Misali; Na samo hakin da zan yi amfani da shi don yin maganin.
ENG; Grass (A turance tana nufin ciyawa)
Hakimi - Tana nufin muƙamin sarauta na shugaban lardi.
Misali; Hakimi aka naɗa shi a shekarar da ta gabata.
ENG; District Head (A turance tana nufin hakimi)
Hakiya - Tana nufin ciwon da ke fitowa a cikin ido.
Misali; Hakiya ce ta fito masa a ido.
ENG; Leucoma (A turance tana nufin hakiya)
Halal - Tana nufin duk abin da addini ya ba da damar a yi.
Misali; Cin naman shanu halal ne a musulunci.
ENG; Any Lawful Act (A turance tana nufin halal)
Kishiyarta; Haram
Halarta - Tana nufin samun damar zuwa gurin da aka gayyaci mutum.
Misali; Taron da aka gabatar a makon da ya gabata, mutane da dama sun halarta.
ENG; Attend (A turance tana nufin halarta)