Terms Dictionary

Famfara - Tana nufin cirewar da haƙoran yara ke yi kafin na girma ya fito. Misali; Muntari yana famfara. ENG; Losing Baby Teeth (A turance tana nufin famfara)
Family - A turance tana nufin iyali. Misali; Yana kula da iyali yanda ya kamata. HAU; Iyali (Tana nufin ahali ko kuma uwa da uba da yaransu)
Famous - A turance tana nufin fitacce. Misali; Alh. Sule fitacce ne a unguwar. HAU; Fitacce (Tana nufin wanda ya shahara)
Fanka - Tana nufin na'urar da ke ba da iska. Misali; An kunna fanka a ɗakin saboda yau ana zafi. ENG: Electric Fan (A turance tana nufin fanka)
Fanke - Tana nufin nau'in abin ci da ake yi da fulawa da sikari da mai da sauransu. Misali; An yi sadakar fanke a gidan mutuwar. ENG; Fried cake made of wheat flour (A turance tana nufin fanke)
Fanko - Tana nufin babu komai. Misali; Gwangwanin fanko ne. ENG; Empty container (A turance tana nufin fanko)
Fansho - Tana nufin kuɗin da ake ba wa mutum bayan ya kammala shekarun aikinsa. Misali; Ma'aikata da dama da fansho suke siyan gida. ENG; Pension (A turance tana nufin fansho)
Faraga - Tana nufin samun dama. Misali; Mun samu faraga mun yi abubuwan alkhairi da yawa. ENG; Opportunity (A turance tana nufin faraga)
Faranta - Tana nufin sanya farin ciki. Misali; Matar ta faranta ran mijinta ta hanyar yi masa girki. ENG; Gladden (A turance tana nufin faranta)
Faranti - Tana nufin mazubin abinci. Misali; Ki zuba abincin a faranti don ya huce da wuri. ENG; Plate (A turance tana nufin faranti)
1 2 3 4 5 17