Fail To Do - A turance tana nufin gaza.
Misali; Sakamakon da ya samu ya gaza kai wa yanda za a ɗuake shi a jami'a.
HAU; Gaza (Tana nufin kasawa)
Faith - A turance tana nufin imani.
Misali; Yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin rukunan imani.
HAU; Imani (Tana nufin yarda, amincewa ko ba da amanna ɗari bisa ɗari)
Fake - Tana nufin samun mafaka.
Misali; Lokacin da ruwan ya sakko a shagon na fake.
ENG; Take shelter or refuge (A turance tana nufin fake)
Fake - A turance tana nufin jabu.
Misali; Madarar jabu ce, idan aka sha tana sa ciwon ciki.
HAU; Jabu (Tana nufin abin da ba shi da inganci)
Fako - Tana nufin ɓuya don kai harin ba-zata.
Misali; Shi suke fako, yana zuwa suka cafke shi.
ENG: Ambush (A turance tana nufin fako)
Faku - Tana nufin mutuwar annabawa ko bayin Allah salihai.
Misali; Ba su san annabi ya faku ba.
ENG; Death (of prophets or saints) (A turance tana nufin faku)
Falala - Tana nufin alkhairai da dama.
Misali; Akwai ɗimbin falala a cikin ambaton Allah.
ENG; Abundance, Fortune (A turance tana nufin falala)
Fale-Fale - Tana nufin abu mara nauyi ko kauri.
Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri.
ENG; Thin and Flimsy (A turance tana nufin fale-fale)
Fallasa - Tana nufin tona asiri.
Misali; An fallasa abin da suka daɗe suna ƙullawa yau.
ENG;Disclose Secret (A turance tana nufin fallasa)
Falmaran - Tana nufin riga mara hannu da ake ɗorawa a kan mai dogon hannu.
Misali; Falmaran ɗin da yarima ya sa ta yi kyau ƙwarai da gaske.
ENG;Waistcoat (A turance tana nufin falmaran)