Tag: yadda ake

  • Asalin Hausawa

    Asalin Hausawa

    Har yanzu ba a tabbatar da asalin Hausawa ko harshensu ba, amma akwai hasashe da dama da ake yi game da asalin Hausawa ko harshen Hausa. Mafi yawan manazarta suna ganin harshen Hausa ya malalo ne daga Arewa maso gabas daga gurbin da yake a yanzu, wato ƙasar Hausa.

    MA’ANAR KALMAR HAUSA

    Ma’anar kalmar Hausa ba ta tsaya ga sunan harshe kaɗai ba, akwai wasu ma’anoni da Hausawa suke danganta kalmar da su. A ƙamusoshi kamar: Bargery (1933) da Abraham (1962) da Garba (1999) da kuma Ƙamusun Hausa (2006), kalmar tana da ma’anoni da aka rege kamar haka:

    1. Kalmar tana nufin harshe ko yare kowane iri. Misali, Ba na jin Hausa tasa. Wato ba na jin harshensa ko yarensa.

    2. Kalmar tana nufin harshen da Hausawa suke magana da shi.

    3. Kalmar tana nufin ƙasar Sakkwato, wadda yanzu ta haɗa da jihohin Zamfara da Kebbi.

    4. Hausa na nufin azancin magana.

    5. Ana amfani da kalmar a ma’anar hikima ko kan gado.

    6. Haka kuma yankin da Hausawa suke zaune ana kiransa da Hausa ko ƙasar Hausa.

    7. Kalmar Hausa tana nufin abin da mutum yake nufi.

    ASALINTA

    Dangane da asali kuwa, har yanzu ba a tabbatar da asalin kalmar Hausa ba saboda saɓanin ra’ayoyi da ake samu dangane da asalin kalmar, kuma ga alama kalmar ba ta daɗe samuwa ba saboda rashin samunta a wasu daɗaɗɗun rubuce-rubuce da aka samu game da Hausawa, da wasu larabawa suka yi, irin su Ibni Sa’id da Ibni Batuta da Almaƙrizi da kuma Leo Afircanus.

    Amma wasu masana sun yi ƙoƙarin bayyana ra’ayinsu game da asalin kalmar kamar haka:

    1. Ra’ayin Skinner (1968) wanda ya ce an samo kalmar HAUSA ne daga Songhai, wai su ne suke kiran mutanen da suke zaune a gabas da ƙasar Songhai da suna ‘AUSSA’ daga nan kalmar ta zama ‘HAUSA’ saboda Hausawa ne suke zaune a gabas da ƙasar Songhai. Haka kuma mutanen gabashin tafkin cadi suke kira mazauna yammacin Tafkin Cadi, ba mamaki kasancewar harshen ya malalo daga wannan waje.

    2. Ra’ayin C. R. Niven (1971) wanda ya ce an samo kalmar ne daga Buzaye, domin suna kira mutane da suke zaune a arewacin kogin Kwara da suna Hausa.

    3. Muhammad U. Adamu (2011) ya ce an samo kalmar ne daga sunan Fir’auna Hausal, wanda yake ganin daga zuriyarsa ne aka sami Hausawa.

    4. Ra’ayin Malam Aminu Kano da Yusif Maitama Sule Ɗanmasanin Kano, waɗanda suka ce an samo kalmar ne daga HABASHA, domin Hausawa daga Habasha suke, kuma kalmar ta sauya daga HABASHA ta koma HABSA sannan ta zama HAUSA.

    5. Ra’ayin sarkin Ningi Haruna, wanda yace an samo kalmar ne sakamakon zuwan Bayajidda Daura, domin ya je ne a kan doki, ita kuma tsohuwar da ya sauka a gidanta ba ta san doki ba, sai ta bayyana shi da wanda ya hau sa, wai daga kalmar ‘HAU SA’ (hawa sa) aka sami ‘HAUSA’.

    Domin karanta Aure A Ƙasar Hausa danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Nasiha A Kan Maganganun Mutane

    Nasiha A Kan Maganganun Mutane

    An tambayi Imam Hasanul Basari?
    Me ya sa ba ka damuwa da maganganun mutane? Sai yace,

    “Lokacin da aka haife ni, ni kaɗai aka haifa,
    Kuma lokacin da zan mutu, ni kaɗai zan mutu
    Kuma ni kaɗai zan kwanta a kabarina,
    Kuma ni kaɗai za a tashe ni a yi min hisabi.
    Kuma ni kaɗai za a ba sakamakona,
    Don haka ina ruwana da maganganun mutane?

    Domin in dai maganganun mutane shi ne damuwarka, sai dai idan ba ka shirya zaman duniyar ba.” Allah ya datar da mu.

    Danna nan don karanta Nasiha mai tsoratarwa

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Awon Juna Biyu

    Awon Juna Biyu

    Awon ciki shi ne gwaji wanda ake yi a lokacin da mace take jin alamu a jikinta kamar ta sami juna biyu. Sakamakon awon shi ne yake tabbatar da gaskiya ko akasin abinda take hasashe. Idan sakamakon ya nuna tabbaci (positive), to, shikenan juna biyu ya tabbata. Idan kuma ya nuna rashin tabbaci (negative), to, juna biyu bai tabbata ba.

    RABE-RABEN AWON JUNA BIYU 

    Awon juna biyu ya rabu zuwa manyan gidaje guda biyu:

    1. Na fitsari (urine test)
    1. Na jini (blood test)

    Amma bayan waɗannan gwaje-gwajen, ana yin wasu, sai dai su ba na tattabatar da shigar juna biyu ba ne, a a na bibiyar halin da juna biyun yake ciki ne bayan an tabbatar da shi. Waɗannan sun haɗa da gwajin hoto na ciki (ultrasound scan) da kuma na jini kamar rhesus factor domin gane ko akwai protein a ƙwayoyin jinin mace, chorionic villus sampling (CVS) da amniocentesis domin gane ko jariri yana da nakasa, glucose test domin gane yiwuwar ciwon sugar, group B streptococcus test domin gane ko uwa tana ɗauke da ƙwayoyin cutar da zata iya sanya ma jaririnta a lokacin haihuwa, da sauransu.

    AWON JUNA BIYU NA FITSARI

    Ana amfani ne da wani tsinke wanda ake kira “strip”, kuma akwai shi na kamfanoni da yawa kamar First Response Early Result, Clinical Guard GCH Pregnancy Test Strip, Clear Blue Rapid Detection, Early@Home Pregnancy Test Strip, Wondfo Pregnancy Test Strip, da sauransu.

    A jikin tsinken akwai sinadarai da ake kira “immunochemical reagents” masu tantance ko akwai sinadaran human chorionic gonadotropin (hCG) a cikin fitsarin. Jikin mace zai fara samar da sinadarin hCG a cikin jininta da zarar ’ya’yan maniyyin namiji (sperm cells) sun ƙyanƙyashe ƙwan haihuwarta (ovum) kuma ƙwanƙyasasshen ƙwan ya maƙale a cikin mahaifa. Don haka idan aka tsoma tsinken strip a fitsarinta zai canza launi, ko ya nuna layi biyu, ko ya nuna alamar tarawa (+).

    Domin samun kyakkyawan sakamako, ana buƙatar a yi amfani da fitsarin farko na safe. Sa’annan kada a sha ruwa da yawa domin fitsarin ya yi kauri (concentrated). Idan akwai hCG a fitsarin, to, zai nuna sakamako cikin minti 5 zuwa 10, ya danganta da kamfanin da ya yi tsinken. Kuma an fi buƙatar yin test ɗin kwana 7 zuwa 14 da gama al’ada. Idan kuma tsinken bai canza ba, to, babu juna biyu kenan.

    Abubuwan da suke sanya a yi awon fitsari kuma a rasa ganin sakamako mai kyau duk da mace tana jin alamun ciki sun haɗa da lalacewar tsinken strip ɗin (expired strip), rashin isasshen fitsari a lokacin da aka yi test ɗin, ko fitsarin da ya haɗu da ruwa (diluted urine). Yawancin mata sun fi son awon juna biyu na fitsari saboda sauƙin kuɗinsa da kuma rashin ɗaukar lokaci kafin a ga sakamako.

    AWON JUNA BIYU NA JINI

    Ana yin sa ne a ɗakin bincike na kimiyya (laboratory). Shi ma abinda ake dubawa a cikin jinin shi ne sinadarin hCG. Wannan awon ya fi tabbas saboda komi ƙanƙantar sinadarin ana iya ganinsa.

    SHIN SAKAMAKON AWON FITSARI DA NA JINI ZA SU IYA NUNA ƘARYA?

    Allah (SwT) da Manzonsa (SAW) su kaɗai ne ba su kuskure. Don haka mai yiwuwa ne shi ma sakamakon awon juna biyu ya nuna kuskure. Amma kashi 99 bisa ɗari (99%) na awon juna biyu, fitsari ko jini, suna ba da sakamako daidai. Sai dai idan an yi kuskure wajen yinsu, ko kuma wanda ya yi bai fahimci yadda ake yi ba. 

    SHAWARA

    Idan kina shakkun  sakamakon awon fitsari, to, a sake yi bayan wani lokaci, haka kuma idan na jini ne, ko kuma a canza wurin awon. Allah yasa mu gama haife-haife lafiya, Allah ya ba mu zuriyya ɗayyiba, amin. 

    Danna nan don karanta yanda ake amfani da na’urar gwajin ciki (juna biyu)

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Kafar Sadarwar Zamani, Amfani Da Ƙalubalenta

    Kafar Sadarwar Zamani, Amfani Da Ƙalubalenta

    Amfani da kafar yanar gizo da kuma kafar sadarwar zamani (Social Media) hade da  ƙalubalen su (Kashi na ɗaya) Daga Abubakar Ibrahim Panshekara

    Samuwar yanar gizo da shahararta a cikin shekarun Alif da ɗari tara da casa’in da tara (1990), ya yi tasiri ga mutane daban-daban musamman matasa, waɗanda ke amfani da sabuwar fasahar a matsayin wata kafa don gani da tunanin duniyar zahiri ko ta yanar gizo. Ta hanyar shiga daga wani hoto ko bidiyo ko jawabin ciki zuwa wani da dai sauran su.

    A matsayin wani ɓangare na haɓakar yanar gizo, wanda aka fi sani a farkon shekarun Dubu Biyu (2000s).  Sabbin hanyoyin kafofin watsa labarai, kamar Friendster, Myspace da Facebook, Youtube da Twitter suka biyo baya.

    Waɗannan dandali sun ɓullo da wani sabon salo na sadarwa, wato (multimedia), da zamantakewar al’uma wanda ke faɗaɗa hankali da tunanin mutane da yawa (musamman matasa) don ganin al’amura masu sun cigaba dai dai da zamani da irin sabuwar duniyar da ƙirƙira da fasaha ta kawo wa mutanen ƙarni na ashirin da ɗaya .

    Wasu daga cikin waɗannan mutane, suna amfani da kafar intanet da sabbin kafofin watsa labarai a matsayin yunƙurin kawo sauyi a cikin neman bayanai, bincike da halaye da ɗabi’un jama’a.

    Duk da yake wannan ba zai zama cikas ba a cikin tunanin mutane masu amfani musamman idan aka yi amfani da su ta hanyar da ta dace, a ta wata fuskar kuma ana iya la’akari da zuwan fasahar zamani a matsayin koma baya ga ƙarfin matasa da ɗalibai yadda ta sanya musu kasala a  harkar ilimi.

    Amma kuma tana iya gyarawa mutane zamantakewa da tattalin arziki idan aka yi amfani da ita ta hanya mai kyau. Idan aka yi la’akari da yanayin karɓuwar da aka yi wa yanar gizo tun da farko, da yawa suna amfani da intanet, kafofin watsa labarun ko fasaha don sana’o’i masu ma’ana kamar su a makarantu, ofisoshi, wuraren kasuwa, zamantakewa da gudanar da mulki.

    A cewar ƙamus na Encyclopedia wato Britannica online, “Internet, wani tsari ne wanda ya kawo sauyi ga tsarin sadarwa na jama’a, kafofin watsa labaru, da kasuwanci ta hanyar ba da damar cibiyoyin sadarwa na kwamfuta daban-daban a duniya su haɗu don ba ta wata mafita ta ilimi da bincike. Wani lokaci ana kiransa “cibiyar sadarwa ta zamani. “Intanet ya ɓullo a Amurka a shekarun 1970 amma bai zama gama gari ba sai farkon shekarun Alif da Ɗari Tara da Casa’in (1990)”.

    A shekarar Dubu Biyu da Ashirin (2020,) kusan mutane biliyan  huɗu da rabi (4.5), ko kuma a taƙaice, fiye da rabin al’ummar duniya, an ƙiyasta  suna iya shiga Intanet. Kuma wannan adadin yana ƙaruwa, musamman saboda yaɗuwar fasahar “smart” da “Internet of Things,” inda na’urori masu kama da kwamfuta ke haɗuwa da Intanet ko mu’amala ta hanyar sadarwa mara waya. Waɗannan “abubuwa” sun haɗa da wayoyin hannu, na’urori, da tsarin hasken wuta.

    Don Karanta Mecece Kwamfuta danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Me Ke Kawo Warin Jiki?

    Me Ke Kawo Warin Jiki?

    Shin za ka iya gane shekarun mutum a yayin da yake zaune a gefenka ta hanyar warin jikinsa? Zai iya yiwuwa mutum yana sanye da turare, amma duk da haka za ka iya gano shekarunsa ta hanyar warin jiki. Ta hanyar bincike, an gano yadda ake gano hakan.

    Shi dai warin jiki ya bambanta tsakanin kowane mutum. Amma kuma yana sauyawa yayin da mutum ke girma. Wannan na faruwa ne ba kawai saboda muhallin da mutum ke zama ba, har ma da yadda yake cuɗanya da al’umma.

    Lokacin da mutum ke ƙarami, warin jikinsa ba ya fitowa sosai saboda rashin aikin gaɓoɓin da ke fitar da zufa yadda ya kamata da kuma ƙarancin ƙananan halittu da ke rayuwa a fatar mutum.

    Amma duk da haka, iyaye na iya tantance warin jikin ‘ƴa’ƴansu ƙanana. Wannan warin jiki na ƙara danƙon soyayya da ƙauna tsakanin iyaye da ƴaƴansu. Kuma hakan na rage damuwa ga iyaye, yayin da suke ƙoƙarin sanya yaran nasu farin ciki, domin warin jikin ƙananan yara na da jan hankali sosai.

    Sai dai kuma masu jegon da kan yi fama da damuwa sanadiyyar haihuwa, ba su iya tantance warin jikin jariransu. A lokacin balaga, warin jikin mutum kan sauya lokaci zuwa lokaci.

    Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da jiki ke fitarwa waɗanda ke haɓɓaka gaɓoɓin saduwa, waɗanda su kuma ke haɓɓaka aikin ɓangaren fatar jiki da ke samar da zufa da kuma maiƙo. Yawancin waɗannan gaɓoɓi na samar da ruwa da kuma gishiri.

    Sinadaran Apocrine, masu samar da maiƙo da zufa na fitar da wani wari, wanda ya sha bamban ga kowane mutum. Sinadaran su ne ke samar da maiƙon da ke sanya fatar kai da ta jiki laushi. Sai dai a lokacin da suka cakuɗa da ƙananan ƙwayoyin halittu, sai su riƙa fitar da warin jiki da zai iya damun mu.

    Yayin da yaran da ke tasowa ke fitar da wani wari, warin kan canza a lokacin da suka balaga, kuma warinsu na asali kan ɓace, wanda hakan ke sanyawa warin ya sha bamban da wanda iyayensu suka sani tun asali.

    Danna nan don karanta gwargwadon shayarwarki gwargwadon kariyarki

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Hani Akan Yin Duba 2

    Hani Akan Yin Duba 2

    Ilimin “Geomancy” shi ake kira da “ramli” ko kuma duba akan yashi (har da biro da takarda duk ana yi). Ilimi ne da ya fita daga rubutaccen ilimin taurari (Astrology), don haka yake da sunaye da kuma salon bincike kusan iri ɗaya da na ilimin taurarin kuma an fi kyautata zaton larabawa su ne suka fara yin sa har ya watsu zuwa ƙasashen Africa da Europe.

    Shi ilimin ramli ɗigo-ɗigo a ke yi kusan kala 14 don a fitar da waɗansu abubuwa daga jikin ɗigon. Wanda na koya ina shekara 13 yana aiki ne da zanen da ya fito bayan ka gama zanen da ba ka ƙirga ba kuma ka soke biyu-biyu daga cikinsa. Idan 1 ta fito to za a auna ta da dai-dai buƙatarka, haka ma idan biyu ta fito. Akwai ababan mamaki a cikin ilimin da suke faruwa amma dai shi ma ana ɗora su ne kamar yadda ake ɗora sauran iliman Astrology.

    Akwai ababan mamaki da suke faruwa a cikin irin waɗannan iliman waɗanda har yanzu kimiyya ta kasa gano ya haƙiƙarsa take. Waɗansu abubuwan kamar “Telepathy”, “Entanglement”, “PSI” da sauransu har yanzu suna ba wa masu kimiyya mamaki duk da suna ɗora su a babin “Pseudosciences”.

    Yadda aka iya gano “Kuantum entanglement” to ana zaton za a iya fahimtar waɗansu abubuwan irin waɗannan da tafiyar lokaci. Zamanin amfani da “Classical Physics” na Newton da ya ɗoru akan lissafin Euclid ya wuce. Yanzu muna kan “Kuantum Mechanics” wanda ƙaryata abu ta farar ɗaya, don dogaro da kimiyya (classical physics) na nuna raunin mutum a sanin kimiyyar.

    Ana buƙatar bincike na sosai akan abu kafin a ƙaryata shi. Yanzu muna kan “super string theory” wanda ya ce duniya tana da “10-dimensions” maimakon 3-dimensions ko 4-dimensions da Einstein ya kawo! Hankali zai ruɗe bai gano haƙiƙar abubuwa masu “10-dimensions” ba amma hakan baya nufin cewa “super string” ƙarya ne don kawai ba ka fahimci yadda yake ba.

    Abu Hamidil Gazhali, a cikin “Almunkidh” yana magana akan “secrets of numbers”, yana faɗin cewa akwai abubuwan mamaki a cikin waɗansu lambobin. Ya ba da hoton waɗansu lambobi da ya ce an kasa gane sirrinsu. Lambobi ne kawai a jere amma idan aka haskawa mai ciki a lokacin da take naƙuda sai a ga ba ta shan wahala sosai!

    Ibn Khaldun ya faɗi waɗansu lafuza da yaren “Armenians” inda ya ce in dai ya karanta su to sai ya yi mafarkin abin da yake so! Abubuwan da ban mamaki ta yadda ake buƙatar a yi zurfaffen bincike a kai. Irin wannan to da su aka ɗora iliman “Numerology” da karanta zanen hannun mutum ko ƙirgen da a ke yi da carbi.

    Danna nan don karanta Hani Akan Yin Duba 1

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Hani A Kan Yin Duba 1

    Hani A Kan Yin Duba 1

    Duba: Shi ne bincikar abin da zai iya faruwa da wani abu nan gaba. Duba ta hanyar taurari shi ake kira da “Astrology” (yana da bambanci da “Astronomy” da take nufin kimiyyar taurari), shi kuma duba ta hanyar zanen ƙasa (ramli) shi ake kira da “Geomancy”.

    Waɗannan ilimai, kamar na bayansu, su ma suna da asali daga mutanen Hindu. Saboda asalin ilimin za a same shi a cikin manyan litittafinsu kamar Beda, inda aka samo “Bedic astrology”, da kuma abubuwan da aka ruwaito a litittafansu a yaren Sanskirt. Tun a zamanin Greek ana haɗe ilimin “Astronomy” da “Astrology” guri guda.

    Ptolemy a cikin littafinsa da ya yi bayani akan  ilimin falaki (Astronomy), a inda ya haɗa da bayanin “Astrology” da kuma yadda yake tafiya a fahimtarsa. Yana faɗar cewa, waɗansu abubuwan suna faruwa ne dai-dai da yanayin tafiyar taurari da kuma tafiyar rana da watanni. Don haka idan aka san yadda taurari suke, to za a iya gano yadda gaba za ta kasance. Ta haka zamu gane cewa ilimin taurari ya gangaro musulunci daga iliman Greeks ne.

    Ibn Khaldun a cikin Muƙaddima, yana cewa akwai buƙatar a san cewa babu wani bincike na haƙiƙa da yake tabbatar da tafiyar taurari da kuma faruwar waɗansu lamura.Wato dai tafiyar falaki ba ta nuna wani abu “supernatural” kamar na tsafi ko bokanci ko kuma faruwar wani abu a nan gaba.

    Sir Isaac Newton, kamar yadda aka ruwaito a cikin littafin “Cambridge Companion to Newton”, ya ba da labarin cewa ya tattauna da wani masanin ilimin taurari (Astrology) sai yake gaya masa haƙiƙar ilimin ba gaskiya ba ne amma hanyar cin abincinsu ce!

    Masana halayyar ɗan Adam (psychologists) sun tabbatar da cewa abin da yasa mutane suke aminta da gaskiyar ilimin taurari shi ne yadda suke ganin abu yana faruwa, bayan an faɗa musu zai faru. A haƙiƙar lamari ba faruwa yake dai-dai da yadda aka gaya musu ba.

    Ɗan Adam yana da saurin manta abubuwa ne, don haka idan mai ilimin taurari ya ce abu zai faru to mutum mantawa yake har sai wani lokaci can idan abu makamancin hakan ya faru, to sai ya yi zaton wanda aka taɓa gaya masa zai faru, shi ne ya faru ɗin.

    Misali, idan nace mahaifinka zai mutu bayan na yi duba, to mantawa za kai da na taɓa gaya maka har sai bayan ya mutu ɗin, wataƙila da ƙarin shekaru masu yawa, kawai sai ka tuna maganar sai ka ce ai dama na taɓa duba maka hakan zai faru! Wannan shi ne abin da suka ce game da yadda abubuwa suke faruwa a ilimin “Astrology”.

    Don Karanta Physiology da Hausa danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tsarin Tazarar Haihuwa Mara Amfani Da Magani

    Tsarin Tazarar Haihuwa Mara Amfani Da Magani

    Wannan tsari shi bature ya kira da calendar method ko calendar period wanda akan ƙauracewa saduwa a wasu keɓantattun kwanaki a yayin da ake neman kaucewa shigar juna biyu saboda wasu dalilai.

    Wannan hanya ta ‘family planning abin da bincike ya tabbatar shi ne tana da sahihanci na kaso 88-95% cikin ɗari na hana shigar ciki. To sai dai duk da haka Allah yakan iya canja ikonsa koda an yi hakan kuma a samu haihuwa, Amma Insha Allah ba a cika samun ciki ya shiga ba idan aka kiyaye hakan. 

    A jikin mahaifar mace, (Uterus) akwai wasu abubuwa kamar hannu guda biyu, ɗaya gefen dama dayan kuma gefen hagun wato bututun da ake cewa (FOLLOPIAN TUBE) a turance wanda ta ciki a rarake yake kamar pipe ɗin ruwa… to a can ƙarshe a bakin kowanne follopian akwai wani kwanson abu ƙullutu (Ovary) wanda a cikinsa ne akwai wasu ƙwayaye.

    Duk sanda Mace ta yi haila bayan Jinin ya ɗauke da kwanaki 14, wancan abu da muka ambata da ƙullutu yana sakin waɗancan ƙwayayen, waɗanda su ne sinadarin da ake haɗawa a samu ɗa wato juna biyu.

    Waɗannan ƙwayaye idan aka sake su sukan biyo bututun su shigo cikin mahaifar mace su yi kwanaki 2 wato awanni 48′ daga nan idan babu abinda ya zo ya taɓa su wato na daga maniyin namiji (sperm) to za su mutu. 

    Toh sai dai kafin a saki waɗannan ƙwayayen su tafi mahaifa jiran maniyyin domin samar da ciki, akwai abinda Allah ya halitta a cikin mahaifar mace wanda kan zo ya share mahaifarta sosai (estrogen), domin mahaifar za ta yi baƙo, wanda baƙon kuwa shi ne wannan ƙwan.

    Akwai wasu jijiyoyi guda biyu na jini, a gefen dama da hagu na mahaifar mace, idan aka zo aka share mahaifar to waɗannan jijiyoyin za su cika da jini sosai, sai su koma ja-ja-wur, suna jiran wannan baƙon da zai shigo mahaifa saboda su yi amfani da wannan jinin da suka cika kansu da shi su ba wa baƙon a matsayin abinci na tsawon awanni 48 da ƙwan kan iya rayuwa. 

    Wanda in ƙwan ya zarce haka ba tare da maniyyi ya zo ya same shi ba, to lalacewa za yi ya mutu. Shi kuwa maniyyin namiji yana yin kwanaki 3 wato awanni 72 a cikin mahaifar mace kafin ya mutu, saɓanin na mace da ke kwana 2 (48hrs). Idan mun fahimci waɗancan bayanan da suka gabata, to yanzu sai mu haɗa su waje ɗaya mu ga yadda abin yake. 

    Idan mace ta gama haila da kwanaki 14 to wancan abun mai kamar tiyo wato bututun (follopian tube) da ya haɗe kwanson OVARY zuwa cikin mahaifa (UTERUS) waɗannan ƙwayayen da ke cikin OVARY ta cikinsa suke shigowa cikin mahaifarta su jira maniyyin namiji ya zo ya same su wanda ake kira (OVULATION).

    Idan sanda suka shigo mahaifa akai dace namiji ya sadu da mace dama ya zuba mata maniyyi ko da kuwa kwanaki 2 da suka wuce ne aka yi saduwar to komi ƙanƙantar maniyyin nan ya wadatar da su. maniyyin zai zamo musu kamar taki don haka za su baibaye shi su haɗu su yi ta girma babu zancen mutuwa kuma wanda da haka ne kuma Allah zai ta sarrafa shi har ya mai da shi jariri ya zamo mutum.

    To idan kuwa sanda ƙwan ya shigo cikin mahaifa babu wani maniyyi da ya shigo gurin a dalilin rashin saduwa da macen da ba ai ba to waɗannan ƙwayayen za su mutu bayan sun yi awa 48 (kwanaki 2) kamar yadda na faɗa a baya cewa ƙwan mace bai wuce kwana 2 zai mutu in bai haɗu da maniyyi ba. 

    Toh idan kuma suka mutu to za su biyo cikin al’aurar mace sai su fito, shi ne sai ka ji mata na tambayar sukan ga wani abu mai kamar majina-majina yana fito musu a al’aura ta wani lokaci, wanda wannan shi ne abinda ke fitowar ba wai infection ba ne. Kuma in ‘yan mata ne da za ku lissafa za ku ga sanda yake fitowar a ƙalla lokacin kun yi ko kun kusa sati 2 da gama haila.

    Wannan yasa malaman mu a misulunci ke cewa babu komai akan wannan abun in mace ta  gani kawai ta wanke shi ba shida wani hukunci, ba wanka ake ba. Amma indai ba sau 1 a wata take ganin wannan ba kuma ya zamto ba irin wajen sati 2 ne da gama haila ba to ƙila abinda kike fitarwa wannan yana da alaƙa da INFECTION musamman idan dususu yake ko kuma kika ji ma yana ƙarni. 

    Duk hakan ya faru ne a dalilin rashin shigar maniyyi da zai girmar da wancan ƙwan, tunda kun ga budurwa dama ba aure gare ta ba. 

    Dalilin rashin maniyyin bayan ƙwan ya lalace ya fita su kuma waɗancan jijiyoyi da suka tara jini a cikinsu, sai su yi wani abu da ake kira fushi, ba su ji daɗi ba, a dalilin haka sai suke kartar jikin mahaifar mace, sai ka ji mace tace maka tana yawan fama da ciwon mara (lower abdominal pain) musamman idan ta gama Haila. A nan za mu fahimci rashin aure na daga abunda ke jawo wannan, kuma maganin haka shi ne aure duk da akan samu masu auren na fuskantar hakan.

    Don karanta lokacin da ya dace mace ta yi amfani da tazarar haihuwa danna nan

    Idan karce jijiyoyin nan ya yi yawa kuma aka yi rashin sa’a sai su fashe, idan kuma suka fashe sai jini ya yi ta fita ba tsayawa a wasu, wannan shi ne ake kira da jinin Istihada, daman Manzon Allah (SAW) ya taɓa gayawa wata mata cewar ai wannan jinin na jijiya ne. 

    Dan haka idan mace me aure ce kuma tana son yin ‘family planning da mijinta, to hanya mafi sauƙi ita ce; kamar yadda muka ji bayan gama hailar ta da kwanaki 14 ake sakin waɗancan ƙwayaye zuwa mahaifa, kuma sukan yi kwanaki 2 kafin su mutu, shi kuma maniyyin namijin yakan yi kwanaki 3 kafin ya mutu. To su ma’auratan kada su yi jima’i tun ranar 11 da gama hailar ta, har sai bayan ranar 17 da gama hailar ta. 

    Ku ɗan tsaya kaɗan a nan kafin ku cigaba ku yi tunanin me yasa nace haka??

    Dalilin hakan kuwa shi ne; ranar 14 ƙwai ke zuwa, to idan suka sadu ranar 12, kada mu manta maniyyi sai ya yi kwanaki 3 kafin ya mutu, to kun ga idan suka sadu ranar 12, maniyyin namijin na nan a mahaifar a raye har ranar 14 da za a sakin ƙwan, zai zauna na tsawon kwanakin 12,13,14 kafin ya mutu, to kun ga za su ci karo ranar 14, kuma babu abinda zai hana shi sarrafa ƙwan nan. 

    An ce kar ku sadu har sai bayan ranar 17 ne saboda shi kuma ƙwan yakan yi kwanaki 2 kafin ya mutu. To waɗannan kwanaki 5 ɗin-12,13,14,15,16 da gama Hailar mace, su ake kira da ‘DANGER PERIODS’ Ma’ana kwanaki masu hatsari, an kira su da haka ne saboda idan dai aka sadu da mace a waɗannan kwanakin to kuwa tabbas za ta samu ciki, sai dai idan mulkin Ubangiji ya shigo ciki ko kuma in dama cikin ma’auratan akwai larurar da ke hana ɗaukar ciki. 

    Amma idan har ma’aurata na son yin ‘family planning’ ba tare da sa ko shan komi ba waɗannan kwanakin za su kaucewa saduwa a ciki wato tun daga ranar 11 da gama haila har sai ranar 17 da gama haila, sati 1 kenan.

    Sannan kuskuren dakan faru wasu na zuwa da sunan a sadun amma in ya ji zai kawo sai ya zare. Ina mai tabbatar ma wannan ruwan me santsi na maniyyi da kan fara fitowa ka zaci maziyyi ne shi kansa ya wadatar yasa ciki ya shiga domin akwai maniyyi daga ƙarshensa. Wannan tasa ‘yan matan da kan auka tarkon samari ke ƙarewa da ciki a zaton ba ai release jikinsu ba, don haka in dai za a yi to a kiyayi kusanta kurum.

    Kuma irin hakan yasa ba a ba hanyar inganci 100% ba domin ko yaya maniyyi yake ya wadatar. Haka kuma wasu matan duk sati 3 suke haila don haka kwanakin fara ovulation ɗinsu ba zai kai har 14 ba, galibi bayan kwana 10 ovulation na iya faruwa, kun ga ita sai dai a ƙaurace mata kwanaki 8 zuwa 13.

    Sannan wani abu; a yayin da ƙwan can ke tafiya a cikin FOLLOPIAN TUBE daga ovary zuwa cikin mahaifa idan ya maƙale a hanya kuma aka zo aka sadu da mace toh shi ne maimakon ciki ya kasance a cikin mahaifa sai ya kasance a wajen mahaifa wanda shi muke kira ECTOPIC PREGNANCY.  Wanda dole sai dai a yi aiki a cire. Kuma wannan follopian tube ɗin ya samu matsala kenan har abada. Sai dai da yake biyu ne, to ɗaya ya isa ta samu ciki da shi. Wata hikima ta Allah shi yasa ya yi biyun. To inko duk biyun suka ta6u aka kuma samu ectopic to fa shi ne ciki sai dai a yi wa mace dashensa, gaskiya ba za ta iya ɗauka ba. 

    Wanda Pelvic inflammatory disease na daga kan gaba abinda ke jawo tangarɗar Follopian tube ɗin don haka mata ku daina sake da infection, a kuma daina amfani da wani maganin matsi ko tsarki da ruwan sassake-sassake in kun ƙi kuma to jiki magayi. A kuma lura da tsafta.

    Danna nan don karanta yadda za a magance ɓallewar jini bayan haihuwa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

     

  • Auren Sayyadi Abdullahi Da Sayyada Aminatu

    Auren Sayyadi Abdullahi Da Sayyada Aminatu

    Abdullahi ɗan Abdulmunaf shi ne mafi soyuwa a gurin Mahaifinsa, ya auri Aminatu ‘yar Wahabu ‘yar Abdulmanaf ‘yar Zuhra ‘yar Kilabu, lokacin yana ɗan shekara goma Sha-takwas (18) a duniya.

    A lokacin da Abdullahi ya auri Aminatu ita ce mafi fifiko a cikin matan zamanin a cikin ƙabila Ƙuraishawa da dangantaka mai kyau, yayin da Abdullahi ya shige ta, sai Allah (Subhanahu wata’ala) ya ba ta rabo na manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), da wata biyu, sai mahaifinsa bai jima a duniya ba, ya yi wafati aka rufe shi a garin Madinah a gurin ‘yan uwansa Banu-Aɗiyyu bin Najar. A wannan lokacin ya kasance ya tafi kasuwanci zuwa Sham (Siriya), sai Ajalinsa riske shi a garin Madinah a kan hanyarsa ta dawowa gida.

    Yayin da lokacin haihuwar Aminatu ya yi, sai ta haifi annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam), an yi bushara da haihuwar wannan babban abin halitta, wanda ya yi dai-dai da ranar litinin, tara ga watan rabi’ul- auwal (Nurul yaƙin shafi na 8) ko kuma goma sha biyu ga watan rabbiyul-Auwal wanda bai yi dai-dai da ashirin ga watan Afrilu ba, shekara ta ɗari da saba’in da ɗaya (571) miladiyya, wanda ya yi dai-dai da shekarar farko ta giwaye.

    Daga ƙarshe, aka sanya masa suna Muhammad, wanda ya ba Labarawa mamaki sosai, saboda a lokacin babu wani mutum mai irin sunansa a zamanin, Saboda Allah (Subhanahu wata’ala) ya nuna matsayinsa ga halittunsa, da dai sauransu.

    Sannan a lamba ta huɗu (4), Yace; “Ummul-Aimana ta raine shi, to a nan ƙa’ida ta raino ga wacce ta ke so ɗanta ya zamo mai hazaƙa, to dole a kanta ta kiyaye irin abincin da za ta ci sannan ta dinga cin halal, sannan ta dinga kula da ɗanta shigarsa da fitarsa haɗi da mu’amala ta gari, Saboda ɗabi’a tana kwaikwayen ɗabi’a ne.

    Danna nan don karanta  Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Amfanin Aya Wajen Samar Da Lafiya A Jiki

    Amfanin Aya Wajen Samar Da Lafiya A Jiki

    Aya ita ake kira “tigernut” ko “chufa” a turance. Aya tana daga cikin nau’ikan ƙananan mabunkura ƙasa (tubers), ko saiwoyi (roots), ko kayan lambu (vegetables). Shekaru aru-aru mutane suna cin aya saboda amfaninta na samar da abinci a jiki (nutritional value) da kuma samar da lafiya a jiki (medicinal value). 

    Muhimman kayan alatun (ingredients) da suke cikin aya su ne:

    1. Dussa (fibre): aya tana ƙunshe da dussa waçce take matsayin abinci, kuma ita ce wannan tuƙar da take ragewa (resistant starch) bayan an taune ta kuma an haɗiye romonta. Maimakon zubar da dussar, idan mutum ya haɗiye ta tana taimakawa wajen narkewar abinci (digestion), samar da ƙoshi (satiety), da kyautata lafiyar tumbi (healthy gut support).
    1. Hanyar samar da sinadarin baiwa jiki kuzari (source of carbohydrates): Aya tana da sinadarin kuzarin jiki a matsayin abu mai ɗanɗanon zaƙi a cikinta.
    1. Lafiyayyen sinadarin maiƙo (healthy fats): Aya tana ƙunshe da maiƙo ko kitse mai saurin narkewa (monounsaturated fats) da kuma maiƙo mai ɗaukar lokaci kafin ya narke (polyunsaturated fats) kamar “omega 6 fatty acids”. Waɗannan nau’ukan maikon ba su da hatsari ga ayyukan zuciya.
    1. Sinadaren gyaran jiki da kuma lafiyar jiki (vitamins and minerals): Aya hanyar samar da sinadaran gyara da lafiyar jiki ce, kamar vitamin C, vitamin E, potassium, phosphorus, magnesium, da iron.

    Idan kuma ana maganar amfanin aya wajen magance cututtuka ne, to, sun ƙunshi:

    1. Narkewar abinci (digestive health): dussar da take cikinta tana taimakawa wajen narkar da abinci (promoting food digestion), hana kumburin ciki (preventing constipation), da tabbatar da lafiyar tumbi (healthy gut flora maintenance).
    1. Daidaita ƙibar jiki (weight management): haɗakar dussa da maiƙon da suke cikin aya tana taimakawa wajen sanya mutum ya ƙoshi, don haka zai rage yawan cin abinci kuma ya daidaita ƙibar jiki.
    1. Lafiyar zuciya (heart health): maiƙo mai saurin narkewa (monounsaturated fats) wanda yake cikin aya yana taimakawa ayyukan zuciya domin yana hana taruwar kitsen cholesterol mai cutar da zuciya wanda ake kira “low-density lipoprotein – LDL”, sa’annan ya ƙara yawan kitse maras cutar da zuciya wanda ake kira “high-density lipoprotein – HDL”.
    1. Kashe kaifin gubar abinci (antioxidant properties): Aya tana ƙunshe da sinadaren kashe kaifin gubar abinci kamar vitamin E wanda yake magance gajiya (stress) da kuma kumburin gaɓoɓi (inflammation).
    1. Rashin bijire ma jiki (allergen-free): Aya tana ɗauke da sinadarin da babu gluten a cikinsa, babu soy a cikinsa, Kuma babu nut a cikinsa. Su sinadaran gluten, da soy, da nut nau’ikan protein ne waɗanda jikunan wasu mutanen suke bijire ma, su sanya musu allergies.
    1. Ƙarfafa damar samun juna biyu ga ma’aurata (couple fertility enhancement): aya tana taimakawa maza wajen samun sinadaran gonadotropins, testosterone, da ingantattun ‘ya’yan maniyyi. Ga mata kuwa, tana ƙara ƙarfin sha’awar saduwar aure, ni’ima, da kyautata zaman jariri a mahaifa.

    Don haka mu daure mu riƙa sayen aya saboda amfanin kanmu Mazaje ku daure ku rinƙa siyawa iyalanku aya. Sannan yana da kyau ku koyi sarrafa ta wajan yin nau’in abubuwa da yawa kamar su su kunun Aya da sauran su.

    Danna nan don karanta amfanin ruwa da lafiya

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu