Tag: yadda ake

  • Auren Annabi SAW Da Nana Aisha

    Auren Annabi SAW Da Nana Aisha

    Bayan an ɗaura auren Sayyada Saudatu da wata ɗaya sai aka ɗaura auren Nana Aisha ‘yar abokinsa Sayyadina Abubakar As-Sadik a lokacin shekarunta bakwai (7), amma Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) bai taɓa auren mace budurwa ba sai ita, daga Imam Bukhari a cikin Manaƙibul Ansar lamba ta (3,894), musannadi Ahmad (10/25.827), da dai sauransu.

    Falalar ta da darajar ta

    1. Zagin Nana Aisha kafiri ci ne kai tsaye, saboda Allah ya hana zagin ta kamar yadda suratul Nur daga kan aya ta 10-20 suka nuna.

    2. Haka kuma ita kaɗai ce wacce annabi yake wanka tare da ita, sannan kuma idan suna tare da annabi wahayi yana sauka.

    3. Ita ce wacce ta taɓa ganin mala’ika Jibrilu a fili.

    4. Nana Aisha an haife ta tsarkakkiya daga mahaifin ta tsarkakke.

    5. Ita ce wacce aka karɓi ran annabi yana hannu ta.

    6. A ɗakin Nana Aisha aka rufe annabi (sallallahu alaihi wasallam) da sayyadina Umar da sayyadina Abubakar.

    7. Mai gudun duniya ce, saboda akwai wata rana wata mace ta zo gidan ta tana bara sai kawai ta ɗauki gurasar ta ba ta baki ɗaya.

    8. Ta ruwaito hadisai guda dubu biyu da goma (2,010), wanda imamul Bukhari da Muslim sun haɗu akan hadisai guda ɗari da saba`in da huɗu (174), sannan kuma Bukhari ya ruwaito hadisai hamsin da huɗu(54) nata, wanda Muslim bai ruwaito su ba, haka kuma Muslim ya ruwaito hadisai sittin da takwas (68) wanda Bukhari bai ruwaito ba.

    9. Nana Aisha ta san ilimin fiƙihu da ilimin adab (waƙa) da ansabu na larabawa.

    Sannan kuma Nana Aisha ta rasu a shekara ta hamsin da da bakwai ko da takwas ko da tara, amma kuma ta rasu ne a ranar talata da daddare a ranar goma sha bakwai (17) ga watan Ramadan, haka kuma a lokacin da ta rasu tana da shekara hamsin da bakwai (57) a duniya, an binne ta a baƙi`ul garƙadi, sannan kuma sayyadina Abu-hurarira shi ne wanda ya yi ma ta sallah, saboda a lokacin wanda yake kula da garin makka ya yi tafiya shi ne Marwana ɗan Hakim.

    Domin karanta Sunayen Annabi SAW danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Wayewar Kan Ɗan Adam 1

    Wayewar Kan Ɗan Adam 1

    Kafin a fassara Wayewar Kai (Civilization da turanci) sai an fassara wasu kalmomi masu alaƙa da shi kamar yadda masanin tarihi Arnold Toynbee ya yi (Toynbee 1988). Wannan kalmomin su ne Society da kuma Culture saboda idan aka fassara su za a samu kyakkyawar fahimtar Wayewar Kai (Civilization). 

    Society wanda za a iya fassara shi a matsayin al’umma yana nufin duk alaƙa da zamantakewar mutanen da suke cikin wannan al’ummar ba wai tarin mutanen ba kawai. Tarin mutane ana kiransa Crowd wanda za a iya tara su, ko a watsa su ko a kashe su saɓanin zamantakewarsu wanda ba jiki ba ne. 

    Culture ana fassara ta a matsayin al’ada, kuma tana nufin ƙa’idojin mu’amalar mutane da kuma duk abinda suka ɗauke shi mai kima (Toynbee 1988: 43). Wayewar kai (Civilization da turanci), akwai bambancin ra’ayi akan manufar wannan kalmar.

    Dalili shi ne a ɓangaren ilmin zamantakewa (social science) ba a samun ma’anar kalmar karɓaɓɓiya ba. Kowane masani yana tabbatar da fahimtarsa yayin da yake fito da ma’ana, kuma suna canjawa da zamani da kuma marubuci. 

    Kamar yadda Claude Levi-Strauss ya faɗa cewa mutanen suna iya ba wa kalmar ma’anar da ta dace, mutuƙar, za su ba da dalilinsu (Braudel 1987: 3). Amma an yi ittifaƙi cewa Civilization ko wayewar kai ta nuna cigaban al’umma ne daga asali. Misali Ɗan Adam ya sami cigaba daga farauta da tara tsirrai zuwa ga manomi mazauni a wuri ɗaya. 

    Yawancin mutane suna ɗaukar shekara 200 zuwa 400 kafin su cigaba daga matsayin mafarauta da tara tsirrai zuwa manoma. Amma kuma noma yana tafiya tare da farauta zuwa tsahon lokaci (Adler 1996: 7).

    Civilization kalma ce ta turanci wanda ta samu asalinta daga kalmar civis ta harshen Latin wadda ta ke nufin citizen mazaunin city babban gari. Kalmar ‘Civilization’ an fara amfani da ita ƙarshen ƙarni na 18, a Fransa. An samo ta ne daga “Civilized” da kuma “to Civilize” wanda an daɗe ana amfani da su a ƙarni na 16.

    A shekarar 1732 Civilization ana amfani da ita a ilmin Shari’a (Jurisprudence) ne kawai, a wannan lokaci tana nufin hukunci wanda ya mayar da trial daga criminal zuwa civil (Braudel 1987: 3). Amma wanda ya fara amfani da kalmar mutumin Faransa ne masanin tattalin arziƙi mai suna Anne Robert Jacques Turgot a shekarar 1752 (Ferguson 2011: 2).

    Shi wannan marubuci ya yi amfani da kalmar lokacin da yake rubuta tarihinsa na duniya amma kuma bai  buga littafin ba. An fara buga Kalmar a shekarar 1756 a wani littafi mai suna Treatise on Population na Victor Riqueti (Braudel 1987: 3). 

    Daga baya turawan ingilishi suka karɓi kalmar Civilization. Faransanci ya fi ingilishi kusanci da harshen Latin inda aka samu civis. Saboda Civilization (Wayewar Kai) ta samu asali daga civis (city) shi yasa masana suka ce (Civilization) ba zai yiwu ba sai cikin mazauna babban gari (city) inda kalmar ta samu asali. Amma kuma birni ɗaya tak ba zai iya kafa Wayewar Kai (Civilization) birane su haɗu su zama jinsinsa ba. 

    Misali kamar ƙasar Mesopotamia tana da birane da suka kasance tushen wayewar ta. Akwai taƙaddama ko za iya samun wayewar kai ba a cikin birni ba wato a ƙauyuka? An samu garuruwa da suke tafarkin wayewa amma kuma ba za a kwatanta su da manyan birane ba.

    Wannan fassarar wayewar kai mai alaƙa da birnanci da Bagby ya yi ta samu karɓuwa a wurin Toynbee wanda ya ƙara da cewa wayewa ba za ta yiwu ba sai dole an samu wasu mutane a cikin al’umma suna aikin da bai shafi noma ko sarrafa abinci ba wato suna yin ayyuka da suka shafi ƙira, ciniki, da kuma wanda ba sa yin ayyukan tattalin arziki, wato kamar kula da sha’anin addini da kuma gudanar da mulki da sauransu (Toynbee 1988: 44).

    Wayewar Kai (Civilization) shi ne koluwar tsarin na Ɗan Adam ya fi daula (sophistication). Kuma asalinsa ya faru ne saboda Ɗan Adam ya mallaki muhalinsa ya kuma samar da isasshen abinci, da ruwa da matsuguni da kuma tsaron al’umma daga hare-hare.

    Yana ƙunsar al’ada amma ba koyaushe ba, haka kuma da addini shi ma wani lokacin da kuma harsuna. A bisa wannan ra’ayi ne wasu masana suke ganin kafin wannan zamanin Wayewar Kai (Civilization) guda biyar kawai aka yi su ne: West (Yammacin Turai), da India, da China, da Byzantium da Islam, wannan shi ne ra’ayin Adda Bozeman. 

    Shi kuwa Mathew Melko guda goma sha biyu ya lissafa, bakwai sun shuɗe su ne: Mesopotamia da Egyptian da Cretan da Classical da Byzantine da Middle American da Andean. Kuma biyar suna nan su ne: Chinese da Japanese da Indian da Islamic da Western shi kuwa Samuel Eisenstadt ya mai da su shida ya ƙara da Jewish (Ferguson 2011: 3).

    Shi kuwa Toynbee a tasa fahimtar ba su zama ƙasa da ishirin ba, kuma wasu suna rushewa wasu na tashi (Hughes-Warrington 2015: 112). Alaƙa tsakanin wannan jinsinan Wayewar Kai da kuma tsakaninsu da muhallinsu tana kawo juyi a tarihin rayuwar Ɗan Adam.

    Kuma suna daɗewa ba su canja ba saboda haka Wayewar Kai (Civilization) shi ne tarihin da ya fi kowane tsaho kuma yake wanzuwa a cikin al’umma da kuma tattalin arziki kamar yadda masanin tarihi Ferdinand Braudel ya bayyana (Ferguson 2011: 3). 

    Danna nan don karanta Cinikin Bayi a Tarihin Afrika

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Birkicewar Tsarin Jijiyoyin Jiki

    Birkicewar Tsarin Jijiyoyin Jiki

    A yanayin mutum zai riƙa fuskantar fargaba, tsoro, faɗuwar gaba, sarƙewar numfashi, rashin bacci, bugawar zuciya far-far-far haka kurum, gami da kasa sukuni, kasa nutsuwa ya zauna guri guda, ruɗewar ciki, har jininsa ya ɗan hau, ga ciwon kai, tare da riƙa jin kamar abu ya tsaya masa a maƙoshi, riƙa jin kamar mutum shi fa lallai wani abu ba lafiya tattare da shi, da ɗai sauransu.

    Amma kuma dalilin wannan yanayin ƙila ya je har asibiti an duba shi, har an yi gwaje-gwaje amma likita yace bai ga matsalar komai ba, ba abinda yake damunsa.

    Wannan shi ake kira ‘Hyperstimulated Nervous System’, wato yanayi ne da sashin da ke sarrafa ƙwaƙwalwa da lakar gadon baya a karan kansa ba tare da buƙatar umarni ba wato autonomic function ke birkicewa ya yi ta rubunbunto ayyukansa ba tare da tsari ba.

    Galibi mutum ba ya buƙatar maganin komai, kurum maganganun kwantar da hankali da koya masa kau da kai daga damuwa da irin wannan yanayin da yake samun kansa kurum za ai, a hankali abin zai bar shi komai jimawa, amma in abin ya cigaba toh sai an ɗora mutum bisa magungunan magance fargaba ko damuwa.

    Danna nan don karanta Ciwon Zuciya
    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Fassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 17 Rajab 1446 AH 17 January 2025

    Fassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 17 Rajab 1446 AH 17 January 2025

    Mai Huɗuba:
    Sheikh Dr Abdurrahman Al Sudais

    Mai Fassara:
    Dr Usman Azzuhri

    Shugaban Shashi
    Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    TAKEN HUƊUBA: GWALA-GWALEN KALMOMI GAME DA KARIYA DA GARKUWA
    17 RAJAB, 1446H

    Huɗuba Ta farko:
    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Masa, muna neman taimakonSa da gafararSa, muna tsarkake Shi tare da gode Masa; Ya ƙaddara al’amura kuma Ya zartar da su, kuma Ya haramta ɓarna da abin da ya yi kama da ita.

    Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Ma’abocin girma, kuma duk wanda ya zama ma’abocin godiya da gode Maka, to, haƙiƙa ya haɗa ababen yabawa. Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, irin yabo da ba ya ƙididdiguwa ga maƙididdigi, shin akwai mai iya ƙididdige tsakwankwani da tsirrai da yashi da ruwa mai mamako.

    Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, shaidawa da take kare jikkuna daga tawaya da ke lulluɓe su. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammadu shi ne mafi alherin halittu kuma mafi tsarkakarsu, Allah Ya yi daɗin salati da sallama da albarka a gare shi, da alayensa da sahabbansa, zaɓaɓɓun halittu kuma mafiya matsayinsu, waɗanda suka kai maƙura a matakan kariya da garkuwa, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako.

    Bayan haka:
    Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah, ku ji tsoronSa a sarari da ɓoye, duk wanda ya lazimci tsoron Allah, to, haƙiƙa ya amsa wa mai kira zuwa ga Allah, ya kuma yi tsauri ga ababe masu ɓatarwa kuma ya gagare su, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun tsarkaka.
    Tsoron Allah shi ne rabautar mutum a kodayaushe, kuma da shi ake ƙetare wahalhalu masu girma.

    ((Ya ku waɗanda ku ka yi imani, ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacca take daidai () Zai gyara muku ayyukanku, kuma Zai gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)).

    Ya ku taron muminai:
    A cikin wannan zamani da ke cike da masifu da ƙalubale, da ɗimuwa da koke-koke, yaro na fatan ya girma, tsoho na burin ina ma ya koma yaro, mara aikin yi yana fafutukar neman aiki, ga ma’abocin aikin yi kuma ya ƙosa da aikin nasa, ma’abocin dukiya na cikin gajiya, shi ma matalauci na cikin gajiyar.

    A cikin wata al’umma da ayyukan sihiri da tsaface-tsafacen shaiɗan ke yaɗuwa, da cututtukan kambun baka da annobar zukata, da abin da ke samun musulmi daga haka na damuwa da jinya, ko tawaya na rayuka da dukiyoyi, da kuma abubawa da Allah tsarki ya tabbata a gare Shi Yake ƙaddarawa na jarrabawa ga ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi.

    Kuma ita jarrabawa tsani ce na samun darajojin kamala ga wasu mutane, ga wasu kuma, kaffara ce daga munanan ayyuka, amma shi lamarin musulmi alheri ne gaba ɗayansa, idan bala’i da ƙunci suka sauko masa ((Kuma zai iya yiwuwa ku ƙi wani abu alhalin shi alheri ne a gare ku, kuma zai iya yiwuwa ku so wani abu alhalin shi sharri ne a gare ku. Kuma Allah Shi yake da sani, ku ba ku sani ba)).

    Ya ku masu Imani!
    Tunatarwa game da maudu’in kariya da garkuwa na daga cikin mafi mahimmancin abin da mutane suke buƙata, musamman ma a wannan zamani da cututtuka masu yawa suke game rayuka kuma suke kutsawa cikinsu, suke fuskantar su da matsaloli kuma suke ratsa su, na farfaɗiya da shafan aljanu da tsafi da kambun baka, da ƙullata da hassada masu kai wa ga mutuwa.

    Haƙiƙa ayoyin Alƙur’ani sun haskaka da manyan hujjoji, Hadisan Annabi da mafi kyawun bayani, da shaida na gani da ido cewa su ne magani da waraka daga kowace gagararriyar cuta, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: ((Ka ce shi (Alƙur’ani) ga waɗanda suka yi imani shiriya ne da waraka)).

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ku bijiro mun da ruƙiyyoyinku, babu laifi a ruƙiyya matuƙar ba shirka ba ce). Muslim ne ya rawaito.
    Sau da yawa za ka ga mara lafiya da yake dab da halaka da mutuwa, wanda manyan asibitoci da ƙwararrun masana da likitoci su ka gagara magance masa cuta, sai ya nemi waraka ta hanyar ruƙiyya ta Shari’a, sai Allah Ya tabbatar masa da lafiya da waraka.

    Imamu Ibnul-ƙayyim Allah Ya masa rahama ya ce: “Alƙur’ani shi ne waraka cikakkiya daga dukkan cututtuka na zuciya da na jiki, idan mara lafiya ya kyautata yin magani da shi, ta yaya ma daman cututtuka za su iya turje wa maganar Ubangijin ƙasa da sama, maganar da da za ta sauka a kan duwatsu da ta rududduge su, ko a ƙasa da ta keta ta”. Allahu Akbar.. Madalla da wannan yaƙini tabbatacce.

    Lalle tofi saboda guba ko kambun baka, idan ya kasance da tsantsan ayoyin Alƙur’ani ko sunnar Annabi ne, to wannan yana daga shiriyar Annabi da Shari’arsa, kuma wannan babu saɓani cewa Sunna ne.

    Ya ku al’ummar Musulmi!
    Kariya da garkuwa hanya ne da ake bi don nisantar cuta da jinya da rashin lafiya, don haka ya ku bayin Allah ina horon ku da kare kanku da ‘ya’yanku da gidaddajinku da wuridodi na Shari’a, da zikirai na safiya da maraice, da zikiran shiga gida da fita, da na ci da sha, da na bacci da farkawa, da wasunsu cikin zikirai da suka tabbata daga Shugaban halittu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, saboda su ne garkuwa mai kariya da izinin Allah, tare da tawakkali mai ƙarfi ga Allah Majiɓinci Mai gani da ji, da mai da lamari ga gudanarwarSa mai tsari da kyawu, kuma yaƙini da Allah shi ne mafi girman ƙudurori, kuma shi ya fi haske a cikin duhun ɗimuwa: ((Yanzu Allah bai ishi bawanSa ba?).

    Na yarda da Ubangijina, kuma na mayar da lamurana gare Shi, kuma Ya isa Ya kasance Mai taimako na. Kada ka yanke tsammani saboda masifun zamani, lallai yaƙini na da Allah shi ne makarina. Bukhari ya rawaito a cikin Sahihinsa daga Hadisin Ibn Abbas Allah Ya ƙara masa yarda cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yi wa Hasan da Husaini addu’ar neman tsari yana cewa: (Lalle mahaifinku yana yi wa Isma’il da Ishaƙ addu’a da wannan addu’ar ta neman tsari: ‘A’uzu bi kalimatillahi at-tammati min kulli shaiaɗanin wahammatin wa min kulli ‘ainin lammah).

    Kuma ya zo a cikin Sahihu Muslim, daga Hadisin Abu Umama Al-Bahili Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (Ku karanta Suratul Baqara, domin lallai karanta ta albarka ne, kuma barinta hasara ne, kuma matsafa ba a datar da su ga koyonta).

    Imam Ahmad ya rawaito a cikin Musnad ɗinsa daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Kada ku sanya gidajenku su zama kaburbura, domin shaiɗan yana guje wa gidan da ake karanta Suratul Baqara a cikinsa), musamman ma ayatul Kursiyyi da ayoyin ƙarshen surar, da Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi kamar yadda hakan ya kasance shiriyar Manzonku.

    Ya ku taron Musulmi,
    Saboda rashin kulawa daga yawancin musulmi wajen neman kariya ga kansu, da ‘ya’yansu, da gidajensu, tare da raunin imani da aƙida ga wanda shaiɗan ya shafa da wasiwasi ko wasu abubuwa masu kama da haka, ko wanda aka shafa da kambun baka ko hassada, wasu daga cikinsu suna tunkarar sihirce-sihirce da tsubbace-tsubbace da tatsuniyoyi, da tsafi da damfara da aikata laifuka, suna faɗawa hannun wasu daga cikin masu raya yin ruƙiyya, ko waɗanda suke raya warware sihiri da makamantansa.

    Sai ka ga mai ruƙiyya yana rubutun da ba a ganewa kuma yana yin laya, wani kuma yana magana mara ma’ana, wani kuma yana tabbatar da cewa cutar kambun baka ce, kuma wanda ya yi kambun bakan a cikin dangi yake, wani kuma ba ya rabuwa da yin duka mai cutarwa, kuma mafi yawan waɗannan masu ikirari suna ɓoye haƙiƙanin lamarinsu ta hanyar bayyana siffofin mutane masu hankali da taƙawa, amma su ba komai ba ne illa mayaudara waɗanda suke cin dukiyoyin mutane, suna neman dukiya ta hanyar aikata rashin gaskiya, kuma ana iya bijiro da shi da wasu siffofi don yaudarar talakawa, musamman ma ta hanyar amfani da tashoshin talabijin da shafukan yanar gizo da kafafen sada zumunta, har ma da wasu manhajoji.

    Ya ku bayin Allah!
    Sannan shi kariya da garkuwa ba ya buƙatar wahala ko tsananta wa kai, ko faɗawa cikin tarkon maƙaryata, bari da, shi amintuwa ne daga waɗannan gaba ɗaya, mutum zai iya yi shi da kanshi, haka tare da iyalanshi da ‘ya’yanshi. Kuma yana taimakawa wajen kiyaye ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi, da kishi wajen ba da kariya ga daɗaɗɗar aƙida, da ƙayatattar Shari’a.

    A’uzu billahi minash-shaiɗanir-rajim: ((Kuma daga Alƙur’ani muna saukar da abin da yake shi waraka ne da kuma rahama ga Muminai; ba kuma zai ƙari azzalumai da komai ba sai taɓewa)). Allah Ya albarkace mu da Alƙur’ani da Sunna, Ya kuma amfane mu Ya ɗaukaka mu da abin da ke cikinsu na ayoyi bayyanannu da hikima.

    Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina nema mana gafarar Allah Mai girma da sauran Musulmi daga kowane kuskure da zunubi, don haka ku nemi gafararSa kuma ku tuba zuwa gare Shi, Lallai Ubangijina Mai gafara ne Mai jin ƙai.

    Huɗuba ta biyu:

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa ni’momi da Ya yi, tsarki ya tabbata a gare Shi Ya yi wa bayinSa baiwa mai yawa. Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya.

    Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu shi ne abin koyi ga masu tsoron Allah, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa masu tsarki zaɓaɓɓu, da Sahabbansa masu biyayya da tsoron Allah, da Tabi’ai da waɗanda suka bi tafarkinsu har zuwa Ranar Alƙiyama. Bayan haka:

    Ya ku bayin Allah!
    Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umurninSa, da kuma guje wa haninSa da jan-kunnenSa, saboda Shi Allah Maɗaukakin Sarki Yana tsinkayar al’amarin da yake ɓoye ko bayyane, da abin da ke ɗarsuwa a zukata da abin da suke ɓoyewa.

    Ya ku taron Muminai!
    Jarabawowi da masifu da tashe-tashen hankula da fitintinu da damuwowi da bala’o’i, da ke samun al’umma ba su ɓuya a gare ku ba, waɗanda suka jawo mata rashin jin daɗi matuƙa. Saboda haka, lallai daga cikin mafi mahimmancin nau’ukan kariya a wannan mawuyacin hali shi ne: Kare hankulan matasa ta fuskar tunani da kuma aƙida.

    Wannan nauyi kuwa ya rataya ne akan malamai da masu wa’azi da iyaye da malaman tarbiya da saita tunani, da kafafen yaɗa labarai da fitattun marubuta. Don haka ya wajaba a kansu gaba ɗaya su ba da gudumawa wajen kare matasa ta ɓangaren tunani da kuma aƙida, da kuma kwaɗaitar da su ga komawa wajen malaman al’umma masana, da kuma yin gargaɗi dangane da fatawowi waɗanda suke bauɗaɗɗu da masu ingiza mutane da kuma masu dilmiyarwa.

    Da kuma faɗakar da su game da ƙalubalen da ke fuskantar su, a wannan zamani da fitintinu na son zuciya da shakku suka yawaita, tashe-tashen hankula suka shiga tsakanin ma’aurata da iyalai da al’umma. Da kuma yin riƙo da hannayensu daga aukawa cikin ramukan gurɓatattaun tunani, tare da wayar da kai ta hanyar bayyana shirin maƙiya da daƙile hanyarsu ta cimma munanan muradansu.

    Allah Ya kiyaye matasanmu da al’ummarmu daga dukkan sharri da munanan abubuwa, Ya kare mana tsaronmu da zaman lafiyanmu da aƙidarmu da shuwagabanninmu, Lallai Ubangijina Makusanci ne kuma Mai amsa addu’a. Ku saurara! Allah Ya yi muku rahama- Ku yi salati da sallama ga shugaban Manzanni da Annabawa, jagoran masu tsoron Allah kuma tsarkaka, kamar yadda Ubangijin talikai Ya Umarce ku da hakan inda Yake cewa:

    (Lallai Allah da mala’ikunSa suna yi wa Annabi salati. Ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi masa salati da kuma sallama mai yawa). Kuma ya zo a cikin ingantaccen hadisi: “Duk wanda ya yi min salati ɗaya, Allah Zai yi masa salati goma.”

    Lallai yin salati ga Annabi babbar riba ce…duk wanda ya same ta, to, ya samu matsayi kuma ya mallake shi. Ku ribaci wannan dama ku riƙa yin salati ga Annabi, kuna masu cewa: Allah Ya yi masa daɗin tsira da aminci, har abada. Ya Allah Ka yi salati da sallama ga Annabinmu Muhammad da Iyalansa masu tsarki da tsarkaka, da Sahabbansa masu haske da ɗaukaka, da Halifofinsa shiryayyu Abubakar da Umar da Usman, da Ali da dukkan sauran Sahabbai gaba ɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako.

    Allah Ka haɗa mu tare da su cikin falalarKa da kyautarKa da karamcinKa, ya Mafi karamcin masu karamci. Muna neman kariyar Ma’abocin mulki da iko, mun yi riƙo da Ma’abocin buyawa da ƙarfi, mun dogara da Mai rai wanda ba ya mutuwa.

    Muna neman kariya da cikakkun kalmomin Allah waɗanda nagari ko fajiri ba su iya ƙetare su daga dukkan wani shaiɗani da dabba mai guba, muna neman kariya da cikakkun kalmomin Allah daga sharrin abin da Ya halitta da wanda Ya ƙaga da wanda Ya samar, da sharrin abin da yake sauka daga sama da sharrin abun da yake fitowa daga ƙasa da ma sharrin kowacce dabba wanda Kai ne Kake riƙe da ita, lallai Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake.

    Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai, Ka kare shingen addini, Ka sanya wannan ƙasa ta zama mai aminci da kwanciyar hankali, da yalwa da wadata, tare da sauran ƙasashen Musulmai. Ya Allah, Ka amintar da mu a ƙasashenmu, ka datar da shuwagabanninmu da jagororinmu, Ka ƙarfafi Shugabanmu kuma Jagoranmu da gaskiya da dace.

    Ya Allah ka datar da Shugabanmu Hadimin Masallatai biyu masu alfarma da Mataimakinsa ga abin da yake ɗaukaka ne ga Musulunci da kuma gyara ga Musulmi, da kuma abin da yake alheri da shiriya ga mutane da ƙasa. Ya Allah ka datar da ɗaukacin jagororin Musulmi.

    Ya Allah, Ka taimaki jami’an tsaronmu da masu dako a iyakokinmu. Ya Allah duk wanda yake nufatarmu da Musulunci da Musulmi da wani sharri, Ka sa ya shagala da kansa, Ka mayar da mugun nufinsa a kansa, Ka sanya dabararsa ta zama hallakarsa, Ya Maji roƙo.
    Ya Allah, Ka haɗa kan al’umma akan Alƙur’ani da Sunna, ya Ma’abocin kyauta da falala da baiwa.

    Ya Allah ba a iya karya rundunarKa, ba a saɓa alƙawarinKa. Ya Allah Ka taimaki ‘yan’uwanmu a Falasɗinu, ya Allah Ka tarwatsa maƙiyansu Ka wargaza taronsu, Ka sanya su su zama izina ga masu lura. Ya Allah, Ka tsara wa wannan al’umma lamari na shiriya, wanda zai ɗaukaka ma’abota biyayya da imani, kuma ya shiryar da masu bijirewa da yin zunubi.

    Ya Allah, muna da ‘yan’uwa waɗanda ɗari da talauci suka shafe su, ya Allah, ya Mai biyan buƙatu, ya Mai kawar da talauci, ya Mai agaza wa wanda ya ke cikin ƙunci, Ka saukar musu daga ɗumin jinƙanKa, Ka wadatar da su da falalarKa da albarkatunKa, ya Maji roƙo, ya Mafi jinƙan masu jinƙai. Ya Allah, Ka ba mu alheri a duniya Ka ba mu alheri a Lahira, Ka tsare mu daga azabar wuta.

    Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Manzanni, godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai.

    Danna nan don karantasahihin sirrin iza ja’a

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

     

  • Rijistar CAC Da Muhimmancinta

    Rijistar CAC Da Muhimmancinta

    Menene CAC Certificate?

    CAC (Corporate Affairs Commission) shi ne certificate ko kuma shaida ce da ake yi wa sana’a babba ko kuma ƙarama. Wannan shaida ta CAC ita ke ba da dama mai yawa a gwamnatance ko daga ɓangaren ƙungiyoyi masu zaman kansu.

    Kowanne kasuwanci yana ƙara inganta ne idan ya kasance ya mallaki wannan shaidar ta CAC, kuma kowa kan yi ƙoƙarin hulɗa da kai ba tare da kokwanto, ko kuma tunanin cutarwa ba.

    A lokuta da yawa da suka wuce gwanatin tarayya da ta jiha sukan ƙirƙiro wani tsare-tsare da za a tallafawa ‘yan kasuwa amma saboda rashin wannan shaida ta CAC kaɗan ne daga cikin al’umma suke amfana, a bayannan gwamnatin tarayya ta fitar da tsarin Survival Fund amma waɗanda suka mori tsarin cikin kwanciyar hankali su ne waɗanda suke da CAC Certificate.

    A wannan gaɓa nake shawartar ‘yan kasuwa manya da ƙanana da su je su yi wannan Certificate na CAC domin yana da matuƙar mahimmanci ga kasuwancin gida da waje.

    Danna nan don karanta yadda ake addu’ar shiga kasuwa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Kafar Sadarwar Zamani, Amfani da ƙalubalenta 2

    Kafar Sadarwar Zamani, Amfani da ƙalubalenta 2

    Amfani da kafar yanar gizo da kuma kafar sadarwar zamani (Social Media) haɗe da  ƙalubalen su (Kashi na Biyu)

    Abubakar Ibrahim Panshekara

    Waɗanann sabbin hanyoyin kafofin watsa labarai wata sabuwar dabara ce wacce ta haskaka zukatan mutane a farkon bayyanarta. Youtube, Twitter, Instagram da sauransu alal misali, suna biyan buƙatun masu amfani.

    Youtube, dandamali ne guda ɗaya wanda duk ya ƙunshi abin da mutum ke buƙata a cikin naɗin sautin bidiyo, yana nuna wakilcin abinda ke faruwa a zahiri ta cikin bidiyo na kusan dukkanin buƙatu. Wato, yana ba da gamsasssun amsoshin tambayoyi a bidiyo daban-daban na masu amfani da shi.

    A mafi rinjayen ra’ayi na cewa hanya ce ta magance matsaloli, Youtube yana ba da cikakkun bayanai. Ko da yake wasu suna kallon abubuwan da ba su kamata ta hanyar shi ba, duk da haka don haka gaskiya ne cewa dandamalin ana da rauni don zama mai rauni, amma duk da haka, yana kawo dama da gogewa marasa adadi ga waɗanda suka yi amfani da shi ta hanyar da ta dace.

    Duk da gaskiyar cewa wasu mutane suna amfani da shi, yana da kyau sosai, fasahar ta fi amfani da ita tare da manufar ƙirƙira ba tare da ƙarin abubuwan da ba dole ba. A matsayin muhimmin dandali don koyo, bai kamata sha’awar zuciya ta rufe idanun masu amfani da dandamalin ba. Yana da kyau a ce, duk wanda ya san cewa ba zai iya sarrafa amfani da Youtube da sauran dandamali ko kafafen ta yadda ya dace ba, yana da kyau su haƙurƙurtar da zukatansu.

    Bugu da ƙari, wasu mutane sun zaɓi yin magana a dandalin sada zumunta waɗanda ba dole ba kuma suna ɗokin bayyana ra’ayinsu a kan batutuwa ko da ba a gayyace su ba. Suna jin kamar suna rayuwa a shafukan sada zumunta ba tare da yin tsokaci ba a cikin sharhinsu, shawarwarin ra’ayoyinsu da shawarwari ko yin rubutu, kamar tunanin rayuwar kifi ne ba tare da ruwa ba.

    Don haka ba sa so su kasance a kan dandamali kamar kurame ma’ana dole ne sai sun yi magana. Waɗanda suke da hikima, suna amfani da kafofin watsa labaru. Ta wannan hanyar, suna amfani da tsarin don koyo da inganta ingantaccen tsari. Mutane da yawa sun sami ayyukan yi da da cigaba ta fannoni da dama, masu kyau sanadiyar amfani da soshiyal midiya.

    Wannan shi ne saboda, suna yin zaɓi mai kyau a cikin irin shafukan da suke bi, rubuce-rubuce ko labaran da suke karantawa da kuma abubuwan da suke kallo. Waɗannan mutane suna bincika kusurwoyi da yawa suna neman damar da za su bi. Shigarsu a kafafen sada zumunta kamar na masu fasahar girki ne wanda soyayyarsu ke girki. Don haka social media kamar soyayyarsu ta biyu ce.

    Domin karanta kafar Sadarwa Amfani Da Ƙalubalenta danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Abubuwan Da Ke Haddasa Yawan Zubewar Juna Biyu

    Abubuwan Da Ke Haddasa Yawan Zubewar Juna Biyu

    Yawan yin ɓarin juna biyun da bai kai makwanni 20 ba, babu zato ba tsammani, shi ne ake kira “spontaneous abortion” a likitance. Abubuwan da suke iya haifar da shi su ne:

    1. Nakasa A jikin Jariri (Fetal Genetic Abnormalities): idan za a haifi jariri da wata nakasa, to, cikin hukuncin Allah SWT, sai cikin ya zube tun kafin a haife shi. Wannan hikimar Allah SWT ce, ma’ana maimakon a haife shi ya rayu cikin wahala, kuma iyayensa cikin wahala, sai a yi barinsa kawai. Binciken kimiyya na asibiti ya tabbatar da cewa kaso 50% na ɓarin da mata suke yi, abinda yake haddasa shi kenan.

    2. Kamuwar Mai Juna Biyu Da Cututtuka (Maternal Health Conditions): Cututtuka masu ƙarfi, kamar ciwon sugar (diabetes), ko cututtukan jakar sinadarin thyroid (thyroid gland disorders), ko ko hawan jini (hypertension), da sauransu, suna haddasa yin ɓarin juna biyu, matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa na magance su ba.

    Sa’annan kamuwa da ƙwayoyin cututtukan numfashi na rubella, ko cutar garkuwar jiki ta cytomegalovirus, ko cutar mu’amala da gurɓataccen abinci ta listeria. Bayan haka, rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai a cikin jikin mace zai iya haifar da ɓarin juna biyu, kamar polycystic ovary syndrome (PCOS) da matsalar rashin ƙarfin bangon mahaifa na luteal phase defects duk suna iya haddasa yin ɓarin juna biyu.

    3.Tsarin rayuwa (Lifestyle Factors): yin ɗabi’ar shan taba (cigarette smoking), ko shan giya (alcoholism), ko ƙiba wacce ta wuce misali (obesity), suna iya haifar da yin ɓari.

    4. Shekaru (Age): matan da suka kai shekaru 35 a rayuwarsu, sun fi hatsarin yin ɓarin juna biyu idan suka samu ciki, saboda akwai yiwuwar kwayoyin halittar jariransu suna iya samun nakasa (fetal chromosomes defects).

    5. Matsalolin Mahaifa Da Bakin Mahaifa (Uterine or Cervical Issues): cututtuka kamar ƙarin mahaifa (uterine fibroids), ko zazzagowar mahaifa (uterine polyps), ko rabewar mahaifa gida biyu (septate uterus), za su iya haddasa yin ɓari. Hakan rashin rufewar bakin mahaifa yadda ya kamata (cervical insufficiency).

    6. Matsalolin Rashin Ƙarfin Garkuwar Jiki (Immune System Disorders): matsalar garkuwar jiki mai haddasa daskarewar jini  (antiphospholipid syndrome), za ta iya haifar da yin ɓari.

    7. Matsalolin Muhalli (Environmental Factors): idan mai juna biyu tana zama a cikin muhallin da ya gurbace da warin hayaƙi, ko sinadaran chemicals, ko hasken radiation, ko ƙura da iska mai guba, to, hakan zai iya haifar mata da yin ɓari.

    8. Bugewa a Ciki (Physical Trauma): idan mace ta buge a ciki sakamakon faɗuwa, ko rauni, ko tsautsayin duka, za ta iya fuskantar yin ɓari.

    Danna nan don karanta Awon Juna Biyu

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Zinariyar Awa Ga Jariran Mu

    Zinariyar Awa Ga Jariran Mu

    Zinariyar awar ita ce awa ɗaya ta farko a duniya ga jarirai bayan an haifo su wato “Golden hour” a turance, a nan ake tantance yanayin lafiya ko nakasa jikin jariri in ya zo da ita, wacce a da sam ba a iya gani ba sanda yake a cikin mahaifa.

    Wannan awa guda ɗin ta farkon rayuwa duk matsalar da jariri ya zo da ita aka yi sakaci ba a iya gano ta ko an yi wani abu ba a cikinta to akwai yiwuwar kaso 99% cikin 100% na mutuwarsa, shi yasa aka kira ta da golden hour saboda muhimmancinta.

    Ita awar na farawa ne da zarar kan jariri ya ɓullo duniya ko da sauran jikinsa bai kai ga ƙarasa fitowa ba. Hakan ke ba wa jami’an lafiya damar nazartar abubuwan da ka iya faruwa ga jariri masu yawan gaske kamar yadda na faɗa a baya.

    A wannan lokacin za a lura da:-

    – Ta yaya ma ya doso duniya,  a gicciye ko karkace?
    – Kalar jikinsa walau ya zo a jansa wato pink color ko kuwa abinda ba a so wata bulu “bluish color,
    – Yanayin kalar ruwan haihuwan da ya fito ciki walau clear kamar dafaffen zaƙi, ruwan ɗorawa (da ke nuna ya yi kashi a ciki wajen fitowa akwai yiwuwar ya sha ko ya shaƙa), ko kuwa kalar kore da ke nuna ya jima da kashi a ciki har ya galabaita.

    – Haka yanayin ƙwallon ƙoƙon kansa
    – Yanayin sautinsa
    – Yanayin bugawar zuciyarsa,
    – Yanayin numfashinsa,
    – Yanayin ƙwarin jikinsa,
    – Yanayin gaɓoɓin hannunsa,
    – Yanayin yadda yake maido da martani in an taɓa wasu sassa na jikinsa da
    – Kuma duk sauran jikinsa walau akwai nakasa a halittarsa ko babu.

    Domin wasu kan zo cikin kashi, wasu ba hanyar numfashi, wasu da lanƙwasassar ƙafa, wasu da al’aura biyu ta mace da namiji, ko ta mata duk biyun, ko namiji duk biyun, ko babu dubura, ko ba hanyar fitsari, ko hanyar fitsari a toshe, ko ta ƙasa ko sama maimakon straight ta kan, ko kumburarren kai in an yi doguwar naƙuda saboda kaucewa jaundice.

    Toh sai dai maƙasudin rubutun shi ne domin yin bayani game da muhimmancin wani abu ƙanƙani amma me matuƙar tasiri a jika. Wato RUNGUME JARIRI ko JARIRIYA ga uwa ba tare da shinge a tsakani ba, wato dai skin to skin contact.

    Galibi ga wanda suka haihu a asibiti ko ɗaliban ilimin lafiyar da ke zuwa asibiti ko kallon video clips na naƙuda zuwa haihuwa, Ko C/S ba za ku rasa ganin yadda nan da nan da an haifo ko an ciro jaririn ake sa tissue kurum a goge jikinsa a ɗora shi jikin uwa ta rungume shi ko a saita shi ya kama nono ba. wani lokacin ma ko goge jaririn za ku ga ba a yi da ruwan haihuwar da komi a jikinsa za a ɗora shi jikin uwar.

    Hakan shi muke kira da “Skin-to-skin contact” ko “kangaroo mother method” wannan abin na da matuƙar muhimmanci ko da a gida aka haihu ya dace unguwoyin zoma suke aikatawa saboda amfanin sa.

    Domin kai tsaye in yaro ya hau jikinta yanayin sanyi da zafin jikinsa zai saitu, idan ya kama nono ko ya kama jikin uwar za ta zamo stimulated har cikin ƙwaƙwalwarta, wannan kama nonon zai sa mahaifarta (uterus) da jaririn ya fito ta harba (contracting) wannan harbawar ce matakin farko wajen taimakawa domin tsayawar jinin haihuwa, wanda galibin matan dakan mutu bayan haihuwa dalilin zubar jini wannan rashin harbawar mahaifa ne kan gaba da kaso tamanin 80% wajen jawo mummunan zubar jinin da matan kan mutu bayan ana murnar sun haihu lafiya da, (Uterine atony).

    Dukkan bincike da nazarin masana a duniyar likitanci ya yi nuni tare da tabbatar da muhimmancin skin to skin ga jaririn tare da uwar baki ɗaya. Ɗora jariri jikin uwa fata na gogar fata ba tare da riga ko zani ya yi shamaki tsakani ba hakan na haɓɓaka ƙwaƙwalwar jariri nan da nan, tare da farkar da ita domin ta karɓi aikinta cewa an zo duniya kuma yanzu.

    Wadda wannan farkowar ce ke nusar da shi cewa akwai buƙatar ya buɗe baki don numfashi da kansa tare da shirin shan nono ko ya sami ruwa da kuzari a jika, domin an yanke waccan hanyar da yake samun abinci a huce, wato an yanke cibiyarsa tunda ta nan yake samun abinci da ba tare da sai ya buɗe baki ya wahala ba.

    Shi jariri in ya shigo duniya bakinsa ke fara amfani kafin ma ya kai ga buɗe ido ya ga a ina yake. Shi yasa ana ɗorashin za ku ga ba abinda yake fara yi sai buɗe baki, ko ido bai buɗewa sai ya fara da buɗe baki, wanda hakan shi ke nuna ya iso lafiya.

    Amma a ce jariri ya zo ba ya kuka akwai matsala, shi yasa sai an ɗan bugi bayan sa domin ya koka, in ko duk da haka yaƙi kuka to akwai matsala gagaruma. Saboda ta kukan ne kurum huhunsa zai fara aikin da zai ba shi damar iya shaƙar iska ya yi numfashi da kansa.

    Toh bayan buɗe bakin a matakin farko to abu na biyu da jariri ke yi shi ne buɗe idanuwa. Buɗe idon nan da zai abinda zai fara arba da shi shi ne fuska ko jikin mahaifiyar sa. Wanda wannan shi zai jawo shaƙuwa da jinta cikin ransa.

    Toh daga sauran alfanun ɗora shi jikinsa shi ne sanya jikinsa fara aiki babu kama hannun yaro wajen:

    ✍- Ɗumama jikinsa tare da saisaita ɗumin jiki don samun nutsuwa.

    ✍- Taƙaita yawan koke-koke, hakan na sa jariri ya zamo mara fitina.

    ✍- Taimakawa jikinsa wajen amfana da sinadaran nutrients ɗin da ya haɗiya a nono

    ✍- Sa wa a ji sannu a hankali jariri na cigaba da ƙara nauyi.

    ✍- Saisaita ƙarfin tafiyar jini a jikinsa tare da saita bugun zuciyarsa cikin aminci, gami da ba shi dama shaƙar iska wadatacciya zuwa cikin huhu da jininsa.

    ✍- Haɓɓaka kwakwalwa tare da ƙulla alaƙa mai ƙarfi da uwa.

    ✍- Yana sa yaro samun isasshen bacci me nauyi cikin nutsuwa.

    ✍- Uwa uba tare da ƙarfafa masa garkuwar jiki.

    Wannan duk za su cigaba da faruwa in kina rungume shi har tsawon watanni 3 a duniya in dai za ki dinga yi masa hakan a kai a kai. Idan kuma bakwaini ne a yi ta masa skin to skin har ya kai tsawon watanni 6 a duniya.

    AMFANIN RUNGUMAR GA UWA KUMA SHI NE:

    1- Kamar yadda na faɗa a baya idan daga haihuwa ne aka yi hakan to yana ba da kariya daga matsalar zubar jini bayan haihuwa (postpartum bleeding). Wato ɗaya daga abinda ke kashe mu ta dalilin haihuwa.

    2- Hakan na sanya wa uwa ƙwarin guiwa da shauƙin son shayarwa, domin da wuya ka sami uwar da ke ɗora jaririn a fatar jikinta na gudun shayarwa ko tunanin zubewar nono.

    3- Hakan na haɓɓaka yawan ruwan nono, ya zamto yana tsatstsafowa a kai-a kai.

    4- Ya kan magance cutar damuwa da kan sami wasu matan bayan haihuwa musamman masu haihuwar farko, da wasu za a ga haka kurum ma kuka suke bayan ko tun kafin haihuwa, tare da jin tsoron jariran ko wurgi da su, ko ƙin ba su nono.

    DON HAKA SKIN TO SKIN CONTACT

    Abu ne ƙanƙani kamar wasa amma sai tarin muhimmanci. Kuma ba iya sanda aka haihu ba ne kurum a a lokaci-lokaci kike haɗa jikinki da nasa kina rungume shi in ya so ki sa abin rufa ki rufe kanku baki ɗaya amma fatar sa kan taki, haɗa jikinki da nasa babu tufafi ya fi duk wasu kayan sanyi da za ki sa masa ki murginar a gado.

    Har kai uba ka dinga yi wa babynka haka zai amfana amma dai jikinka ya zamto a tsaftace ba bayan ka yi zufa ka bushe ba.

    Don karanta Haifo Jarirai Cikin Rigar Sac danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Hani A Kan Yin Gaba

    Hani A Kan Yin Gaba

    Gaba: Rashin magana da juna bisa ga wani dalili wanda ya haɗa wasu mutane faɗa ko husuma ko jayayya da dai sauran su.

    Saboda haka, gaba ba ta da wani amfani ga musulmi ko addinin musulunci, saboda addinin musulunci, addini ne wanda yake buƙatar mutanensa su dinga magana da juna, wasa da dariya haɗi da nishaɗantar da juna tare da kyautatawa juna, amma kuma ita gaba duk ta hana aikata haka.

    Haka kuma Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya nuna mana irin sharrin da gaba take iya haifarwa ga al’umma, misali tana iya rushe zaman lafiya ga mutane, rashin samun gafarar Allah, rashin samun yarda ko amincewar Allah, rashin samun taimakon Allah da dai sauransu.

    Sannan kuma ita gaba babu wani abu wanda take iya haifarwa , illar rashin jituwa atsakanin musulmi haɗi da daina ko rashin tatttaunawa da junansu, wanda shi kuma addinin musulunci baya buƙatar aikata haka, saboda shi musulunci addini ne na zaman lafiya

    Bugu da ƙari kuma, gaba tana haifar da faɗa, rikici ko rigima atsakanin mutane haɗi da faɗin magan-ganu mara sa daɗi ko amfani ga addinin musulunci

    Misali, idan wani mutumin wani gari yana gaba da wani mutumin wani garin, to wasu matsaloli za su iya faruwa atsakanin su, saboda shaiɗan yana murna da farin ciki, idan an samu wasu mutane suna gaba da juna.

    Sannan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) ba ya karɓan addu’ar mutanan da suke gaba da juna, ma’ana idan sun ɗaga hannunsu sun roƙi Allah (Subhanahu wata’ala), to Allah ba zai karɓi addur’ar su ba.

    Haka kuma idan salihan bayin Allah sun yi addu’a ga mutane waɗanda suke da wata buƙata a wajen Allah, to ba za a sanya su a cikin addu’ar ba, har sai sun sasanta junan su haɗi da yafewa akan abin da ya wuce .

    Misali mutum ɗan kasuwa ne ko wanda yake buƙatar Allah (Subhanahu wata’ala) ya kawo masa canji a cikin rayuwar sa, amma kuma yana gaba da wani mutum akan wani dalili, wanda ya haɗa su, to Allah ba zai karɓi addu’arsu ba, har sai ya daina yin gaba da wancan mutumin, saboda ita gaba tana hana addu’ar wucewa lafiya sumul ƙalau.

    Musulmi ɗan uwan musulmi ne a duk inda yake a cikin faɗin duniyar nan, tatttaunawa, tausayawa, taimakawa, shawartawa da juna da dai sauransu, waɗannan su ne ake buƙata a tsakanin musulmai.

    Saboda haka, ya kamata ‘yan uwana musulmai mu fahimci haɗarin da gaba take iya haifarwa haɗi da sharrin da ke cikinta. Sannan kuma gaba tana iya kawo rabuwar kai a tsakanin musulmai, saboda haka idan haka ya kasance a junansu, to maƙiya za su iya samun damar shiga tsakanin su, domin su raba kawunan su.

    Misali kamar rukunin ko garken dabbobi ne, waɗanda suke fita kiwo tare da juna kullum, sai wata rana, wata dabbar daga cikin su, sai ta juyawa sauran baya, ta fita kiwo ita kaɗai, can sai ga zaki da kura nan sun tunkaro ta, sannan kuma ita kaɗai ce a cikin daji, shin akwai wata ƙofar gudu a gare ta?

    Saboda haka, gaba kamar gini ne wanda ya rushe ko kuma jirgi ne wanda ya tashi sararin samaniya, sai kuma mai ya ƙare masa a sama, idan ya faɗo ƙasa, kun san abin da zai iya faruwa da jirgin.

    Har ila yau, gaba tana iya haɗa ƙiyayya mai ɗorewa haɗi da wasiya akan aikata abu mara kyau da dai sauran su. Misali idan wani mutum yana gaba da wani mutum ko kuma akwai gaba a tsakanin su, to yakan iya sanarwa da ‘ya’yan sa waccan gaba take tsakanin su da wannan mutumin haɗi da jaddada musu matsayin sa akan wannan gaba.

    Sannan kuma gaba takan iya haifar da sare-sare haɗi da kashe-kashe a cikin wasu guraran ko unguwannin da suke gaba da juna. Misali idan wani mutum faɗa ya haɗa su da wani mutum har sai da ya kai da sanadiyar sare-sare ga waɗancan mutanan, haka kuma wanda ya samu raunin mai yawa, to mutanen sa za su iya ɗaukar mataki akan aikata haka (fansa), kamar su rama abin da aka yi wa ɗan uwan su ko hana mutanen wancan layin shiga layin unguwar su.

    Saboda aikata haka yana iya kawo rabuwar zukatan musulmai, rashin kulawa da juna, tausayawa juna haɗi da asarar jinane ko kuma rayuka ga waɗanda ba su ji ba su gani ba.

    Sannan kuma Allah (Subhanahu wata’ala)  yace “ku ji tsoran fitinar da za ta faɗawa mutane baki ɗaya”, ma’ana idan wani ko wasu mutane suka janyo rigima a cikin wani gari ko jiha ko kuma ƙasa baki ɗaya, to zai iya shafar kowane mutum, haka kuma su waɗancan mutanan da suka haifar da wannan rigimar, to laifin aikata haka yana kan su.

    Misali idan wani mutum ya koyawa wani mutum karatul Alƙur’ani mai girma, sana’a ko kuma dukkanin wani aikin alheri, to Allah (Subhanahu wata’ala) zai ba shi lada mai yawa a duk lokacin da shi wancan mutumin ya aikata haka.

    Kamar mutumin da ya koyawa wani mutumin aikata aikin sharri ne kamar su ƙarya, zina, sata, fushi, gulma da dai sauran su, to a duk lokacin da shi wannan mutumin ya aikata haka, to shi ma za a rubuta masa zunubi mai yawa akan hukuncin koyar da saɓawa Allah (Subhanahu wata’ala) da manzon Sa (Sallallahu alaihi wasallam) .

    Saboda Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yace “Duk wanda ya shiryar da mutane akan hanyar (aikata) alheri, to shi ma za a rubuta masa ladan kwatan-kwacin wanda ya aikata haka”. Misali idan wani ko kuma wasu mutane (ƙungiya) a cikin unguwa ko a gari suna ganin waɗansu mutane suna aikata abu mara kyau da amfani ga mutanen wannan unguwar ko garin, sai su yi yunƙurin hana su aikata haka, to Allah (Subhanahu wata’ala) zai ba su lada mai yawa saboda ƙoƙarin hana yaɗuwar ɓarna a doran ƙasa.

    Saboda haka waɗanda suke yunkurin haddasa gaba a tsakanin mutane, to su sani fa kamar waɗanda suke umarni ne da aikata ɓarna ko sabon Allah (Subhanahu wata’ala) a doran ƙasa da dai sauransu.

    Sannan kuma dukkanin wanda ya yi umarni da a saɓawa Allah (Subhanahu wata’ala) a doron ƙasa, to ya san hukuncin sa haɗi da makomar sa a ranar lahira, ma’ana gidan wutane gidan sa a ranar lahira, saboda umarnin da ya yi na bijirewa Allah (Subhanahu wata’ala), bayan kuma Allah ne ya halicce su, ya kuma raya su, sannan kuma ya ba su abin da zai yi musu amfani a rayuwar su.

    Saboda haka, ya kamata dukkanin abin da mutum zai aikata ko kuma muke so a ran mu za mu aikata a cikin rayuwar mu ta yau da kullum, to yana da matuƙar kyau mu tsaya mu yi tunanin sosai kafin mu aikata haka, saboda mu samu damar wucewa kan gadar tsira ranar lahira lafiya sumul ƙalau.

    Bugu da ƙari kuma, yana da mahimmanci akan musulmi ya san hukunce-hukuncen irin abubuwan da yake aikatawa a rayuwar sa ko kuma ya dinga tambayar malamai hukuncin aikata kaza da kaza da fatan Allah(Subhanahu wata’ala) zai daidaita zukatan mu, ameen summa ameen.

    Domin karanta Hani Akan Yin Gori danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hani Akan Cin Amana

    Hani Akan Cin Amana

    Amana: Wani zance ne ko magana ne, kaya ko dukiya wanda wani mutum ya ɗauka ya ba wani mutum ko ya faɗa masa, saboda amincewar da ya yi da shi.

    Cin Amana: Zambo cikin aminci, yaudara ko ha’intar wani mutum akan wani abu wanda wani mutum ya ɗauka ya ba shi ko ya faɗa masa, saboda yarda da ya yi da shi.

    Saboda haka, addinin musulunci ya hana mu cin amanar juna ta kowane irin siga ko hanya, saboda addinin musulunci, addini ne na tausayawa juna, kulawa da juna, kare mutuncin juna haɗi da dukiyar juna da dai sauran su.

    Haka kuma cin mutuncin juna, wulaƙanta juna, cin amanar juna ta kowane gwadabe, to ba halaye ba ne na addinin musulunci, ɗabi’a ce ta mutane marasa tunani da hankali.

    Bugu da ƙari kuma, duk inda mutum musulmi yake, to ya san akwai waɗansu dokoki wanda Allah ya tsara, domin kula da rayuwar sa ta yau da kullum tare da tunani da hankali mai kyau haɗi da amfanin rayuwar sa.

    Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci akan kowane musulmi ya yi iya ƙoƙarin sa wajen bin dokokin addinin musulunci haɗi da al’adar sa, matuƙar addinin musulunci bai hana aikata haka ba.

    Sannan kuma cin amana laifi ne mai girma haka kuma yana ɗaya daga cikin manya-manyan laifuffuka, wanda ya kamata musulmi ya yi la’akari da su sosai, saboda sun iya katange mutum daga shiga gidan aljannah .

    Saboda ita amana malamai sun ce za ta zo ta tsaya akan siraɗi ranar lahira duk wanda ya ci amana, to za ta kama shi ta yi ƙasa da shi da dai sauran su .

    Misali, idan wani mutum ya ba ka amanar wani abu, sai kai kuma ka ci amanar wannan abun, to ranar lahira wancan amanar da ya ci za ta zo ta tsaya akan siraɗi, idan ya zo zai wuce, sai ta kama shi ta faɗa da shi cikin wani rami mai zurfi sosai. Sai a ce da shi waccan ita ce amanar da ya ci.

    Saboda haka sai ya bita ya kamo ta, idan kuma ya tafi zai ka mota, sai ya kamota ya kusa fito da ita waje, sai ta ƙwace ta sake komawa cikin rami wanda shi zurfin ramin tafiyar shekara ɗari biyar ne (500), haka kum mutum zai ta yi, ita kuma tana ƙwacewa.

    Saboda haka mutum ya yi tunani sosai akan aikata haka, kada ranar lahira ya taho da aikin lada mai ɗimbin yawa, amma kuma ya ci amanar mutane, ka ga wannan amanar da ya ci, to sai ta hana shi shiga gidan aljanna.

    Bugu da ƙari kuma riƙon amana yana ɗaya daga cikin abin da yake nuna ilimin mutum haɗi da tunanin sa da hankalin sa. Saboda Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yace “mutane uku munafikai ne ko da ko sun ambata suna yin sallah, aikin hajji da ummara (su ne waɗanda) idan sun yi alƙawari da wani mutum sai sun saɓa, idan kuma mutum ya amince musu sai su yi ha’inci (cin Amana) da dai sauran su.

    Saboda haka a nan ma ka ga cin amana yana kai mutum zuwa munafunci, sannan kuma shi munafiki idan bai tuba ba, ya mutu a wannan hali, to Allah (Subhanahu wata’ala) yace a cikin Alƙur’ani mai girma “su munafikai suna cikin ƙarƙashin wutar jahannama “. Suratul Ma’ida.

    Saboda haka idan mutum yana aikin gina-ginai, sai wani mutum ya kira shi zai yi masa aikin ginin gida, to wajibi ne a kansa, idan an gama gina gidan, kada ya faɗawa ɓarayi ko kuma waɗansu ɓata garin mutane yanayin ginin gidan, saboda su samu damar shiga cikin gidan a cikin sauƙi, domin su samu damar yin sata.

    Sannan kuma idan mutum yana sana’ar kafinta ko rafta ko kuma saitin setilait, to kada ya yi amfani da wata hanya mara kyau wajen rage katako ko kuma fallasawa waɗansu mutane yanayin tsarin gidan, domin samun damar yin aika-aika, to aikata haka, laifi ne mai girma.

    Misali idan mai dukiya ko wani Alhaji ya kira wani mutum ya yi masa aiki a cikin gidan sa, to wajibi ne akan mai aikin ya kiyaye amanar da aka ba shi ma’ana kada ya ɗauko ɓata gari ko ɓarayi, sannan ya fayyace musu sirrin cikin gidan baki ɗaya, to aikata haka laifi ne mai girma, saboda dai-dai yake da wanda ya ci amana.

    Sannan kuma Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yana cewa “Dukkanin ku (mutane) masu kiwo ne, sannan kuma za a tambaye ku akan irin kiwon da aka ba ku “.

    Saboda haka mutane ya kamata mu fahimci cewa dukkanin abubuwan da muke aikatawa a rayuwar mu, to mu sani fa amana ce a gare mu, saboda za a tambaye mu ranar lahira yadda muka gabatar da rayuwar mu.

    Haka kuma idan wani mutum ya ba wani mutum wani ko ya faɗa masa wata magana bisa ga sharaɗi ba zai faɗawa kowane mutum ba, to idan ya faɗawa wani mutum wancan magana, bisa ga wannan sharaɗi, to shi ma ya ci amana, saboda wanda ya faɗa masa maganar bai aminta wani mutum ya san wancan maganar ba.

    Saboda haka ita riƙon amana tana da mugun sha’ani kuma ga sanya takura a cikin al’amuran rayuwar wanda yake ɗauke da ita. Misali wani mutum ya ba ka ajiyar waɗansu kuɗi da niyyar zai karɓe su zuwa wani lokaci nan gaba, domin biyan waɗansu buƙatun sa, to kuma sai wata matsala ta samu wanda ya ba shi ajiyar kuɗin.

    To idan ya ɗauki kuɗin ya yi amfani da su ba tare izinin wanda ya ba shi ajiyar kuɗin ba, to ya karya ƙa’idar musulunci, sai dai idan lokacin da zai karɓe kuɗin yace da shi, to fa idan wata matsala da same shi zai yi amfani da kuɗin, sannan kuma sai shi wancan mutumin ya amince akan haka, to babu komai a kansa.

    Sannan kuma idan wani mutum ya ba wani mutum ajiyar dukiya ko kuma kadara, sai kuma a samu wata matsala wacce ta hallaka dukiyar ko kadarar ko kuma ya yi amfani da ita, to sai ya yi saurin sanar da wanda ya ba shi dukiyar, ma’ana halin da ake ciki, domin samun mafita akan wannan matsala .

    Saboda haka dukkanin wanda akwai wani abu wanda yake shugabanta kamar su shugabanci, koyarwa ko aikin gwamnati, jinga ko ƙwadago, kafinta, wanki, direba, gyara da dai sauran su, to yana da matuƙar kyau ko amfani a gare su, su kula da su da idon basira sosai, saboda ranar lahira za a tambaye su akan yadda suka gudanar da su a cikin gidan duniya.

    Bugu da ƙari kuma, dukkanin wanda ya ci amana, to amana shi ma za ta ci shi, wanda kuma ya kiyaye amana a nan gidan duniya, to ita ma za ta kare shi daga shiga wuta, muna roƙon Allah(Subhanahu wata’ala) da ya ba mu ikon sauke amanar da ke kan mu.

    Danna nan don karanta Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Edita; RMK