Tag: yadda ake

  • Mu Koyi Addini Kashi Na Farko

    Mu Koyi Addini Kashi Na Farko

    Farillan alwala guda 7 ne:
    • Niyya
    • Wanke Fuska
    • Wanke hannaye zuwa gwuiwar hannu
    • Shafar kai
    • Wanke ƙafafuwa
    • Cuccuɗawa
    • Gaggautawa

    SUNNONIN ALWALA

    • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu
    • Kurkure baki
    • Shaƙa ruwa
    • Fyacewa
    • Juyo da shafar kai
    • Shafar kunnuwa
    • Sabunta ruwa a garesu
    • Jeranta tsakanin farilla

    MUSTAHABBAN ALWALA

    • Yin bismilla
    • Goga asuwaki
    • Ƙari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
    • Farawa daga goshi
    • Jeranta sunnoni
    • Ƙaranta ruwa a bisa gaɓoɓi
    • Gabatar da dama kafin hagu.

    Danna nan don karanta Nasiha

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Wayewa Da Cigaba A Mesopotamia III

    Wayewa Da Cigaba A Mesopotamia III

    Kafa Garuruwa

    Kamar yadda aka yi bayani a baya wayewar kan Ɗan Adam tana tabbata ne da kafa garuruwa. An fara gina garuruwa kamar shekara 7000 da suka shige a tabkuna inda mutane suke noma.

    Mutane sun kasance da yawa a wannan wurare wanda ana hasashen cewa sun kai 30,000 zuwa 40,000 a ƙasar Mesopotamia wannan shi ne dalilin da yasa suka fara kafa garuruwa (McGregor 2010: 69). Sumerians (mutanen Mesopotamia) su ne suka fara kafa manyan garuruwa. Dalili kuwa shi ne masarautun ƙasar sun fara haɓaka, dole ne a sami yadda za a tabbatar da zamantakewa mai inganci saboda haka suka ƙirƙiro garuruwa.

    Gudanar da wannan garuruwa babban aikin kuma mutanen Mesopotamia su ne suka fara ƙirƙiro tsarin gudanarwar saboda haka masana suke faɗa cewa duk wannan gari na duniya ya samu ɓirɓishin ƙwarai Mesopotamia in ji McGregor (2010: 72) yana faɗa cewa a asalin kowanne birni akwai tasirin Mesopotamia.  Birnin da aka fara kafawa shi ne Eridu sama shekara 7000 da suka shige, hasashe ya nuna cewa kamar shekara 5500 garin yana da mutane 4000 kuma yana da faɗin hecta goma (Robert 15). 

    Birnin Uruk, wanda yake tsakanin Baghdad da Basra. Kasar Iraq ta samo sunanta daga Uruk. Kuma shi ne birnin da fara yin tasiri a Mesopotamia. Garin an gina shi ya tumbatsa sau ɗaya daga 3900 BC zuwa 3100 BC tsahon shekara 800 kuma tun kusan shekara 6000 da suka shige aka fara gina garin.

    Bayan Uruk kuma garin da ya yi tasiri shi ne garin ‘yan “cult” Jemdet Nasr daga 3100 BC zuwa 2900 BC. An yi hasashen cewa mutum 50,000 suke zaune a birnin Uruk lokacin da ya yi tashe (Hattstein 2009: 20). Garin ya shahara a ƙasar Mesopotamia saboda abubuwan tarihi da aka samu a cikinsa (McGregor 93). Sun haɗa da manyan gine-gine irin fadadoji, da wuraren bauta (temples) da manyan gumaka (sculptures).

    Ma’ikata birnin an tsara da yadda ake raba kaya an tsara su daki-daki, kuma harkar bauta tana tsare ƙarƙashin sarakuna masu kula da bauta (priest-kings) saboda mutanen sun yarda cewa abubuwan bautawarsu ne suka kafa birnin. Lokacin mulkin farko wato daga 2900 BC zuwa 2340 BC rigingimu sun yi yawa har sukan zama yaƙi tsakanin wannan birane: Uruk da Ur da Lagash-Girsu da Umma da Adab da Kish. A wannan lokcaci Uruk da Kish su ne suka fi tasiri (Hattstein 20). 

    Uruk da Nippur su ne manyan garuruwan a kudancin Iraq (Mesopotamia) da ake bukukuwa a cikinsu. Wannan garuruwa biyu da kuma irinsu Eshnunna, da Ur, da Lagash da Tutub sun shahara a tarihin Mesopotamia. An tuno abubuwa a Inanna (Sanctuary) a garin Uruk da suka nuna cewa a nan aka fara rubutu, da kayan mulki irinsu hatimi, da gini wanda yanuna ƙwarewa da kuma abubuwan ala’da (visual culture) (Firefly 2007: 214-215).

    Yawancin ɓangororin rubutu an samo su ne daga garin Uruk (McGregor 93).  An tono gunkin Sarki Gudea na garin Lagas, ya yi mulkinsa sama da shekaru 4200 kuma wannan gunkin ya nuna ƙwarewar mutanen garin a harka zane da sassaka (Roberts 1980: 19).

    Shi kuwa birnin Ur shekara kamar 4700 da ta shige (2700 BC) yana da mutane 24,000 kuma da girmansa ya kai hecta 120. A cikin kaburburan sarakuna da aka tono na birnin Ur an sami kayan ado na gwal da kujeru wanda aka yi amfani da su kimanin shekara 4550 suka shige wato 2550 BC.

    An sami ƙasusuwan iyalan sarki da suka bi shi kabarinsa suka ɗauki ransu ta hanyar shan guba. Rubututtukan Cuneiform sun ƙunshi bayanai akan cinikai masu yawa a biranen ƙasar irin su Ur da Lagash (Hattstein 2009: 20). 

    A birnin Ur aka haifi Annabi Ibrahim (alaihi salam). Mutanen garuruwan yawancinsu manoma ne. Kuma suna gina gidajensu da tubali saboda babu dutse a kusa. Masu kuɗi suna gasa tubalin a wuta don ya yi ƙarfi wanda ba su da kuɗi suna shanya shi a rana. Ginin tubali yana saurin rushewa (Roberts 15).

    Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka samu Ur, garin da ya fi kowane mahimmanci a Sumeria (Mesopotamia), shi ne alamar (Standard of Ur) an yi shi tsakanin shekara 4400 zuwa 4600. Wannan abu yana da mahimanci a tarihin Ɗan Adam saboda shi ne abin da aka fara samu wanda aka haɗa shi da abubuwa daban a wuri ɗaya. Kafin wannan yawanci abubuwa ana yin su da abu guda ɗaya ko dutse ko itace ko ɓangori.

    Wannan kuwa an yi shi da lapsis lazuli daga Afghanistan, jan dutse (red marble) daga India da kuma kwanson teku (shells) daga Gulf, kwaltar da aka jona abubuwan da ita kaɗai ce ta ƙasar (Iraq). Wannan abun ya nuna zurfin ƙwarewar mutanen ƙasar Mesopotamia kuma da martabar garin Ur. An samo wannan Alamar (Standard of Ur) a cikin wani kabari da aka haƙo a shekara 1920 (McGregor 2010: 72-73).

    Haka kuma a cikin ɗaya daga cikin manyan wuraren da aka binne mutane wanda aka yi su kusan zamani ɗaya Dala Kuffu (Cheops Pyramid) na Misira, an tono kayan gashin kai na gwal (golden headdress) da kofin gwal na sacrifice da hular kai da gwal da wuƙaken gwal wanda a jikinsu aka sa duwatsu masu ƙayatarwa, da kuma abin kiɗa (harp) shi ma mai ƙayatarwa, da wani abin wasa mai kama da fefen Chess (Gombrich 2008: 18).

    Birnin Ur, wanda yanzu shi ne a kira Tell al Muqayyar, a kudancin Iraq, ya shahara da arziƙi tsakanin shekara 4004 da 4112 da suka shige. A wannan lokaci shi ne babban garin (capital) ta dynasty na uku wanda suka gina manyan wurare da filaye na jama’a. Ginin da ya fi kowanne a garin shi ne wurin bautawa wata da ake kira da suna Nanna. Sarki Ur-Nammu (2112-2095 BC) shi ne ya fara gina shi kuma ɗansa Shulgi (2095-2047 BC) ya kammala shi. Wannan gini shi ne ake kira Ziggurat (Firefly 2007: 216). 

    Gininnikan da suka fi kowanne girma da ƙayatarwa su ne wuraren bauta (temples) na garin Uruk. An sami ɗaya daga cikinsu wanda aka gina shi da gasassun tubula akan (terrace) kuma yana da tsahon meter 12 ana zaton a ƙalla mutum 1500 suka yi aikin ginin a cikin shekaru biyar, sama da shekara 5500. Irin wannan ayyuka sun nuna cewa shugabanin Sumeria sun iya haɗa mutane da yawa duk lokacin da buƙatarsu ta taso.

    Addini yana da muhimanci a wurinsu shi yasa su girmama da kuma ƙawata wuraren bauta (temples). Sun yarda cewa abubuwan da suke bautawa suna sama, shi yasa suke dogwayen gininnika don su zama kusa da su. Wannan gininnika ana ce masu Ziggurats ana yin su a sama sai an bi ta kan matattakala (terrace). Wasu masana suna zaton cewa sun yi su a saman matattakala saboda su gujewa ambaliyar ruwa.

    Birnin Lagash ya haɓaka ne a ƙarƙashin mulkin da Ur-Nanshe ya kafa a misalin 2480 BC. Ur-Nanshe ya gina wuraren bauta (temples) da yawa da magudanar ruwa (canals). An samu bayanai daga rubututtukan da suka yi na aikin gudanar da mulki. Eannatum jikan Ur-Nanshe ya mallaki ƙasar a misali 2450 BC .

    Ya yi yaƙi da sunan Ningirsu abin bautar mutanen birnin. Wannan shi ne farkon yunƙurin haɗa kan ƙasar Mesopotami. Eannatum ya faɗa a shahararren rubutunsa ‘Stele of the Vultures’ cewa Ningirsu ya ba shi mulkin birane da suka haɗa da Lagash da Kish. Sarakunan Lagash da matansu sun kula da tattalin arziƙi da aka tsara a ƙarƙashin wurin bauta (temple) wadda alama ce ta tsarin tattalin da hukuma ta kafa (Hattatsien 2009: 20-21).

    Tsarin Mulki

    Sumerians suna da masarautunsu daban-daban kusan kowanne gari yana da masarautarsa kuma su asalinsu mutanen Caucasus wato suna amfani da harshe irin na Caucasian. Su Sumerians suna aske gashinsu su kuma Semites (irin Larabawa da Yahudawa) suna barin gashin kansu da kuma gemu a fuskarsu (Clement 1936: 68).

    Suna kuma maƙwabtaka ƙabilun Semitic masu harshe irin na larabawa da yahudawa. Wani Sarki, mai suna Sargon daga cikin ƙabilun Semitic ya kafa daularsa a garin Akkad arewa da Sumer. Wannan Sarki ya bunƙasa kuma ya yi ƙarfi ya cinye garuruwan Sumeria ya kafa haɗaɗɗiyar daula mai hukuma ɗaya ta farko a wannan ƙasa tunda ga Akkad a Arewacin Iraq har zuwa kudanci inda ta haɗa da su Ur da Uruk. Ya kafa daula ne kamar shekara 4350 zuwa 4400 da suka shige.

    Sargon (the Great) ya yi ƙarfi kuma ya shahara. Ya mallaki ƙasa daga Palestine har zuwa Persian Gulf kuma ana kiranta Akkadian ko Sumerian Empire, ya kai hari Misira da kuma Habasha (Ethiopia). An ce rundunar sojansa mai mayaƙa 5000 suna cin abinci a fadarsa. Shi ne Sarkin da ya fara kafa babbar daula (Empire) a tarihi kuma haɗaɗɗiyar hukuma ta farko a Mesopotamia amma ba ta daɗe ba saboda ta rushe a zamanin mulkin jikansa.

    Sarakunan da su ka gaje shi suna kiran kansu Sarkin Sumer da Akkad. Daular Sargon ta shekara kamar 200 kafin ta rushe wato a cikin 2200 BC. Kabilun kan dutse su ne suka rusa wannan daula saboda hare-haren da suke kawo mata. Bayan rushewarta sai ƙasashen Sumeria suka koma kamar yadda suke a da kowanne gari yana mulkin kansa. Kasar Ur ta fi kowacce a wannan lokacin Sarakunan Sumeria na Kasar Ur sun fi na ko ina shahara.

    Kafin Sarki Sargon I ya cinye ƙasar Sumeria, an yi wani Sarki a birnin Lagash mai suna Urukagina ana kuma kiransa da wani karin sunan Urunimgina kimanin shekara 2350 BC. Ya hau mulki lokacin rigingimu saboda masu arziƙi da dukiyar kansu sun fara bulo. Ya ƙirƙiro tsarin zamantakewa.

    Kasar Misira (Egypt)

    Mutane daga bangarorin duniya daban-daban sun sauka a gefen kogin Nile saboda albarkar ƙasar shekaru kamar 12,000 da suka shuɗe.

    Danna nan don karanta Wayewa Da Cigaba A Mesopotamia

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Ciccikowar Maman Mace

    Ciccikowar Maman Mace

    CICCIKOWAR NONON MACE ALHALIN BABU CIKI, KO SHAYARWA, KO AL’ADA, KO SAKA KWAN HAIHUWA, KO YAYE (BREAST ENGORGEMENT IN WOMEN WITHOUT PREGNANCY, OR BREAST FEEDING, OR MENSTRUATION, OR OVULATION, OR WEANING)

    Nonon mace yana iya ciccikowa ya kumbura, har ya riƙa yin ciwo ko kuma fitar da ruwan nono ko da kuwa ba ta ɗauke da ciki, ko tana shayarwa, ko lokacin al’adarta, ko lokacin saka ƙwan haihuwarta, ko lokacin yaye ba. Ga wasu dalilai da suke iya haifar da hakan:

    1. Rashin Daidaiton Zubar Ruwan Sinadarai (Hormonal Imbalance): Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace yana iya sanya nononta ya cicciko. Matsalolin rashin lafiya kamar Polycystic Ovary Syndrome (PCOS) ko ciwon jakar sinadarin thyroid (thyroid gland disorders) suna iya haifar da wannan yanayin.
    1. Laulayin Amfani Da Magunguna (Medication Side Effects): Wasu magungunan da mata suke yin amfani da su, kamar magungunan tazarar haihuwa (hormonal contraceptives) ko magungunan da suke haɓaka yawan sinadaran da mace take da ƙarancinsu (hormone replacement therapy), ko magungunan ciwon ƙwaƙwalwa (antipsychotics), ko magungunan ciwon damuwa (antidepressants), ko magungunan ciwon cancer (chemotherapy drugs), duk suna iya haifar da ciccikowa da zubar ruwan nono.
    1. Kumburin Nono Saboda Shigar Ƙwayoyin Cuta (Mastitis): A wasu lokuta, kumburin nono yana iya zamowa sakamakon shigar ƙwayoyin cuta a cikin nono ne (mastitis) ko da ba lokacin shayarwa ba.
    1. Ƙullutun Nono (Cysts or Fibrocystic Lumps): Kullutu zai iya fitowa mace a cikin nononta, sa’annan ya kumbura, ya haifar mata da taruwar ruwa da ciccikowar nono, ko rashin jin daɗi a nonon.
    1. Shiga Cikin Yanayin Tashin Hankali Ko Tsananin Rashin Hutu (Stress): Babbar damuwa ko rashin hutu suna iya shafar tsarin sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace, kuma hakan zai iya haifar da ciccikowar nono ko zubar ruwan nono.
    1. Bugewa Ko Samun Rauni A Nono (Breast Physical Trauma Or Injury): Idan mace ta sami rauni a nono ko yankin ƙirjinta, hakan yana iya haifar mata da ciccikowar nono ko zubar ruwan nono.

    Idan ciccikowar nono ko zubar ruwan nonon ya daɗe, ko ya haɗu da jin ciwo mai tsanani, ko wasu alamu waɗanda ba a saba gani ba, to, ya kamata mace ta je asibiti domin a yi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa da ita.

    Domin karanta Matakan Kariya Daga Ciwon Hanta danna nan

      Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Isra’i Da Mi’iraji

    Isra’i Da Mi’iraji

    Ranar 27 ga watan Rajab

    Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya hau kan shimfiɗar “Rafarahu”, domin ganawa da Allah (Subhanallahu wata’ala).

    Ranar ce, annabi Muhammad ya haɗu da;

    1. Annabi Adamu (A.S) a sama ta ɗaya.

    2. Annabi Isa (A.S) da Annabi Yahya (A.S) a sama ta biyu .

    3. Annabi Yusuf (A.S) a sama ta uku.

    4. Annabi Idris (A.S) a sama ta huɗu

    5. Annabi Haruna (A.S) ta biyar.

    6. Annabi Musa (A.S) a sama ta shida

    7. Annabi Ibrahim (A.S) a sama ta bakwai , yana kishingiɗe da ma’ul ma’amur.

    Sannan kuma mala’iku miliyan tara ne (9,000,000) suka karɓi Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) a ranar da ya yi Isra’i da Mi’iraji. Guda miliyan bakwai (7,000,000) suna yi masa lale, guda miliyan biyu kuma suna feshin turare mai ɗan karan ƙamshi.

    Don karanta Munasabar Isara’i Da Mi’iraji danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Munasabar Isra’i Da Mi’iraji

    Munasabar Isra’i Da Mi’iraji

    Ranar 27 ga watan Rajab, rana ce da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi Isra’i da Mi’iraji.

    Isra’i: Shi ne tafiyar da annabi ya yi daga Makka zuwa masallacin Aƙsa.
    Mi’iraji: Shi ne tafiyar da annabi ya yi daga masallaccin Aƙsa zuwa sama ta bakwai har zuwa wajen da suka yi munajati da Allah (Subhanahu wata’ala).
    Wannan ranar, ta kasance rana mafi daraja a wajen musulman duniya, saboda daga ita ne aka samu tabbatuwar salloli guda biyar, (wanda a farko guda hamsin ne).

    Abubuwan da aka samu a wannan rana:
    1. Salloli guda biyar.
    2. Tabbatar aure.
    3. Rabon gado.
    4. Hanyoyin samun aljanna.
    5. Tsarin gudanarwar rayuwar mutane.
    Da sauransu

    Danna nan don karanta Ranar Isra’i Da Mi’iraji

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Ranar Isra’i Da Mi’iraji

    Ranar Isra’i Da Mi’iraji

    An yi imanin cewa Al Isra wal Miraj shi ne daren da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hau shahararriyar tafiyar dare da hawan sama, wanda kuma aka fi sani da Miraj. Ana tunawa da daren ne, a duk ranar 27 ga watan Rajab.

    Tafiyar dare da mi’irajin Annabi Muhammad (SAW) lamari ne mai ban mamaki inda ya yi tattaki daga Makka zuwa Masallacin Al-Aƙsa da ke Kudus kafin ya hau sama, duk a dare ɗaya. Isra’i ita ce tafiyar dare daga Makka zuwa Masallacin Aƙsa.

    Mi’iraj ita ce tafiya daga Masjidul Aƙsa zuwa sama. Yayin da a cikin Larabci, ana kiran wannan da Al Isra’ Wal Mi’raj, a cikin yarukan Bangla, Persian, Iranian, Pakistan da Indiya, wannan shahararriyar tafiya wani lokaci ana kiranta da Miraj, ko, Daren Miraj.

    A lokacin ne aka fara yi wa Manzon Allah (SAW) salloli biyar farillai. Haka nan kuma ya jagoranci sauran Annabawa sallah ya gana da wasu daga cikinsu. Abubuwa masu ban mamaki da yawa sun tabbata daga Manzon Allah (SAW) a wannan tafiya.

    Haka nan jarrabawar ban-gaskiya ce ga muminai a lokacin kuma wata dama ce ga muminai na gaskiya su haskaka. Zamanin tarihi da tafiyar dare da mi’iraji ya gudana, lokaci ne da Annabi Muhammad (SAW) ya fuskanci tsananin ƙunci da baƙin ciki bayan rasuwar wasu daga cikin ’yan uwa da magoya bayansa a jere a jere, tare da fuskantar rashin amincewa da zaluncin da aka yi masa (mutanen Ta’if).

    Ana kyautata zaton an yi shekara ɗaya kafin Hijira (Hijira) daga Makka zuwa Madina. Allah (SWT) ya albarkaci Annabi (SAW) da wannan mu’ujiza wacce ta yi tasiri a rayuwar Manzon Allah (SAW) da Musulunci kamar yadda muka sani.

    Yaushe ne Al Isra’ wal Mi’raj (27 ga Rajab) 2025? 

    Ana sa ran daren Al Isra’ wal Mi’raj zai faɗo ne da yammacin ranar 26 ga watan Janairun 2025 (bisa ga ganin wata). Ranar Miladiyya wacce ta zo daidai da 27 ga watan Rajab 2025 ita ce 27 ga Janairun 2025.

    Menene Ma’anar Al Isra’ Wal Mi’raj (27 ga Rajab)?

    Tafiyar dare (Al Isra’ wal Mi’raj) tana da darussa da falala masu yawa da za mu yi tunani a kai, musamman a kan gabacin watan Ramadan. Halin da ya faru a cikinsa yana da matuƙar muhimmanci, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cikin tsananin wahala da wahala.

    Matarsa (SAW) masoyiyarsa kuma musulma ta farko, Khadijah (RA) ta rasu. Baffansa (SAW) Abu Talib, wanda yana daga cikin manya-manyan magoya bayansa wajen yaƙar Ƙuraishawa shi ma ya rasu a wannan lokacin a shekara ta baƙin ciki. Shekaru 10 kenan da Manzon Allah (SAW) ya fara wa’azinsa. Har ila yau, mutanen Ta’if suka yi masa muguwar ƙiyayya a wajajen wannan lokaci, waɗanda ya yi fatan isar da saƙon musulunci gare su.

    Bayan da aka tafi da Manzon Allah (SAW) ta hanyar mu’ujiza da dare zuwa masallaci mafi nisa a birnin Ƙudus, sai mutane suka fara magana game da shi. Wasu daga cikinsu sun yi watsi da imani da imani da shi. Sai suka nemi Abubakar suka ce: “Shin ka ji abokinka ya yi zaton an kai shi da dare zuwa ɗaki mai alfarma?

    Abubakar ya ce: “Shi ne ya ce?” Suka ce “Eh.” Abubakar ya ce: “Idan ya faɗi to shi ne gaskiya”. Suka ce: “Shin, kun yi ĩmãni ya tafi Haikali mai alfarma da dare, ya dawo tun da asuba?” Abubakar ya ce, “Na’am. Lallai, na yi imani da wani abu da ya fi wannan ban mamaki. Na gaskanta ya sami wahayi daga sama saboda duk abin da yake yi.

    Don haka ne aka sanya wa Abubakar suna mai gaskiya, al-Siddiƙ”. Aisha (R.A) – daga Dalā’il al-Nubuwwah na Bayhaƙī 2/361 Bikin Al Isra’ wal Mi’raj (27 ga Rajab) Musulmai da yawa suna alamar Al Isra’ wal Mi’raj a matsayin ɗaya daga cikin manyan ranaku a cikin kalanda na Musulunci.

    Iyalai suna murna da mu’ujizar hawan Manzon Allah (SAW) zuwa sama da albarka da kyaututtuka da aka yi a wannan dare na musamman, ciki har da salloli biyar. Wasu ƙasashen musulmi sun gudanar da hutun ƙasa domin tunawa da wannan taro mai albarka. Iyalai suna bikin Al Isra’ wal Mi’raj ta hanyar ƙara karatun Alqur’ani da Salawat, suna ƙawata gidansu ko masallacin unguwarsu da fitulu, da kuma taruwa cikin rukuni don raba abinci da jin labarin tafiyar dare.

    Karatun Al-Isra’ Wal Mi’raj (27 ga Rajab) A kowane dare mai albarka kamar Al Isra wal Mi’raj, yana da kyau mu yawaita addu’o’inmu ga Allah, kuma mu roƙi Allah ya biya mana buƙatunmu da buƙatun ‘yan uwa musulmi a faɗin duniya. Yana da kyau a yi salati na nafila (na zaɓi), da yin salati ga Annabi (SAW), da ƙara karatun Alƙur’ani.

    Azumin Isra’il Miraj (27 ga Rajab)

    Azumin watanni masu alfarma yana samun lada mafi girma a wurin Allah Maɗaukakin Sarki fiye da azumin sauran shekara. A cikin Hadisin da aka tambayi Ibn Umar ko Annabi (SAW) ya kasance yana azumi a Rajab? Sai ya ce: Na’am, kuma zai girmama shi (watan Rajab). Musulmai sun zaɓi yin azumin ranar Al Isra wal Mi’raj a matsayin hanyar tunawa da ranar mai albarka da samun ƙarin lada.

    Falalar Lailatul Isra’il Miraj (27 ga Rajab)

    Daren Al Isra wal Mi’raj yana da matuƙar muhimmanci ga musulmi kuma lamari ne mai matuƙar muhimmanci. Yana da tasiri kai tsaye a rayuwarmu ta yau da kullum, kasancewar wannan daren ne aka umarci Manzon Allah (SAW) da ya tsayar da Sallah. Mu’ujizar Al Isra’ wal Mi’raj kuma tana nuna mana takalmi na iko da ɗaukakar Allah mara iyaka, da abin da ya wuce gaibi, da kuma son Annabi (SAW) ga Allah.

    Daren Al Isra wal Miraj (27 ga Rajab), da kuma yawaita sallolin nafila, da ba da Sadaƙa da yawaita ibada. Yana da muhimmanci mu yi tunani a kan Al Isra wal Mi’raj kuma mu zana darussa daga taron mai albarka wanda zai iya taimaka mana sosai.

    Danna nan don karanta Sunayen Watanni Da Hausa

    Edita; Rumasa’u M. Kalllamu

  • Tarbiyyar Yara

    Tarbiyyar Yara

    KU KOYAWA YARANKU HALAYE UKU:

    1. Yawan gaishe da na gaba da su.
    2. Nutsuwa da barin wasa a hanya.
    3. Fita cikin kyakkyawar shiga.

    KU HANA YARANKU HALAYEN NAN:

    1. Yawan yawace-yawace.
    2. Yawan Abokai/ƙawaye barkatai.
    3. Rashin kunya da faɗace-faɗace.

    KU RIƘA GWAƁE BAKIN YARANKU:

    1. Idan suna sa baki a maganar manya.
    2. Idan suna kawo tsegumi da gulma.
    3. Idan suna zagi ko ƙaryata manya.

    KU YI MUSU HORO MAI TSANANI:

    1. Idan suna wasa da Sallah.
    2. Idan suka fara kwaɗayi da roƙo
    3. Idan suka fara ƙarya da lalaci.

    KU ƘARA JAWO YARANKU JIKI:

    1. Idan suka balaga.
    2. Idan ba su da lafiya.
    3. Idan kuna gida a zaune.

    KU KWAƊAITAR DA YARANKU:

    1. Nacin karatu da rubutu.
    2. Dagewa wajen cimma buri.
    3. Lada da nasara in an bi hanyar Allah.

    KU NUNAWA YARA MUHIMMANCIN:

    1. Riƙo da addinin musulunci.
    2. Zumunci da ziyarar dangi.
    3. Lafiya, lokaci da chance/ƙuruciya.

    KU DAINA WAƊANNAN A GABANSU:

    1. Bayyana tsiraici/mu’amalar aure.
    2. Wasan banza na ƙuruciya, kallo.
    3. Bayyana rashin jituwa a tsakaninku.

    KU YAWAITA A GABAN YARANKU:

    1. Karatun Alƙur’ani da salloli.
    2. Aikata gaskiya da riƙon amana.
    3. Wadatar zuci da godiyar Allah.

    SUKE JIN TSORON KU TA HANYAR:

    1. Tsawatar musu in sun zo da wargi.
    2. Rashin barinsu babu abin yi.
    3. Taƙaita nuna musu so ƙuru-ƙuru.

    KU DAGE KU CIREWA YARANKU:

    1. Tsoron mutuwa.
    2. Tsoron talauci.
    3. Tsoron wanda ba ya tsoron Allah.

    KU GOYI BAYAN YARANKU IN HAR:

    1. Su ne ke da gaskiya.
    2. Ba saɓo suka aikata ba.
    3. Sun yi abu domin kare mutuncinku.

    KUKE TSORATAR DA YARANKU:

    1. Illar haɗama.
    2. Fitinar rigima.
    3. Haɗarin taƙama da girman kai.

    KU RIƘA SANAR DA YARANKU:

    1. Asali da tarihi.
    2. Mutuwa da kabari.
    3. Daɗi da rashin sa.

    KU BA WA YARANKU HORO NA:

    1. Taƙaita cin abinci.
    2. Ƙarancin bacci da zaman hira.
    3. Watsar da dogon buri da sharholiya.
    Allah ya ba mu ikon tarbiyyar yaranmu.

    Don karanta Ra’ayin Wani Masani Game Da Tasirin Bincike A Rubutu danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Fassara Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 24th January 2025

    Fassara Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 24th January 2025

    Sheikh Dr Saleh Bin Abdullahi Bin Humaid

    Mai Fassara:
    Dr Abdullahi Yunusa Machina

    Shugaban Shashi
    Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Huɗubar Masallaci Mai Alfarma
    Sheikh Bandar Abdul-Aziz Balila 23/07/1446H

    HUƊUBA TA FARKO
    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, mafakar waɗanda ke cikin tsoro da ƙa-ƙa-ni-ka-yi, Mai ba da kariya ga masu neman mafaka. Ina yaba Masa, kuma ina gode Masa, tsarki ya tabba a gare Shi, Mai taimakon mabuƙata, Mai rarrashin waɗanda suka karaya, kuma Mai karbar tuban masu tuba.

    Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ubangijin masu rauni, mai taimakon waɗanda aka zalunta, kuma Mai karɓar addu’ar waɗanda suke cikin tsanani. Kuma ina shaidawa lallai Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, jagoran masu hasken fuska, Mai shiryar da dukkan halittu, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa tsarkaka nagartattu, da Sahabbansa masu ɗa’a da albarka, da Tabi’ai, da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar ƙiyama.

    Bayan haka:
    Ya ku mutane!
    Ina yi mana wasiyya da tsoron Allah, saboda haka, ku ji tsoron Allah, Allah Ya rahamce ku, ku yi riƙo da igiyarSa, kuma ku nemi mafaka a wajenSa, sai burukanku su cika, kuma ku ji daɗin haɗuwa da Shi, lallai duk wanda ya kira Shi kuma ya roƙe Shi, to, ba zai taɓe ba, kuma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa gare Shi kuma ya yi fatan haɗuwa da shi, to, ba zai yi nadama ba, ta yaya hakan ba zai kasance ba, alhali Shi ne Mai cewa: (Shin wanene zai amsa wa wanda ya shiga cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi yayin da ya kira Shi?).

    Sannan ku sani, Allah Ya yi muku rahama, cewa lallai duniya tana gudana ne bisa ƙaddarawarSa da hukuncinSa, kuma gudanar da al’amuran halittu tana kasancewa ne bisa nufinSa da yardarSa, kuma zukatan mutane suna tsakanin yatsun Ubangijimmu Mai rahama, yana jujjuya su yadda ya so a cikin ƙasa da sama, don haka, ku kyautata zato ga Ubangijinku, kuma ku yi fatan samun alheri daga Mahaliccinku, domin lallai wanda ya kyautata zato ga Allah, to, zai isar masa, kuma Zai jiɓinci lamuransa, kuma Ya ba shi abin da yake fata da buri.

    Allah Ya ce a cikin Hadisi Ƙudusi: “Ni ina daidai da zaton bawana gare Ni, kuma Ina tare da shi idan ya ambace Ni, idan ya ambace Ni a asirce, sai na ambace shi a asirce, idan kuma ya ambace Ni a cikin dandazon jama’a, sai In ambace shi a cikin dandazon da ya fi wancan alheri, idan kuma ya kusance Ni da ɗani ɗaya, sai In kusance shi da zira’i, idan kuma ya kusance Ni da zira’i, sai in kusance shi da gaba guda, idan kuma ya zo gare Ni yana tafiya, Zan zo masa da gaggawa. (Bukhari da Muslim suka rawaito)

    Ya ku bayin Allah!
    Kyautata zato ga Allah ibada ce daga cikin manyan ibadu, kuma aiki ne daga cikin mafi girman ayyukan neman kusanci ga Allah, wanda yake nuni a kan cikar imani, da kyawun zuciya, da yarda da abin da Allah Mai rahama Ya ƙaddara.

    An rawaito daga Abdullahi ɗan Mas’ud Allah Ya ƙara masa yarda, ya ce: “Ina rantsuwa da wanda babu abin bauta bisa cancanta koma bayansa, ba a ba wa wani bawa mumini wani abu da ya kai kyautata zato ga Allah Maɗaukakin Sarki alheri ba, ina kuma rantsuwa da wanda babu abin bauta bisa cancanta koma bayansa, bawa ba zai kyautata zato ga Allah Maɗaukakin Sarki ba, face sai Allah Ya ba shi abin da ya zata, hakan ya kasance ne saboda alheri a hannunSa yake”. Ibnu Abid-dunya ne ya rawaito.

    Kuma shi ne ƙudurce abin da ya dace da Allah Maɗaukakin Sarki na ma’anonin kyawu da buwaya, a sunayenSa da SiffofinSa, da maganganunSa da ayyukanSa masu daraja, tare da cikar iko a cikin abinda ya gabata da wanda zai zo nan gaba, da abin da yake ginuwa a kan haka na tasiri da ɗabi’u kyawawa.

    Shi Allah Maɗaukakin Sarki Shi ne Mai rahama, Mai jinƙai, Mai karamci, Mai yawan baiwa, Mai tausayi Mai yawan kyauta, Mai tausasawa, Mai yawan tagomashi, Mai tsananin ƙarfi Mai cikakken iko, Mabuwayi Mai girma, Mai amsa addu’ar masu tsananin buƙata, Ubangijin uwayengiji, Mai gudanar da gizagizai, Mahaliccin halittunSa daga turɓaya, rayayye da ba ya mutuwa, tsayayye da ba ya bacci.

    Shi ne Makusanci tare da ɗaukakarSa, Maɗaukaki tare da kusancinSa, Masanin abin da Ya rubuta kuma Ya gudanar da shi, halin halittunsa da ke ƙasa ko sama ba ya ɓuya a gare Shi, Mai hikima a ayyukanSa, Mai tausayin bayinSa, Mai taimakon wanda ya nemi kariyarSa da jiɓintarSa.

    Zuwa ga wanda jinya ta kwantar da shi kuma ta wahalar da shi, ta danƙwafar da shi a kan gadajen asibitoci, har suka zama su ne gidansa da makwancinsa, ga addu’ar Annabi Dawuda lokacin da jinya ta tsananta gare shi, lokacin da ta rinjaye shi ta ramar da shi, sai ya risina ga Allah Maɗaukakin Sarki ya kira Shi, yana mai bayyana buƙatarsa zuwa ga Ubangijinsa Majiɓincinsa:

    ((Kuma ka tuna) Ayyuba lokacin da ya roƙi Ubangijinsa (yana cewa): “Lallai cuta ta same ni, kuma Kai ne Mafi jinƙan masu jinƙai” () Sai Muka amsa masa (roƙonsa) sannan Muka yaye cutar da take tare da shi, Muka kuma ba shi (madadin) iyalansa (da ya rasa) da kuma kwatankwacinsu tare da su don jinƙai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu bauta (ga Allah)).

    Zuwa ga wanda aka haramta masa mai ɗebe kewa daga ƙawa ta rayuwa, wanda aka sanya masa kewa saboda kaɗaici, da shagaltuwar kowane ma’abocin iyali da duniyarsa, a ina ka bar addu’ar Annabi Zakariyya tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayin da ya risina wa Majiɓincinsa Allah, ya roƙe Shi a boye, ya nemi agajinSa kuma ya yi fatan samun rahamarSa, da wata addu’a da duk wani ma’abocin rayuwa zai raurawa da ita, kuma idanuwa su kwaranyo da hawaye saboda ita:

    ((Ka tuna) kuma Zakariya’u lokacin da ya roƙi Ubangijinsa (cewa): “Ya Ubangijina, kada Ka bar ni ni kaɗai (ba magaji), Kai ne kuwa Fiyayyen magada”. () Sai Muka amsa masa Muka ba shi Yahya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa. Lallai su sun kasance suna gaggawa wajen yin alheri, suna kuma roƙonmu suna masu kwaɗayin (rahamarmu) kuma masu tsoron (azabarmu), sun kuma zamanto masu ƙasƙantar da kai gare Mu).

    Haka kuma zuwa ga wanda bashi ya durƙusar da shi kuma ya gajiyar da shi, samunsa ya yi ƙaranci, matsalolin rayuwa suka yi masa dabaibayi suka taɗe ƙafafuwansa a hanyar neman abinci, ina ka bar karamcin Mai karamci! da arziƙin Mai yawan azurtawa da kyautar Mai yawan kyauta! Wanda Yake cewa a cikin Littafinsa: (kuma idan bayina sun tambaye ka game da Ni, To Ni kusa nake da su, ina amsa kiran mai kira idan ya kira Ni; to, su amsa Min nawa kiran, kuma su yi imani da Ni, don su shiryu) kuma Shi ne Mai cewa: (Sai na ce: “ku nemi gafarar Ubangijinku, lallai Shi Ya kasance Mai Yawan gafara ne() Zai saukar muku da ruwan sama mai yawa() kuma Ya daɗe ku da dukiyoyi da ƴaƴaye Ya kuma sanya muku gonaki Ya gudanar muku da ƙoramu).

    Zuwa ga wanda ya shiga cikin tsanani, abokan gaba suka haɗe masa, duniya ta yi masa ƙunci, ku ɗaga hannu, ku yi ƙanƙan da kanku, ku roƙi Allah kuna masu yaƙini da cewa Zai amsa muku, domin Allah Maɗaukakin Sarki yana ganin bigirenku, Ya san cututtukanku kuma Yana ganin hawayenku Yana jin kokenku, Shi ne kuma Mai ikon cin galaba a kan abokan gabarku, idan Allah Mai girma da ɗaukaka Ya yi nufin wani abu, sai Ya samar masa da sanadi.

    Don haka sai ku kyautata zato ga Ubangijinku, ku yi riƙo da LittafinSa da kuma Sunnar Annabinku tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, saboda a nan ne nasara da tabbatuwa suke, kuma dai da su ne ake samun kuɓuta ta gaskiya (Har yayin da Manzanni suka ɗebe ƙauna da imanin mutanensu, su kuma kafiran suka yi zaton an faɗa musu ƙarya ne game da zuwan azabar Allah, sai taimakonmu ya zo musu, sai Muka tserar da wanda Muka ga dama; ba kuwa za a kawar da azabarmu daga mutane masu laifi ba).

    Ya ku bayani Allah! Ahir ɗinku da ɗebe ƙauna da kuma fitar da rai daga rahamar Allah, domin su ne hanyar kafirci da ɓata, kamar yadda Ma’abocin girma da buyawa Ya ce: (Kada ku ɗebe ƙauna daga rahamar Allah, lallai ba mai ɗebe ƙauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai).

    Kuma Ya ce: (Ba wanda zai ɗebe ƙauna daga rahamar Ubangijinsa sai ɓatattun mutane), domin lallai ɗebe ƙauna daga rahamar Allah yana daga cikin munana zato ga Allah, Allah Ya ce: (Kuma idan Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya kuma juya kwuiɓinsa; idan kuwa sharri ne ya same shi sai ya zama mai yawan yanke ƙauna).

    Kuma ku kiyayi masu sa yanke ƙauna, masu kashe gwuiwa, masu sa cire rai daga rahamar Allah: Ka ce wa wanda ya cika zuciyarsa da munanan zace-zace, wanda yake ƙuntata mana duniya cewa: sirrin rabauta shi ne: Kyautata tsammaninka ga wanda ya halicci rayuwa ya kuma raba arziki.

    Imam ibnul Ƙayyim Allah ya yi masa rahama ya ce: Duk lokacin da bawa ya kasance mai kyautata tsammani ga Allah, mai kyautata fata gare Shi, mai dogoro na gaskiya da Shi, to, lallai Allah ba Zai tozartar da fatansa ba har abada, domin Shi Allah Tsarki ya tabbata a gare Shi baya tozarta fatan mai fata, Baya kuma lalata aikin mai aiki.

    Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da sauran Musulmi daga kowane laifi, saboda haka ku nemi gafararSa, lalle Shi ne Mai yawan gafara Mai yawan jinƙai.

    HUDUBA TA BIYU

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, kamar yadda ya dace da cikarSa da wadatarSa, kuma ina gode Masa godiya da za ta yi daidai da kyautarSa da baiwarSa. Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya a ƙasa da sama, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad BawanSa ne kuma MazonSa, ya kai maƙura cikin kamala ta bil’adama, tsira da amici da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waɗanda suka bi tafarkinsu da hanyarsu.

    Sa’annan, ku sani, ya ku bayin Allah! Lallai a cikin wuraren da kyautata wa Allah zato yake ƙarfafa, kuma ake rinjayar da fatanSa akan tsoronSa da fargabarSa, idan mutuwa ta zo wa bawa, ya yi dab da rabuwa da duniya, saboda lallai shi Mumini duk yadda ya kai da sakaci, duk yadda ya kusanci saɓo da munanan ayyuka, manya da ƙanana, ya sani cewa lallai Allah Mai ji ne Mai gani ga bayinSa, kuma Mai cikakkiyar masaniya ne game da rauninsu, Kuma Shi Mai tausayin su ne da suturta su.

    An karɓo daga Jabir bin Abdullahi Al’ansari Allah Ya ƙara musu yarda, ya ce: “Na ji Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kafin ya rasu da kwana uku yana cewa: (Kada ɗayanku ya kuskura mutuwa ta riske shi face yana kyautata wa Allah Maɗaukakin Sarki zato). Muslim ne ya ruwaito shi.

    Malamai Allah Ya yi musu rahama sun ce: “Wannan jan kunne ne game da yanke tsammani, da kuma kwaɗaitarwa a kan kyakkyawan fata a yayin cikawa, wato shi ne ya sa rai cewa lallai Allah Zai ji tausayin sa, kuma Ya yafe masa”. Sannan ku yi yi salati da sallama ga mafi alherin halittun Allah, Muhammad bin Abdillah, domin haƙiƙa Ubangijinku Ya umurce ku da haka, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: (Lallai Allah da Mala’ikunsa suna salati ga Annabi, Ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa).
    Ya Allah Ka yi daɗin tsira da aminci da albarka ga BawanKa kuma ManzonKa Annabinmu Muhammadu.

    Ya Allah Ka ƙara yarda da Halifofi guda huɗu, Jagorori nagartattu, Abubakar da Umar da Usman da Ali, da sauran Sahabbai goma da aka yi wa bushara da Aljanna, da waɗanda suka yi mubaya’a ƙarƙashin bishiya, da sauran Sahabbai baki ɗaya, da Tabi’ai, da waɗanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

    Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmi, Ka kiyaye shingen Addini, Ka taimaki bayinKa masu Tauhudi, Ya Mai tsananin ƙarfi. Ya Allah, Ka kawar da damuwar masu damuwa daga cikin Musulmi, Ka yaye ƙunci ga waɗanda ke cikin tsanani, Ka biya bashin masu bashi, Ka warkar da marasa lafiya daga cikin Musulmi.

    Ya Allah, Ka ba mu tsaro a ƙasashenmu, Ka gyara shugabanninmu da majiɓinta al’amuranmu, Ka ƙarfafi shugabanmu, majiɓincin al’amuranmu, Hadimin Masallatai biyu masu alfarma, Ya Allah! Ka tsawaita rayuwarsa cikin lafiya da kwanciyar hankali, da ni’ima mai yawa.

    Ya Allah, Ka datar da shi tare da Yarimansa amintacce, akan dukkan abin da zai kawo gyara ga ƙasa da al’umma, da kuma ɗaukaka ga Musulunci da Musulmai, Ya Ubangijin talikai.
    Ya Allah, Ka zama mai ƙarfafa da ba da nasara da taimako ga ‘yan’uwanmu masu Rauni.
    Ya Allah, Ka taimake su a Falasɗinu da duk inda suke, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah, Ka kare sojojinmu masu tsaron iyakoki da fagagemmu.

    Ya Allah, Ka kiyaye su da idanunka waɗanda ba sa barci, Ka ƙarfafe su da ƙarfi daga gareKa wanda ba ya gushewa, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah, Ka sanya mu cikin waɗanda za a tsawaita rayuwarsu, kuma ayyukansu su yi kyau, cikin lafiya da Imani da alheri da kyautatawa. Ya Allah, Ka sanya mafi kyawun ayyukanmu su kasance na ƙarshe, mafi alherin lokutan rayuwarmu su kasance ƙarshensu, kuma mafi kyawun ranakummu ranar da za mu haɗu da Kai, kuma Ka karɓi rayukanmu alhalin Kana yarda da mu, ba Ka fushi da mu, Ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah, Ka sanya zukatanmu su ratayu da yardarKa, Ka raya su da tsoronKa da kiyaye dokokinKa, Ka sanya mu cikin masu kyautata zato gare Ka a duniya da Ranar haɗuwa da kai, Ya Mafi tausayin masu tausayi. Ya Ubangijinmu, Ka ba mu kyakkyawa a duniya, kuma Ka bamu kyakkyawa a lahira, Ka tsare mu daga azabar wuta. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Manzanni, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Don karanta Tsarabar Makon Sabbai 2025 danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Wayewa Da Cigaba A Mesopotamia

    Wayewa Da Cigaba A Mesopotamia

    Greeks (Girkawa) su ne suka sawa ƙasar da take tsakanin kogunan biyu Tigris da Euphrates suna Mesopotamia. Wannan koguna sun kwaranyo daga duwatsu a ƙasar Turkey. Sun rabu gida biyu daga asalinsu sannan suka yi tafiyar mil 400 suka shiga Persian Gulf.

    Ƙasar Mesopotamia yanzu ita ce gabas ɗin Iraq. Wannan ƙasa ta Mesopotamia ana ce mata (Fertile Crescent) ta ƙunshi kudu maso gabacin Anatolia, da Syria da Iraq. Wanda suka fara kawo ci gaba ko wayewa a wannan wuri ko ƙasa su ne Sumerians. Mutanen da suka yi mulki a wannan ƙasa ta Mesopotamia tun daga farkon wayewa Clement (1936: 67) ya kasa su kashi shida:

    1. Sumerians wanda su asalinsu Caucasians ne da ƙasar Asiya, sun shigo ta Arewacin Mesopotamia sun yi mulki sama da shekara 6000 da suka wuce wato daga 4000 BC zuwa 2750 BC.
    2. Semites: Akkadian da Babylonian daga Arewacin Mesopotamia sun yi mulki daga 2750 BC zuwa 900 BC an kori Akkadiyawa, sannan daga bisani Babyloniyawa suka zo bayan wani lokaci. Sarakunansu da suka yi fice su ne Sargon I da kuma Hammurabi.
    3.  Assyrians su ma semite ne sun yi mulki daga 900 BC zuwa 612 BC su ma daga Arewacin ƙasar suka fito. Shahararrun sarakunansu su ne Sargon II da Sennacherib da kuma Assurbanipal 
    4. Chaldeans su ma Semite sun zo daga kudancin ƙasar sun yi mulki daga 612 BC zuwa 538 BC wanda ya fi shahara a cikinsu shi ne Nebuchadnezzar.
    5. Persians sun zo daga gabas su Ayrans (Indo-Europeans) sun yi mulki daga 538 BC zuwa 331 BC.
    6. Alexander mutumin Grika ƙasar Mecedonia ya zo ya cinye ƙasar da  yaƙi ya kafa daularsa (Empire) daga 331 BC 323 BC. Daga baya kuma Rumawa sun mallaki ƙasar kafin zuwan Musulunci.

    Sumerians su ne suka fara zuwa wannan ƙasa daga gabashin Asiya (Caucasians) shekaru 7000 da suka shige. Sun zauna a wannan tabkin kuma a hankali suka mulki maƙwabatansu kuma su ma asalinsu ɗaya na harshen Semitic. Kamar shekara 5000 da suka shige sai suka fara karɓe ƙasashen maƙwabtansu kuma suka wayar musu da kansu.

    Sumerians su ne mutanen farko da suka fara gina manyan garuruwa, babban birninsu yana da mutane 100,000 a wancan lokacin. Dalilin haka ne yasa ake cewa su ne suka fara wayewar kafa garuruwa (wato urban Civilization). Sumerians sun kafa Uruk wanda shi ne babban birni na farko a tarihin duniya sun kuma kafa Lagash da Ur (Adler p. 15).

    Sumerians sun shahara a tarihi saboda abubuwan da suka ƙirƙira. Su ne suka fara ƙirƙiro rubutu na ƙwarai (sophisticated). Su ne suka ƙirƙiro ƙasaitaccen gini na farko, wanda aka yi amfani da linta da ginshiƙai yadda iska ba za ta faɗar da shi ba kuma har yanzu ana amfani da dabararsu.

    Su ne ake zaton sun ƙirƙiro taya mai juyawa (wheel). Su ne kuma suka ƙirƙiro (gravity flow irrigation). Su ne suka fara yin tsarin makaranta a tarihin ɗan Adam, haka kuma su ne suka ƙirƙiro gasasshen tubali na gini (Adler p. 15). Sun ƙware a ƙirar kayan ƙarafa (bronze), da tukwane masu juyawa, da kekuna masu tayar ƙarfe da kwale-kwale da sassaƙa da manyan gininnika da kuma abinda ya fi kowane mahimanci –plow.

    An samu waɗannan bayanai a cikin dubunnan kayayakin da suka zana a wurare daban-daban. Sumerians sun shahara a harkar saƙa da rini kuma suna yin kaya na ƙasaita shuwagabaninsu na sa wannan kayayyaki masu kyau da burgewa. Wannan sana’oin sun haɓaka kasuwanci a garuruwan Mesopotamia da kuma cinikayya tsakanin su da sauran ƙasashe. Ana kai kayansu ƙasashe daban-daban. Kuma saboda wannan arziƙi da ƙasar take da shi shi ne yasa ake yin gagarumin biki na ƙasaita wanda ya sa ƙasar ta shahara (McNeill).

    Shekaru kamar 4200 da suka shige, wani mahari, kuma ɗan Semitic, Sargon (the Great) ya shigo ya cinye ƙasar Mesopotamia ya kafa mulkinsa da daularsa a garin Akkad kusa da garin Baghdad (ta wannan zamanin). Kafin zuwan Sumerians a garuruwansu suke babu sarki ɗaya da yake mulkar su,  shi ne ya haɗa ƙasar ƙarƙashin jagoranci ɗaya.

    Daular Akkadiyawa ba ta kai shekara 200 ba amma duk da haka sun yadda da wayewar kai irin na ƙasar Sumeria a gabas ta tsakiya. Kuma mulkinsu ya haɗa gabas ta tsakiya da kuma Misira. Bayan wannan daular ta Akkad aka samu daular Babylon daga nan kuma aka sami daular Assyria.

    Abinda yasa cewa aka yi Daular Akkad “Empire” ta farko saboda su ne suka fara mulkar  mutane daban a wata ƙasar. Mulkinsu ya faɗaɗa a doran ƙasa daga arewancin Iraqi zuwa kudancin ƙasar. Ita ce “Empire” ta doran ƙasa ta farko a tarihin duniya. Bayansu an samu “Empires” iri-iri a tarihin duniya (Howe 2002).

    Domin karanta Wayewar Farko danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Kaluluwa

    Kaluluwa

    Axillary yana nufin wani yanki ne a ƙarƙashin hammata wato kusa da nono, kuma akwai manyan jijiyoyin jini a wurin waɗanda suke haɗuwa da tsokokin wurin su zamo kaluluwa (lymph nodes). Ita kuwa kaluluwa wata jaka ce wacce take tattare ƙwayoyin cututtuka idan suka shiga jiki  domin ta hana su watsuwa zuwa sauran sassan jikinki. Don haka kaluluwa ba cuta ba ce, tana taimakawa jiki ne  wajen rage watsuwar ƙwayoyin cuta a cikinsa.

     Don haka duk wacce aka mata awon mammogram scan  ya nuna ‘axillary pain” ko “axillary inflammation”, to, yana nufin cewa akwai kumburin kaluluwa ne a wajen hammatarta, Ma’ana, ba yana nufin cewa ana ɗauke da  ciwon cancer nono ba ne. Yana nufin cewa garkuwar jiki tana ƙoƙarin yaƙi da ƙwayoyin cututtukan da suka shiga jikinki ne (lymphadenopathy).

    Jin ciwo a nono ba tare da kumburi ko zubar ruwan nono ba yana iya zamowa saboda zafin kaluluwar ne yake kai wa zuwa ga nono  (referral pain). Za a iya magance kaluluwarki wacce take sanya jiki jin zafin nono da hannu ne ta hanyar yin amfani da magungunan antibiotics ko antiviral ko antifungal idan aka gano ainihin ƙwayoyin cutar da suke haddasa kaluluwar.

    Sa’annan za ku iya gasa hammatar da nonuwan da ruwan dumi (warm compress) safe da yamma, ko kuma yin wanka da ruwan dumi. Bayan haka, a riƙa motsa hannuwan, samun isasshen hutu, shan maganin kashe raɗaɗi, tare da yawaita shan ruwa.

    Don karanta Zinariyar Awa Ga Jariranmu danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu