Matakan Kariya Daga Ciwon Hanta

0
20

Adadin mutane masu ɗauke da cutar hanta abin mamaki, ƙara yawaita yake duk kuwa da irin alluran riga-kafin da ake yi gami da wayarwa da mutane kai da muke yi a asibiti  da Social media.

Haka zalika sai dai wasu ciwon nasu ba dalilin virus ba ne na hepatitis wanda ake riga-kafi, dalilin matsala ne ta fatty liver…. wato kitse ya sarƙe hantar har ba ta iya aikinta yanda ya kamata, wanda hakan ke sa ciwon suga fara farautar mutum.

Kuma wannan matsalar ta fatty liver an fi samunta a mutane marasa jiki wato sirara dalilin raunin tunaninsu na cewa ai mu ko me muka ci ba ma ƙiba, wanda hakan ke sa su ciye-ciye iri-iri ba tare da suna sauraren jikinsu ba.

Shi yasa a ko yaushe ina faɗin kada ku ruɗu da siffar jikinku a waje, kar ku ruɗu da yadda kuke jin jikinku… Ta can ciki nan ne abin tunani. Shi yasa hatta hawan jini matasa na nan birjik da shi ba su san suna da shi ba domin ba ya sa wasu alamu, shi yasa ake ce masa SILENT KILLER.

Wasu kuma sun sani suna da hawan jini amma sun yi watsi da shi ko kuwa sun biye zantukan wasu can cewa ai suna da ƙananun shekaru ba sai sun sha magani ba, alhalin abunda ya kamata a yi ba a yi ba. To ai shi kenan in ya gama lalata muku jijiyoyin jini, ya haddasa muku ciwon ƙoda lokacin mutum ya farka sanda ya riga ya makaro.

Eh a bayanai na game da hanta! Na sha faɗa akwai healthy carrier da wasu kan ƙare rayuwarsu ba tare da ya rikiɗa ba, in me alaƙa da virus ce kenan kamar “Hepatitis B” ba tare da virus ɗin ya fara hayayyafa ba. Amma hakan bai nuna ba za ka iya yaɗata ba.

Idan ka je aka gwada ka ya nuna REACTIVE Ko POSITIVE ta tabbata akwai shi. Reactive duk yare ne daidai yake da Positive. Kamar yadda Non-Reactive ke nufin Negative wato babu abun.

To bayan test ya nuna Reactive kan hepatitis ba fa za a dogara da cewa ba ka da alamun ciwon ba ne kurum shi kenan ta wuce. A a akwai sauran aiki. Duk da sau tari na fi ganin laifin ƙananun ma’aikatan kula da lafiya a matakin farko (PHC) domin sun fi kusa da al’umma suke sakaci.

Kun fi kowa kusa da jama’a dole ku ke faɗa musu gaskiya ko da ‘yan uwanku ne a kan abin da ya dace su yi babu wani abu, sai dai in ba ka san me ya dace ka yi ba in ka samu case ɗin to ga shi zan sanar maka.

Gano ƙwayar hanta na da muhimmanci, ba kurum an yi ya nuna positive ba shi kenan ai babu alamu je ka cigaba da harkokinka. Me yasa ake gwajin ciwon hantar hatta a masu juna biyu?

Saboda idan an tabbatar a san yadda za a yi a kiyaye jaririn kada ya kamu wajen haihuwa da kuma bayan haihuwar. Haka nan wani ciwon hantar AUTO IMMUNE ne, wato garkuwar jikinki ce karan kanta ke lalata maka hanta a zaton ƙwayoyin cuta ne don haka faɗaɗa bincike nan ma wajibi ne.

Don haka abinda ya kamata a ce ku ‘yan uwan ma’aikatan lafiya shi ne: Bayan an yi ya nuna POSITIVE sai ku ce masa wane gwajinka na hanta ya nuna kana ɗauke da ƙwayoyin cutar don haka yanzu dole akwai buƙatar ƙarin gwaje-gwaje guda 2 biyu: (Profile Test na kalar hepatitis ɗin walau B ko C) wanda shi zai nuna cewa; Shin kana da garkuwar ciwon ma a jika kuwa? Shin ciwon ya fara hayayyafa? Shin za ka iya yaɗa ta ga wani? Ka daɗe da kamuwa ko kuwa ba ka daɗe ba? 

Daga nan idan mun ga bai fara hayayyafa ba kuma ba za ka iya yaɗawa ba, to za a yi gwajin aikin hantar (liver enzymes) inda daga nan ne za mu tabbatar Eh da gaske ba ka buƙatar a ɗora ka akan magani sai dai a ba ka shawara ka kawo mai ɗakinka in kana da aure ita ma a duba ta ko kuwa.

Idan kuwa gwajin ya nuna lallai cutar ta fara hayayyafa, ba ka da garkuwa kuma ta jima a jika, sannan gwajin sinadaran hantarka duk ya nuna sun hauhawa. To a nan za mu tura ka ka ƙara yo gwaji na uku wato na ƙarshe da zai nuna adadin lodin da virus ɗin ya yi cikin jininka (HBV DNA) inda kai tsaye za a ɗora ka akan magani ko mu tura ka asibitin da za ka je ka ga babban likita a ɗora ka kan magani a shawo kan matsalar tun kafin ta kwantar da kai ko ta yi maka illa.

‘Yan uwa ma’aikatan lafiya in kuka yi haka kun yi aikinku, in mutum ya ga ba zai je ba shi kenan ku dai kun yi naku ya rage nasa. Babu wanda ya cancanci ya mutu dalilin ciwon hanta sai dai in an makaro ba a gano da wuri ba.

Ko kuwa mutum ya zamto mai kunnen ƙashi ba ya ɗaukar shawara, domin ana magance shi muddin aka gano shi da wuri, kuma ka kiyaye ƙa’idojin magani kuma ka kiyaye dokokin abubuwa da likita yace ka ci da wanda yace kar ka ci, domin ita da kanta hantar za ta taimaka maka wajen gyara kanta da kanta. 

Sai dai in ciwon hantar auto immune ne wannan ya fi hatsari bai fiye jin magani ba har sai ta kai ga an yi wa mutum dashen wata hantar, wanda ke nuna ɗorewar rayuwarka sai wani ya mutu. Ko ko idan ki ka yi watsi da umarnin kowa kamar yadda nace, to tabbas za ki wayi gari wataran cikinki a kumbure, kafin kai wasa zance ya ɓaci lokaci guda kina iya mutuwa domin gubar da jikinki zai dinga saki ta ammonia ba za ki iya mata ba, sai ta fara lalata miki ƙwaƙwalwa ki hargitsa ta sannan ki mutu.

Ko hantar ta kumbura ki fama da jinya, an kashe kuɗaɗe, in ma ba ai muwafaƙa ba ki haɗu da cancer hanta musamman a masu hepatitis C ko kuma hantar ta lalace ta ru6e (cirrhodsis) yanda in ba dashe aka yi ba kowa ma ya san lokaci kurum kike jira.

Don haka lallai duk wanda ya san an taɓa gwada shi an same shi Positive/Reactive da hepatitis ya kamata ya miƙe tsaye ya je yai ƙarin gwaje-gwajen Hepatitis Profile testing ko da kuwa an shekara 10 da gwadakan domin hankali ya fi kwanciya da kyau. 

Wanda kuma bai san ma matsayinsa ba lallai ya dace ya je yai gwajin kamar yadda nakan ba da shawara a haɗa har da na sugar da Blood pressure duk a yi.

Domin karanta bayani akan ciwon kai na gado danna nan    

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu  

labarin da ya wuceAbubuwan Da Ya Kamata A Lura Da Su Kafin A Ɗora Mace Akan Magungunan Tazarar Haihuwa
Labarin na GabaYadda Za a Magance Ɓallewar Jini Bayan Haihuwa