CICCIKOWAR NONON MACE ALHALIN BABU CIKI, KO SHAYARWA, KO AL’ADA, KO SAKA KWAN HAIHUWA, KO YAYE (BREAST ENGORGEMENT IN WOMEN WITHOUT PREGNANCY, OR BREAST FEEDING, OR MENSTRUATION, OR OVULATION, OR WEANING)
Nonon mace yana iya ciccikowa ya kumbura, har ya riƙa yin ciwo ko kuma fitar da ruwan nono ko da kuwa ba ta ɗauke da ciki, ko tana shayarwa, ko lokacin al’adarta, ko lokacin saka ƙwan haihuwarta, ko lokacin yaye ba. Ga wasu dalilai da suke iya haifar da hakan:
- Rashin Daidaiton Zubar Ruwan Sinadarai (Hormonal Imbalance): Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace yana iya sanya nononta ya cicciko. Matsalolin rashin lafiya kamar Polycystic Ovary Syndrome (PCOS) ko ciwon jakar sinadarin thyroid (thyroid gland disorders) suna iya haifar da wannan yanayin.
- Laulayin Amfani Da Magunguna (Medication Side Effects): Wasu magungunan da mata suke yin amfani da su, kamar magungunan tazarar haihuwa (hormonal contraceptives) ko magungunan da suke haɓaka yawan sinadaran da mace take da ƙarancinsu (hormone replacement therapy), ko magungunan ciwon ƙwaƙwalwa (antipsychotics), ko magungunan ciwon damuwa (antidepressants), ko magungunan ciwon cancer (chemotherapy drugs), duk suna iya haifar da ciccikowa da zubar ruwan nono.
- Kumburin Nono Saboda Shigar Ƙwayoyin Cuta (Mastitis): A wasu lokuta, kumburin nono yana iya zamowa sakamakon shigar ƙwayoyin cuta a cikin nono ne (mastitis) ko da ba lokacin shayarwa ba.
- Ƙullutun Nono (Cysts or Fibrocystic Lumps): Kullutu zai iya fitowa mace a cikin nononta, sa’annan ya kumbura, ya haifar mata da taruwar ruwa da ciccikowar nono, ko rashin jin daɗi a nonon.
- Shiga Cikin Yanayin Tashin Hankali Ko Tsananin Rashin Hutu (Stress): Babbar damuwa ko rashin hutu suna iya shafar tsarin sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace, kuma hakan zai iya haifar da ciccikowar nono ko zubar ruwan nono.
- Bugewa Ko Samun Rauni A Nono (Breast Physical Trauma Or Injury): Idan mace ta sami rauni a nono ko yankin ƙirjinta, hakan yana iya haifar mata da ciccikowar nono ko zubar ruwan nono.
Idan ciccikowar nono ko zubar ruwan nonon ya daɗe, ko ya haɗu da jin ciwo mai tsanani, ko wasu alamu waɗanda ba a saba gani ba, to, ya kamata mace ta je asibiti domin a yi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa da ita.
Domin karanta Matakan Kariya Daga Ciwon Hanta danna nan
Edita; Rumasa’u M. kallamu