Tag: yadda ake

  • Menene Writer’s Block?

    Menene Writer’s Block?

    Writer’s block, yanayi ne da marubuci ko marubuciya ke jin kasalar kasa rubutu kwata-kwata, ko kuma an fara rubutun a ji an gaji ba a so a ci gaba. Haka nan writer’s block, na iya zama kufcewar basira yayin rubutu, wato a nemi basira sama ko ƙasa a rasa.

    Shin kun taɓa fuskantar irin wannan yanayin? Idan irin Haka ta faru me ya kamata marubuci ko marubuciya su yi?

    1. Barin rubutu na ɗan wani lokaci, ƙwaƙwalwa ta huta, wato a samu hutu. Yin hakan zai taimaka tunanin mutum na abin da ya kamata ya rubuta ya dawo.

    2. Sauya muhallin zama: wato mutum ya bar wurin da yake zaune zuwa wani sabon wuri daban, hakan zai taimaka masa sosai.

    3. Yin abubuwa da suka shafi nishaɗi, lamar wasannin mosta jiki, kallon fim, ko sauraron kaɗe-kaɗe.

    4. Tafiya, wato mutum ya bar wurin ya yake ya yi tafiya, da yake an ce tafiya mubuɗin ilimi.

    Danna nan don karanta Amfanin Yin Bincike A Rubutu

    Edita; RMK

  • Kira Ga Masu Son Yin Ƙiba

    Kira Ga Masu Son Yin Ƙiba

    Akwai wani kuskure da ke cigaba da faruwa tsakanin mata na shan maganin da suke kira Sha-ka-fashe domin son sui ƙiba. Wannan magunguna kala biyu da in kun haɗa kuke kira da sha-ka-fashe tabbas magungunan asibiti ne da aka ware musamman don wasu keɓantattun matsaloli amma ba sa ƙiba ba.

    Likitoci na amfani da su ne wajen tackling histamine receptors a ƙwaƙwalwa da kuma guda wajen raunana garkuwar jiki da bai wa jiki damar warkewa daga masassarar duka sassan jiki me miki, ko bai wa jiki ikon karɓar baƙon abinda aka dasawa mara lfy a jika kamar a masu ciwon ƙoda da aka yi musu dashe, ko amfani da shi dalilin cuttukan kafofin numfashi da kan shafi huhu har ma da cutar cancer.

    Shi wannan maganin na da illa a sanda kake yi wa mara lafiya amfani da shi don maganin cutuka kamar a me cutar cancer ko ƙanjamau wanda illar kuwa ita ce hura mutum (Teɓa) wato abinda muke kira da DRUG SIDE EFFECTS! yakan haddasa kumburin dukkan sassan jiki ya zamto mutum ya yi ƙiba.

    Wannan illar tasa ita ce ta sa mata ke rububinsa har suka halastawa kansu shi matsayin maganin sanya ƙiba. A yau za ka samu mace a bushe, ba ta da wata cima me kyau ko inganci kurum ƙarau-ƙarau a bushe amma ta samo shi ko kuwa wata ta ba ta shawarar nemo shin, tana ta sha kan za ta yi ƙiba.

    Mata sun matuƙar buɗe ido da shi ƙauye da birni, har ta kai ana samun wasu ƙananun jami’an lafiyar da ba su da ilimin magani suma suna rubutawa mata shi. To albishirin duk wacce ta ɗau wannan layin na shan sha-ka-fashe, Ina me tabbatar muku da ku kwan da shirin za ku haɗu da ciwon sugar (Diabetes mellitus) yes!

    Ko kwanaki na yi magana a game da yadda ‘yan mata 4 tun ba su kai ga aure ba suka jawo wa kansu DIABETES dalilin shan wannan maganin. Sun je suna fama da wasu complaints an duba su an ce suna da ciwon sugar. Ɗaya har tana haƙƙaƙe mun wani ma’aikacin jinya ne (Nurse) ya rubuta mata.

    Wanda kun ga wannan na daga cikin abinda ke nuna Trust wato yarda tsakanin jami’in lafiya da mara lafiyansa. Illa iyaka shi ya biyewa me take son cimmawa ba tare da ya yi aiki da iliminsa ya yi tunani ba, wanda wannan shi ne abinda da yawa ƙananun ma’aikatan lafiya ke yi. Duk da ku ma mutanen sanda ake faɗa muku gaskiya ba kwa ji sai kun shiga wahala.

    Don haka ina ƙara jaddada muku cewa ko da a yanzu kin daina sha kuma buƙatarki ta biya ƙibar da kika nema ta samu, to ina me shawartar ki da lallai duk bayan wata 4 ki ke zuwa gwajin sugar a jika. Domin idan matsalar ta yi KICK-IN ki tare ta da wuri kafin ta yi miki gagarumar illa. Kin riga kin cutar da jikinki.

    In ko kin ƙi to fa in kika yi wasa ciwon sugar ya shige ki ba ki fargaba akan ƙari ba har sai da alamu suka bayyana. Toh ba makawa akwai yiwuwar za ki mutu ba ki san ma waye kanki ba saboda tsananin jinya. Babban abin tsoron shi ne ciwon sugar ɗin da masu wannan halayyar kan haɗu da shi ba irin type 2 diabetes ba ne da ke jin magani ta baki in an sha.

    A a STEROIDS DIABETES ne me kama da Autoimmune wacce maganin ciwon SUGAR ma na shan ba ya yi sai dai mutum ya riƙa yin allurar insulin. Idan kuwa ba ku san nawa ce allurar insulin ba to ku tambaya ku sha labari don ku ji a sati 1 ta dubu nawa kuke buƙata a ƙalla. 

    Babu wani medical doctor da ya san me yake da zai taɓa ba wa mace shawarar shan wannan maganin don tana son ta yi ƙiba. Galibi wannan matsalar ƙananun ma’aikatan lafiya ke assasa ta domin 99% ba su san ma pharmcodynamic na magunguna ba su dai sun ga wani ya yi su ma sun rubuta.

    Don haka ku takawa wannan ɓarnar birki. Baya ga ciwon sugar, cutar hawan jini da gudardaji cikin jini (blood clots) duk matsaloli ne da ka iya faruwa dalilin hakan wanda bugun zuciya ko strokes na iya kashe mutum farar ɗaya. 

    Na faɗa zan ƙara maimaitawa; Ba a taɓa samun ƙiba ta hanyar magani, har yau har gobe babu wannan maganin a duniyar likitanci da aka yi shi don yasa a yi ƙiba, ƙiba a abinci da kwanciyar hankali take sai kuma in ka gada. Duk maganin da za a ba ka in dai ba MULTIVITAMIN da zai sa ku kama abinci da kyau ba ko ƙibar ta samu to tabbas an shiga kame-kame. Ko shi kun ji na ce cin abinci zai sa,  kun ga kenan ba Multivitamin ne zai sa ƙiba ba abinci ne.

    Don haka ku daina sa wa jikinku unnecessary products walau na Bature ko supplements. Kowa ya yi wa kansa faɗa, in ma kina sha to ki watsar da su tun wuri. In kuma an ƙi ji toh ba a ƙi gani ba. Kai kuma duk wacce ta zo da ƙorafin tana ramewa to ba magani ake tunani ba ƙoƙari ma za kai ka gano dalilin ramewar tukun.

    Domin cutar HIV, Depression, Diabetes, Cancer, Tuberculosis da sauransu duk na daga cuttukan da ka iya sanya rama a jika. Meye amfanin magani in ba ka magance tushen matsala ba. Ba ma MATA ba HAR DA MAZA masu sha kuma ku shiga taitayinku illa guda zai muku.

    Don Karanta Sinadarin Ka-fi Suga danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Siffofin Shugaban Da Ya Kamata Mu Zaɓa

    Siffofin Shugaban Da Ya Kamata Mu Zaɓa

    Assalamu Alaikum

    Ya ku ‘yan uwana al’ummar Najeriya masu daraja! Hakika na yi bincike lokaci mai tsawo a cikin Alkur’ani mai girma da littattafan tafsirai daban-daban, musamman akan ƙissar Bani Isra’ila, Annabi Shamwilu da Daluta; da ƙissar Annabi Musa, da ƙissar Annabi Dawud; da kuma Hadisan Manzon Allah (SAW) da littafan addinin Musulunci waɗanda suka yi magana akan shugabanci da muhimmancinsa da kuma siffofin irin shugaban da ya kamata ya shugabanci al’umma, domin a samu ingantaccen shugabanci nagari wanda zai amfani al’ummah baki ɗaya.

    Kuma kowa ya ji daɗi, a samu zaman lafiya, haɗin kai da cigaba mai ɗorewa. Na binciki littafai irin su Ahkam Al-Sultaniyyah na Imam Al-Mawardi da Ahkam Al-Sultaniyyah na Imam Abu Ya’ala da As-Siyasah Ash-Shar’iyyah na Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah, da sauran littafai muhimmai, ire-irensu, waɗanda suka yi magana akan shugabanci da siffofin shugaba nagari.

    A cikin binciken da na yi, alhamdulillahi, na fitar da siffofi guda ashirin (20), waɗanda Allah da Manzonsa (SAW) da kuma malamai suka bayyana; siffofin da ya kamata a ce duk shugaban da zai shugabance mu yana da su. Shawarwari ne da jan hankali, waɗanda addinin Musulunci ya bai wa al’umma, waɗanda ya kamata su yi la’akari da su, musamman wurin zaɓen shugaba, in dai har suna son samun walwala da ci gaba a cikin al’ummarsu.

    Waɗannan shawarwari haƙiƙa, idan al’umma ta bi su wurin zaɓen shugabanni, to za su yi nasara kuma su ji daɗi. Amma kuma idan al’umma suka ƙi bin waɗannan shawarwari, suka bi son zuciyarsu, to tabbas sai sun yi dana-sani game da sha’anin lamarin shugabancinsu.
    Saboda sha’anin shugabanci ba abun wasa ba ne da za mu yi wasa ko sakaci da shi, ko kuma mu taƙaita shi akan la’akari da wata jam’iyyah ta siyasa, ko kuma la’akari da yaren shugaba ko ƙabilarsa, ko yankin da ya fito, ko kuma mu mayar da shi akan tafarki na karɓa-karɓa.

    Wanda duk waɗannan hanyoyi ne na shirme da shiririta! A sha’anin shugabanci, cancanta kawai ake bi da dacewa. Wanda ya cancanta kuma ya dace, shi ne ya zama wajibi mu zaɓa. Idan muka kuskura muka zaɓi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, to lallai mu sani, za mu sha wahala a nan duniya, kuma lahira za mu amsa tambayoyi a gaban Allah, akan duk wata irin gudunmawa da muka bayar wurin ɗora shugaban da muka san bai dace ba akan al’ummah!

    Ya ku jama’ah! Ku sani, lallai sha’anin shugabanci ya wuce haka, kuma yafi ƙarfin haka. Bai kamata mu taƙaita maganar shugabanci da wani son zuciya ba, kasancewar duk wanda zai shugabance mu, lamarin rayuwar mu gaba ɗaya ya rataya ne akan yanayin irin shugabancin da ya yi mana.

    Duk wanda ya zama shugaba a cikin mu, ya zama wajibi ya kare addininmu, da rayukanmu, da dukiyoyinmu, da hankalin mu da nasabar mu ko dangantakar mu, tare da ƙoƙarin samar mana da sauran ababen more rayuwa, domin rayuwar mu ta inganta, mu ji daɗin bautawa Allah cikin hayyacinmu.

    To tun da haka ne, kenan ya zama dole, kuma wajibi mu san wanene zai shugabance mu. Ga siffofin shugaban da ya kamata ya shugabance mu kamar haka:

    1. Dole ne duk shugaban da za mu zaɓa ya zamanto yana da ilimi, yana da hikima, yana da hangen nesa da ƙwarewa (Knowledge, wisdom, vision and competence).

    2. Dole ne shugaba ya zamanto mai ƙarfi a jiki, mai kazar-kazar, mai kwarjini (Power/Strength).

    3. Dole shugaba ya zamanto yana da hikima wurin zartar da hukunci, domin ya iya zartar da hukunci ingantacce (Sound Judgement).

    4. Dole shugaba ya zamanto mai haƙuri, mai juriya, sannan mai yafiya (Patience, Tolerance and forgiveness).

    5. Dole shugaba ya zamanto adali kuma marar nuna bambanci tsakanin ‘yan ƙasa (Justice and fairness).

    6. Dole ne shugaba ya zamanto yana da fasaha, hikima da basira wurin isar da saƙo zuwa ga al’umma (Communication skills).

    7. Dole ne shugaba ya zama mai tsoron Allah (Piety/At-Taqwah).

    8. Dole shugaba ya zama mai sauƙin kai, ba mai kafiya ko kangara ba, mai kwarjini da kazar-kazar sannan mai cikakken hankali da tunani (Simplicity, emotional and spiritual intelligence).

    9. Dole shugaba ya zamanto mai gaskiya ba abun zargi ba (Truth).

    10. Dole shugaba ya zama lafiyayye; mai lafiyar ƙwaƙwalwa da ruhi da jiki (Sound and good health/Soundness in mental and physical condition).

    11. Dole ne shugaba ya zamanto mai amana da iya riƙon amana kuma mai mutunci (Trust and Integrity).

    12. Dole be shugaba ya zama mai tuntuɓa kafin ya zartar da wani abu (Consultation).

    13. Dole ne shugaba ya zamanto mai iya zartar da hukunci bayan ya tuntuɓi masu ilimin fannin, ba tare da tsoro ko fargabar kowa ba (Decisiveness/Decision making ability after consultation).

    14. Dole ne shugaba ya zamanto mai dogaro tare da tawakkali ga Allah, ya zamo jarumi, marar tsoro, kuma mai cikakken yaƙini (Dependence on Allah, courage, bravery and confidence).

    15. Dole ne shugaba ya zamanto mai sadaukarwa wurin kowane lamari (Spirit of sacrifice).

    16. Dole shugaba ya zama mai cika alkawari, kuma mai mutunta alƙawurran da ya ɗaukar wa al’umma, ba mai karya alkawari ba (Honouring the pledge).

    17. Dole ne shugaba ya zamanto mai kyauta, mai alkhairi, karimi ba marowaci ba (Generosity).
    18. Dole ne wanda za’a zaba ya zamanto shugaba ya kasance zai iya, kar mu zaɓi wanda muka san cewa ba zai iya ba, ko dukkanin alamu sun nuna ba zai iya ba (Capacity to govern).

    19. Dole ne shugaba ya zama yana ƙoƙarin binciken kansa da kuma dukkanin ma’aikatansa. Dole ya zama mai tsantseni da kula da dukiyar baitul mali. Kar mu zaɓi shugaban da muka san cewa zai yi ƙoƙarin arzurta kansa da dukiyar al’umma. Kuma kar mu yarda mu ɗora almubazzari akan dukiyar ƙasa (Accountability/Ihtisab).

    20. Dole ne shugaba ya zamanto mai faɗa da cikawa; wanda zai yi wa al’umma aiki, ba surutun banza da yawan magana ba. Kar mu ɗora wanda muka san mai faɗa ne kawai, amma ba zai cika ba (Action not just words).

    Ya ku ‘yan uwa! Waɗannan kaɗan kenan daga siffofin shugaba nagari da ya kamata mu zaɓa a wannan zaɓe mai zuwa da ikon Allah. Tun daga zaɓen shugaban ƙasa har zuwa na Gwamnoni; kar mu yarda mu yi sake, ko kuma mu zaɓi shugaban da muka san bai cancanta ba ko bai dace ba.

    Ku sani, ana maganar Najeriya ce fa, ƙasar mu ta gado; ƙasar da muke so kuma muke ƙauna. Ƙasar da ba mu da wani wurin zuwa idan ba ita ba. Kasa mai arziƙi, wadata da yalwa, amma rashin samar da shugabanci nagari ya sa muna ta shan wahala. Kasa mai ɗauke da al’ummomi har mutum sama da miliyan dari biyu.

    Kasa irin wannan, wallahi bai kamata mu kasance masu sakaci wurin zaɓar mata shugabanni ba. Ko kuma mu rungume hannu, muna kallo a rinka ɗora mana shugabannin da mun san ba za su iya ba, ko kuma ba su dace ba, ba su cancanta ba! Ya zama wajibi mu zaɓi shugabanni nagari, waɗanda suke son mu muke son su, suke yi muna addu’a muke yi masu addu’a.

    Ba shugabannin da za su rinƙa zagin mu ba muna zaginsu, suna la’antarmu muna la’antarsu. Don haka, muna kira ga al’umma baki ɗaya cewa, in dai har da gaske ne muna son Allah ya taimake mu, ƙasar mu ta gyaru, to sai kowa ya tashi tsaye wurin yin abun da ya kamata wurin zaɓen shugaba nagari, tare da yin addu’ar Allah ya kawo mana sauƙi, ya fitar da mu daga tsananin da muke ciki.

    Mu gyara halayenmu da ɗabi’unmu, kuma mu yi ta addu’a da roƙon Allah ya arzurta mu da shugaban ƙasa nagari a wannan zaɓe mai zuwa; shugaba mai tausayi, mai fahimta, mai son al’umma, mai ƙwarin jiki da lafiyar jiki da ta hankali, mai son haɗin kan ƙasa, mai kishin Najeriya da ‘yan Najeriya da arewa da kowane yanki baki ɗaya; mai sauƙin kai da karɓar shawara, sannan kuma ƙwararre wurin iya mulkin ƙasa, wanda ba ɗan koyo ba kuma ba sabon shiga ba.

    Mu yi fatan irin wannan shugaba Allah ya ba shi nasarar cin zaɓe a wannan zaɓe mai zuwa, kuma Allah ya ba shi nasara wurin aikata alheri a cikin shugabancinsa. Sannan game da abinda yake faruwa a ƙasarmu, game da canjin kuɗi a halin yanzu, ina kira da mu yi haƙuri. Mu sani, babu wani gyara da za a yi a duniya, kuma a ko’ina ne, ba tare da an sha wahala ba! Mu bincika da kyau mu gani, duk wata ƙasa a duniya, mu koma mu bibiyi tarihin manyan ƙasashen duniya, kafin su kai matsayin da suke akai a yau, sai da suka sha wahala sosai!!

    Kai a wasu ƙasashen ma, wasu jinin su suka ba da, balle wai don muna shan wahala saboda canjin kuɗi. Malamai magana fa ake yi ta gyaran Najeriya da izinin Allah da iyawarsa! Mu yi haƙuri har a yi zaɓe lafiya a gama lafiya. Kar mu yarda a zuga mu, ko a harzuƙa mu, ko a yi amfani da mu, mu tayar da hankali, ko mu yi hargitsi, ko mu yi wata zanga-zanga ko hayaniya.

    Mu sani, komai mai wuce wa ne da yardar Allah, kuma da izinin Allah, wata rana sai labari. Amma dai mu yi ƙoƙari mu zaɓi shugaba nagari a ranar zaɓe, wanda da ikon Allah, Allah zai yi amfani da shi wurin taimakon Najeriya da taimakon dukkanin ‘yan ƙasa baki ɗaya.
    Kar mu yarda mu biye wa ‘yan wasu yanki masu ƙone-ƙone da kashe-kashe da tayar da hankula da zanga-zanga, domin mu irin wannan aiki sam ba tarbiyyar mu ba ce.

    Sannan kar mu yarda mu biye wa wasu Gwamnoni masu ƙoƙarin harzuƙa mu da zuga mu akan mu yi tawaye, da sunan wai saboda talakawa suke yi, alhali duk wani mutum mai hankali ya san ba domin talakawa suke yi ba, domin kawunansu kawai suke yi. Kar mu taɓa yarda da duk wani abu da zai tayar da hankalin ƙasarmu mai albarka!

    Sannan mu sani, duk mai hankalin da ya kai shekarun zaɓe, tabbas ya san dacewa da cancantar wanda ya kamata ya zaɓa, kar ka yarda da wai wani yasa ka zaɓi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, domin mun san irin wahalhalun da muka sha, da irin bala’in da Allah ya jarabe mu da shi. Kuma masu hikima sun ce idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!

    Kuma idan wani yasa ka zaɓi wanda bai dace ba kuma bai cancanta ba, to ka sani, a ranar da za ka amsa tambayoyi a gaban Allah, wannan mutum ko waye shi ba ya wurin bare har ya cece ka daga azabar Allah! Wassalamu Alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.

    Domin karanta Haƙƙoƙin Mabuya Akan Shugabanni danna nan
    Edita; Rumasa’u M. Kallamu
  • Waƙar Ilimi

    Waƙar Ilimi

    Waƙar ilimin zamani ta Mu’azu Haɗeja

    1. Gishiri in ba kai ba miya,
    Ilimi mai gyaran zamani.

    2. Jama’armu ku jawo hankulanku,
    Mu lura da halin zamani.

    3. Iko, mulki, ƙarfi, duka,
    Na ga wanda ya ƙaddari zamani.

    4. Ilimi shi ke gyaran ƙasa,
    Har a santa a wannan zamani.

    5. Babu jin kunya gun mai limi,
    Jahili shi ke ta wuni-wuni.

    6. Yanda kaska ke tsotsar jini,
    Haka jahilci gun zamani.

    7. Da tsiya da talauci duk suna,
    Gun da jahilci ya yi sansani.

    8.Wa’azinmu ga mai karɓa duka,
    Masu murnar gyaran zamani.

    9. Masu son lardinmu ya ɗaukaka,
    Bisa kan juyawar zamani.

    10. Kar su fara faɗar da-na-sani,
    Da mun yi karatun zamani.

    Allah ya gafartawa Malam Mu’azu Haɗeja da sauran magabata.

    Danna nan don karanta saƙo cikin waƙa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Ɓacewar Ashanar Hannu Ta Tazarar Haihuwa

    Ɓacewar Ashanar Hannu Ta Tazarar Haihuwa

    Abu ne mai yiwuwa ashanar hannu wacce ake soka ta a cikin tsokar damtsen mace domin yin tazarar haihuwa (contraceptive implant), ta ɓace ta yadda idan aka zo cire ta, a kasa ganinta. Ana kiran wannan yanayin “implant migration” ko “deep insertion” a likitance.

    Abubuwan da suke haddasa ɓacewar ashanar hannun su ne:

    1. Soka Ta A Can Cikin Tsokar Hannu (Deep Insertion): Idan ma’aikacin lafiya ya yi kuskuren soka ashanar hannun a can cikin tsokar damtsen mace, maimakon a kasan fatar hannunta, to , hakan zai iya haifar da ɓacewar ta, har a kasa ganinta a lokacin da aka zo cirewa.   
    1. Matsawa Daga Wurin Da Aka Soka Ta (Migration): Tsinken ashanar hannu zai iya motsawa zuwa wani ɓangaren tsokar hannun mace ko kuma wani ɓangaren jikinta daban. Abinda yake sanya motsawar shi ne yawan motsa hannun (frequent movement), ko, bugewa (trauma), ko takurewar tsokar (muscle contraction).
    1. Sauye-Sauyen Ƙibar Jiki (Weight Changes): Idan mace ta ƙara ƙibar jiki , ko kuma ta rame sosai bayan an sanya mata ashanar hannu, to, wannan sauyin jikin zai iya haifar da motsawar ashanar daga asalin gurin da aka soka ta. 
    1. Rashin Soka Ashanar Yadda Ya Kamata (Improper Insertion Technique): Idan ma’aikacin lafiya wanda ya yi aikin soka ashanar bai soka ta yadda ya kamata ba saboda rashin ƙwarewa ko kuma kuskuren sokawar, to, mai yiwuwa ne ashanar ta motsa daga wurin da aka soka ta.

    Idan ashanar hannu ta motsa daga wurin da aka soka ta har aka kasa gane inda take a lokacin da za a cire ta, to, hanyoyin da za a iya bi wajen gano ta su ne: 

    1. Mammatsa tsokar hannun (Physical Examination): Ma’aikaciyar lafiya za ta mammatsa tsokar hannun a daidai wurin da soka ta da kuma tsokar kewayen wurin, har a gano ta.
    1. Ɗaukar Hoton Wurin (Imaging Techniques): Idan aka kasa gano ashanar hannun ta hanyar mammatsa tsokar hannun, to, mataki na gaba shi ne a yi hoton ultrasound scan na hannun. Wannan dabarar ta fi yin tasirin gano ɓataccen tsinken ashanar hannu, domin za a ganta ƙiriƙiri. Sa’annan wannan dabarar ba ta ƙunshi yanka jikin mace ba (noninvasive technique) wajen nemo ashanar.
    1. Yin Aikin Tiyata (Surgical Removal): Da zarar an gano wurin da ashanar hannun take, to, za a iya yin aikin tiyatar yanka wurin domin a cire ta. Yawanci akan yi allurar kashe raɗaɗi (anesthesia) idan za a yi aikin tiyatar.

    Ana buƙatar idan mace ta sanya tsinken robar ashanar hannu ta tazarar haihuwa, to, ta riƙa shafa wurin lokaci-lokaci domin tabbatar da cewa ashanar ba ta motsa daga wurin da take ba. Idan kuma ta ji alamun cewa ashanar ta motsa, to, sai ta sanar da ma’aikatan lafiya domin ɗaukar matakin da ya dace cikin gaugawa.

    Don karanta Contraceptive Implants : Ana Kiranta Ashanar Fata Da Hausa Wannan Wata Hanya Ce Da Ake Dasa Wani Roba Ƙarami A Hanun Mace

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Hani Akan Yin Gulma

    Hani Akan Yin Gulma

    Gulma: Shi ne ɗaukar zancen wani mutum zuwa ga wani mutum ba tare da yardar sa ba, don tayar da husuma (faɗa).

    Saboda haka, addinin musulunci, addini ne na haɗin kai (zukata), addini ne na zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda yake so ya ga ya haɗa zukatan mutanensa baki ɗaya a duk inda suke a cikin duniya.

    Haka kuma Allah (Subhanahu wata’ala) da manzon Sa annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) sun yi mana bayanin sharrin da gulma take iya haifarwa misali kamar su raba kawunan mutane, husuma ko jayayya, munafunci da dai sauran su.

    Saboda haka ne ma Allah (Subhanahu wata’ala) ya ja kunnen mu da aikata haka ta harshen annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) kamar yadda ya faɗa;

    لا يدخل الجنة نمام. Magulmaci (annamimi) ba zai shiga (gidan) Aljanna ba”. 

    Saboda haka, ka ga wannan hadisin ya ƙara nuna mana sharrin da gulma take iya haifarwa, saboda za ta iya hana mutum shiga gidan aljanna matuƙar ya mutu a wannan hali na gulmace-gulmace . Haka kuma gulma ko ƙarya ta wani fannin tana da ɗan amfani kaɗan, amma kuma ga wanda yake son ya ga ya haɗa kawunan wasu mutane waɗanda suke gaba da juna.

    Misali idan akwai wasu mutane da ba sa jituwa da juna, to ya halatta ko kuma babu laifi akan wani mutum sai ya tashi ya samu wani mutum daga cikin su ya gaya masa magana mai daɗi haɗi da wata kyauta idan yana da hali, sai yace da shi “ga shi abin ka wane ne yace na kawo maka, sa’annan kuma yana gaishe da kai, haka kuma sai ya sake samun ɗayan shi ma ya faɗa masa haka.

    Amma kuma a wannan lokacin gulma ta yi ƙaura a tsakanin mata da mata ta koma maza da maza ko maza da mata, wanda a lokutan baya da suka wuce an fi samun mata da gulmace-gulmace irin na su, amma kuma a yanzu haka wai har ma maza su ma suna yin gulmace-gulmace, kai! Hm! Wai faɗuwar girma ne ga raƙumi ya shanye ruwan ɗantsako.

    Bugu da ƙari kuma, duk me yin gulma shi ne wanda ba shi da aikin yi, saboda wanda yake da abin yi a gabansa, ba shi da lokacin yin gulmar wani mutum . Saboda haka, gulma ta wani fannin tana da alaƙa da hassada.

    saboda idan wani mutum suna faɗa da wani mutum ko kuma wani mutum Allah ya ɗaukaka shi, sai ka ga wani mutum yana faɗar wata magana mara kyau a gare shi, haka kuma sai ka ga yana ɗaukar maganar wani mutum yana faɗawa wani mutum, don ya ga ya haɗa su husuma ko kuma rashin jituwa a tsakanin su.

    Haka kum akwai hanyoyin da za a iya magance gulmace-gulmace da dama, misali idan wani mutum ya kawo maka gulman wani mutum, sai ka ƙyale shi har sai ya gama zayyano maka dukkanin zantukan sa, bayan ya gama, sai kawai kace da shi “to ai wannan gulma ce.

    Sa’annan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) haɗi da manzon Sa annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) sun hana aikata haka, saboda haka daga yau kada ka sake kawo min irin wannan maganar, sa’annan kuma ka tuba ka daina aikata haka tun kafin ka haɗu da fushin Allah”, da dai sauran su.

    Danna nan don karanta hani akan yin gori

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Hani Akan Yin Gori

    Hani Akan Yin Gori

    Gori: shi ne yin isgili, shaguɓe, habaici akan wani mutum, wanda yake da kashi a gindinsa, ko kuma wanda yake da wata matsala kamar sata ko zina.

    Saboda haka, addinin musulunci ya hana yi wa wani mutum gori akan wani abu, saboda haka ne ma Allah (Subhanahu wata’ala) ya hana yin gori akan wata kyauta da wani mutum ya yi wa wani mutum, idan kuma mutum ya yi wa wani kyauta, sai kuma wata rana kwatsam ya goranta masa, to kyautarsa ta ɓace, ma’ana ba shi da ladan kyautar da ya yi har abada.

    Haka kuma, an hana yin gori ga wani mutum wanda yake aikata wani laifi a baya, ko dai ta hanyar daina  aikata laifin ko kuma ta hanyar tuba, misali idan wani mutum yana yin zina ko sata a baya, sai kuma yanzu ya gane kuskuren aikata haka, sai ya tuba. To addinin musulunci ya hana kowane musulmi ya yi masa gori akan irin abin da yake aikatawa a baya, idan wani abu  ya haɗa su na cacar  baki ko faɗa kamar “him! aikin banza ai daman can shi ɓarawo ne ko mazinaci” da dai sauran su.

    Saboda haka, akwai wata mace kirista ta musulunta, to sai wani abu ya haɗa su da wata mace musulma, to kuma ita wannan ita ce ba ta da gaskiya (musulmar), sai ta kalli wancan macen, sai tace da ita “Um! ki rufewa mutane baki tubabbiya kawai, kin gama iskancinki yanzu kin zo za ki faɗawa mutane maganganun banza”. Sai ita waccan macen ta yi kamar ta fita daga musulunci, saboda irin waɗancan maganganun da ake faɗa mata, amma da yake addinin ya shiga cikin zuciyarta, sai ta kau da kai.

    Har ila yau, idan wani mutum yana aikata saɓon Allah kamar su ƙarya, ha’inci, gori, shirka, algus, bokanci ko dabo, gulma, da dai sauran su, to idan wani mutum ya musulunta akan irin waɗancan abubuwan da yake aikatawa ko ya tuba daga aikata haka, to shari’ar musulunci ta hana kowane mutum ya faɗawa wani mutum baƙaƙen maganganu kamar su cewa ai maƙaryaci ne, mushriki ne, boka ne, magulmaci ne, maha’inci ne, mazinaci ne da dai sauran su.

    Saboda haka, ya kamata  musulmin da yake aikata haka, ya yi gaggawar daina aikatawa, saboda samun damar tserata daga fushin Allah (Subhanahu wata’ala) da manzon Allah (Salldlahu alaihi wasallam).

    Saboda dukkanin wanda yake yi wa wani mutum gori akan wani abu da ya ba shi ko kuma wani abu wanda wani mutum yake aikatawa mara kyau, sai kuma ya tuba ya daina aikatawa, to wanda yake yi musu gori akan haka, to zai iya shiga cikin fushin Allah (Subhanahu wata’ala) matuƙar bai daina aikata haka ba.

    Saboda haka gori ba shi da wani amfani ga musulmi mai hankali da tunani, saboda addinin musulunci ya yi hani akan aikata haka. Sa’annan kuma ko a a hankalce da tunani, to gori ba shi da wani amfani, saboda a wani lokacin gori yana kamanceceniya da tonon silili, wanda shi ma aikata haka ba shi da amfani ga musulmi.

    Haka kuma tonon silili da wasu mutane suke yi wa junan su, wannan kuskure ne, haka kuma ba shi da amfani ga addinin musulunci. Har ila yau, yunƙurin binciken laifin wani mutum wanda yake aikatawa ko kuma wanda ya daina aikatawa, to yin hakan kuskure ne, saboda idan wani mutum ya shagala da binciken laifin wani mutum, sai kuma ya manta da laifin kansa, to zai yi mutuwar biyu babu ko kuma kamun gafiyar ɓaidu.

    Saboda haka, yana da matuƙar mahimmanci akan musulmi dukkanin abin da zai aikata, to ya yi ƙoƙarin sanin hukuncin aikata haka da fatan Allah ya sa mu dace, sannan kuma mu nisanci aikata haka, haka kuma yana da matuƙar amfani ga mahukunta su ɗauki wani mataki ko tsari ga masu aikata haka, don samun ci gaban addinin musulunci baki ɗaya.

    Danna nan don karanta sauro halittar Allah mai ban Al’ajabi

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Fassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 10 Rajab 1446 AH 10 January 2025

    Fassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 10 Rajab 1446 AH 10 January 2025

    Mai Huɗuba:
    Sheikh Dr Saleh Bin Abdullahi Bin Humaid

    Mai Fassara:
    Dr Abdullahi Yunusa Machina

    Shugaban Sashi
    Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Transcribe
    Aminu Bashir

    Huɗubar Masallaci Mai Alfarma
    Sheikh Dr. Abdullah Awwad 12/06/1446H

    HUƊUBA TA FARKO
    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Masa, muna neman taimakonSa da gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunammu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah Ya shiryar, to, babu mai ɓatar da shi, kuma duk wanda Ya batar, to babu mai shiryar da shi.

    Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. (Ya ku waɗanda kuka ka yi Imani, ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kusa Musulmi)

    Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matars (Ya ɗaga shi, kuma ya yaɗa maza da mata masu yawa daga gare su, kuma ku ji tsoron Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye yanke zumunci, lallai Allah Mai kula da ku ne)

    (Ya ku waɗanda kuka yi Imani, ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacce take daidai, Zai kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubbanku, kuma duk wanda ya yi ɗa’a ga Allah da ManzonSa, to haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)

    Bayan haka:
    Lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi sharrin lamura su ne ƙirƙirarru, kuma kowane ƙirƙirarren abu bidi’a ne, kuma kowace bidi’a ɓata ce.

    Bayan haka:
    Ya ku mutane! Lallai Allah Wanda hikimarSa ta ɗaukaka, Ya halicce ku ne domin ku bauta Masa, kuma Ya kallafa muku ayyukan da za ku iya, don haka, ku aikata su. Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umarninsa, da nisantar abin da ya hana da manyan zunubai, kuma ku yi la’akari da abin da ke cikin Alƙur’ani mai girma na ababen lura, haƙiƙa Allah ya saukar da shi a gare ku don ku bi shi, domin lallai yana daga cikin mafi girman tanadi na samun tsira.

    Saboda abin da yake ƙunshe da shi na farillai da mustahabbai da halacci da haramci da wa’azozi da jan kunne, to me ya sa zukata ba sa bin umarninsa, kuma ba sa barin abin da ya hana kuma ya tsawatar, kuma ba sa jin tsoron wanda ya san bayyane da ɓoyayye cikin ayyukan bawa, da sirrikansa da kuma zahirinsa!

    Haƙiƙa gafala ta yi musu katutu, kuma sha’awace-sha’awacen zukata sun kautar da su daga lura da ababen suka saɓa musu, sai su ka ji daɗin ɗanɗanon ɓarnarsu, kuma suka jahilci ɗacin sakamako da za a musu a lokacin mutuwarsu, don haka, sai suka doge a kan saɓonsu, ba su ji tsoron yini da za a damƙe su ta ƙafafunsu da makwarkwarɗarsu ba.

    Ranar da za a ninka azaba ga wanda ya bar salla kuma ya tozarta ta, wanda ya yi sakaci game da lamarin zakka kuma ya ƙi ba da ita, wanda ya keta alfarmar watan Ramadana ya sha azumi a cikinsa, wanda ya jinkirta faralin Hajji alhalin yana da ikon yi kuma ba tare da wani uzuri ba.

    Ranar da za a shayar da mashayin giya da ruwan ɗiwa, a kwankwaɗa masa abin da zai ɗanɗani kaito da kuɗarsa da shi daga ruwan mugunyar ‘yan wuta. Ranar da za a sako harasan wuta ga mazinata da fajirai, kuma a dake su da bulalunta ta gabansu da bayansu.

    Maciyin riba kuma ya ci daga bishiyar zaƙƙum, lallai zina da cin riba ba su taɓa bayyana a cikin wasu mutane ba face sai sun sakko wa kansu da azabar Allah, muna neman tsarin Allah daga fushinsa da azabarsa, kuma azzalumai za su wanzu a cikin iska mai tsananin zafi da kuma tafasasshen ruwa, da kuma inuwa ta turnuƙun hayaƙi.

    Ku saurara! Lallai duk wanda ya shagala da kansa, to, ba zai samu lokacin aibata waninsa ba, kuma duk wanda gazawarsa ta dame shi, to, idanuwansa za su makance daga ganin gazawar waninsa da abin da yake aikatawa, don haka, ku kame harsunanku daga keta mutuncin mutane- Allah ya muku rahama- saboda lallai Allah Yana kusa da harshen duk wani mai magana, kuma duk wanda ya keta mutuncin ɗan’uwansa kuma ya cutar da shi da magana ko da aiki, to, Allah Shi ne Abokin husumarsa.

    Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: ((Waɗanda suke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayyananne)).
    Babban malami Ibnu Usaimin Allah Ya masa rahama ya ce: “Wato suna jifansu da abin da ba su aikata ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage, wato ƙarya.

    Ƙage kuma, shi ne ka ambaci ɗan’uwanka da abin da bai tare da shi; don haka ne ma lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi tambaya game da yi da wani, sai ya ce: “Shi ne ka ambaci ɗan’uwanka da abin da yake ƙi”. Ya ce: Ya Manzon Allah! Idan ɗan’uwana yana tare da abin da nake faɗi fa? Ya ce: “Idan yana tare da abin da kake faɗi, to haƙiƙa ka ci namansa, idan kuma ba ya ɗauke da shi, to, haƙiƙa ka masa ƙage”. Muslim ne ya rawaito.

    Sannan Allah Ya masa rahama ya ci gaba da cewa: Kuma cutar da mumini yana kasancewa da magana da kuma aiki, kuma hanyoyinsa na da yawa, lallai waɗanda suke cutar da muminai ba tare da sun yi laifin komai ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage wa kawunansu, kuma shi ne ƙarya, da kuma laifi bayyananne, shi ne uƙuba mai girma, Allah Ya amintar da mu”.

    A nan maganarsa ta ƙare, Allah Maɗaukakin Sarki Ya masa rahama kuma Ya saka masa da alheri bisa hidimarsa ga Musulunci da Musulmi. Ya Ubangijinmu, Ka sanya harsunanmu su kasance masu tsarki, zukatanmu su kasance masu ƙaunar muminai. Ya Ubangijinmu, Kada Ka sanya ƙiyayyar waɗanda suka yi imani a cikin zukatanmu. Ya Ubangijinmu, lallai Kai Mai tausayawa ne, Mai jinƙai.

    Ya Allah Ka tsare mu daga son zuciya, da kuma bin zuciya mai yawan umarni da mummuna, sannan Ka tsare mu daga shaiɗan la’ananne. Ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah! Kuma ku yi gaggawar yin amfani da damar da aka ba ku matuƙar tana nan. Ku ci gaba da ingantattun ayyukanku muddin ana karɓar su, kuma ku kakkaɓe kawunanku daga aikata laifi matuƙar igiyar rayuwa bata katse ba.

    Kuma ka rage buri, ya kai wanda ya ruɗu, domin rayuwa gajeriya ce. Ka tsarkake aikinka ga Allah domin Mai duba aikin Mai gani ne, kuma ka bar kusakuranka, domin lissafin mai tsauri ne. Kuma ka gyara laifukanka ta hanyar tuba, domin makoma ta yi maka daɗi.

    Imam Ahmad Allah Ya yi masa rahama, da Imamul Bukhari Allah Ya yi masa rahama a cikin “Al-Adabul-Mufrad”, da kuma Albaihaƙi da isnadi mai kyau, sun rawaito daga Abdullahi bin Amr Allah ya yarda da su: cewa Annabi tsira da amincina Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ku yi jin ƙai, za a jiƙanku, ku yi gafara, za a gafarta muku.

    Kaicon waɗanda suke zama kamar masakin magana. Bone ya tabbata ga masu dogewa da yin abin da suka sani cewa mummuna ne). Ma’anar “Masakin magana”: su ne waɗanda suke sauraron magana amma ba sa fahimtar ta, kuma ba sa aiki da ita.

    A’uzubillahi minash shaiɗanir rajim, bismillahir Rahmanir Rahim: (Sai ka yi bushara ga bayina () Su ne waɗanda suke sauraron magana kuma su bi mafi kyawun ta, Waɗannan ne waɗanda Allah ya shiryar, kuma waɗannan su ne ma’abota hankula). Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da kuma dukkan Musulmi, don haka, ku nemi gafaranSa, lallai Shi Mai yawan gafara ne kuma Mai jin ƙai.

    HUƊUBA TA BIYU
    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai ɗorewa tare da wanzuwarSa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo da ba ya ƙarewa sai idan Ya nufa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo na dindindin, ba abin da zai samu wanda ya faɗe shi sai yardarSa.

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo dawwamamme a kowane ƙiftawar ido da numfashin abu mai rai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa da waɗanda suka bi shiriyarsa kuma suka yi kira irin kiransa.

    Bayan haka:
    Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmi don ku rabauta, ku fargar da kawunanku daga gafala, kuma ku bi hanyar tsira, idan ba ku aikata haka ba kuka tsaya, to fa ku sani cewa shi ajali tafiya yake da ku, kyawawan ranaku na wucewa, ita mutuwa kuma tana farke a farfajiyarku, kuna nufin samun duniya Shi kuma Allah Yana nufin Lahira.

    Ya ku bayin Allah!
    Ku yawaita salati da sallama ga mafakar mutane a babbar matsaya Ranar Alƙiyama, Annabinmu kuma mai cetonmu Muhammadu tsira da amincin Allah mai yawa su tabbata a gare shi da Alayensa. Ya Allah ka ƙara yarda da Halifofi shiryayyu da sauran Sahabbai gabaɗaya, da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

    Ya Allah Ka amfanar da mu da son su, kuma Ka tashe mu cikin tawagarsu, kuma kada Ka karkatar da mu daga bin tafarkinsu da hanyarsu ya Mafi karamcin masu karamci.
    Ya Allah! Ka ƙarfafa Musulunci da Musulmi, Ka ɗaukaka Kalmar gaskiya da Addini da falalarka.

    Ya Allah! Ka ƙarfafa Shugabanmu kuma Majiɓincin lamuranmu da gaskiya da yin daidai da dace, Ka yi riƙo da hannunshi ga ayyukan nagarta da taƙawa, Ka azurta shi da mashawarta nagari, Ka ɗaukaka AddininKa da kalmarKa da shi, Ka sanya shi ya zama mai taimako ne ga Musulunci da Musulmi, kuma Ka haɗa kan Musulmi da shi a kan gaskiya da shiriya ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah! Ka datar da shi da Yarimansa da ‘yanuwansa da mataimakansa zuwa gaskiya da shiriya da kuma duk abin da yake akwai gyara ga al’umma da ƙasa a cikinsa, Ka saka musu da alheri saboda kulawarsu da Masallatai biyu masu alfarma da daraja, da kuma duk abin da suke gabatarwa saboda cigaban Musulunci da Musulmi.

    Ya Allah! Ka datar da masu jagorancin Musulmi ga yin aiki da Littafinka da Sunnar Annabainka Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Ka sanya su su zama rahama ga bayinKa Muminai, Ka haɗa kansu akan gaskiya ya Ubangijin talikai, Ka kuma datar da duk jagororin Musulmi ga duk abin da yake gyara ne ga ƙasa da mutanen.

    Ya Allah! Ka saki labulan suturtawarka akan ƙasarmu da kuma dukkan ƙasashen Musulmi.
    Ya Allah! Muna kamun ƙafa da yardarKa kada Ka yi fushi da mu, kuma muna kamun ƙafa da amincinKa kada Ka yi mana uƙuba, kuma muna nema tsarinka daga azabarKa, ba mu iya kaiwa matuƙa wurin yaɓonKa kamar yadda Ka yabi kanKa.

    Ya Allah! kada ka yi mana azaba da munanan ayyukanmu, kuma kada Ka kama mu da abin da wawayen cikinmu suka aikata, Ka isar mana duk wani abin da ya dame mu, kuma Ka kasance Mai ƙarfafawa da ba da nasara a gare mu. Ya Allah! Lallai mu muna roƙon Ka farin ciki da zai lulluɓe zukatanmu da ‘yantuwar Masallacin Ƙudus daga hannu Yahudawa ‘yankwace.

    Ya Allah Ka jefe su da kibiyarKa da ba ta kure, Ka saukar musu da uƙubarKa mai tsanani, ya Majiɓincin masu rauni, ya Ma’boci ƙarfi mai tsanani! Ya Mai gudanar da giragizai! Ya Mai rusa rundunonin maƙiya! Ka saukar wa ‘yan ta’adda azaba mafi tsanani, Ka sanya su abin ɗaukar izina ga masu hankali. Ya Allah! Muna roƙon Ka farin ciki saboda samun nasarar Musulmi a kan abokan gabansu azzalumai.

    Ya Allah! Lallai mu muna roƙon gafararKa, saboda lallai Kai Ka kasance Mai yawan gafara ne, don haka Ka saukar mana da ruwan sama mamako, ya Allah! Ka saukar mana da ruwan sama, ya Allah! Ka saukar mana da ruwan sama, ya Allah! Lallai mu wata halitta ce cikin halittunKa, don haka kada Ka hana mu falalarKa saboda zunubanmu.

    Ya Allah! Ka karɓa daga gare mu lallai Kai Mai ji ne kuma Masani, kuma Ka karɓi tubarmu lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne Mai tsausayi. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Manzanni, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Don karanta falalar tafiya masallacidanna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Yaron Da Ke Ƙin Shan Nono

    Yaron Da Ke Ƙin Shan Nono

    Ba ko yaushe ba ne don jariri ko yaro ɗan kasa da shekaru biyu ya ƙi shan nono, ko ya zamto mai saurin sakin nonon da zarar ya fara sha za a ce ba shi lafiya ba, a hau neme-nemen magani ana ɗura masa. 

    Na sha faɗa magani guba ne kowanne iri muddin aka sha shi ba tare da tabbatuwar ciwon da ya dace da maganin ba! Har kuwa su Paracetamol, B-complex, ɗin nan da multivitamins da ake rainawa.

    Don haka kamar yadda lafiya ƙalau amma saboda wani abu kuke kasa cin abinci shi ma jariri mutum ne haka yake! Kar ku ɗauka don kurum ɗan mitsitsi ne hakan na nuna bai san komai ba, sai kun ɗura masa abinci ko ba ya so. 

    Wasu lokutan ku ke hana shi sha; musamman in yaro ba ya kuka, ba ya rikici, ba ya ƙwalla, ba kuma ya zazzaɓi hakan na nuna ƙalau yake wani dalili ne ya hana shi:

    * Ƙarancin tsafta daga uwar! Kila hammatarta babu aski, ko kuwa kin yi aiki kin yi zufa kin zo kin ɗora shi a cinya alhalin iska na kaɗo masa tashin matse-matsin hammatarki, ko da ya kama nono tabbas zai saki, domin shi ma yana jin tsamin.

    * Rashin tsaftar hannayenki, ƙila jikinki tsaf amma kin taɓo abu mai ƙarni, ko wari a hannunki kuma kin zo yayin sakar masa saleɓar brazier ɗinki kin dunguri kan nonon nan ma yana iya ƙin sha. In kika matsa kuma ya sa kuka.

    * Rashin tsaftar rigar nono da kuma rashin wanke ko goge kan nonon sosai bayan yaro ya kammala sha, wasu rigar nonon ce sai ta shafe yini biyu jikinsu, zufa da kuma normal bacteria ɗin kan fatarki na da tasiri musamman in ya zamto dama da kin gama ba da nono kurum jan saleɓar rigar nonon kike yi mayar ba kya tsaftace kan nonon, haka anjima za ki ciro ki ƙara cusa masa a baki, hakan har gudawa yana iya jawoma jaririnki. Don haka sai an kiyaye.

    * Canjin sabulun wanka me ƙarfin ƙamshi, wani yana kama fata har a baki a ji shi, don haka wannan ma na hana yaro kama nono, har sai kin koma irin wanda ya saba da shi mara ƙarfi da baya iya jin sa.

    * Shafa turare me ƙarfi wanda shi ma bai saba da shi ba, kamar mu ne kai ma akwai turaren da in wani ya sa sai ka ji kamar za ka ce wayyo Allah in ya tsaya kusa da kai, to su ma haka ne, wannan na iya hana su shan nono.

    * Juyowar kwanakin haila, shi ma na sa yaro ya ƙauracewa shan nono domin mizanin sinadarin gishiri-gishiri a cikin nono wato sodium & chloride na ƙaruwa, yayin da sinadarin kanwa-kanwa da zaƙi ke yin ƙasa wato potassium & lactose wanda kuma su yaro ya fi so. Kun ga ko a manya in gishiri yai yawa a abinci wani ba ya iya ci. 

    * Haka nan yayin HAILA ko da canjin ɗanɗanon nono bai canza ba akan samu adadin ruwan nono ya ɗan yi ƙasa hakan ma iya sa jariri in ya ji ba ya isarsa yai zuciya ya dena wahalar da bakinsa saboda gajiyar tsotso alhalin babu wadataccen ruwa.

    * Haka nan ma samuwar juna biyu alhalin ga wani ana shayarwa shi ma na iya sa irin wancan canjin da ake fuskanta yayin haila, wanda hakan na iya sa yaro ya yaye kansa.

    * Haka nan wani magani da ke uwar ke sha walau na Hausa ko na asibiti, galibi na asibiti shi yasa likita ke tambaya ko kina da ciki ko shayarwa kafin a rubuta miki magani, idan kikai masa ƙarya alhalin kina shayarwa irin abunda zai iya faruwa kenan, yaronki ya ƙi nono kuma ki zo nonon yai ta ciwo. Haka cin irinsu tafarnuwa ko wani nau’in abinci da a da ba kya ci wanda suna iya ratsa ruwan nono.

    * Ko yawan dauke hankalin yaro wato distracting, don wani yaron ko ya ya ji magana ko motsi sai ya waiga, shi yasa za ka ga suna shan nono suna saki. Irin wannan maganinsu kike shiga inda yake tsit babu hayaniya sai ku yi shayarwarku a nutse, ko a tsohe kunnuwan da wani abu kamar auduga kafin a gama in ba haka ba ko ya ya ji motsi ba fasa juya zai ba.

    Waɗannan su ne wasu daga mahimman ababen da ke sa yaro ƙauracewa nono. Don haka kiyayewa kurum suke buƙata babu buƙatar zuwa ki yi ta cusawa yaro magani, ki lura da kyau, sai dai in akwai alamun rashin lafiya toh sai a taho ga likita.

    * Sannan kar ki manta duk sanda kika gama bai wa yaro nono kike dora shi a kafaɗa kina shafa bayansa har sai kin ji ya yi gyatsa. Hakan alama ce ta ya ƙoshi, in bai gyatsa ba a kuma maida shi kan nono.

    * Ganin jariri na yawan ƙwalla ko hawaye ko da ba ya kuka haka alama ce ta nono ba ya isarsa, ko da kuwa ana ba shi ƙila ruwan nono babu sinadaran da za su ƙosar da shi, sai a nemo madara wacce take ta yara irin NAN ɗinnan a ƙara masa da ita.

    *Ganin jariri ko yaro na yawan tsilla fitsari hakan alama ce ta yana samun kyakkyawan shayarwa.

    Fatan an ilmantu. Burina na ga al’umarmu mun yi lafiya, rayuwarmu ta canza, birni da ƙauye ana samun lafiyayyun yara masu tasowa.

    Don karanta jerin abincin da ke ƙarawa mata masu shayarwa ruwan nono danna nan

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

          

  • Waye Bahaushe?

    Waye Bahaushe?

    A yanzu sanin kowa ne ne Bahaushe na asali sai an yi ƙoƙarin tantancewa, saboda irin cuɗanyar da Hausawa suka yi da wasu ƙabilu wadda ta yi sanadiyar sauyawarsu. Don haka siffa ko harshe ba ya tabbatar da Bahaushe.

    Hausawa sun yi cuɗanya da ƙabilu masu yawa ta fuskar kasuwanci da ƙodago da addini, kamar, Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da Jukunawa da wasu ƙabilu na Afirka masu yawa ciki har da Buzaye da Larabawa.

    Wannan cuɗanya ta haifar da auratayya da cakuɗuwar al’adu a tsakaninsu da Hausawa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mayar da wasu Hausawa ta fuskar harshe da al’ada duk da cewar hakan bai hana su iƙirarin asalinsu ba. Za a iya fahimtar Hausawa ta waɗannan fuskoki:

    1. Hausawa ta fuskar harshe waɗanda babu kwata a bakinsu (tsamin baki wajen kasa furta wasu sautuka a harshen Hausa)

    2. Hausawa ta fuskar muhallin zama. (gari ko yankin da suke zaune)

    3. Hausawa ta fuskar addini. Yawancinsu musulmi ne ko maguzawa.

    4.Hausawa ta fuskar halayya da al’ada.

    5. Hausawa ta fuskar asali. Waɗanda suke iƙirarin su Hausawa ne iyaye da kakanni.

    Don haka a yanzu Bahaushe shi ne mutumin da yake ba shi da wani harshe sai harshen Hausa, kuma al’adunsa na Hausawa ne, ko da kuwa yana iƙirarin wani asali daban, yana zaune ne a ƙasar Hausa ko a wajen ƙasar Hausa. A yanzu kalmar Hausa ta zama ta harshe ba ta ƙabila ba. Domin kalmar ƙabila, kamar yadda Zarruk da wasunsa (2009) suka bayyana na nufin:

    “… al’umma mai asali ɗaya, da yare ɗaya, da ƙirar jiki kusan iri ɗaya, da al’adu iri ɗaya, da falsafa ko ra’ayin zaman duniya iri ɗaya. Bayan haka cikin al’ummar kowa zai riƙa alfaharin shi ɗan ƙabilar ne.”

    Ƙasar Hausa ta asali tana yankin Afirka ta Yamma a farfajiyar da ke a Arewacin Nijeriya da kuma Kudancin Jamhuriyar Nijer. Daga Gabas ta yi iyaka da yankin Mangawa da Badawa a gabas kaɗan da garin Haɗejiya ta Jihar Jigawa, daga Yamma ta yi iyaka da ƙasar Zabarmawa daidai doron Kogin Kwara, daga Arewa ta yi iyaka da ƙasar Agadas wato yankin Buzaye (Auzinawa) a Kudancin ƙasar Nijer.

    Sannan daga Kudu ta yi iyaka da ƙasar Gwari da wasu ƙananan ƙabilu da ke Kudancin ƙasar Zazzau (Zariya) a jihar Kaduna. Manyan garuruwan ƙasar Hausa a yanzu sun haɗa da Kano da Katsina da Daura da Sakkwato da Kebbi da Zazzau (Zariya) da Gusau da Haɗejiya da Bauci da Azare (ƙasar Guddiri) a arewacin Nijeriya, da kuma Damagaran da Maraɗi da Filinge da Dogon Dutse da Ƙonni a jamhuriyar Nijer.

    A taƙaice ƙasar Hausa ta asali, daula ce da ta wanzu a tsakanin daular Borno daga gabas da kuma daular Songhai daga yamma, ko da yake tarihi ya fi ganin yankin a matsayin daular birane, inda kowane sarki yake da ikon cin gashin kansa, wato babu wani shugabanci da ya haɗe yankin a matsayin dunƙulalliyar daula.

    Domin karanta mutuwa da rabon gadon Bahaushe danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu