Tag: yadda ake

  • Azumin Ranar Arfa

    Azumin Ranar Arfa

    Ranar Arfa ita ce ranar tara ga watan Zul- Hajji, rana ce mai cike da darajoji, ana son yin azumi da yawaita ibada a wannan rana. Sai dai an hana yin wannan azumin ga wanda yake aikin Hajji.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Ranar Arfa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Yin Umara A Watan Ramadan

    Falalar Yin Umara A Watan Ramadan

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu anhu) ya ce: “Yin umara a watan Ramadan daidai da ladan aikin Hajji ne, ko kuma daidai da ladan aikin Hajjin da aka yi tare da ni yake”. (Bukhari 1764, Muslim !69).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙara Yawaita Ibadu Da Alhairi A Goman Ƙarshe Na Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tsayuwar Watan Ramadan danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Sallar Idi

    Yadda Ake Sallar Idi

    Sallar Idi babba da ƙarama sunna ce babba mai ƙarfi,a mazhabar Malik da Shifi’I, amma a mazhabar Abu Hanifa da Ahmad sallar idi wajibi ce, wannan shi ne zaɓin Shaihul Islam Ibn Taimiyya.

    Sallar idi ana yin ta a bayan gari, raka’a biyu ce, ba a yi mata kiran salla, ballantana iƙama, ana ƙara kabbarori guda shida bayan kabbarar harama a raka’ar farko, da kuma kabbarori bayan raka’a ta biyu, a bayyane ake yin karatunta sannan ana yin huɗuba bayan an gama sallar.
    Waɗannan su ne ingantattun nafiloli na sallah, Allah ya sa mu dace.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nafilolin Azumi danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Sujjadar Godiya Ga Allah

    Yadda Ake Sujjadar Godiya Ga Allah

    Sujjadar godiya ga Allah wacce ake kira “Sujudus Shukri” sujjada ce da ake yi domin godiya ga Allah Ta’ala kan wata ni’ima ko yayewar wani bala’i. Ana yin ta kamar yadda ake yin sujjadar tilawa, kuma ana yin ta koda ba alwala kuma ko ba a kalli alƙibla ba, wannan shi ne zance mafi inganci.

    Sujudus Shukir ta tabbata a hadisin Ka’ab Ibn Malik (Radiyallahu anhu) lokacin da aka yi masa albishir da karɓar tubansa, sai ya yi sujjada domin godiya da Allah”. (Bukari 4418 Muslim 2769) haka kuma ya zo a hadisin Abi Bakarata cewa, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance in wani abin murna ya zo masa, ko aka yi masa albishir sai ya sunkuya ya yi sujjada yana mai godiya ga Allah” Abu Dawud 27774, Tirmizi 1578 Ibn Majah 1394

    Domin karanta cikakken bayani a kan

    Sujjadar godiya ga Allah wacce ake kira “Sujudus Shukri” sujjada ce da ake yi domin godiya ga Allah Ta’ala kan wata ni’ima ko yayewar wani bala’i.Ana yin ta kamar yadda ake yin sujjadar tilawa, kuma ana yin ta koda ba alwala kuma ko ba a kalli alƙibla ba, wannan shi ne zance mafi inganci.
    Sujudus Shukir ta tabbata a hadisin Ka’ab Ibn Malik (Radiyallahu anhu) lokacin da aka yi masa albishir da karɓar tubansa, sai ya yi sujjada domin godiya da Allah”. (Bukari 4418 Muslim 2769) haka kuma, ya zo a hadisin Abi Bakarata cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance in wani abin murna ya zo masa, ko aka yi masa albishir sai ya sunkuya ya yi sujjada yana mai godiya ga Allah” Abu Dawud 27774, Tirmizi 1578 Ibn Majah 1394

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Idi danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Sujjadar Tilawa

    Yadda Ake Sujjadar Tilawa

    Sujjada ce guda ɗaya da ake yi, yayin karanta ko sauraron ayar da sujjadar take a cikin Al-kur’ani. Sujjadar tilawa sunna ce mai ƙarfi, har ma waɗansu malaman suna ɗaukar ta a matsayin wajiba.

    Ana yin kabbara yayin sujjada da kuma ɗagowa, ba a sallama, ana yin tasbihi a cikinta ,ana son a faɗi wannan zikirin a cikinta “Sajada wajhi lallazi khalkahu, wasawwarahu wa shaƙƙa sam ahu wa basarahu bi haulihi wa ƙuwwatihi”.
    Mafi yawan malamai suna ganin tilas sai da alwala, kuma sai an fuskanci alƙibla; sannan a lokacin da ya halatta a yi nafila ake yinta. Amma Ibn Hamz da Ibn Taimiyya suna ganin duk wannan ba sharaɗi ba ne, tun da dai ba salla ba ce, idan mutum yana sallah sai ya karanta ayar sujjada, zai iya yin sujjadar sannan in ya ɗago ya ƙara karantun ko kuma ya yi ruku’u kawai.

    Wuraren da ake yin sujjadar tilawa a Ƙur’ani su ne kamar haka:

    Suratul A’araf aya ta 206.
    Suratul Ra’ad aya ta 15
    Suratul Nahli aya ta 49 – 50
    Suratul Isra’I aya ta 109.
    Suratul Maryam aya ta 58.
    Suratul Hajj aya ta 18.
    Suratul Furkan aya ta 60
    Suratul Namli aya ta 26.
    Suratul Sajda aya ta 15.
    Suratul Fussilat aya ta 37/38

    Waɗannan wurare babu wani saɓani a kansu tsakanin malamai. Sai kuma wuraren da aka yi saɓani a kansu amma dalilansu sun inganta su ne:

    11. Suratul Sa’adi aya ta 24.
    12. Suratul Najmi aya ta 62.
    13. Suratul Inshiƙaƙi aya ta 21.
    14. Suratul Alaƙ aya ta 19.
    15. Suratul Hajj aya ta 77.
    Waɗannan wurare na ƙarshe, ba a sami hadisi a kansa ba, sai dai an samo sujjada daga sahabbai da dama da kuma tabi’ai.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sujjadar Godiya Ga Allah danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Sallar Roƙon Ruwa

    Yadda Ake Sallar Roƙon Ruwa

    Ana yin wannan sallah yayin da fari ya afkawa al’ummar musulmi. Ruwa ya yi jinkiri ko ya dakata. Ana yin ta ne raka’a biyu kacal a bayan gari (filin masallicin idi) kamar dai yadda ake yin sallar idi sai dai ita ba a yi mata kabbarori irin na sallar idi.

    Ana so kowa ya fito cikin kasƙantar da kai ga Allah, ba tare da an yi ado ba. Cike da tsoron Allah da nutsuwa da nuna nadama. Liman zai yi huɗubar kafin ko bayan idar da sallar, a cikin huɗubar ya yawaita addu’a. ya fuskanci alƙibla ya ɗaga hannayensa sama sosai, ya kifasu, sauran mutune ma kowa ya ɗaga hannnunsa, kuma ana so liman ya juya mayafinsa ko alkyabbarsa ko babbar rigarsa domin fata Allah ya kawo sauyin yanayi.
    A cikin huɗubar nan tasa, liman ya ja kunnen mutane ya tsawatar da su kan saɓon Allah da zalunci ya umarce su da su tuba su bai wa masu haƙƙi haƙƙinsu, kowa ya gyara halinsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sujjadar Tilawa danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Sallar Istihara

    Yadda Ake Sallar Istihara

    Sallar Istihara salla ce da ake yin ta domin neman zaɓin abin da ya fi alheri tsakanin aikata ko barin wani abu wanda yake halal a shari’ance. Saboda haka ba a yin istihara kan abinda aikata shi yake wajibi ko haram ko mustahabbi.

    Bayan yin Istiharar sai mutum ya ci gaba da aikata abinda yake ciki in ba alkhairi bane ba zai yiwu ba. Babu wani mafarki da mutum zai yi a matsayin amsa ga istihararsa, kuma ka sani cewa, ana yin istihara ne kafin yanke wata shawara a zuciya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Sallar Istihara danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Sallar Walaha

    Sallar Walaha

    Sallar walaha ana yin ta daga kimanin minti goma sha biyar bayan fitowar rana har zuwa lokacin sallar Azahar. Mafi ƙarancin sallar walaha shi ne raka’a biyu daga nan har zuwa raka’a goma sha biyu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Sallar Walaha danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Asham Da Raka’o’inta danna nan.

    Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Ake Yin Sallar Wutiri.

    Yadda Ake Yin Sallar Wutiri.

    Hadisai da dama sun zo kan bayanin siffofin wutiri kamar haka:

    1- Wutri da Raka’a Ɗaya:

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Sallar dare raka’a biyu-biyu ce, idan ɗayanku ya ji tsoron fitowar alfijir, ya sallaci raka’a ɗaya ta zama wutri ga abin da ya sallata”. Kuma ya ce, “Wutiri raka’a ɗaya ne a ƙarshen dare”. (Muslim 752).

    2- wutiri da Raka’a Uku: ana yin sa ta hanyoyi biyu:

    i. A yi raka’a biyu a yi sallama , sannan a yi wutri a yi sallama. Wannan ya inganta a hadisan Sayyada A’isha da Ibn Abbas da kuma Ubayyu Ibn Ka’ab (R.A) kuma ya inganta cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana karanta Suratul A’ala a raka’ar farko, sai Suratul  Kafirun a raka’a ta biyu sannan sai Suratul Iklass  a raka’ar wutiri.(Bukhari 991, Malik 1/125, ) Tahawi 1/285). Amma karanta Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi, wannan ya zo a Hadisi mai rauni.

    ii. A yi raka’a ukun a jere ba tare da an yi zaman tahiya ba, sai a raka’a ta uku. (Bukhari 1147, Muslim 783)

    iii. Wutiri da Raka’a Biyar: Ana so ga wanda zai yi wutiri da raka’a biyar ya yi su a jare kada ya yi zaman tahiya sai a raka’a ta biyar. Wannan ya inganta a Hadisin A’isha (R.A) wanda Muslim ya ruwaito.

    iv. Wutiri da Raka’a bakwai ko Raka’a tara: Ana so ga wanda zai yi irin wannan wutiri, ya yi su a jere kada ya zauna sai a raka’a ta shida ko ta takwas,sannan ya tashi ya kawo raka’a ta bakwai ko ta tara sannan ya yi sallama. Wannan ya zo a Hadisin. (Muslim 746, Abu Dawud 1328 da Nasa’I 2/199).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Shin Dole Ne A Yi Shafa’i Kafin Wutiri? danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Nauye-nauyen Rayuwar Aure

    Nauye-nauyen Rayuwar Aure

    A Musulunci, rayuwar aure ba ta kyautatuwa ta zama nagartacciya, har sai idan an aiwatar da ita ta salon da Musulunci ya tsara, ta hanyar ɗora wa ma’aurata wasu nauye-nauye da ake buƙatar  da su sauke su kamar haka:

    1. Haƙƙoƙin mace a kan mijinta.
    2. Haƙƙoƙin miji a kan matarsa.
    3. Haƙƙoƙin da miji da mata suke tarayya a kansu.
    4. Haƙƙin wanda mutuwa ta raba shi da abokin zamansa daga cikin ma’aurata.

    1. Haƙƙoƙin Mace a Kan Mijinta:

    (a) Sadaki: Wanda bayaninsa ya riga ya gabata.
    (b) Ɗora iyali a kan bin Allah tare da rainonta da kyawawan ɗabi’u.
    Shi wannan haƙƙi na biyu da samuwarsa da kuma ɗorewarsa ne mace za ta kyautata tsakaninta da ubangijinta, da kuma tsakaninta da bayinsa.

    Da farko Allah Mai girma da Buwaya ya ce:
    “Ka ambaci (labarin) Isma’il cikin wannan littafi (Alƙur’ani), haƙiƙa shi mai cika alƙawari ne, kuma Annabi ne Manzo. Ya zamanto yana umartar iyalinsa da (tsaida sallah da kuma ba da zakka, sannan kuma shi yardajje ne a wajen ubangijinsa ).

    Abin nufi a nan, Annabi Isma’il yardajjen Allah, a zamansa da iyalinsa yana umartar su ne da su riƙa tsayar da sallah, kuma su riƙa bayar da zakka, domin alaƙarsu da Ubangiji ta kyautata.

    Sannan kuma mun ji cewa shi mutum ne mai cika alƙawari, sanin kowa ne kuma duk wanda yake haka za ka tarar yana ƙoƙarin rainon iyalinsa da yin haka. Sannan kuma Allah ya ce da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi):

    “Ka umarci iyalinka da tsaida Sallah kai ma kuma ka yi haƙurin dawwama a kan tsaida ita, ba za mu tambaye ka dukiya ba, mu ne ma za mu azurta ka, kuma kyakkyawan ƙarshe (duniya da lahira ) ga masu tsoron Allah yake”.

    Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya aiwatar da wannan umarni da Allah yayi masa kamar yadda Imamut- Tirmizi ya rawaito hadisi cewa, an karɓo daga Ummu-salama Allah ya yarda da ita ta ce:

    “Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan watan Ramadan ya rage kwana goma ya ƙare, ba ya barin ko da mutum ɗaya daga cikin mutanen  gidansa matukar dai zai iya yin sallar dare face sai ya tashe shi (domin ya yi)”.

    To, ‘yan uwa, idan Annabi bai bar sallar nafila ta wuce mutanen gidansa ba; ina kuma ga sallar farilla. Sannan kuma Allah Maɗaukaki ya ce:

    “Ya ku waɗanda kuka ba da gaskiya, ku tserar da kanku da kuma iyalanku (daga shiga ) wuta (wadda ) mutane da duwatsu ne makamashinta, kuma akwai wasu ƙarfafan mala’iku masu kauri da suke tsaron ta, waɗanda ba sa saɓa wa Allah abin da ya umarce su da shi, kuma suna aikata duk abin da aka umarce su da shi”.

    A wannan ayar kuma kiran muminai gaba ɗaya Allah ya yi, sannan ya umarce su da su dage su bi irin turbar da Annabawa suka bi, wajen ɗora kansu da iyalansu akan hanyar bin Allah da nisantar saɓa masa, domin su gudu tare su kuma tsira tare. Har wa yau, Bukhari ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Malik ɗan Huwairis Allah ya yarda da shi yace: Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce da (ayarin) jama’ar Abdul- Kais da suka zo wajen

    “Su kiyaye imaninsu da kuma ilmin da ya sanar da su shi, sannan kuma ya ce da su, “Ku koma wajen iyalanku ku sanar da su”.

    Saboda waɗannan dalilan da muka ji ya zama lallai akan miji ya sanar da matarsa ilmin yadda za ta bauta wa ubangijinta, ko kuma ya tura ta inda za ta je ta koya, kamar yadda matan sahabbai suke zuwa wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) su koyo addini.

    Bayan haka, an karɓo daga Amru ɗan Ahwas Allah ya yarda da shi ya ce, ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a hajjinsa na bankwana yana cewa: “Ku saurara, ku yi wa mata wasici da alheri”. ( Tirmizi ne ya rawaito shi ). Haka kuma an karɓo daga A’isha (Allah ya yarda ita ) ta ce: ” (wata rana ) Yahudawa sun zo wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai suka ce da shi: “Assamu alaikum” wato halaka ta tabbata a kanku, a maimakon su ce: “Assalamu alaikum” wato amincin ya tabbata a gare ku, jin haka, sai A’isha ta ce: Halaka a kanku, Allah kuma ya tsine muku; ya yi fushi da ku. Sai Annabi ya ce da ita:

    A a A’isha, yi a hankali, ina umartar ki da yin sauƙi, kuma ki kiyayi kausasawa da munanan maganganu. Sai kuwa ta ce da Annabi ba ka ji abin da suka ce ba ne? Annabi ya ce: To ke ba ki ji abin da na ce da su ba? Ai na mayar musu da martani da cewa a kansu dai. Sai Allah ya amsa mini addu’ar da na yi musu, su kuma ba zai amsa musu wadda suka yi mini ba. (Bukhari ya rawaito shi).

    A nan idan muka lura da kyau, za mu fahimci cewa, waɗannan hadisai suna ɗora magidanta ne a kan hanyar da ya kamata su ɗora matansu a kai, ta nusar da su yadda ya kamata su zauna da mutane a cuɗanyarsu da su. Allah dai ya ba mu ikon kulawa da kuma aiki da wannan koyarwar ta Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), amin.

    (c) Samar wa Mace Mazauni (Gida ko ɗaki):

    Shi kuma wannan nauyi ya hau kan miji ne a sakamakon faɗar Allah Madaukaki da ya ce:
    “Ku zaunar da su (mata) a inda kuke zaune daidai halinku, kar ku cuce su don ko ƙuntata musu”. Da kuma faɗar Allah Maɗaukaki cewa: “Ku ji tsoron Allah Ubangijinku kada ku fitar da su daga ɗakunansu, suma kada su fita, sai dai idan sun zo da mummunan aiki mabayyani, waɗancan iyakokin Allah ne, to haƙiƙa ya cuci kansa”.

    Saboda haka, haramun ne mai gida ya ce da matarsa ta fice ta bar masa gidansa, ko ɗakinta don ya sake ta, matuƙar dai ba ta gama idda ba. Haka kuma ita ma mace bai halatta ta bar gidan mijinta ba don ya sake ta har sai bayan ta gama idda. Wannan sai ya tabbatar mana da cewa alhakin miji ne ya tanadar wa matarsa mazauni.

    (d) Ciyarwa da Tufatarwa:

    Haka ma ciyarwa da tufatarwa, haƙƙƙi ne da mace take da shi a kan mijinta. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki ya ce: “Ciyar da mata da tufatar da su gwargwadon iko, wajibi ne a kan wanda aka haifawa ɗa, ba a ɗora wa (kowanne) rai sai gwargwadon ikonsa”.

    A wata ayar kuma Allah Maɗaukaki ya ce: “Mai yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuma aka ƙuntata arzikinsa, (wato talaka), to, ya ciyar daga ɗan abin da Allah ya ba shi, Allah ba ya ɗorawa kowacce rai sai abin da ya ba ta, da sannu Allah zai sanya sauƙi bayan matsi (tsanani)”.

    A hadisance kuwa, an karɓo daga Hakim ɗan Mu’awiya daga mahaifinsa (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Na tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa, menene haƙƙin matar kowannenmu a kansa? Sai ya ce: “Ka ciyar da ita idan ka ci, ka kuma tufatar da ita idan ka tufata…”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi).

    Sannan kuma sahabin Annabi Amru ɗan Ahwas ( Allah ya yarda da shi ) ya ce: Haƙiƙa ya ji Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a hajjinsa na bankwana yana cewa: “Ku saurara, haƙiƙa matanku na da haƙƙi a kanku, haƙƙinsu a kanku, ku kyautata tufatar da su, da ciyar da su”.( Tirmizi ne ya rawaito).

    Bisa dogaro da waɗannan dalilai, ya zama tilas a kan miji ya ciyar da matarsa, ya tufatar ita gwargwadon irin halin da yake da shi. Sannan kuma amana ce a wuyan miji ya ciyar da matarsa da halal ba da haramun ba.

    Haɗarin Ƙuntata wa iyali wajen ciyarwa

    Musulmin da Allah ya yi masa yalwar abin da zai ciyar da iyalinsa, da abin da zai tufatar da su, amma sai ya zama yana ƙuntata musu, ta hanyar ƙin wadata su da abin da zai ishe su, to, a zahirin gaskiya babu wanda yake cuta sai kansa, domin kuwa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ya isa mutum laifi, ya riƙa tozarta wanda yake ci a ƙarƙashinsa”. (Abu Dawuda ne ya rawaito shi).

    Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) yace: Haƙiƙa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya ce: “Babu ranar da bayi za su wayi gari a cikin ta, face sai wasu mala’iku biyu sun sauko, sai ɗaya daga cikinsu ya kama cewa: “Ya Allah ka bai wa mai ciyarwa”. Sai shi kuma ɗayan ya ce: “Ya Allah ka haɗa matsolo da asara”. (Bukhari da Muslimu ne suka rawaito shi). Don haka, ‘yan uwa sai a yi hattara.

    Bayan haka, da Allah zai datar da iyalan malam matsolo da samun wata kafa da za su riƙa ɗiban abin da zai ishe su daga cikin dukiyarsa, a shari’ance, ba su yi laifi ba, in sun ɗebi abin da zai ishe su, matuƙar dai ba za su yi ɓarna ba.

    An karbo daga A’isha (Allah ya yarda da ita) ta ce: “Hindu ‘yar Utba matar Abi Sufyanu ta shiga wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai ta ce: “Ya Manzon Allah, mijina Abu Sufyan matsolon mutum ne, ba ya ba ni abin ciyarwa da zai ishe ni, kuma ya ishi ‘ya’yana, sai in na ɗebi wani abu daga cikin kudinsa ba da saninsa ba, shin ko ina da laifi game da hakan da nake yi? Sai Annabi ya ce: “Ki ci gaba da ɗaukar abin da zai ishe ki ya ishi ‘ya’yanku daga kuɗinsa”. Wato yin hakan ba laifi ba ne. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

    Sannan dai ita wannan ta’ada ta matsolanci, haɗarin ta yana da yawan gaske, domin kuwa tana sa mai yin ta ya rasa samun alherin da masu ɗaukar abin hannunsu su bayar suke samu:
    Na Farko: zai rasa samun addu’ar alherin da mala’ika yake yi wa masu ɗaukar abin hannunsu su bayar duk wayewar garin Allah, kamar yadda muka ji.
    Na Biyu: Ya rasa kwarjinin da masu bayar da abin hannunsu suke samu a wajen waɗanda suke agazawa.
    Na Uku: An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Hannun da yake bayarwa ya fi hannun da yake karɓa. (In za ka bayar) ka fara da wanda nauyinsa ke kanka, ka ba wa babarka, da babanka, da ‘yan uwanka, sannan wanda ya fi kusa da kai, sai wanda yake da kusanci da kai”. (Nasa’i da Darakudni ne suka rawaito shi, kuma Darakudni da ibn Hibban suka inganta shi).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Dokokin Suturar Musulma danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu