Tag: yadda ake

  • Ciwon Hanta (Hepatitis B)

    Ciwon Hanta (Hepatitis B)

    Hanta, ɗaya ce daga cikin sassan jikin ɗan adam. Kuma jigo ce wajen kula da tafiyar da jikin ɗan adam. Mutum ba zai iya rayuwa babu hanta ba. Abubuwa da dama suna iya janyo ciwon hanta mai tsanani wanda zai iya yin sanadiyar mutuwar mutum.

    Akwai ciwon hanta mai tsanani da mara tsanani. Akwai mai dogon zango da mai gajeran zango. Kuma kowanne daga cikin nau’o’in ciwon hanta zai iya kashe mutum.

    Amfanin Hanta

    Amfanin hanta yana da yawa a jiki, amma ga kaɗan daga cikin su:

    1. Sarrafa abinci: Hanta tana kula da daidaituwar abinci a jiki. Misali, idan mutum ya ci shinkafa mai yawa, hanta ce take sarrafa abincin domin a ajiye shi zuwa wani lokaci.

    2. Sarrafa magunguna: Hanta tana taka rawar gaske wajen kula da shige da ficen magungunan a jikin ɗan adam.

    3. Samar da sinadarai: Hanta tana samar da sinadaran da jiki yake buƙata wajen yaƙar cututtuka da kuma samar da zaman lafiyar jiki. Sinadaran sun haɗa da: bile, plasma proteins, clotting factors da sauransu.

    4. Fitar da datti; Cututtuka da sinadarai marasa amfani daga jiki kamar su ammonia, billurubin da sauran su.

    Abubuwan da suke janyo ciwon hanta

    1. Ƙwayar cutar Virus: Kamar Hepatitis (A, B, C, D da E) virus, cytomegalovirus (CMV), Epstein-Barr virus da sauransu.

    2. Shan giya: Giya tana janyo cututtuka iri daban daban a jikin ɗan adam, daga ciki har da ciwon hanta.

    3. Shan magunguna barkatai: Wasu daga cikin magungunan da muke amfani da su, suna iya janyo ciwon hanta musamman idan ana shan su ba bisa ƙa’ida ba.

    Abubuwan da suke janyo ciwon hanta suna da yawa. Amma zan yi bayani a kan ciwon hanta wanda ƙwayar virus ta Hepatitis B take janyowa.

    Ciwon hanta na Virus ɗin Hepatitis B:

    Mutane da dama a Nigeria suna ɗauke da wannan ƙwayar cutar. Wasu sun san suna da ita, da yawa ba su san suna da ita ba. Virus ɗin Hepatitis B tana iya lalata wa mutum hanta, tana janyo ciwon hanta mai tsanani kuma tana iya janyo cutar dajin hanta (cancer).

    Yadda ake ɗaukar ƙwayar cutar Hepatitis B Virus

    Virus ɗin Hepatitis B tana shiga jikin mutum ne ta hanyar cakuɗuwar jinin mai ɗauke da virus din da jinin wanda ba shi da cutar. Misali:

    1. Yankewa: Idan wanda yake ɗauke da ƙwayar cutar Hepatitis ya yanke da abu mai kaifi (kamar reza, wuƙa, aska, almakashi da sauransu), to duk wanda ya yi amfani da wannan abu mai kaifin, kuma shi ma ya yanke, to virus ɗin za ta iya shiga jikinsa.

    2. Ƙarin jini: Idan aka ƙara wa mutum jini mai Hepatitis, to zai iya ɗaukar virus ɗin.

    3. Jima’i: Wanda yake da Hepatitis B Virus zai iya shafawa wanda ba shi da ita a lokacin jima’i.

    Yadda ake samun kariya daga cutar Hepatitis B virus

    1. Rigakafi: Akwai allura da ake yi domin samun kariya daga kamuwa da cutar Hepatitis B virus. Ana yin allurar ne sau uku, a tsawon wata shida. Idan aka yi wa mutum rigakafin, zai samu kariya mai yawan gaske.

    2. Kaucewa amfani da abu mai kaifi: A yi ƙoƙari wajen kaucewa amfani da duk wani abun da zai iya yankar mutum. idan kuma lallai sai anyi amfani da abu mai kaifi kamar lokacin yanke farce ko aski da sauransu, to kowa ya yi amfani da nasa shi kaɗai. A daina yi wa mutane aski ko yankan farce da abu guda ɗaya.

    3. Gwajin ƙwayar cutar Hepatitis B virus: Yana da kyau mutum ya je a yi masa gwajin ƙwayar cutar Hepatitis B virus domin ya san ko yana da ita ko ba shi da ita. Idan ba shi da ita, sai ya je a yi masa allurar rigakafi. Idan kuma yana da ita, sai ya yi ƙoƙari wajen kaucewa yaɗa ta.

    4. Kaucewa taɓa jinin mutum: Taɓa jinin wanda yake ɗauke da virus ɗin Hepatitis B ba tare da safar hannu ba, za iya janyowa a ɗauki cutar musamman idan akwai ciwo (komai ƙanƙantar sa) a hannun.

    5. Tantance jini kafin ƙara wa mutum: Masu aiki a ɗakin gwaje-gwaje da ɗaukar jini, su tabbata sun yi gwajin Virus ɗin Hepatitis B da ma wasu cututtukan kafin su ɗauki jinin mutum.

    Alamomin ciwon hanta na Hepatitis B virus

    Idan virus ɗin Hepatitis B ta shiga jikin mutum, ba lallai ya ji wata alama ba, kuma ba lallai ya san ya ɗauki cutar ba. Amma wani lokacin, cutar hanta tana iya nuna waɗannan alamomi idan ta shiga jikin mutum;

    • Zazzaɓi
    • Kasala
    • Ciwon ciki
    • Canjawar ido zuwa launin rawaya (yellow) ko kore
    • Ciwon jiki da sauransu
    Bayan waɗannan alamomin na ɗan wani lokaci, virus ɗin za ta iya ci gaba da zama a jikin mutum ba tare da ta janyo masa wani abu ba.

    Rayuwar Hepatitis B Virus a jikin ɗan adam

    Idan cutar Hepatitis B virus ta shiga jikin mutum, ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan za su faru:

    1. Ƙwayar virus ɗin za ta iya janyo wa mutum ciwon hanta mai tsanani wanda zai iya yin sanadiyar mutuwar mutum.
    2. Ƙwayar virus ɗin za ta iya ci gaba da zama a jikin mutum na tsawon lokaci ba tare da ta janyo masa ciwon hanta mai tsanani ba, amma zai iya yaɗa cutar.
    3. Ƙwayar virus ɗin za ta iya mutuwa da kanta ba tare da an sha mata wani magani ba.

    Alamomin ciwon hanta mai tsanani sun haɗa da:

    • Kumburin jiki, musamman ciki da ƙafa
    • Aman jini
    • Yin kashi baƙiƙƙirin kamar kwalta
    • Ramewa
    • Fita daga hayyaci

    Maganin Hepatitis B virus

    A likitance, babu magani guda ɗaya wanda yake kashe virus ɗin. Amma akwai wasu magunguna da ake ba wa mai cutar domin rage ƙarfin tasirin ta a jikinsa. Ba a bayar da maganin sai mai cutar ya cika wasu ƙa’idoji da sharuɗa.

    Idan mutum bai cika waɗannan ƙa’idoji da sharuɗa ba, to ba za a rubuta masa maganin ba. Zai ci gaba da gudanar da rayuwar sa kamar yadda ya saba. Sai dai kawai zai dinga zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci domin kula da ci gaban cutar.

    Shawarwari ga masu ciwon Hepatitis B virus

    • Za ka iya ci gaba da gudanar da rayuwarka cikin ƙoshin lafiya duk da cewa kana da Hepatitis B virus. Amma akwai buƙatar a dinga zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci.

    • A Kaucewa yaɗa cutar ta hanyar daina yin amfani da abubuwa masu kaifi na kowa da kowa kamar su almakashi da reza da abin yankan farce da sauransu.

    Wasu abubuwa da ake alaƙanta su da ciwon hanta

    1. Shan rake: Shan rake ba ya maganin ciwon hanta ko wane iri ne.

    2. Sinadarin abinci mai gina jiki (Protein): Mai cutar Hepatitis B virus, zai ci abinci kamar yadda kowa yake ci. Babu abin da zai hana shi cin abinci mai gina jiki kamar su nama, kifi, ƙwai, gyaɗa, wake da sauransu.

    Idan mutum yana da ciwon hantar da ya janyo masa rashin lafiya mai tsanani, ana buƙatar ya rage cin abinci mai gina jiki (protein) ya kuma yawaita cin abinci mai sa kuzari kamar su tuwo, shinkafa, doya da sauransu (Carbohydrate).

    A kula sosai, ban ce a daina cin mai gina jiki ba, cewa na yi ya rage. Kuma ba a ce ya dinga shan rake ba, cewa aka yi abinci mai saka kuzari.

    Wannan bayani an samo shi ne daga Hamisu Adam Abubakar.

    Domin karanta Ciwon Suga (Diabetes) danna nan.

  • Jiga-jigan Magunguna

    Jiga-jigan Magunguna

    Ga abin da Allah (Subhanahu wata’ala) Ya ce game da mafificin littafinsa Alƙur’ani mai tsarki.“Kuma muna saukar da abin da yake waraka da jinƙai a wannan Alƙur’ani ga muminai kuma ba ya ƙarar azzalumai (wato kafirai) da komai sai taɓewa”.

    Kuma Allah Ya ce da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam):“…. ka ce shi (Alƙur’ani) shiriya ce da waraka ga waɗanda suka yi Imani”.

    A sakamako wannan bayani na Allah (Subhanahu wata’ala) Alƙur’ani waraka ce game da matsalolin zukata kuma magani ne game da cututtukan jiki.

    Kuma shi ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake karanta Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi ya shafe jikinsa duk dare.
    Kamar yadda Hadisi ya inganta cewa ɗaya daga cikin sahabbai ya yi wa wani mutum da kunama ta harba ruƙuya da fatiha ya warke nan take.

    Kuma an karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda da su daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce “Waraka na tare da abubuwa Uku:

    1. Jinin da aka jawo da ƙaho
    2. Maƙwararar zuma
    3. Lalas (sakiya) da wuta. Sai dai ni ina hana al’ummata yin lalas.”
    Bukhari ne ya rawaito shi.

    Sannan kuma ƙwayoyin baƙin algaru (habbatus-sauda) suna bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawar da cututukan sanyi, kamar yadda bayani ya gabata.
    Nonon raƙumi da fitsarinsa magani ne da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa ya yi umarni da a sha su don samun waraka daga cuta. Kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

    Bayan haka, addu’a ma na maganta matsaloli da cututtukan da suka addabi bayi, kamar yadda bayani ya gabata cewa, Annabi Ayyub (Alaihis-Salam), ya roƙi Allah warakar ciwon da ya same shi, Allah ya amsa masa Ya yaye masa ciwon.
    Haka kuma sadaka na maganta cututtuka; ta kuma tafiyar da zunuban bawa kamar yadda ruwa yake kasha wuta. kamar yadda hadisai tabbatattu suka tabbatar.

    Amfani da ruwan Zam-Zam yana maganin cutar da aka sha shi dominta, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin A Kula Da Lafiya wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa shi. Domin karanta cikekken littafin danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Yin Air-Freshner Na Ruwa.

    Yadda Ake Yin Air-Freshner Na Ruwa.

    Air-freshner sinadarin ƙamshi ne da ake amfani da shi, wajen ƙawata guri ko muhalli. Yakan taimaka matuƙa wajen bayar da ƙamshi mai daɗi da saka nutsuwa a guri.

    Ana  bukatar air-freshner ya zama mai daɗi da lallausan ƙamshi domin mutane su ji daɗin sa. Akwai air-freshner iri daban-daban a kasuwanni, amma ingancin wanda za a haɗa shi zai sa a samu nagartar sa.

    Abubuwan Da Ake Bukata

    Sinadaran Haɗin                 Adadi
    1. Ruwa                          5 liters
    2. Ethanol                       5 liters
    3. Catalyst                      30mls
    4. Industrial camphor   ½ na ƙaramin cokali
    5. Menthol                  ½ na ƙaramin cokali
    6. Turaren Ambipure        50mls
    7. Turaren rose                50mls
    8. Kala                           Yadda ake so

    Yadda Ake Haɗin

    1. A auna ruwa liter 1 a cikin abin kwaɓin
    2. Sannan a zuba ethanol a cikin ruwan
    3. Sai a zuba irin kalar da ake so a ciki
    4. A zuba menthol, catalyst da industial camphor a ci gaba da damawa, har sai ya yi laushi
    5. Sai a ɗauko turarukan haɗin guda biyun a zuba a cikin haɗin, daga nan kuma an kammala haɗin sai a zuzzuba a cikin robobi domin amfanin yau da kullum.

    Domin sanin yadda ake Dettol, Da yadda ake bleach da yadda ake sabulu na ruwa domin wanke mota , Da yadda ake sabulun wanki na ruwa, Da yadda ake sabulun wanka, Da yadda ake sabulun wanki danna koren rubutu.

     

  • Yadda Ake Dettol

    Yadda Ake Dettol

    Dettol sinadari ne da ake amfani da shi wajen kashe kwayoyin cututtuka. Akan zuba shi a cikin ruwan wanka domin a kashe kwayoyin cutar da yake a ruwa, sannan sau da yawa akan yi amfani da shi wajen goge ɗanyen ciwo da yake a kan fata, domin a kawar da kwayoyin cuta da yake a kan ciwon. Sau da yawa akan yi amfani da shi a ciikin ruwan wanki, domin kawar a ƙwayar cuta.

    Amfani da Dettol na da matukar amfani, domin kuwa har mata masu jego kan yi amfani da shi wajen ɗaurayar kayan yaransu, duka saboda kawar da cututtuka da ke a kan fata, kaya har ma da goge-gogen kan tayels.

    Abubuwan Da Ake Bukata

    Sinadaran Hadin            Adadi
    1. Pine oil                        10cl
    2. Phenol (water based)    30cl
    3. Carbolic acid                30cl
    4. Texapol                       10cl
    5. Ruwa                          5 liters
    6. Kala                           Yadda ake so
    7. IPA / methanol            2 liters
    8. Preservation (formalin) 5CL
    9. Flavor Yadda ake so

    Yadda Ake Haɗin

    1. A kala da ruwa a dama.
    2. Sannan a zuba phenol a ci gaba da damawa.
    3. Sai a zuba IPA, texapol, carbolic acid da pine oil a ciki a ci gaba da damawa.
    4. A zuba flavor da preservative
    5. Daga nan kuma an kammala hadin sai a zuba a cikin robobi domin amfanin yau da kullum.

    Domin sanin yadda ake Bleach, Da yadda ake sabulu na ruwa domin wanke mota, Da yadda ake sabulun wanki na ruwa, Da yadda ake sabulun wanka, Da yadda ake sabulun wanki danna koren rubutu.

     

     

  • Yadda Ake Dettol

    Yadda Ake Dettol

    Dettol kowa ya sani sinadarin kashe kwayoyin cututtuka ne. Akan yi amfani da shi wajen zuba shi a cikin ruwan wankanmu ko a kan ciwo, domin kashe ƙwayar cuta, domin sau da yawa akan saka shi a cikin  akwatin taimakon gaggawa. Amfani da Dettol a ruwa ko da yaushe yakan ƙara wa jiki lafiya .

    Sau da dama akan yi amfani da shi wajen ɗaurayar kaya domin kashe ƙwayoyin cuta da yake a kan kayan, sannan ana zubawa a cikin ruwan goge-goge. Muna iya amfani da shi a wurare da dama domin kashe ƙwayoyin cuta. Mata masu jego na amfani da Dettol wajen inganta lafiyar jariransu.

    Abubuwan Da Ake Buƙata 

    Sinadaran Haɗin                        Adadi
    1. Pine oil                10cl
    2. Phenol (na ruwa)             30cl
    3. Carbolic acid              30cl
    4. Texapol             10cl
    5. Ruwa              5cl
    6. Kala             yadda ake so
    7. IPA / methanol              2 liters
    8. Preservation (formalin)  5cl
    9. Flavour yadda ake so

    Yadda Ake Haɗin 

    1. A haɗa ruwa da kala a dama.
    2. Sannan a zuba phenol a ci gaba da damawa.
    3. A ƙara IPA da sauran sinadaran Haɗin a dama su.
    4. A zuba flavor da preservative a cigaba da damawa har sai ya damu da kyau.
    5. Daga nan kuma an kammala haɗin , sai a zuzzuba a robobi domin amfaninmu na yau da kullum.

    Domin  sanin yadda ake Bleach, Da yada ake sabulu na ruwa domin wanke mota, Da yadda ake sabulun wanka, Da yadda ake sabulun wanki na ruwa, Da yadda sabulun wanki.

  • Yadda Ake Haɗa Sinadarin Bleach

    Yadda Ake Haɗa Sinadarin Bleach

    Bleach kowa ya sani sinadari ne da ake amfani da shi wajen ƙara wa fararen kaya, banɗaki da tiles ɗinmu haske.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    Sinadaran Hadin            Adadi
    1.  HTH ( chlorine )         1kg
    2. Sodium hydroxide       5kg
    3. Soda-ash                    1 kg
    4. Ruwa                          20 liters
    5. T.P.P                           0.25 kg

    Yadda Ake Hadawa

    1. A auna HTH din a cikin bokiti.
    2. A zuba hydroxide, soda-ash da stpp a ciki a motsa su
    3. A kawo 10 liters na ruwa a zuba a ciki sai a dama .
    4. A bar shi ya jiƙu, har na tsawan awa 72, sai a tace shi.
    5. A saka alimun a ciki ko da akwai sauran abin da bai narke ba, zai narkar da shi.
    6. A zuba a jarka , daga nan kuma ya kammala sai amfanin mu na yau da kullum.

    Domin sanin yadda ake sabulu na ruwa domin wanke mota Da yadda ake sabulun wanki na ruwa Da yadda ake sabulun wanki Da yadda ake sabulun wanka koren rubutun

     

     

  • Yadda Ake Sabulu Na Ruwa, Domin Wanke Mota

    Yadda Ake Sabulu Na Ruwa, Domin Wanke Mota

     Da yawa an sani cewa, ba a wanke mota da kowane irin sabulun wanki, sai da sabulun wanke mota wato (Car wash solution).  Amfani da kowane irin sabulu wajen wanke mota, yana saka kalar motar kodewa, sannan ya lalata ainihin kalar motar. Abu mafi sauƙi da inganci wajen wanke mota shi ne subulu na ruwa domin wankin Mota (car wash solution).

    Wannan haɗin na da matukar sauƙi da amfani, kuma ana samun gwaggwabar riba wajen yin sana’ar sa. Mu jarraba domin mu koya kuma mu ci ribarsa.

    Abubuwan Da Ake Bukata

     Sinadaran Hadin          Adadi
    1. Antisol or parasol         25kg
    2. Light Soda-ash             5kg
    3. Sulphonic acid              5 liters
    4. Colorant                       Yadda ake so
    5. Fragrance                     Yadda ake so
    6. Water                           Yadda ake so
    7. Sodium Benzoate           30 mls
    8. SLS                               ¼ kg
    9. Texapoon                       250 mls

     Yadda Ake Hadawa

    1. A jika Antisol da ruwa ya kwana sannan a dama shi ya yi laushi, har sai ya saki jikinsa daga curin da ya yi.
    2. A narkar da soda-ash a cikin ruwa kaɗan.
    3. A zuba soda-ash a cikin kwabin antisol din nan a dama su tare.
    4. A zuba sulphonic acid, sls da texapoon a cikin hadin a cigaba da motsawa.
    5. A kwaɓa kala da ruwa, sannan a zuba a cikin haɗin.
    6. A ci gaba da damawa har sai ya y,i laushi ya damu da kyau.
    7. Daga nan kuma an kammala haɗin, sai amfanin yau da kullum.

    Domin sanin yadda ake sabulun wanki na ruwa da sabulun wanka da sabulun wanki dannan koren rubutun

     

     

     

     

     

  • Yadda Ake Sabulun Wanki Na Ruwa

    Yadda Ake Sabulun Wanki Na Ruwa

     Sabulu wanki na ruwa an sani sabulu ne mafi karfi a cikin sabulai. Akanyi amfani dashi wajen abubuwa da dama kamar : wankin kaya, wankiin bandaki da wankin kwanuka.Za’a iya fara wannan hadin  da kudi kalilan, kuma hadin shi yana da matukar sauki.

    Abubuwan Da Ake Bukata

    Sinadaran Hadin          Adadi

    1.  Pac-R                          25Kg
    2.  STPP                           5Kg
    3.  Table salt (NaCI2)         75gm
    4.  SLES                            1/2Kg
    5.  Turaren hadin               Yadda akeso
    6.  Kala                             Yadda akeso
    7.  Ruwa                           20 liters

    Yadda Ake Hadawa

    1. A auna duka adadin abinda ake bukata na sinadaran hadin din.
    2. A saka SLES din a cikin kwano/ ko robar da za’a kwaba, sannan a zuba ruwa kadan a ciki.
    3. A dama shi yayi laushi.
    4. A zuba 0.25kg na Pac-R sannan a cigaba da dama/motsa shi har sai yayi laushi, a dinga kara ruwa a lokacin da yake kara kunburi.
    5. A saka STTP a cikin kwano na daban na ruwa madaidaici a dama sosai, sannan a zuba shi a kwabin farko.
    6. A shigaba da damawa har sai ya damu da kyau.
    7. A kwaba wannan gishirin da ruwa , sannan a zuba a cikin kwabin a cigaba da damawa.
    8. A zuba turaren hadin wato a cikin kwabin a cigaba da damawa.
    9. Daga nan kuma sabulu ya kammala , sai a zuzzuba a robobi a fara amfani dashi.

    Domin Sanin yadda ake sabulun wanki ko sabulun wanka dannan koren ruubutun

     

  • Yadda Ake Sabulun Wanka

    Yadda Ake Sabulun Wanka

    Sabulun wanka shi ne sabulun da muke amfani da shi wajen wanke fatar jikinmu, wato (wanka). Domin haka, ana buƙatar ya zama mai kumfa da ƙamshi mai daɗi da kala mai kyau. Sannan ana buƙatar ya zama mai taushi a kan fata.

    Ana haɗinsa kwatankwacin yadda ake haɗin sabulun wanki, sai dai wasu abubuwan hadin sun bambanta da juna.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

     Sinadaran Hadin                       Adadi
    1. Palm Kannel Oil                      3 liters
    2. Caustic-soda ( Na Oh )            0.5 kg
    3. Coconut Oil                             0.5 liter
    4. Bleached Palm Oil                    0.5 liter
    5. Silicate                                    0.5 liter
    6.  Colourant                               Yadda akeso
    7. Perfume                                   Yadda akeso
    8. Titanium Dioxide                       10 kg
    9. Glycerin                                    250 mls
    Yadda Ake Hadawa:
    1. A hada Caustic-Soda din ta hanyar narkar da 1kg caustic soda a cikin 4.5 liters na ruwa. A tabbatar da cewa nauyinsa ya kai 1275kg/m3 kamar yadda aka yi wajen haɗin sabulun wanka. A bar haɗin ya kwana uku domin samun nagartarsa, kuma domin gujewa samun matsala a fata.
    2. A kawo mayukan duka: Palm kannel oil, Coconut oil, Bleach palm oil ɗin a zuba su duka a cikin kwano daban.
    3. Idan ya yi ɗumi sai a zuba colourant a yi ta juyawa har sai ya damu da kyau.
    4. Sannan a ɗauko wannan caustic-soda ɗin da aka dama da ruwa tun a farko, a juye a cikin kwaɓin mayukan wato (oils) ɗin nan.
    5. Idan aka motsa shi, aka tabbatar ya haɗe ko ya damu da kyau, sai a ɗauko sodium silicate a zuba a ciki, idan an zuba sai a bar sa ya huce.
    6. Idan ya huce sai a zuba turaren hadin(perfume) a ciki.
    7. Sai a kuma juya shi, sannan a zuba a cikin gwangwanayen sabulan.
    8. A bar shi ya yi ƙarfi/tauri a cikin gwangwanayen.
    9. Bayan awa 24 sai a yi tambari a kai, a yi masa fasali irin yadda ake so, sannan a yi pakeji. Daga nan kuma sabulu ya kamala.

    Domin Sanin yadda ake sabulun wanki na ruwa dannan koren rubutun

     

     

  • Yadda Ake Sabulun Wanki

    Yadda Ake Sabulun Wanki

    Idan aka ce sabulun wanki, an san ana nufin sabulun da ake amfani da shi wajen wanke tufafi, domin cire dauɗa, datti da wari da yake a jikin tufafi. Yana da kyau ya zama ingantacce, domin cire dauɗar da take a jiki kayan.

    • A saka a rai cewa, akwai sabulai kaloli kuma iri daban-daban a kasuwanni, amma hadin nan da za a yi zai zama haɗi ne da za a iya shiga ko wani irin gasa ba tare da fargaba a rai ba.
    • Wajen wannan haɗin a tabbata an yi amfani da turaren haɗin sabulu mai kamshi domin jan hankalin masu siya, turare mai daɗi sirri ne sosai wajen ɗaukar hankali.
    • A yi amfani da Kala (colourant) mai kyau wajen haɗin, domin samun ingantaccen sabulu bayan an kamala hadin. Yin hakan zai taimaka wajen samun nasara a cikin abin da aka haɗa.
    Na fara saka wannan gargaɗin ne domin a kula wajen haɗin da kokarin kare lafiyar kai, lafiya ita ce garkuwarmu, lafiya uwar jiki.
    1. A tabbatar an gane abin da yake a rubuce.
    2. Ya zama babu kuskure wajen awon kayan, ko adadin chemicals ɗin da za a yi amafani da su.
    3. Sannan a daidaita hadin chemicals ɗin a gwangwanayen su, domin samun abin da ake so.
    4. Abi shawarwarin koyarwar.
    5. Takunkumin hanci na da matukar amfani, domin gujewa  shaƙar chemical ɗin da zai iya cutarwa.
    6. Takunkumin hannu wato (Rubber hand gloves) Shi ma yana da matukar amfani wajen haɗin kayayyakin chemicals din nan, domin gujewa afkuwar kuna a hanu ko a fata. Wasu chemicals din suna da matukar zafi a fata ko tafin hannu.
    7. Za a iya amfani da rigar Lab coat wato (laboratory coat) wajen haɗin domin gujewa fallatsar chemicals ɗin a kaya.
    8. Kar a taɓa gangancin gwada chemicals  ɗin da hannu, ba tare da saka safar hannu ta rubber ba, yin hakan na da matuƙar hatsari.
    9. A yi nesa da ido wajen wannan haɗin domin kare lafiyar ido.
    10. A tabbatar ko wani kayan haɗin nan yana da ma’ajiya ta musamman domin yara, kuma da zarar an gama amfani da su, a mayar da su ma’ajiyar su a ɓoye.
    11. A karshe a tanadi (First-aid box) domin taimakon gaggawa a lokacin da abin da ba a fata ya afku wato fallatsar chemical mai zafi a fata, ko idan ya fallatsa a cikin baki a rashin sani. Domin haka sai a yi gaggawar wanke wajen da ruwan sanyi, idan kuma a baki ne sai anyi gaggawar kuskure baki, sannan a sha ruwan sanyi ko manja. Idan ba a samu sauƙin sa ba, sai a tuntubi likita.
    • Ba za a taɓa cin arzikin wannan sana’ar ba, idan ba a jarraba ta ba. Mashinan, karafe / gwangwanayen aikin da sinaran haɗin duka suna da saukin samu. A fara jarrabawa da abin da ya sauwaka, babu shakka za a yi murmushi a gaba da ikon Allah(S.W.A). Kar a taɓa cewa sai an tara kuɗi da yawa za a yi sana’a.
    • Hadin kayan nan yana tafiya ne wajen jarrabawa a koda yaushe, yin hakan ne kawai zai taimaka a ƙware.
    • Kar a taɓa karaya ko a ji tsoro cewa, akwai ƙwararrun masu haɗin, su ma da sannu suka kai matsayin da suke.
    • A sani kuma a saka a zuciya cewan kowane mutum da irin arzikin kasuwancinsa.
    • Idan an gamsu da shawarata to, a fara jarraba wannan sana’ar a yau. A gaba ba iya ribar iya sana’ar za a ci ba, harda ribar koyawa wasu.
    • Ina muku fatan Alkhairi.

    Abubuwan Da Ake Bukata:

    Sinadarai                              Adadi

    1. Caustic soda (Na OH)          1 kg
    2. Palm Kennel Oil ( P.K.O )     6 Liters
    3.  Soda ash ( light )              0.25 kg
    4. Silicate                              0.25 kg
    5. Sodium sulphate                 3 kg
    6. kala                                   Yadda ake so
    7. Ruwa                                  4.5 liters
    8. Turaren hadi                        Adadin da ake so
    9. Sinadarin kumfa                   250 mls
    Yadda Ake Hadawa:

    A hade Caustic-soda din ta hanyar narkar da 1kg Caustic-soda a cikin  4.5 liters na ruwa. A tabbatar da cewa nauyin sa  ya kai 1275kg/m3. A bar hadin ya kwana uku domin ya narke da kyau. A tabbatar ya yi wannan kwanakin domin samun nagartarsa, kuma domin gujewa samun matsala a fata ko a kan kaya.

    1. A zuba soda-ash ɗin a cikin wannan caustic soda ɗin da aka dama, aka bar shi ya yi kwanaki, sannan a yi ta motsa damun har sai ya yi yadda ake so, wato ya damu da kyau.
    2. sai ɗauko wannan Kalar ( colorant ) shi ma a zuba a cikin haɗin a ci gaba da damawa.
    3. Sannan kuma a ɗauko duka ( P.K.O ) wato Palm kennel oil a juye a cikin haɗin a juya ko na ce damawa ta tare da an mayar da hannu baya ba, kar a yi gaba ai baya nake nufi.
    4. Da kuma foaming agent wato ( sinadarin saka kumfa ) tare da Silicate a zuba su a ciki a ci gaba da motsawa.
    5. A ɗauko sinadarin kamshi wato turaren hadin sabulun, a zuba a cikin hadin. Sannan a zuba shi a cikin gwangwanayen sabulan,sai a bar shi na tsawan awa 24 ( 24hrs ) domin ya hade ya yi karfi.
    6. Bayan awa24 ( 24hrs ) nan kuma sai a yi tambari a kai, a yi masa fasali irin yadda ake so, sannan a yi pakajin su. Daga nan kuma sabulu ya kammala.

    Domin Sanin yadda ake sabulun wanka danna koren rubutun nan