Air-freshner sinadarin ƙamshi ne da ake amfani da shi, wajen ƙawata guri ko muhalli. Yakan taimaka matuƙa wajen bayar da ƙamshi mai daɗi da saka nutsuwa a guri.
Ana bukatar air-freshner ya zama mai daɗi da lallausan ƙamshi domin mutane su ji daɗin sa. Akwai air-freshner iri daban-daban a kasuwanni, amma ingancin wanda za a haɗa shi zai sa a samu nagartar sa.
Abubuwan Da Ake Bukata
Sinadaran Haɗin Adadi
- Ruwa 5 liters
- Ethanol 5 liters
- Catalyst 30mls
- Industrial camphor ½ na ƙaramin cokali
- Menthol ½ na ƙaramin cokali
- Turaren Ambipure 50mls
- Turaren rose 50mls
- Kala Yadda ake so
Yadda Ake Haɗin
- A auna ruwa liter 1 a cikin abin kwaɓin
- Sannan a zuba ethanol a cikin ruwan
- Sai a zuba irin kalar da ake so a ciki
- A zuba menthol, catalyst da industial camphor a ci gaba da damawa, har sai ya yi laushi
- Sai a ɗauko turarukan haɗin guda biyun a zuba a cikin haɗin, daga nan kuma an kammala haɗin sai a zuzzuba a cikin robobi domin amfanin yau da kullum.
Domin sanin yadda ake Dettol, Da yadda ake bleach da yadda ake sabulu na ruwa domin wanke mota , Da yadda ake sabulun wanki na ruwa, Da yadda ake sabulun wanka, Da yadda ake sabulun wanki danna koren rubutu.