Yadda Ake Yin Sabulun Wanki

0
1478

Sabulun wanki shi ne sabulun da ake wanke tufafi, domin cire dauɗa da warin da yake a jikin tufafi. Yadda ake sabulun wanki ya haɗa da:

Abubuwan Da Ake Buƙata

  Sinadiran Haɗawa                Adadi

  1. Caustic soda (Na OH)             1 kg
  2. Palm Kernel Oil ( P.K.O )         6 ltrs
  3. Soda ash ( light )                   0.25 kg
  4. Silicate                                  0.25 kg
  5. Sodium sulphate                    3 kg
  6. Kala(colour)                           Daidai Misali
  7. Ruwa                                    4.5 ltrs
  8. Sinadarin Ƙamshi                   Daidai Misali
  9. Sinadarin Saka Kumfa             250
Yadda Ake Haɗawa:
  1. A narkar da 1kg na caustic-soda a cikin 4.5ltrs na ruwa, nauyinsa ya kasance ya kai 1275kg/m3. A bar haɗin ya yi kwana uku domin ya narke da kyau. A tabbatar ya yi wannan kwanakin domin samun nagartarsa, kuma domin gujewa samun matsala a fata, ko a kan kaya.
  2. A zuba soda-ash ɗin a cikin wannan caustic-soda ɗin da aka dama aka bar shi ya yi kwanaki, sannan a yi ta motsa damun har sai ya yi yadda ake buƙata, wato ya damu da kyau.
  3. A ɗauko wannan launin (colour), shi ma a zuba a cikin haɗin, a ci gaba da damawa.
  4. A ɗauko duka (P.K.O) wato palm kennel oil a juye a cikin haɗin a juya ko na ce damawa ba tare da an mayar da hannu baya ba, kar ayi gaba ai baya nake nufi.
  5. A ɗakko sinadarin saka kumfa, tare da silicate a zuba su a ciki a cigaba da motsawa.
  6. A ɗakko sinadarin ƙamshi (wato turare) a zuba a cikin haɗin. Sannan a zuba shi a cikin gwangwanayen sabulan, sai a bar shi na tsawan awa ashirin da huɗu(kwana ɗaya) domin ya haɗe jikinsa,don ya yi ƙarfi.
  7. Bayan awa ashirin da huɗu ɗin nan kuma, sai a yi tambari a kai, a yi masa fasali irin yadda ake so, sannan a yi fakejin su. Daga nan kuma sabulu ya kammala.

Gargaɗi:

  • A saka a rai cewa akwai sabulai kaloli kuma iri daban-daban a kasuwanni, amma haɗin nan da za a yi, zai zama haɗi ne da za a iya shiga kowace irin gasa ba tare da fargaba a rai ba.
  • Wajen wannan haɗin a tabbata an yi amfani da turaren haɗin sabulu mai ƙamshi domin jan hankalin masu saya. Turare mai daɗi sirri ne sosai, wajen ɗaukar hankalin masu saye.
  • A yi Amfani da kala mai kyau wajen haɗin, domin samun ingantaccen sabulu. bayan an kammala haɗin. Yin hakan zai taimaka wajen samun nasara a cikin abin da aka haɗa.

Domin karata yadda ake sabulun wanka dannan koren rubutun nan.

labarin da ya wuceBa Duka Wanda Ke Da Ciwon Dake Warkewa Ba Ne Yake Warkewa
Labarin na GabaAbubuwan Dake Jawo Asarar Lokaci A Rayuwar Ɗan Adam