Yadda Ake Sabulun Salo Na Amare

0
3766

A yau za mu koyi yadda ake sabulun salo na amare domin gyaran jiki da fata ta yi kyau, kyalli da kuma laushi.

Abubuwan da ake buƙata

Sabulun salo 8
Sabulun wanka 6
Majigi 3

Man kwakwa cokali 2
Mai Zaitun babban cokali 2
Zuma cokali babba 3

Lemon tsami rabi
Jar kanwa kwata
Aloevera 3
Kwanduwar kwai 3

Yadda ake haɗawa

Ki goga sabulun wanka a magogi, ki haɗa shi da sabulun salo a cikin turmi.

Sai ki kawo dukkan kayan haɗin nan, ki zuba su a turmi.

Ki yi ta dakawa har sai sun haɗe jikinsu tsab.

Sai ki dinga dangwalar man kwakwa a hannunki kina gutsura sabulu.

Sai ki cura shi yadda kike son girmansa.

Domin sanin yadda ake omo danna nan