Yadda Ake Garin Sabulu (Omo)

0
2265

A yau za mu koyi YADDA AKE OMO, Omo na ɗaya daga cikin abubuwan amfanin gida na yau da kullum, wanda ke da matuƙar amfani, haɗa omo na da sauƙi da kuma samun sauki a yin sa, musamman ma idan aka bi ka’idojin sa

Abubuwan da ake buƙata

Safar hannu
Flavour
Kala
Taxapon kilo 1
Soda ( Ash light) kwano 1.

Yadda ake haɗawa

  1. A samu Roba a juye Taxapon kilo 1 da Soda kwano 1.
  2. Sai ki sa safar hannu, ki haɗe su ki yi ta juyawa.
  3. Ki ci gaba da murzawa, har sai ya zama gari luƙui.
  4. Sai ki sa flavour ƙamshin da ki ke so.
labarin da ya wuceWace Ce Ta Karɓi Haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)?
Labarin na GabaYadda Ake Sabulun Salo Na Amare
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.