Dettol kowa ya sani sinadarin kashe kwayoyin cututtuka ne. Akan yi amfani da shi wajen zuba shi a cikin ruwan wankanmu ko a kan ciwo, domin kashe ƙwayar cuta, domin sau da yawa akan saka shi a cikin akwatin taimakon gaggawa. Amfani da Dettol a ruwa ko da yaushe yakan ƙara wa jiki lafiya .
Sau da dama akan yi amfani da shi wajen ɗaurayar kaya domin kashe ƙwayoyin cuta da yake a kan kayan, sannan ana zubawa a cikin ruwan goge-goge. Muna iya amfani da shi a wurare da dama domin kashe ƙwayoyin cuta. Mata masu jego na amfani da Dettol wajen inganta lafiyar jariransu.
Abubuwan Da Ake Buƙata
Sinadaran Haɗin Adadi
- Pine oil 10cl
- Phenol (na ruwa) 30cl
- Carbolic acid 30cl
- Texapol 10cl
- Ruwa 5cl
- Kala yadda ake so
- IPA / methanol 2 liters
- Preservation (formalin) 5cl
- Flavour yadda ake so
Yadda Ake Haɗin
- A haɗa ruwa da kala a dama.
- Sannan a zuba phenol a ci gaba da damawa.
- A ƙara IPA da sauran sinadaran Haɗin a dama su.
- A zuba flavor da preservative a cigaba da damawa har sai ya damu da kyau.
- Daga nan kuma an kammala haɗin , sai a zuzzuba a robobi domin amfaninmu na yau da kullum.
Domin sanin yadda ake Bleach, Da yada ake sabulu na ruwa domin wanke mota, Da yadda ake sabulun wanka, Da yadda ake sabulun wanki na ruwa, Da yadda sabulun wanki.