Sabulu wanki na ruwa an sani sabulu ne mafi karfi a cikin sabulai. Akanyi amfani dashi wajen abubuwa da dama kamar : wankin kaya, wankiin bandaki da wankin kwanuka.Za’a iya fara wannan hadin da kudi kalilan, kuma hadin shi yana da matukar sauki.
Abubuwan Da Ake Bukata
Sinadaran Hadin Adadi
- Pac-R 25Kg
- STPP 5Kg
- Table salt (NaCI2) 75gm
- SLES 1/2Kg
- Turaren hadin Yadda akeso
- Kala Yadda akeso
- Ruwa 20 liters
Yadda Ake Hadawa
- A auna duka adadin abinda ake bukata na sinadaran hadin din.
- A saka SLES din a cikin kwano/ ko robar da za’a kwaba, sannan a zuba ruwa kadan a ciki.
- A dama shi yayi laushi.
- A zuba 0.25kg na Pac-R sannan a cigaba da dama/motsa shi har sai yayi laushi, a dinga kara ruwa a lokacin da yake kara kunburi.
- A saka STTP a cikin kwano na daban na ruwa madaidaici a dama sosai, sannan a zuba shi a kwabin farko.
- A shigaba da damawa har sai ya damu da kyau.
- A kwaba wannan gishirin da ruwa , sannan a zuba a cikin kwabin a cigaba da damawa.
- A zuba turaren hadin wato a cikin kwabin a cigaba da damawa.
- Daga nan kuma sabulu ya kammala , sai a zuzzuba a robobi a fara amfani dashi.
Domin Sanin yadda ake sabulun wanki ko sabulun wanka dannan koren ruubutun