Tag: yadda ake

  • Yadda Ake Haɗa Hallaka Kwabo

    Yadda Ake Haɗa Hallaka Kwabo

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin hallaka ƙwabo ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Hallaka kwabo nau’in alawa ce da ake yi da gyaɗa wadda za a iya ajiyewa domin ba wa yara.

    Abubuwan Buƙata

    1. Gyada mai kyau
    2. Sugar
    3. Lemon tsami (a matse ruwan)

    Yadda ake haɗawa

    1. A daddaka gyaɗa, amma ba sosai ba
    2. Cikin tukunya mai tsafta a zuba ruwa, sugar da lemon tsami, a bar shi ya dahu na mintuna 18-20
    3. A zuba gyaɗa, a ci gaba da juyawa sai ya yi brown sosai
    4. A shafa mai a farantin silver sai a juye wannan hallaka kwabo a kai, a baza shi sosai
    5. Sai a yayyanka shi zuwa desired shapes

    Domin koyon Yadda Ake Biskit din Gyaɗa (groundnut cookies) danna nan

  • Yadda Ake Haɗa Lemon Gyaɗa, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake)

    Yadda Ake Haɗa Lemon Gyaɗa, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake)

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake yin lemon gyaɗa, shinkafa da dankalin Hausa (groundnut, rice, sweet potato shake) ku biyo ni a sannu, domin mu koya tare……

    Ko kun san Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.

    Abubuwan Buƙata

    1. Shinkafa ½ rabin kofi
    2. Gyaɗa ½ rabin kofi
    3. Dankalin Hausa
    4. Gyaɗa soyayyiya
    5. Siga
    6. Madara

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A wanke shinkafa a jiƙa ta, sai ta yi laushi.
    2. A fere dankalin Hausa a yayyanka.
    3. A soya gyaɗa a busar da ita.
    4. Sai a haɗe gyaɗa, dankali da kuma jiƙaƙƙiyar shinkafa a markaɗa a tace da abun tata.
    5. A raba ruwan gyaɗa biyu, a ɗora a wuta har sai ya yi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke a haɗe da ragowar ruwan gyaɗar, a saka madara da siga. Za a iya ƙara ruwa daidai kaurin da ake so.
    6. Za a iya tace shi da rariya, idan ya yi gudaji-gudaji, sai a saka a fridge ya yi sanyi.
    7. Asha lafiya.
  • Yadda Ake Biskit Ɗin Gyaɗa (groundnut cookies)

    Yadda Ake Biskit Ɗin Gyaɗa (groundnut cookies)

    Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake yin Biskit ɗin Gyaɗa (groundnut cookies); ku biyoni a sannu domin mu koya tare…

    Ko kun san Gyaɗa na rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya wato cardiac disease.

    Abubuwan Buƙata

    1. Fulawar gyaɗa ½ kofi
    2. Fulawa 1 cup
    3. Bota ½ cup
    4. Siga ½ rabin kofi
    5. Filebo flavor babban cokali daya
    6. Baƙin hoda Baking powder ½ tablespoon
    7. Bicarbonate soda ½ teaspoon ƙaramin chokali

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A buga siga da bota sai aukin ya ninku
    2. A saka sauran kayan (fulawa, filebo, baking powder, bicarbonate soda da sauransu). A juya har sai yayi tauri.
    3. A murza da rolling pin sai a saka cookies cutter a yayyanka zuwa shape kala-kala
    4. A gasa cikin abun gashi na minti 15 sai a fito dashi

    Domin koyan Yadda Ake Kek Ɗin Gyaɗa (Groundnut Cake) danna nan

  • Yadda Ake Donut

    Yadda Ake Donut

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake yin donut na gyaɗa. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san kwaɓin biredi da doughnut iri ɗaya ne?

    1. Idan dough ɗin ya tashi, sai a sami chopping board da rolling pin; ana gutsurar wannan dough ɗin ana sake murza shi sai a saka donut cutter a yanka.
    2. A ɗora mai a wuta, idan ya yi zafi, a saka wannan donut ɗin; idan ya yi golden brown sai a juya ɗaya ɓarin.
    3. Idan dukkannin ɓarin sun soyu, a kwashe a matsami, za a iya sha da lemo ko shayi.

    Domin sanin Yadda Ake Biredin Gyaɗa danna nan

  • Yadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread)

    Yadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread)

    Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na Girke-Girken WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake yin Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread); ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san Gyada na ɗauke da sinadarin protein wanda ke taimako wurin gina jikin mu.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Fulawa kofi 3
    2. Bota ¼ kofi
    3. Fulawar gyaɗa (Groundnut flour) kofi ɗaya
    4. Yis (Yeast) ƙaramin cokali 1
    5. Bakin hoda I (Baking powder)1 rabin ƙaramin cokali
    6. Ƙwai guda 1
    7. ½ rabin kofin siga
    8. ½ rabin ƙaramin cokali na gishiri

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A zuba ruwa a kofi, sai a zuba yeast da sugar a juya abarshi kamar minti 3-4.
    2. A haɗa sauran kayan haɗi (flour, butter, ƙwai, fulawar gyaɗa, gishiri). Kar a manta a chakuɗa sosai.
    3. A zuba ruwan yis sai a ɗan ƙara ruwan ɗumi a cakuɗa har sai ya haɗe jikinshi. Note:- ya ɗan fi kwaɓin cincin amma karya kai na fanke tsaka-tsaki.
    4. A sami film ko tsumma mai kyau a rufe a kai shi rana ya tashi sai ayi punching tsakiyar iska ya fita sai abarshi ya ƙara tashina minti uku zuwa huɗu.
    5. A yayyanka a sakashi a cikin gwangwanin gashi da aka shafa bota da flour. A ƙara barin shi ya tashi.

    A saka biredin cikin abun gashi sai yayi golden colour. Temperature 1800c.

    Domin sanin yadda ake kek ɗin gyada danna nan

  • Yadda Ake Kek Ɗin Gyada (Groundnut Cake)

    Yadda Ake Kek Ɗin Gyada (Groundnut Cake)

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake kek ɗin gyaɗa (Groundnut Cake). Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san gyaɗa tana ɗauke da sinadarai irin su vitamin E, zinc da kuma magnesium wanda yake taimako wajen gyara fata.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Soyayyar gyada.
    2. Fulawa kofi ɗaya
    3. Fulawar gyada ¼ cup
    4. Siga ½ kofi
    5. Bota ¼ kofi
    6. ƙwai 4
    7. Flavour 1 teaspoon
    8. Baƙin hoda (Baking powder) 1 teaspoon
    9. Madara ½ kofi.

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A buga bota da siga da kyau, har sai aukin botar ya ninku.
    2. Sai a zuba filabo (flavour), ƙwai da madara, a sake buga su sosai.
    3. Sannnan a zuba flour da baking powder, sai a buga shi kamar na minti uku zuwa huɗu sai a zuba marmashasshiyar gyaɗa a juya.
    4. A shafa wa gwangwanin cake bota, sai a barbaɗa fulawa.
    5. A zuba kwaɓin cake a cikin gwangwanin, sai a ɗauko crushed gyaɗa a barbaɗa a saman kwaɓin
    6. A saka cake a cikin abin gashi kamar na minti 15 ko idan an zura tsinke ya fito babu ƙullin kek a jiki.

    Domin sanin Yadda Ake Kunun Gyaɗa danna nan

  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida NIjeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake Kunun Gyaɗa Mai Gasara. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Abubuwan buƙata

    1. Gasarar gyaɗa (groundnut butter)
    2. Gero
    3. Citta [optional]

    Yadda ake haɗawa

    1. A jiƙa gero da daddare zuwa safe, sai a saka citta a kai markaɗe, in an dawo a tace, a fitar da dusa.
    2. A ɗebo gasarar gyaɗa sai a zuba wadataccen ruwan da zai dama kunu. A juya da kyau a sa rariya a tace a cikin tukunya mai zurfi a ɗora a kan wuta.
    3. Idan gasarar gyaɗar ya tausa sai ajuye a cikin gasarar gero a juya. Sai a zuba lemon tsami, ko tsamiya ko ɗan tsami
    Domin sanin yadda ake kunun gyada danna nan
  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin  kunun gyaɗa. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san kunun gyaɗa mai shinkafa na bayar da kuzari wanda carbohydrate ke badawa? Sannan gyaɗa na ba anadario vitamin B3 (niacin) wanda ke taimakon breaking down carbohydrates into energy.

    Abubuwan Buƙata

    1. Gyaɗa (kofi ɗaya ) (a soyata sannan a bakace)
    2. Shinkafa [kofi ɗaya]
    3. Citta [optional]
    4. Lemon tsami [to taste] [har sai ya ji]

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A zuba gyaɗa cikin tukunya mai dan zurfi, sai a soya ta sama-sama,  sai a juye a bakace ta, a fitar da fatar tas.
    2. Sannan cikin bokiti ko roba mai zurfi, a zuba shinkafa da gyaɗa, citta in ana buƙata sai a kai markaɗe.
    3. Idan an markaɗo sai a saka abin tata a tace.
    4. Sai cikin tukunyar mai zurfi sai a zuba gasarar kunun a yi ta juyawa har sai ya yi ƙauri.
    Sai a zuba lemon tsami a taɓa a ji, in tsamin ya yi ko bai yi ba. A yi a hankali wurin zuba lemon tsamin, kar ya yi yawa. Kuma kar ya yi kaɗan saboda in ya yi kaɗan kunun zai iya tsinkewa
    Domin sanin Yadda Ake Abincin Yara danna nan
  • Yadda Ake Therapeutic Food (Abincin Yara)

    Yadda Ake Therapeutic Food (Abincin Yara)

    Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake Abinci yara (therapeutic food); ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san:- Yara masu cutar yunwa (tamowa) idan ana basu wannan zai kara musu kuzari da kumara a jiki.

    Abubuwan Buƙata

    1. Gyaɗa (kofi biyu)
    2. Waken suya (kofi biyu)
    3. Dawa (kofi shida)
    4. Siga
    5. Madara (in ana buƙata).

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A soya Gyaɗa a busheta sannan a niƙa
    2. A soya Waken (Soya Beans) shima a niƙa
    3. Dawa itama a soyata sannan a niƙa
    4. Cikin roba mai kyau a haɗa dukkanin garin (Wake Soya, Dawa da kuma Gyaɗa) a juya da kyau sai a sami leda mai kyau a juye a cikin sannan a saka a roba mai murfi a rufe. Duk sanda za’ayi sai a ɗiba.

    Yadda ake haɗa kunun

    • A ɗora tukunya mai zurfi sannan azuba ruwan zafi kaɗan yadda zai isa (kamar talge).
    • A ɗan kofi ko roba a ɗebi garin kunun yara sai azuba ruwa a cikin ɗan kaɗan a dama.
    • Idan ruwan ya tausa sai azuba wannan gasarar kunun a cikin ruwan ayita juyawa har sai yayi kauri
    • Za’a iya saka madara domin ƙarin daɗi kuma za’a iya sha a haka.

    Domin sanin Yadda Ake Gasarar Gyaɗa (Peanut Butter) danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal

    Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal

    A yau za mu koyi yadda ake shinkafa ‘yar Senegal. Shinkafa ‘yar Senegal na da matuƙar daɗi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Shinkafa
    • Karas
    • Koren wake
    • Tattasai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Niƙaƙƙen nama
    • Magi
    • Kori
    • Garin tafarnuwa da citta

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A ɗora tukunya da ruwa a cikinta, har sai ya tafasa, sannan a ɗauko shinkafa ’yar wara a wanke a zuba a ciki.
    2. Idan ta ɗan tafasa kamar na minti 10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
    3. Sannan a samu ɗanyen nama a niƙa shi. Naman ya kasance da ɗan yawa.
    4. A sake ɗora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyaɗa a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai.
    5. Sannan sai a zuba niƙaƙƙen naman a ciki, a ci gaba da soya shi, sannan a ɗauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa.
    6. Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a sauke.
    7. A samu salad a yayyanka a dafa ƙwai a zuba “cream” sannan a ɗora a ci, ita da jus ɗin lemo.

    Domin sanin yadda ake sharbar dankali danna nan