Tag: yadda ake

  • Yadda Ake Sharɓar Dankali

    Yadda Ake Sharɓar Dankali

    A yau za mu koyi yadda ake Sharɓar Dankali

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Kayan ciki
    • Dankalin Turawa
    • Kayan ƙamshi
    • Sinadarin ɗanɗano
    • Kayan miya
    • Ganyen fasali

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A samu kayan ciki na rago ko tunkiya, sai a wanke shi tas.
    2. A fitar da duk dauɗar da ke maƙalewa, sai a yanka su ƙanana, sannan a ɗora a wuta.
    3. Sai a zuba kayan kamshi da sinadarin ɗanɗano da gishiri a zuba albasa da tafarnuwa mai yawa.
    4. Sai ki bar shi ya dahu, Sannan a fere dankali a yanka shi ƙanana a kwance.
    5. Idan an tabbatar kayan cikin sun dahu, sai a ɗauko jajjagen kayan miya a zuba a ciki, tare da man girki.
    6. Idan ya yi kamar minti biyar, sai a zuba dankalin nan da aka yanka a ciki.
    7. Sai ki zuba sinadarin dandano a ciki ki juya, a bar shi ya dahu. Amma fa shi wannan girkin ruwa-ruwa ake cin sa.
    8. Don haka, idan ana dahuwar za a tafasa ruwa, a ajiye a gefe ko akwai buƙatar ƙarawa. Idan ya dahu sai a sauke, a ci shi da ruwa-ruwa.

    Domin sanin Yadda Ake Plantain Pie danna nan

  • Yadda Ake Plantain Pie

    Yadda Ake Plantain Pie

    A yau za mu koyi yadda ake Plantain Pie. Plantain Pie abinci ne da ake yinsa daga plaintain, yana da matukar amfani a jiki.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Ayaba
    • Ƙwai
    • Magi
    • Tafarnuwa
    • Citta
    • Kori
    • Attarugu
    • Koren tattasai
    • Albasa
    • Takardar foil

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A ɓare ayaba, sannan a silala shi kamar yadda ake yin dambun tsaki.
    2. Bayan ya nuna, sai a saka a kwano a ɗaɗɗana ta da ludayi.
    3. A yayyanka albasa da ɗanyen tafarnuwa da citta ƙanana, sannan a daura man gyaɗa a wuta. Idan ya yi zafi, sai a zuba albasa da yankakkiyar tafarnuwa da citta a gauraya su.
    4. Sannan a zuba yankakken tattasai da da yankakken karas, a yi ta soya su, sai a zuba magi da kori, sannan a ɗauko ƙwai kamar huɗu ko biyar, a fasa a ciki, a yi ta gaurayawa har sai ya soyu sannan a kwashe a ajiye a gefe.
    5. Sai a wanke hannu a goge, sannan a shafa man gyaɗa a tafin hannu, sannan a mulmula ayabar.
    6. A shimfiɗe ta a kan takardan ‘foil’ sai a baza ta kamar yadda ake ‘meat pie’.
    7. Sannan a zuba wannan ƙwan a cikin ta sai a rufe ta da ɗayan gefen.
    8. A sami cokali mai yatsu a ɗaɗɗana bakin, sai a ɗaura man gyaɗa a wuta bayan ya yi zafi sai a riƙa jefawa, idan ya soyu sai a ajiye a gefe.
    9. Za a iya cin wannan girkin da shayi a matsayin abin buɗa baki ko karyawa da safe lokacin da ba na azumi ba.

    Domin sanin Yadda Ake Mashe danna nan.

  • Yadda Ake Mashe

    Yadda Ake Mashe

    A yau za mu koyi yadda ake mashe.

    Mashe abinci ne mai kama da masa, amma ya fi masar ƙanƙanta; sannan abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa shi daban yake da na masa, ko waina.

    An fi cin wannan irin abincin ne a Ƙasar Hausa, domin karyawa da safe. Sannan mafi yawanci, sun fi son cin sa da yajin ƙuli-ƙuli ko kuma yajin barkono.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Garin gero
    • Man gyaɗa
    • Magi
    • Yis
    • Fulawa
    • Gishiri
    • Ƙuli/yaji

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A samu gero sannan a wanke a cire tsakuwa a busar, sannan a niƙa ba tare da an saka kayan ƙamshi ba, ko kayan yaji.
    2.  Bayan haka, sai a tankaɗe wannan garin, sannan a sa a roba, sai a samu garin fulawa a zuba a ciki, a gauraya su garayu sosai.
    3.  A ɗumama ruwa sannan a zuba yis a ciki idan ya ɗan tashi,
    4. Sai a zuba a cikin haɗin garin gero da fulawa.
    5. A samu ruwa ana zubawa ana kwaɓa haɗin har sai ya yi kauri kaɗan. Hadin ya kasance ba mai kauri sosai ba sannan a rufe a sanya a rana har sai kullun ya tashi.
    6. Sannan a ɗora tukunyar tuya a wuta, a zuba man gyaɗa da albasa su soyu. Sai a dauko ƙullun ana yankawa da ludayi ko cokali daidai girman da ake so ana soyawa kamar yadda ake tuyar fanke sannan a kwashe.
    7. A samu yajin ƙuli mai ɗauke da magi a ci da shi ko kuma yaji mai ɗauke da magi ana ɗangwalawa ana ci.

    Domin sanin Yadda Masar Dankali danna nan.

  • Yadda Ake Masar Dankalin Turawa

    Yadda Ake Masar Dankalin Turawa

    A yau za mu koyi yadda ake masar dankalin Turawa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Dankalin Turawa
    • Attarugu
    • Albasa
    • Ƙwai
    • Gishiri da magi
    • Kori

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A fere dankali, sai a ɗora shi a wuta, ya nuna ya yi luguf sosai.
    2. Sannan sai a ɗauko roba ko kwano mai zurfi a zuba a ciki.
    3. A ɗebo ƙwai mai ɗan dama a fasa a kan dankalin.
    4. Sai a samu ludayi a dama dankalin da ƙwan, har sai sun haɗu sosai.
    5. Sai a debo albasa da attarugu a jajjaga, su sannan a zuba a kan haɗin dankalin da magi da gishiri da kori daidai kayan ɗanɗano,
    6. Kuma a sake dama haɗin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.
    7. A ɗauko tanda a dora a kan wuta, a zuba man gyada a kowane gida sannan a ɗebo ƙullun dankalin a zuba a kowane gidan tandar.
    8. Sai a ɗan ba shi mintuna, domin dahuwar cikin masar, idan gefe ɗaya ya yi, sai a sake juya wainar zuwa dayan gefen har sai ta nuna kafin a sauke daga wuta.

    Domin sanin Yadda Ake Lemon Ardeb danna nan.

  • Yadda Ake Lemon Ardeb

    Yadda Ake Lemon Ardeb

    A yau za mu koyi yadda ake lemon ardeb, da yawan mutane ba su san me ake kira ‘Ardeb’ ba.

    Wannan ardeb dai lemo ne kamar lemon tsamiya. Kuma yana da alaƙa da mutanen Maiduguri. A irin wannan yanayi da muka shiga, ana yawan haɗa wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi, ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Tsamiya
    • Siga
    • Masoro
    • Kanamfari
    • Citta
    • Ruwa

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A samu tsamiya a wanke tsaf, ya fita sannan a jiƙata ta jiku, sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari.
    2. Sannan a ɗora tukunya a wuta, bayan ta yi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa.
    3. A ɗauko wannan jiƙaƙƙiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan;
    4. Kuma sanya shi a gidan sanyi domin ɗanɗano ya fito sosai.
    5. Daya hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace.
    6. A ɗora tukunya a wuta bayan tukunya ta yi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Haɗin ‘ardeb’ ya haɗu.

    Domin sanin Yadda Ake Tsiren Nama danna nan

  • Yadda Ake Tsiren Nama

    Yadda Ake Tsiren Nama

    A yau za mu koyi yadda ake tsiren nama; Tsiren nama abinci ne mai matuƙar daɗi musamman ma idan aka haɗa shi yadda ya kamata, kuma aka lura da dukkanin tsabtar abubuwan amfanin zuwa kayan haɗawar.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Tsokar nama
    • Jajjagen attaruhu da albasa
    • Magi
    • Curry
    • Spices
    • Fennel seed
    • Albasa
    • Tattasai
    • Koren tattasai
    • Tumatir
    • Garin yaji
    • Tafarnuwa domin buƙata
    • Mai
    • Tsinken yin tsare
    • Bama

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A sami nama me kyau gurin tsoka inda babu jijiya, sai a yayyanka shi madaidaita.
    2.  A wanke shi tas a caccaka masa wuƙa saboda Idan an yi haɗi ya ratsa cikin, a tsane ruwan. Sannan a saka fennenl seed.
    3. A jajjaga tafarnuwa Idan ana buƘata, curry, spices, garin citta, Maggi, bama, jajjagen taruhu da albasa kaɗan, da garin yaji shi ma kaɗan.
    4. Sai a jujjuya sosai har ko’ina ya ji, sai a saka a fridge na tsawon awa 1 da rabi. Sai a jiƙa tsinken yin tsire a ruwa na mintuna 30 sannan a cire.
    5.  A yayyanka albasa yankan manya, tattasai ma haka, tumatir da koren tattasai duk a yi musu yankan manya.
    6.  Sai a ɗauko tsinken a soka albasa, sannan nama, sannan Koren tattasai sannan nama sannan albasa sai tumatir, sai jan tattasai haka za a yi ta yi har a gama.
    7. Sai a kunna abin gashi, Idan ya yi zafi sai a ɗauko tsiran, a jera sannan a yaryaɗa mai a kai sai a bar shi ya gasu, a dunga juyawa akai-akai saboda kar ya ƙone.
    8.  Ana yi ana yaryaɗa mai har a gama. Za a ji yana ƙamshi.
    9. Idan aka tabbatar ya gasu, sai a cire a saka a kwano ko faranti.
    10. A ci da ɗuminsa ya fi daɗi. Za a iya saka wa a tsakiyar bread a ci. Shi ma akwai daɗi.

    Domin sanin Yadda Ake Onion Rings danna nan.

  • Yadda Ake Onion Rings

    Yadda Ake Onion Rings

    A yau za mu koyi yadda ake onion rings.

    Onion rings abinci ne na maƙwalashe wanda ake yin sa daga albasa yana da matuƙar daɗi musamman ma idan aka haɗa shi da lemo me ɗan sanyi, ko kuma da shayi mai daɗi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Albasa
    • Fulawa
    • Man gyaɗa
    • Garin burodi (Breadcrumbs)
    • Yeast
    • Baking powder
    • Gishiri

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A samu albasa mai kyau manya guda biyu ko uku (ko adadin yawan sanwar da za ayi)
    2. Sai ta ɓare ta, sannan a yayyanka sala-sala (Slices)
    3. Daga nan sai a yi wara-wara da ita kamar yadda ake warware awarwaro na hannu sannan sai a ajiye a gefe
    4. Daga nan sai a ɗauko kwano a juye fulawa kamar gwangwani biyu a ciki sai ta ɗauko baking powder a zuba cikin cokali ɗaya
    5. Sannan a ɗauko Yeast shi ma cikin ƙaramin cokali
    6. Sai a dauko gishiri a zuba kaɗan, sai a dama a kwaɓin, amma kada ya yi ruwa sosai
    7. A dinga ɗauko wannan albasar ana tsomawa a cikin kwabin a jujjuya sosai sannan sai a tsame ta a saka a kan wannan garin burodin a jujjuya sosai sai a ajiye
    8. Sannan sai a ɗauko kaskon suya a ɗora a wuta sai a zuba man gyaɗa, bayan ya ɗan yi zafi sai a dinga ɗauko wannan haɗin albasar ana soyawa ana tsamewa
    9. Har a gama duka, amma a kula sosai kada suyar ta ƙone.

    Domin sanin Yadda Ake Miyar Zogale danna nan.

  • Yadda Ake Miyar Zogale

    Yadda Ake Miyar Zogale

    A yau za mu koyi yadda ake miyar zogale.

    Zogale na ɗauke ne da sinadaran dake maganin cututtuka fiye da 100, kamar maganin ciwon gyambon ciki, (Ulcer), maganin hawan jini da ƙara wa mutum kuzari da dai abubuwa da dama.

    Za a iya cin wannan miyar da tuwon shinkafa ko na dawa ko masara da kuma na alkama.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Busasshen zogale
    • Attaruhu
    • Nikakkiyar gyaɗa
    • Tumatir
    • Albasa
    • Wake
    • Magi
    • Garin tafarnuwa
    • Manja
    • Nama ko kifi (Idan da hali)

    Yadda Ake Haɗawa

    1. Da farko dai za a yanka albasa, sannan a jajjaga tumatir da attaruhu
    2. A dafa wake ya nuna sosai, sannan a ajiye a gefe. A silala nama da gishiri da albasa.
    3. Bayan haka, sai a ɗora tukunya a wuta sannan a zuba manja, kuma a soya albasa ta ɗan fara soyuwa.
    4. Sannan a zuba wannan jajjagen kayan miyar. A yi ta soyawa har sai ya soyu kamar yadda ake yi wa miyar dage-dage.
    5. Sannan a ɗauko wannan romon silalen nama da naman a zuba. Sai a ɗauko magi da garin tafarnuwa da kuma kori a zuba.
    6. Sai a rufe tukunyar, bayan ta tafasa sannan a zuba wannan waken a ciki a gauraya, har sai ya gaurayu.
    7. Sannan a ɗauko niƙaƙƙiyar gyaɗar nan a zuba ruwa a gauraya ya koma kamar za a yi kunu, sannan sai a zuba a gauraya. Bayan gyaɗar ta nuna, sai a ɗauko busasshen zogale ko ɗanyen zogale a zuba a gauraya sannan a rufe.
    8. Haka za a yi har sai zogalen ya nuna sannan a kwashe.”

    Domin sanin Yadda Ake Gas Meat danna nan.

  • Yadda Ake Gas Meat

    Yadda Ake Gas Meat

    A yau za mu koyi yadda ake gas meat.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Jan nama
    • Albasa ko lawashi
    • Markaɗaɗɗiyar gyaɗa
    • Kori
    • Thyme
    • Tattara
    • Attaruhu
    • Tumatur kaɗan
    • Maggi
    • Kabeji
    • Tafarnuwa
    • Foil paper ko takardan cementi
    • Da leda baƙi

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A wanke nama.
    2. A yanka albasa ko lawashi.
    3. A jajjaga tattara da attaruhu.
    4. A yayyanka tumatur.
    5. A haɗa nama, albasa, da kayan miya, da gyaɗa, kori, thyme, maggi da sauran kayan ƙamshi a gauraya, idan ana so a sa tumatur ko kuma a bar shi sai bayan kori ya nuna a zuba shi ɗanye a kan naman a ci.
    6. A juye haɗin baki ɗaya a cikin foil paper a kunshe ko kuma a leda, sai a sa ledar a cikin takarda, takardan kuwa a cikin wani leda.
    7. A ɗora tukunya da ruwa, idan ya yi zafi ko ya tafasa a dora matsami kamar za a yi dahuwar dambu, a dora ƙunshi a kai a rufe da marfin tukunya a bari ya nuna.
    8. Idan ya nuna za a iya garnishing da cabbage, tumatur, koren tatttasai a ci.
    9. Za a iya kuma amfani da oven in da hali ba dole sai tukunya ba.

    Domin sanin Yadda Ake Stuffed Meat danna nan

  • Yadda Ake Stuffed Meat

    Yadda Ake Stuffed Meat

    A yau za mu koyi yadda ake stuffed meat.

    Stuffed meat abinci ne da ake yin sa daga nama, yana da matuƙar daɗi musamman ma wajen karin kumallo na safe ko tarbar baƙi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Nama me girma
    • Kakide (kitse)
    • Butter
    • Tumatur
    • Jan tattasai
    • Green pepper
    • Albasa
    • Nama sala sala masu kauri
    • Kayan ƙamshi
    • Citta

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A wawwanke cikin naman nan a yi aljihu biyu abar kasan naman kar a yanka shi.
    2. A ɗumama butter a soya tumatu a yanka tattasai duka a cire ‘ya’yan a soya da albasa.
    3. A zuba naman nan sala-sala a ciki a zuba maggi da kayan ƙamshi.
    4. A zuba kwatan naman nan da hadi a aljihu daya, kwata a daya aljihun sannan a zuba rabi a saman.
    5. A nannaɗe a ɗaure a sa abu me nauyi a danne.
    6. Asa a gwangwanin baking a gasa ana zuba kakide a hankali har ya gasu.
    7. A barbaɗa kayan yaji a kai in ana so.

    A ci da daɗi.

    Domin sanin Yadda Ake Bandashe danna nan