Tag: yadda ake

  • Yadda Siffofin Masu Ba Da Tarbiya Suke

    Yadda Siffofin Masu Ba Da Tarbiya Suke

    Masu hikima suna cewa: In mutum ya ce zai ba ka riga to ka dubi ta jikinsa kuma “wanda ba shi da abu ba zai iya bayar da shi ba.”

    A kan haka ya wajaba a kan duk wani wanda nauyin tarbiyya ya hau kansa iyaye, malamai da shugabanni ya kasance mai tarbiyya ne shi a kan kansa.

    Wani mutum ya tambayi malamansa cewa ya koya masa yadda ake yin tarbiyyar ‘ya’ya a lokacin ‘yarsa ta fari tana wata ɗaya da haihuwa, sai malamin ya ce da shi ai kuwa ka makara. Saboda ita tarbiyya tun kafin a yi aure ake fara yin ta ba sai an haifi ɗan ba.

    Malamai sun yi bayanin siffofin da ya wajaba mai ba da tarbiyya ya siftantu da su in dai yana son ya sami nasarar aikin tarbiyya kuma ya yi tasiri.

    A Taƙaice Ga Waɗannan Siffofin

    Ya kasance mai haƙuri da juriya da naci, kada ya ɗauka cewa tarbiyya aiki ne na sha yanzu magani yanzu.

    1. Ya yarda cewa haƙƙi ne wajibi a kansa. Ya rinƙa jin haka a ransa a kowane lokaci. wannan zai hana shi yin watsi da tarbiyyar iyalinsa.
    2. Ya rinƙa sa ido da lura da bibiya, saboda tarbiyya kamar dashe ne in ba a bibiyarsa da kula da shi sai ya bushe ya lalace ko dabbobi da ƙwari su kashe shi.
    3. Yi dan Allah (Ikhlasi) kada mutum ya nemi wani lada ko yabo a kan tarbiyyar ‘ya’yansa da iyalınsa sai a wurin Allah kawai. Saboda haka ban da alfahari ban da fariya ban da gorantawa ‘ya’ya da iyali ban da raina ‘ya’yan wasu.
    4. Tarbiyya tana buƙatar tausasawa da bin al amura sannu-sannu daki- daki, tsanani da gallazawa kawai ba sa kawo gyara, dole sai ana cizawa ana hurawa.
    5. Mai ba da tarbiyya shugaba ne, saboda haka ya kamata ya siffantu da siffofi na shugabanci ya kasance jarumi, mai adalci, mai kwarjini, mai iya ɗaukar nauyin waɗanda yake jagoranta, mai kyauta, sauƙin kai da saussauci a inda ya dace, mai tsanani a inda ya dace, da dai sauran siftofi na jagora ko shugaba na gari.
    6. Harkar tarbiyya ba abu ne da ake yinsa da ka ba, lallai sai an yi karatun tarbiyyar saboda tana farowa, tun kafin a auri uwar da har ta haife shi ya balaga, za a yi masa tarbiyyar jiki, Imani, halaye, ladabai, haƙƙoƙi, siyasa da sha’awa. To in ba ilimi ta yaya wannan aiki zai yiwu.
    7. Wajibi ne mai tarbiyya ya kasance mai adalci.
    8. Ya kasance yana ɗaukar matakai na gasakiya a komai ya daidai ta tsakanin tsanani da sassauci da sakin hannu da rowa, ya kasance tsaka-tsaki a komai.

    9 Wanda yake da tsananin rowa da ƙanƙamo da masifar son abin duniya ba zai iya tarbiyya ba. Dole ya kasance mai sakin hannu da sakin fuska. Kada ya ɗauka asarar kuɗi yake yi in ya biya kuɗin makaranta ko ya sai abinci da sauran buƙatun ‘ya yansa.

    10 Ya kasance mai nuna ƙauna ta gaskiya ga’ ya’yansa maza da mata ‘ya’yan uwar gida da na amarya.

    11 Dole ne mai tarbiyya ya kasance nutsattse mai hankali da tsari a rayuwarsa.

    12 Wajibi ne mai tarbiyya ya kasance ya siffantu da kyawawan halayen da yake umarni da a aikata su, yana nisantar munanan ayyukan da yake hanawa. Kada ya zama fitina ga waɗanda suke a ƙarkashinsa.

    13 Ya kasance mai kyakkyawan fata da sakakkiyar zuciya kada ya rinƙa camfa abubuwa ko saurin siƙewa da fidda rai kan samun nasara.

    14 Ya kasance mai jin ƙai da tausayi.

    15 Ya kasance mai tsoron Allah (Taƙawa) wannan sharuɗɗa muhimmancinsa ya gawurta.

    Karanta Masu Rera Waƙa

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Yadda Ake Wuturi

    Yadda Ake Wuturi

    Hadisai da dama sun zo kan bayanin siffofin wutiri kamar haka

    1-  Wutiri da Raka’a Ɗaya:

    Manzon Allah (S. A. W.) ya ce:  “Sallar dare raka’a biyu- biyu ce, idan ɗayanku ya ji tsoron fitowar alfiji, ya sallaci raka’a ɗaya ta zama wutiri ga abin da ya sallata” kuma ya ce ” wutiri raka’a ɗaya ne a ƙarshen dare” (Muslim 752).

    2- Wutiri  da Raka’a Uku:

    A yi raka’a biyu a yi sallama, sannan a yi wutiri a yi sallama. Wannan ya inganta a hadisan Sayyada Aisha, Ibn Abbas, da Ubayyu Ibn Ka’ab (RA) kuma ya inganta cewa Manzon Allah (S.A.W.) yana karanta sabbi isma Rabbikal A’ala raka’ar farko, ƙulyaa ayyuhal kafirun a raka’a ta biyu sannan ƙulhuwallahu a raka’ar wutiri. (Bukhari 991, Malik 1/125) Tahawi  1/285). Amma karanta ƙulhuwallahu da falaƙi da Nasi wannan ya zo a Hadisi mai rauni.

    A yi raka’a ukun a jere  ba tare da an yi zaman tahiya ba sai a raka’a ta uku. (Bukhari 1147, Muslim 783)

    3- Wutiri da Raka’a Biyar:

    Ana so ga wanda zai yi wutiri da raka’a biyar ya yi su a jare kada ya yi zaman tahiya sai a raka’a ta biyar. Wannan ya inganta a Hadisin Aisha (RA) wanda Muslim ya ruwoito.

    4- Wutiri da Raka’a bakwai ko Raka’a tara:

    Ana so ga wanda zai yi irin wannan wutiri, ya yi su a jere kada ya zauna sai a raka’a ta shida ko ta takwas, sannan ya tashi ya kawo raka’a ta bakwai ko ta tara sannan ya yi sallama. Wannan ya zo a Hadisin. (Muslim 746, Abu Dawud 1328 da Nasa’I  2/199).

    Danna nan don karanata Rafkanuwa a Sallar nafila

    Edita:@rumasau-kallamu

     

  • Yadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya

    Yadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya

    Ko kun san yadda ake yin lemon tsamiya? To ku biyo mu domin ku ji yadda ake yi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Tsamiya
    • Sugar
    • Kanunfari
    • Citta
    • Lemon tsami

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A dafa suger da ruwa bar shi ya huce. A dafa tsamiya da ruwa, kanunfari da citta har misalin minti 30. A tace tsamiyar a bar ta ta huce, har ta yi sanyi.

    2. A matse lemon tsami, a kuma yanka guda biyu yankan faɗi. Haɗa dafaffen sugar a cikin tsamiyar. A zuba lemon tsami da kuma wanda aka yanka a cikin jug.

    3. A saka cikin frig (Refrigerator) ya yi sanyi sosai kafin a sha. Za ka zuba ruwa daidai tsamin da kake so kafin sha.

    Domin sanin Yadda Ake Lemon Ardeb danna koren rubutu

  • Yadda Za Mu Yi Koyi Da Annabi (S.A.W.)

    Yadda Za Mu Yi Koyi Da Annabi (S.A.W.)

    Duk Wanda ya ce shi Musulmi ne, to lallai ne abin koyinsa ya zamo Manzon Allah (S.A.W), a dukkanin tsare-tsare na rayuwarsa.

    Misali: Tsarin Ilimi, tsarin zamantakewa, tsarin Tattalin arziƙi, tsarin siyasa (shugabanci) da tsarin shari’ah. Abin nufi a nan shi ne, duk waɗannan tsare-tsare na rayuwa su zamo a kan tsarin alƙurani da sunnah, bisa fahimtar magabata na ƙwarai.

    Kada mutum ya zama sai a sallah, Azumi, aikin Haji kaɗai, yake Musulmi. Watau ya zama yana bin tsarin da ya saɓa wa na Allah. Allah (SWT) Yana cewa:

     Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku shiga Musulunci gaba ɗaya (watau ku miƙa wuya gaba ɗaya). Kada ku bi takun sheɗan, ba na Allah ba). Shi abokin gaba ne a gare ku, bayyananne” (suratul BAƙarah, Aya ta: 208).

    Abin takaici shi ne, a halin da muke ciki a yanzu, za mu ga cewa a dukkanin tsare-tsare nan na rayuwa babu wanda muke tafiyar da shi a kan tsarin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo da shi. Misali: Tsarin Iliminmu ba ya koya mana tauhid da tsoron Allah da ranar lahira da Tarbiyyar Musulunci. A tsarin zamantakewa. Idan muka ɗauki zamantakewarmu ta aure da zaman iyali, ba a kan alƙur’ani da sunnah take ba.
    Tsarin tattalin arzikinmu cike yake da cin hanci da rashawa, cin Riba, gululu’ (Watau satar dukiyar jama’a) da sauransu. Tsarin siyasarmu (shugabanci) tsari ne na Damakwaraɗiiyya, wanda babu Allah a  cikinsa. Shi kuwa tsarinmu na shari’ah kowa ya san dokokin ‘yan Adam muke fifitawa a kan dokokin Allah (SWT). Abin nufi a nan shi ne, son Annabinmu  na baka ne kawai. Ba a aikace yake ba. Gashhi kuwa Allah (SWT) yana cewa:

    Gaya musu, idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku, ya gafarta muku zunubanku. Allah mai gafara ne, mai rahama” (Suratu Ali Imrana, Aya ta:31)

    Allah (SWT) yana cewa: Ka ce musu Idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan’uwanku  da matanku, da danginku da dukiyoyinku da kuka nema da hanyar samunku da kuke gudun kada ta yi tasgaro da gidajen da kuke jin daɗinsu, su suka fi soyuwa a  gare ku, maimakon Allah da Manzonsa, da  ƙoƙarin tabbatar da tsarinsa, to ku zauna, har sai Allah ya zo da lamarinsa (Mutuwa ko halakarwa). Allah ba ya shiryar da mutane fasiƙai” (suratul Taubah, Aya ta:24).

    Wannan duka yana nuna cewa ba za mu zama Musulmi ba sai mun gudanar da kowane ɓangare na rayuwarmu bisa tsarin Allah. Wannan kuma ba zai samu ba sai ta hanyar koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), watau ta hanyar ruƙo da alƙur’ani da Sunnah. Annabi(S.A.W) ya ce:

    “Na bar muku nauyaya guda biyu, ba za ku ɓata ba, matuƙar kun yi ruƙo da su: Littafin Allah da sunna ta”

    DOMIN SANIN YADDA ZA KA YI KOYI DA ANNABI (S.A.W) DANNA KOREN RUBUTU

  • Yadda Sahabbai Suka Yi Koyi Da Annabi Muhammad (S.A.W)

    Yadda Sahabbai Suka Yi Koyi Da Annabi Muhammad (S.A.W)

    Sahabban Annabi Muhammad (S.A.W) sun yi koyi da shi a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu. Ba kawai sai a salla, zakka, Azumi da Hajji kaɗai ba. Ga wasu misalai ‘yan kaɗan da za su nuna mana haka.

    Dab da Annabi Muhammad (S.A.W) zai yi wafati ya zartar da wata rundina ta yaƙi, ƙarƙashin shugabancin Usamatu bin Zaid. Bayan wafatin annabi Muhammad (S.A.W) sai wasu suke ganin ya kamata a dakatar da wannan runduna tukuna, kasancewar an sami wasu suna ƙin bayar da zakka. Har ma aka zama cikin tsoron kawo hari cikin Madina. Me Abubakar yayi a matsayinsa na shugaba? Abubakar bai yarda a dakatar da wannan runduna ba. Cewa ya yi:

    “Ba za ta yiwu ba a gare ni, na kwance tutar da Manzon Allah (S.A.W) ya ƙulla”.

    Haka nan sauran sahabbai suka goyi bayan Abubakar, Usamatu ya shugabanci wannan yaƙi kuma aka yi gagarumar nasara. Game da Madina kuwa, abin da Abubakar ya yi shi ne, sai ya sanya wasu daga cikin manyan sahabbai suka shugabanci wata runduna domin ba ta kariya, kamar su: Aliyyu bin Abi Ɗalib,
    Zubairu binil Auwam, Sa’adu bin Abi Waƙƙas, Abdullahi bin Mas’ud da abdur Rahman bin Aufin.

    Wani abin da Sayyidina Abubakar ya yi (na ruqo da tsarin Annabi) bayan wafatinsa (S.A.W), wanda yake nuna dagewarsa, shi da sauran sahabbai, a kan Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W) (watau tsarinsa na rayuwa) shi ne, wasu Larabawan ƙauye sun ƙi bayar da zakka bayan wafatin Annabi Muhammad (S.A.W). A wannan lokacin cewa ya yi:

    “Wallahi! Idan da za su hana ni dabaibayi, wanda suka kawo wa Manzon Allah (S.A.W), da sai na yaƙe su”.

    Wani abin da za mu sake lura da shi shi ne, yanayin da Nana faɗinmah ‘yar Manzon Allah (S.A.W) ta nemi gadon Annabi Muhammad (S.A.W), a nan ma sai y ace mata ya ji Manzon Allah ya ce:
    “Mu jama’ar Annabawa ba a gadon mu. Abin da muka bari, sadaka ne”

    (Bukhari da muslim ne suka ruwaito).

    Wani misalin shi ne, wata rana Sayyidina Umar ya zo zai sumbaci  Hajarul Aswadi sai ya tsaya ya ce:

    Ni na san kai dutse ne. Ba ka cutarwa, ba ka amfanarwa. In ba domin na ga  annabi  (S.A.W) yana sumbatar ka, da ba zan sumbace ka ba”.

    (Bukhari ne ya ruwaito).

    Wata rana Abdullahi bin mas’ud ya zo zai shiga masallaci sai ya ji Annabi Muhammad (S.A.W) yana
    cewa:

    “A zauna”. Sai ya zauna a kan dokin ƙofar masallaci. Bai ƙara yin gaba ba ko kaɗan, sabo da cika umarni.

    Haka nan sahabbai suka yi ta koyi da Annabi Muhammad (S.A.W), a dukkanin tsare-tsaren rayuwa. Wata rana Abdullahi bin Mugaffal ya ga wani mutum (ko wani ɗan ɗan’uwansa), yana yin jifan da ake kira ‘Hazfu (wadda akan sa tsakuwa a tsakanin babban ɗan yatsa da ɗan ali, a wulla ta). Sai ya ce da shi:

    “Manzon Allah (S.A.W) ya hana yin hazfu. Da ya sake ganinsa yana yi sai ya ce:

    “Ina gaya maka Manzon Allah (S.A.W) ya hana yin hazfu kana sake yi? Ba zan sake yin magana da kai ba, har abada

    (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito).

    Har ma ta kai cewa wasu daga cikin sahabbai suna koyi da Annabi, hatta a abubuwan da Annabi yakan y,i ba da nufin lallai sai an yi koyi da shi ba.

    Abdullahi bin Umar ya shahara game da haka.

    Abdullahi bin Umar ya kasance yana zuwa ƙarƙashin wata bishiya a Madina, ya yi baccin rana. Da aka tambaye shi game da haka, sai ya ce shi kawai ya ga Annabi yana yin baccin rana a ƙarƙashinta.

    Wata rana Abdullahi bin Umar yana cikin tafiya tare da mutane, sai aka ga ya kewaye wani wuri, bai bi ta wurin ba, (Alhali babu komai a wurin), da aka tambaye, shi sai ya ce, ya ga Annabi wata rana suna tafiya ya kewaye wurin.

    Haka nan wata rana an ga ya sauka a wani wuri tsakanin Makka da Madina, ya yi salla, dalilin sa shi ne, ya ga Annabi ya yi sallah a daidai wannan wurin suna halin tafiya. Duk da kasancewar a lokacin mutane sun yi masallaci a kusa da wurin, shi sai ya ƙi yin salla a masallacin, ya je ya yi a daidai inda Annabi ya yi (S.A.W)

    Domin karanta cikekken littafin danna wannan koren rubutu

  • Yadda Ake Haɗa Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake

    Yadda Ake Haɗa Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake

    Barkanmu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut, rice, sweet potato shake, ku biyo mu a sannu domin mu koya tare.

    Ko kun san Gyaɗa na da sinadarin minerals kamar su: copper, manganese, potassium, calcium, iron, magnesium, zinc da kuma selenium wanda suke ƙara ƙarfin ƙashi da haƙori.

    Abubuwan Buƙata

    1. Shinkafa ½ rabin kofi
    2. Gyaɗa ½ rabin kofi
    3. Dankalin Hausa
    4. Gyaɗa soyayyiya
    5. Siga
    6. Madara

    Yadda ake haɗawa

    1. A wanke shinkafa a jiƙa ta, sai ta yi laushi
    2. A fere dankalin Hausa a yayyanka
    3. A soya gyaɗa a busar da ita
    4. Sai a hade gyaɗa, dankali da kuma jiƙaƙƙiyar shinkafa a markaɗa a tace da abun tata
    5. A raba ruwan gyaɗa biyu da aka ɗora a wuta har sai ya yi kauri (kamar kunun gyaɗa). Sai a sauke, a haɗe da ragowar ruwan gyaɗar a saka madara da siga. Za a iya ƙara ruwa daidai ƙaurin da ake so.
    6. Za a iya tace shi da rariya, idan ya yi gudaji-gudaji, sai a saka a fridge ya yi sanyi.
    7. Asha lafiya.
  • Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls

    Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls

    Ko kun san:- Groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin ɗan adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Soyayyar gyaɗa ¼ cup
    2. Dankalin hausa matsakaita
    3. Albasa a yanka ƙanana ko a jajjaga
    4. Curry ½ tablespoon
    5. Markaɗaɗɗen nama
    6. Sinadarin ɗanɗano
    7. Attaruhu guda biyar jajjagge
    8. Tafarnuwa
    9. Breadcrumbs 1 cup
    10. Ƙwai 3 (a fasa a kaɗashi)
    11. Man gyaɗa na suya

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A cikin kwano mai ƙyau a zuba dafaffiyar dankali sai a farfasata su fasu da kyau.
    2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin ɗanɗano, curry, thyme da nama a juya a hankali.
    3. A samu ɗan faranti a ringa ɗiban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye.

    A tsoma wannan ball cikin ƙwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe.

    Domin sanin Yadda Ake Donut danna nan

  • Yadda Ake Yin Ƙuli-ƙuli

    Yadda Ake Yin Ƙuli-ƙuli

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake. Tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin Ƙuli-ƙuli, ku biyo mu a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san ƙuli-ƙuli abincin yara ne? ko ince yara na son ƙuli-ƙuli, kuma ana iya sarrafa shi ta hanyar yin garin ƙuli-ƙuli sannan ya zama ingredients ɗin abincin kowa.

    Abubuwan Buƙata:

    1. Gyaɗa
    2. Gishiri
    3. Citta
    4. Barkono
    5. Sinadarin ɗanɗano
    6. Sugar

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A soya gyaɗa sama-sama sai a ɓarza ta, a tabbatar an tsince an ɓarza (babu mai bori kwata-kwata).
    2. A fitar da baƙin gyaɗa, domin tana saka ɗaci.
    3. Sai ka kai, a markaɗa kar a zuba ruwa kamar ƙullin gyaɗa (peanut butter)
    4. A jiqa.
    5. A tsince gyaɗa, a cire mai bori sannan a cire baɗin gyaɗar sai a soyata sama-sama karta ƙone
    6. A markaɗa gyaɗa ɗan gishiri, citta ko in mai sugar za a yi sai an ɗan saka sugar.
    7. A tace ruwan tsamiya a bar shi ya kwanta, sai a juye a abu mai kyau.
    8. Bayan an markaɗa gyaɗa, sai a saka ta a cikin kwano mai zurfi a zuba wannan ruwan tsamiya kaɗan a yi ta juyawa da muciya ko cokalin katako har sai an ga mai ya fara fitowa.
    9. Sannan za a ga gasarar tana curewa ko ince yana dunƙulewa. Sai a tsiyaye mai, sannan a cura ƙullin a soya ta.

    Domin koyon Yadda Ake Yin Daƙuwa danna nan

    Domin koyon Yadda Ake Kunun Gyaɗa danna nan

  • Yadda Ake Yin Kantun Ghana

    Yadda Ake Yin Kantun Ghana

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abinci, namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe, tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin kantun Ghana. Ku biyo mu a sannu domin mu koya tare…

    Dama kin san yadda za ki ringa yin kantun Ghana a gida kina siyar wa yara. Da kin huce takaicin rashin kuɗi.

    Abubuwan Buƙata

    1. Gyaɗa
    2. Sugar
    3. Citta

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A tsince gyaɗa, a gyara, sannan a daka ta sama-sama kar ta yi laushi.
    2. A zuba suga a tukunya, sai a ɗora wuta idan ya narke sai a zuba gyaɗa a yi ta juyawa sai ya yi golden brown. A sauke a yayyanka ƙanana.

    Domin koyan Yadda Ake Haɗa Hallaka Kwabo danna nan

  • Yadda Ake Yin Daƙuwa

    Yadda Ake Yin Daƙuwa

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau zamu koyar da yadda ake yin daƙuwa ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san daƙuwa abin marmari ce wadda ake sakawa a cikin garar amarya?

    Abubuwan Buƙata

    1. Aya 1 cup
    2. Gyaɗa ½ cup
    3. Ƙaramin ½ chokalin barkono
    4. Ƙaramin ½ chokali citta
    5. ½ cup sugar ko zuma
    6. ½ ƙaramin chokalin gishiri

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A tsince aya a wanke ta fita fes sai a shanya
    2. A gyara gyaɗa a soya ta, ta soyu da kyau
    3. A soya aya ta soyu sosai sai a kwashe a daka gyaɗa separately ita ayar haka
    4. A haɗe waje guda sai a zuba kayan ƙamshi
    5. A zuba zuma sai a turashi.

    Domin koyon Yadda ake haɗa hallaka-kwabo danna nan