Tag: yadda ake

  • Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Hanyoyin Tabbatar Da Adalci – Majaddid shaihuna Usman ɗan Fodiyo Allah ya ƙara rahama a gare shi; ya rubuta littafi mai suna; “Usulul adli liwalatil umuri wa ahlil fadli” – wato Ginshiƙan kafuwar adalci domin shugabanni da manyan mutane.

    A cikin wannan littafi, ya yi bayanin hanyoyi goma waɗanda in dai shugabanni daga sama har ƙasa za su yi bi su; babu makawa za su kasance masu adalci a shugabancinsu.

    A taƙaice ga waɗannan ginshiƙai na hanyoyin tabbatar da adalci;

    Tushe Na Ɗaya

    Shugaba ya san matsayi da darajar shugabanci da yake yi. Ya sani cewa shugabanci ni’ima ce babba; wacce in ya yi gaskiya da adalci za ta kai shi ga samun ni’ima madawwamiya a lahira da kyakkyawan suna a duniya. Idan kuwa aka samu akasi to zai gamu da matsananciyar azaba a duniya da lahira; saboda haka kada ya yi wasarere da shugabanci ya riƙe shi ƙam ƙam ya yi da gaske ba wasa.

    Tushe Na Biyu

    Lallai ne shugaba ya ja malamai masu tsoron Allah da aiki da iliminsu masu son alhairi ga al’umma masu faɗar gaskiya marasa tsoro marasa kwaɗayi, ya ja su a jikinsa ya rinƙa neman shawarwarinsu da fatawa akan al’amuran shugabancinsa; ya kuma rinƙa amfani da shawarwari da nasihohi da suke yi masa.

    Haka kuma ya nemi masana ƙwararru a kowane fanni na rayuwa kamar manyan ‘yan kasuwa; tsofaffin shugabanni, da ma’aikata na kowane ɓangare dattawan gari har ma da matasa maza da mata masu tsoron Allah da kishin ƙasa domin ya amfana da iliminsu da ƙwarewarsu a fannonin rayuwa da sauransu.

    Tushe Na Uku

    Kasancewarka mai gaskiya da riƙon amana da adalci ba zai kuɓutar da kai ba a wurin Allah; sai ka tabbatar mai ma’aikatanka da jami’an gwamnatinka suna da hali irin naka. Amma idan kana ganin ɓarna ka yi shiru; to haƙiƙa sai ka ba da amsa akan wannan ɓarnar; kuma sai an tuhume ka akan duk ɓarnar da akayi kana sane ka yi shiru ayi maka azaba a kanta ranar ƙiyama.

    Tushe Na Huɗu

    Lallai ne shugaba ya kasance mai yawan haƙuri; afuwa da kau da kai ya guji saurin fushi da yanke hukunci cikin ɓacin rai.

    Tushe Na Biyar

    A duk lokacin da za ka ɗauki wani matakai ko yanke hukunci ko shawara ko sanya hannu akan wani ƙudiri; waɗanda suke ƙarƙashinka ka ɗauki kanka a matsayin ɗaya daga cikin talakawa duk abinda ba za ka so a yi maka ba to kada ka yi wa waninka, duk abinda za ka so ayi maka to ka zartar da shi.

    Tushe Na Shida

    Kada ka wulaƙanta talaka da sauran mutane masu kawo buƙatunsu gare ka da koke – kokensu; saboda babban amfanin shugabanci shine sharewa mabiya hawayensu da sauran buƙatunsu da yin abinda ya kamata akansu.

    Tushe Na Bakwai

    Ka yi rayuwa matsakaiciya tare d tsantseni da wadatar zuci kada ka sabawa kanka da zurfafawa da al’mubazzaranci; a wajen jin daɗi da kece raini wannan zai sa ka mance da wahalhalun da talakawa suke ciki zuciyar ka ta bushe; in suna kuka ka rinƙa jin kamar kukan daɗi suke yi. Kana sheƙa dariya abinka.

    Tushe Na Takwas

    Dukannin abinda zai yiwu cikin sauƙi da lumana, kada ka bi hanyar tsanani ne da tursasawa wajen tabbatar da shi. Ana amfani da tsanani kawai a lokacin da sauƙi ba zai yi amfani ba.

    Tushe Na Tara

    A kowane lokaci ka rinƙa tunanin mutuwarka da kwanciyar ƙabari da tashin alƙiyama da musiba da azabobin da suke cikinta; da kuma ni’ima da rahamar da Allah ya tanada ga masu binsa. Ka rinƙa tunanin shin kai a wane ɓangare za ka kasance idan Allah ya tashi alƙiyama.

    Tushe Na Goma

    Ka sanya tsarin shugabanci na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance madubinka, ma’aunin shugabancinka ka rinƙa kwaikwayonsa gwargwadon ikonka.

    Bayan waɗannan tuwassa goma waɗanda Shaihu Usman ɗan Fodiyo; ya ambata ya kuma ce imamul Gazzali ne ya faɗe su a cikin wani littafinsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’a Biyu Kafin Magariba danna nan

  • Yadda Sakamakon Zalunci Yake

    Yadda Sakamakon Zalunci Yake

    Shi kuwa zalunci babu abin da yake haifarwa ga azzalumai da ƙasa sai musiba da bala’i a duniya da lahira.

    Sakamakon Zalunci – Kowane irin zalunci babba da ƙarami gamammen zalunci wato zalunci da shugabanni suke yiwa miliyoyin mabiyansu; da kuma zalunci da ɗaiɗaikun mutane suke yi wa junansu, kamar zalunci tsakanin ma’aurata; da ubangida da yaronsa da maƙocin da malami da ɗalibansa da sauran rukunonin al’umma; duka irin waɗannan zalunce-zalunce Allah Ta’ala ba ya barinsu su wuce kawai ba tare da wani sakamako ba.

    Sakamakon wani zalunci yakan kasance hallakar da gaba ɗayan al’umma; kamar yadda ya faru ga Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luɗu. Wani sakamakon yakan tsaya ne kawai a kan wanda ya aikata zalunci shi kaɗai.

    Amma kuma idan mutanen kirki suka rungume hannu suka zura wa azzalumai ido suna sheƙe ayarsu, babu mai kwaɓar su, to sakamakon in ya zo yakan shafi kowa da har managartan, saboda ƙin ɗaukar matakin hana zalunci sakamakon zalunci yakan kasance ta hanyoyi daban-daban kamar talauci mai naci, taɓarɓarewar tsaro, yunwa, azzaluman shugabanni da koma baya da rashin ci gaban al’umma.

    Alƙur’ani mai girma da hadisan manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cike suke da bayanan mummunan sakamakon azzalumai a duniya da lahira.

    A dunƙule ga abin da suke nunawa;

    1. Allah Ta’ala baya ƙaunar zalunci ba ya kuma ƙaunar azzalumai, yana fushi da su yana la’antarsu.

    2. Zalunci yana janyo musiba a bayan ƙasa kamar girgizar ƙasa, ambaliyar ruwa, tsawa, iska, gobara, yawan mace-mace, annoba, fari da sauransu.

    3. Zalunci yana jefa mutane cikin ɗimuwa da kiɗima da rashin samun shiriya ta yadda za a fita daga halin da ake ciki, haka kuma yakan ƙeƙasar da zuciya, azzalumai su ƙi tuba har su mutu a kan zaluncin su gamu da matsananciyar azaba a lahira. Shi ne ma’anar faɗin Allah Maɗaukaki:”Allah ba ya shiriyar da azzalumai.

    4. Allah Ta’ala ba ya ba da nasara da rinjaye ga azzalumai koda kuwa an ga sun ci wata nasara to ba mai ɗorewa ba ce, kuma abin da zai biyo baya na musiba da sharri ba ƙarami ba ne.

    5. A lahira azzalumai ba za su ji da daɗi ba domin akwai azzaluman da za su shiga wuta har abada ba za su fita ba, waɗansu kuma za su daɗe a cikinta gwargwadon irin zaluncin da suka yi.

    6. Azzalumai ba za su samu rabauta ba a lahira.

    7. Ba za su samu kariyar Allah ba.

    8. Ba za su shiga inuwar Allah ba.

    9. Allah Ta’ala zai haɗa su da waɗanda suka fi ƙarfinsu su gana musu uƙuba.

    10. ƙasar da zalunci ya samu wurin zama, sama da ƙasa ba za ta samu bunƙasa ba, ba za a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya ba a cikinta, komai sai ya sukurkuce a yi ta ragabza ba ji ba gani ana ci gaban mai haƙan rijiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma danna koren rubutun nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kura-kuran Masu Bayar Da Tarbiyya. danna koren rubutun nan

  • Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma

    Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma

    Duk shugaba ko ma’aikaci ko wani wakilin jama’a da dukiyar al’umma take gilmawa ko shigowa hannunsa to haƙiƙa yana cikin babban haɗarin da babu abinda zai ƙwace shi sai tsananin yaƙi da zuciya wajen kau da kai da haƙuri da kaucewa cin wa wannan dukiya ta hanyar da ba ta halattaba, tare da yawaita addu’ar Allah Ta’ala ya ba shi ikon sauke nauyin da yake kansa da kula da amanar da aka damƙa masa.

    Amfani da wannan nasihohi goma za su taimaka ƙwarai da gaske wajen tabbatar da haka;

    1) Ka kasance mai imani da cewa dukkanin dukiya ta Allah ce shi kaɗai kai matsayin wakili kawai kake, shi ne ma ya sa aka shata maka dokoki da sharaɗai kan yadda za ka yi mu’amala da wannan dukiyar kuma za a bincike ka a kan hakan ranar lahira. Saboda haka ka tabbatar duk abinda zai zo hannunka ka tabbatar halal ne tsantsa kuma ka yi amfani da shi ta hanyar da ta dace da shari’ar Allah Ta’ala.

    2) Ka kasance mai imani na gaskiya mai amana da kamewa da wadatar zuci sannan ka san hukunce-hukuncen musulunci, da suka shafi harkokin dukiya da kula da ita da kuma yin aiki da su.

    3) Ka sani cewa dukkanin ɗan ƙasa yana da haƙƙi a cikin dukiyar ƙasa kai ma ɗaya ne daga cikinsu, saboda haka, kada ka nuna son kai ko son zuciya da bambanci wajen baiwa mai haƙƙi haƙƙinsa.

    4) Ka sani cewa kare dukiyoyin al’umma daga sata, salwanta da lalacewa wajibi ne a kan kowa, musamman ma’aikata da shugabanni. Saboda tsaron dukiyar al’umma yana daga cikin manufofin shari’ar addinin musulunci.

    5) Ka guji cin amana da ɓarnatar da dukiyar al’umma ka sani ranar ƙiyama za a bincike kan duk abinda ka mallaka ka yi bayanin ta yadda ka same shi da kuma yadda ka yi amfani da shi.

    6) Ka guji yin amfani da dukiyar al’umma a kan buƙatunka na ƙashin kanka wanda ba su shafi aikinka ba. Misali kada ka rinƙa amfani da motar ofis wajen kai mata ko yara unguwa ko makaranta, ko ka ɗauki wani abu ka kai gidanka kana amfani da shi, ko kuma ka rinƙa amfani da injina ko kayan aikin ofis ɗinka ko ma’aikatarka.

    7) Ka yi mu’amala da dukiyar al’umma kamar yadda ake mu’amala da dukiyar maraya. Duk abinda mutum ya ci daga dukiyar marayu ba tare da haƙƙi ba, ya ci wuta balbal. Wajibi ne a rinƙa juya dukiyar marayu tana ƙaruwa, kuma a yi saboda Allah ba don neman a biya ka ba, sai dai in ka kasance mabuƙaci to sai a rinƙa biyanka ladan aikinka. To albashin ma’aikaci da shugabanni shi ne a matsayin ladansu.

    8) Ka sani cewa kare dukiyar al’umma wajibi ne akan kowa da kowa da kowa ba wai sai shugabanni ba kawai, saboda haka ya wajaba kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen yaƙar ɓarnatar da dukiyoyin al’umma gwargwadon ikonsa.

    9) Ka guji ƙoƙarin tara kuɗi ta hanyar amfani da ofishinka, kada ka yi sata, kada ka danne haƙƙin kowa, kada ka karɓi na goro, kada ka ci hanci da rashawa.

    10) Ka sani cewa Allah Ta’ala zai yi maka hisabi kan duk abinda ka aikata a ranar da dukiya da ‘ya’ya da ‘yan uwa ba za su yi wa mara gaskiya wani amfani ba. Yi ƙoƙari ka bar wa ‘ya’yanka halal komai ƙanƙantarsa sai Allah ya sanya masa albarka ya inganta bayanka.

    Kada ka tara haram ka mutu ka bar magada, ba za su yi albarka ba, kuma bayanka ba zai yi kyau ba. Ɗan uwa ka kula da wannan nasihohi ka yi aiki da su za su amfane ka a duniya da lahira. Allah ya sa mu dace amin.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa. danna nan.

    Don karanta bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma

    Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma

    Akwai hanyoyi da yawa da shugabanni da ma’aikata suke bi wajen ɓarnatar da dukiyoyin al’umma kuma sai Allah ya hukunta su a kansu domin nau’i ne na cin amana da rusa tattalin arziƙin ƙasa.

    Kaɗan daga cikin waɗannan hanyoyi su ne;

    1) Fantamawa da wadaƙar da shugabanni da manyan ma’aikata suke yi; da su da iyalansu da abokansu da surukansu da barorinsu da dukiyar al’umma musamman a lokacin bukukuwansu.

    2) Antaya dukiya ga wanda aka ga dama haka kawai; saboda an ga dama ya zama miloniya ya yi nashe-nashe yana muwalat ya zama kamar wani sabon mutum. A can gefe kuma ga talakawa suna ta kuka wasu ma suna mutuwa; an hana su ɗan abinda za su sayi abinci da magani.

    3) Tara dukiyar ƙasa da taskance ta da hana talakawa da sauran mabuƙata sai dai a yi ta cewa tattalin arziƙin ƙasa ya haɓaka; asusun gwamnati ya cika maƙil da kuɗi; amma babu wani talaka da zai gani a ƙwaryar tuwonsa sai dai a yi ta surutu maras kan gado. Wanda in ba su masu faɗar ba, babu mai fahimtar abinda suke faɗa.

    4) Yin amfani da dukiyar al’umma a kan buƙatun ƙashin kai, kamar motoci, injina; kayan aiki da kuɗin al’umma a gonakinsu, ko ma’aikatunsu ko gidajensu da sauransu.

    5) Fifita manya da masu hannu da shuni a kan waɗanda ba su da komai ko ba su san kowa ba; ta hanyar rage, ko yafe musu haraji ko kuɗin fito ko ɗaukar su ko ‘ya’yansu ko matansu aiki; ko ba su bashi don su juya wataƙila ma a ce an yafe musu.

    6) Kashewa mawaƙa da makaɗa kuɗaɗe masu yawa don kawai neman suna; alhali ga malaman makaranta da likitoci da sauran talakawa suna fama da ƙarancin albashi wanda ya jawo taɓarɓarewar aikin gwamnati da rashin zaman lafiya a ƙasa, sai ka ga a lokaci guda wani mawaƙi ko ɗan bal ko wata ‘yar fim suna zama miloniyoyi a sama.

    7) Kashe kuɗaɗe masu nauyin gaske a kan harkokin zaɓe; waɗanda da za a tsakuro ɗaya bisa ukunsu a sa a ɓangaren ilimi ko noma ko lafiya ko tsaro da an ga canji a rayuwar al’umma.

    Amma ina sai a yi watsi-watsi da waɗannan kuɗaɗe masu ciwon gaske a yi abinda aka ga dama; a ce an zaɓe wane ya ci wane ya faɗi.

    8) Kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tarbar shugabanni na gida da na wajen domin ƙawata tituna; tara musu talakawa, shirya abinci da sauran abubuwa na ganin ido sai ka ga a yini ɗaya an kashe miliyoyin nairori na fitar hankali; saboda wai shugaba wane zai kawo ziyara ƙasa ko jiha.

    9) Warewa harkokin wasannin kuɗaɗe masu ɗimbin yawa fiye da kuɗin da aka warewa ma’aikatar lafiya; tsaro, ilimi da sauransu waɗanda suka fi wasanni muhimmanci; amma dai haka suke rufe idanunsu su toshe kunnuwansu su narka kuɗi a can ba ruwan su.

    10) Caɓawa masallatai ado wani lakacin da gwalagwalai amma a yi burus da limamai da ladanai da ma su kansu masallatan masu sallah a wasu masallatan; sai ka ga adon yana shagalar da masu sallah maimakon su tara hankalinsu ga sallarsu; sai su yi ta kallon ƙyale – ƙyalen da aka yi.

    A wasu ƙasashen kuma sai a gina masallaci gari guda amma kuma babu masu sallar, sai dai ‘yan yawon buɗe idanu ne za su rinƙa zuwa suna ɗaukar hotuna a cikinsa.
    Kamar yadda a waɗansu ƙasashen ake ƙawata ƙaburburan shaihunai a kashe miliyoyin daloli domin kawai a samu goyon bayan mabiyan wannan mamacin (shehin).

    11) Rashin kula da aiki ta hanyar zuwa a makare da tashi kafin lokacin ya yi; da ma ƙin yin aikin ai an je wurin aikin sai a ɓuge da hira ko karance-karancen jaridu ko matse-matsen waya da kallon talabijin; ka ga kuɗin da ake kashewa kan waɗannan ayyukan da ma’aikatan kusan duk asarar su ake yi.

    12) Kashe dukiyar al’umma kan bukukuwa na ƙasa ko na siyasa ko bukukuwan da ake danganta su ga addini kamar bikin ranar samun ‘yancin kai, Bikin ranar demokuraɗiyya; bukukuwan mauludin Annabi da na shaihunai, sai ka ga an fitar da miliyoyin kuɗi an yi watandar su, alhali ga lalurorin rayuwa babu cikakkiyar kulawa.

    13) Biyawa ‘yan siyasa da ‘yan jagaliya aikin hajji ba don komai ba sai don kawai sun yi wa shugaba yaƙin neman zaɓe sai ya saka musu da kujerun hajji, waɗansu ma in sun je hajijiya kawai za su yi su dawo. Amma malamai masu koyar da alhazai aikin hajji da likitoci da sauran maa’aikatan da za su taimakawa alhazai su yi ibada cikin nutsuwa da inganci waɗannan babu wani laifi don gwamnati ta biya musu aikin hajji amma a ji tsoron Allah a yi gaskiya da adalci a dubi cancanta wajen zaɓar waɗanda za a biyawa.

    14) Ha’inci wajen ba da kwangila ta hanyar kashe-mu-raba tsakanin ‘yan kwangila da jami’an gwamnati; sai a zaftare kuɗin ko dai a ƙi yin aikin sam ko kuma a yi shi mara inganci ta yadda da an kwana biyu zai tashi daga aiki, in titi ne sai ya ɓaɓɓagure in gini ne ya rushe in wasu injina ne su lalace. Subhanallah.

    15) Wawashe kuɗaɗen al’umma a je a damfare su a bankunan ƙasashen turai, su yi ta gina kansu da su; ‘yan ƙasa kuma suna ta mutuwa. Waɗansu ma sai su je can su kafa masana’antu alhali ga miliyoyin ‘yan ƙasa ba su da aikin yi.

    16) Tarukan siyasa musamman na neman zaɓe da karɓar waɗanda suka baro jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar gwamnati; in ka ji yawan kuɗin da ake kashewa a irin wannan harkar abin akwai matuƙar takaici da ɗaure kai.

    17) Ware kuɗi mai yawan gaske da sunan wai za a yi addu’ar neman zaman lafiya ga ƙasa; ko kuma samun nasara a zaɓe. Sai dai abin takaicin shi ne mafi yawancin wannan kuɗi masu addu’ar ta gaske; saboda Allah ko labarinsu ba su ji ballantana su gan su. Sai a a yi dumbuza ana bai wa bokaye da miyagun malamai da matsafa da waɗanda ma ba musulmi ba. In ya zama dole sai an fitar da wannan kuɗi kamata ya yi a bi talakawa da gajiyayyu da malaman zaure da na tsangayu da ɗalibansu a ba su abinda zai faranta musu rayuka su ma su sami sa’ida da walwala to ko ba su yi addu’a ba; Allah zai biya buƙata sakamakon faranta musu da aka yi.

    A gaskiya hanyoyi da waɗansu shuwagabanni suke bai wajen tarwatsa da ɓarna da dukiyar al’umma suna da yawan gaske, abin fa ya zama sai dai a ce innalillahi wa inna ilaihirraji’un.
    Ya Allah ka ba mu ikon gyaran halayen mu, ka yi mana a fuwa da gafara ka a zurtamu da shugabanni managarta masu ƙarfi da amana amin.

    Domin karanta cikakken bayani akan Hidisai Goma Kan Hatsarin Shugabanci danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Haramcin Zalunci, Tasirin Addu’ar Wanda Aka Zalunta Da Wajabcin Sa danna nan.

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Ɗagowa Daga Ruku’u

    Ɗagowa Daga Ruku’u

    Ɗagowa Daga Ruku’u: Bayan kowacce gaɓa ta koma mazauninta; ya tsaya daram kar ya mayar da hannuwansa kan ƙirjinsa, wato; (Qabdu) su ne kaɗai zai bar su a sake kamar yadda mafi yawan malamai suka ce.

    Sannan sai ya yi kabbara, ya tafi sujuda; zai tafi sujuda ne da hannuwansa a wajan wasu malamai; ko da gwuiwar kafafunsa, a wajan wasu malamai ana so ya saɓawa yadda raƙumi ke faɗuwa idan zai kwanta.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Yin Sallar Istihara danna nan.

  • Hidisai Goma Kan Hatsarin Shugabanci

    Hidisai Goma Kan Hatsarin Shugabanci

    Hatsarin Shugabanci: Shugabanci komai ƙanƙantarsa wani nauyi ne babba a kan wanda ya hau kansa, wanda in ba a ɗauke shi an sauke shi daidai ba; in ba a yi gaskiya da adalci ba, in ba a riƙe amana ba; tabbas zai zama nadama da takaici ga wanda ya yi wannan shugabanci.

    Da mun san hatsarin da yake cikin shugabanci koda an yi shi bisa gaskiya da riƙon amana; da babu wanda zai nemi a ba shi shugabanci; da sai an zo ana bin mutum ana haɗa shi da Allah don ya karɓi muƙami yana gudu yana a kai kasuwa. To amma rashin sanin hatsari da yake ciki; da kuma kallon da kwaɗayin ɗan roman da yake cikinsa, shi ne yasa ake ta yin kokawa; har ma ana kashe kuɗaɗe masu ciwo da ma roƙon Allah duk don a ɗare kan karagar mulki.

    Ga wasu daga hadisan da shugaban halitta ya faɗa a kan hatsarin shugabanci:

    Hadisi Na Ɗaya

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa; “Kowane ɗaya daga cikinku makiyayi ne (shugaba ne) kuma za a tambaye shi a kan waɗanda aka ba shi kiwo; shugaba makiyayi ne kuma za a tambaye shi a kan waɗanda aka ba shi kiwo (mabiyansa), magidanci makiyayi ne a kan iyalansa kuma za a tambaye shi a kansu.

    Matar aure mai kiwo ce a gidan mijinta kuma za a tambaye ta a kan waɗanda aka ba ta kiwo. Yaron gida/kanti makiyayi ne a cikin dukiyar uban gidansa; kuma; kowa za a tambaye shi a kan abin da aka ba shi kiwo. Dukkanninku makiyaya ne, kuma za a yi masa tambaya a kan abin da aka ba shi kiwo.
    Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

    Karin Bayani

    Wannan hadisi ne mai girma da muhimmanci wanda ya ƙunshi abubuwa da dama kaɗan daga cikinsu su ne:

    1. shugabanci kalma ce mai faɗi bai taƙaita a kan masu riƙe da madafan mulki ba, a’a duk wani wanda waɗansu suke ƙarƙashinsa komai rashin yawansu to shi ma shugaba ne, kamar yadda hadisin ya faɗa:
    Mai mulki shugaba ne, mai gida shugaba ne a gidansa, matar aure shugaba ce a gidan mijinta, bara ko yaron gida ko angulun kanti, shugaba ne a kan dukiyar uban gidansa. Haka dai har shugaban aji da ɗalibai da na ƙungiyoyi da kwamitoci da sauransu.

    2. Kowa za a yi masa hisabi ranar lahira; za a bincike shi kan yadda ya gudanar da shugabanci da aka ba shi.

    3. Duk azabar da za a yi wa azzalumin shugaba; da kuma falala da rahamar da Allah yake yi wa adalin shugaba zai samu mai gida da uwargida, da yaron gida da sarki har zuwa shugaban ƙasa,babu bambanci, sai dai kuma kayan wani sun fi na wani yawa da nauyi.

    4. A duk lokacin da ake maganar shugabanci yabo ko zargi alhairi ko sharri kafin ka yi tunanin shugaban ƙasa ko gwamna ko sarki ko wani na can sama; ka fara duba kanka ka yi wa kanka hisabi. Shi shugabancin da aka ba ka, kana kula da shi yadda ya kamata? Shin kana ba da haƙƙoƙin da suke kanka?.

    Hadisi Na Biyu A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Anas ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah zai tambayi kowane makiyayi a kan abin da aka ba shi kiwo, shin ya kiyaye shi ko ya tozarta shi? Har ma za a tambayi mutum a kan iyalansa”.
    Ibn Hibban ne ya rawaito shi a cikin sahihinsa.

    Karin Bayani
    Lallai ne magidanta masu tozarta haƙƙoƙin iyalansu su bar ‘ya’yansu kamar marayu, matansu kamar kuyangi ba tarbiyya ba cikakkiyar lafiya har dabbobin da suke kiwatawa ma sai su fi iyalansu jin daɗinsu, su ji tsoron Allah su riƙe iyalansu da gaskiya su sani cewa amana ce Allah ya damƙa musu kuma za su yi bayani ranar ƙiyama kan wannan amanar.

    Hadisi Na Uku A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda ya zama alƙali haƙiƙa an yanka shi ba da wuƙa ba”.
    Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

    Karin Bayani

    Duk alƙalin da ya yi rashin gaskiya a kan aikinsa, haƙiƙa ya yi babbar asara ya halaka; ba wai rayuwarsa kawai ya rasa ba, har ma da addininsa wato wanda aka yanka da wuƙa zai fi shi samun sauƙin mutuwa da halaka. Wannan hadisi yana bayanin hatsarin da yake cikin alƙalanci; saboda haka ya zama wajibi ga alƙalai su yi taka tsantsan su rinƙa kwatanta gaskiya da adalci su guji zalunci, da cin hanci da murɗe gaskiya.

    Hadisi Na Huɗu A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Auf ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “In kuna so zan ba ku bayani a kan shugabanci ko yaya yake? Sai na ɗaga muryata na ce, “Yaya yake ya Ma’aikin Allah? Sai ya ce: “Farkonsa zargi ne, na biyunsa nadama ce, na ukunsa azaba a ranar ƙiyama sai dai wanda ya yi adalci”.
    Bazzar da Ɗabarani ne suka rawaito shi.

    Ƙarin Bayani

    Wannan hadisi ne mai ɗimbin fa’ida da bayanin ɗabi’ar mulki duk daga taƙaitattun kalmominsa

    • Mai mulki ba ya kuɓuta daga zargi da tuhuma da munana masa zato daga waɗanda yake mulka; da abokan hamayyarsa komai ƙoƙarinsa na kwatanta gaskiya. Haka zai ta shan suka da ƙalubale ta kowanne ɓangare, dukkanin idanu da kunnuwa suna kansa, komai ya faru shi ne ko bai sani ba, kuma ya fi ƙarfinsa.

    – Yayin da abubuwa suka dagule, matsaloli suka kunno kai ta ko’ina, magoya baya suka fara juya baya ga shugaba, barazana da fargaba ta yawaita a gida da waje, shugaba yakan tsinci kansa a halin da- na-sani, da nadamar karɓar wannan shugabanci.

    – Haka kuma bayan shugaba ya bar mulki musamman in an bi shi da jafa’i da bincike-binciken neman laifi da gazawa, wannan ma yana jefa masu mulki cikin kogin nadamar karɓar mulki.

    – Mafi munin yanayi kuma shi ne, matsananciyar azaba da take jiran azzaluman shugabanni a lahira da tozarta da wulaƙanta tun daga duniya.

    A taƙaice wannan hadisi yana ɗauke da tsoratarwa a kan shugabanci na zalunci da kwaɗaitarwa kan adalci saboda shi adalin shugaba babu ruwansa da wannan azabar.

    Hadisi Na Biyar A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Abu Zarr (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Na ce ya Ma’aikin Allah shin ba ka ba ni wani muƙami ba? Sai ya ɗora hannunsa a kan kafaɗata, sannan ya ce; “Ya kai Abu Zarrin haƙiƙa kai mutum ne mai rauni, shi kuma shugabanci amana ne, kuma yana jawo kunyata da nadama ranar ƙiyama; sai dai wanda ya kula da haƙƙoƙin shugabanci ya sauke nauyin da yake cikin shugabanci.

    Hadisi Na Shida A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga gare shi (Abu Zarr) Radiyallahu Anhu, haƙiƙa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da shi; “Ya kai Abu Zarr haƙiƙa na ga kai mutum ne mai rauni, kuma ina so gare ka abinda nake so ga kaina. Saboda haka, kada ka shugabanci koda mutum biyu, kuma kada ka karɓi riƙon dukiyar maraya.

    Muslim da Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi.

    Ƙarin Bayani

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) shugaba ne da yake lura da halin kowa kuma yake ba shi aikin da ya dace da shi.
    Duk tsoron Allah na mutum da yawan ibadarsa bai kamata a ba shi shugabanci ba, in dai ba shi da ƙarfi da gogewa kan al’amuran mulki. Wannan ne ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ƙi ya ba wa Abu Zarr wani muƙami saboda ya san rauninsa da matsanancin sauƙin kansa da gudun duniya; har ma ya ba shi shawarar cewa ko da shugabancin mutum biyu aka ba shi kada ya karɓa.

    Haka kuma kada ya karɓi ajiyar dukiyar marayu ba don yana tsoron zai cinye ba, a’a sai don gudun kada tausayi ya sa ya yi sadaka da wannan dukiyar.

    Ɗan’uwa idan an faɗa wa Abu Zarr (Radiyallahu Anhu) duk da falalarsa; ina ga mutanen yanzu da za ka ga har kuɗi ake kashewa, ko a yi ta yin rigima a kan neman shugabanci, ba kuma tare da wata cikakkiyar cancanta ko manufa ko tsari ba.

    Hadisi Na Bakwai A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzo Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Haƙiƙa za ku rinƙa kwaɗayin shugabanci, kuma haƙiƙa zai zama sanadin nadama ranar alƙiyama. Madalla da mai shayarwa tir da mai yayewa”.
    Bukhari da Nasa’i ne suka rawaito shi.

    Ƙarin Bayani

    Wannan abu da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa na tsananin kwaɗayin shugabanci kamar a yanzu yake maganar. Sai ka ga ɗaruruwan mutane suna takarar kujera ɗaya; kuma a yanzu kowa so yake ya zama shugaba, sai ka ga komai da shugabansa; kuma har ana rigima a kan wannan shugabanci. Amma duka a ƙarshe nadama ce take biyo baya.
    Mai shayarwa da mai yayewa shugabancin ake nufi, wato kamar yadda yaro yake jin daɗi lokacin da ake shayar da shi, kuma yake shan wahala da fama da laulayi iri-iri lokacin yaye shi to haka daɗin shugabanci yake a farkon da kuma wahala da damuwa da ake shiga in an sauka.

    Hadisi Na Takwas A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Kaicon sarakuna, kaicon wakilai, kaicon amintattu. Wallahi waɗansu mutane (waɗanda suka karɓi shugabanci) a ranar ƙiyama za su yi burin ina ma da a ce a ɗaure gashinsu a jikin tauraron surayya; su yi ta reto tsakanin sama da ƙasa a maimaikon shugabancin da suka riƙe.

    Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi.

    Hadisi Na Tara A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa; “Zamani ya kusa zuwa da mutum zai yi burin gara a ce ina ma ya faɗo daga tauraron Surayya (zai fi masa sauƙi) a kan mulkin da ya yi komai ƙanƙantarsa”.

    Hakim ne ya rawaito shi.

    Ƙarin Bayani

    Waɗannan hadisai guda biyu suna bayanin hatsarin shugabanci ta yadda mutum zai ji a ransa cewa gara a rataye shi da gashinsa a jikin tauraro ya yi ta reto; ko kuma a jefa shi daga can sama ya yi ƙasa ya ratattake a maimakon azabar da za a yi masa; saboda rashin adalci da gaskiya da ya gudanar a shugabancin.

    Hadisi Na Goma A Kan Hatsarin Shugabanci

    An karɓo daga Abdurrahman bin Samura (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da shi; “Ya kai Abdurrahman ɗan Samura kada ka nemi shugabanci, saboda in ya zo maka ba tare da ka nema ba, Allah zai taimake ka a kansa; in kuwa aka ba ka shugabanci saboda nema da ka yi sai Allah ya bar ka da dabararka”.

    Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

    Ƙarin Bayani

    Duk wanda ya san hatsarin shugabanci da makomarsa; ba zai iya nacewa ya yi ta kokawar sai ya sami muƙami ba. To irin wannan idan aka ga cancantar su aka tilasta musu lallai sai sun karɓi muƙamin za su sami tallafi da agaji daga Allah.
    Wanda kuwa ya nace sai an ba shi muƙami musamman in bai cancanta ba ko kuma yana da wata muguwar manufa a ransa to ba zai yi wani abin kirki ba sai hauma-hauma da zalunci.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A Kan Shugabanci); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Tafiya Sujudah

    Yadda Ake Tafiya Sujudah

    Tafiya Sujudah: Akwai hadisin da ya ce mai sallah ya fara ajiye gwuiwarsa kafin hannayensa. Ruwayar (wa’il ibnu hujur).

    Akwai kuma hadisin da ya ce ; ya fara ajiye hannayensa kafin gwuiwarsa, ruwayar (Abu Huraira); shi ne wasu malaman suka ce; gwuiwar raƙumi a hannunsa take saboda haka, da hannuwanka za ka tafi ba da gwuiwa ba.

    Wasu malaman kuma suka ce; ruwayar (Wa’il ibnu Hujur) ita ce ta zo daidai ruwayar (Abu Huraira); ta zo a baibai ne, saboda haka da gwuiwar ƙafafunsa zai tafi sujuda ba da hannuwansa ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya yi Bayan Ya Tafi Sujudah danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sallar Roƙon Ruwa danna nan.

  • Tatsuniyar Gizo Da Namun Daji

    Tatsuniyar Gizo Da Namun Daji

    Ga ta nan ga ta nan ku

    Gizo ne dai yana son ya ci nama, amma ba shi da shi. Ya rasa yadda zai yi. Sannan ya ce a ransa, “Bari dai in yi wata dabara”. Sai ya sayo goro ya rarraba wa namun daji da tsuntsayen gida. Sai ya fara kai wa kaza, ya ce, “Ga shi, goron wasa ne wanda za a yi a cikin daji, naki ne wannan” .

    Sai kaza ta ce, “To. Amma fa kada ka kai wa muzuru”. Sai ya ce, “Haba, me zai sa in kai masa?” Da gizo ya fita, sai ya shiga gidan muzuru, ya kai masa goro. Sai shi ma muzurun ya ce, “To, amma kada ka kai wa kare”. Sai gizo ya ce, “Haba me zai sa in kai masa?”

    Da dai gizo ya fita, sai ya shiga gidan kare ya ba shi nasa goron. Kare ya ce, “To, amma fa kada ka kai wa kura”. ‘Gizo ya ce, “Haba me zai sa in kai mata?” Da ya fita, sai ya kai wa kura nata goron. Kura ta ce, “To, amma fa kada ka kai wa Zaki”.

    Ya ce, ‘Haba kura, me zai sa in kai wa Zaki?’

    Shi ke nan, sai ya kai wa Zaki nasa goron, ya ce, “Ranka ya daɗe. Wani ɗan wasa za a yi na kawo maka goro”. Da Zaki ya karɓa, sai ya ce, “To, Allah ya kai mu”. Shi ke nan. Da ya fita, sai ya shiga ya kai wa damisa. Damisa ta ce, “In ce ko dai ba ka kai wa Sarki Zaki ba?”
    Sai Gizo ya ce, ‘Haba, haba. Wane ni da gayyatar Sarki?’ Sai damisa ta ce, ‘To, Allah ya kai mu”.

    Da ya fito sai kuma ya shiga gidan giwa ya kai mata nata goron. Sai giwa ta ce, “To, in ce ko baka kai wa manyan dawa ba?’ Ya ce, “Mhm! Yaya zan kai?” Ko kai masa ne ma ai ke zan bai wa ki kai masa “. Shi ke nan. Ana nan ana nan, sai ranar wasa ta zo. Gizo ya bayyana musu wurin da za su haɗu a yi wasan. Ya ce musu, “To, ku tafi zan same ku. Ni daga baya zan taho tare da makaɗa’. Shi ke nan. Sai kaza ta fara tafiya. Ashe ba su sani ba, gizo ya riga su isa can. Sai kaza ta isa can. Gizo ya yi mata maraba. Ya ce,

    “Shiga wannan bukkar kafin su zo”.

    Shi ke nan. Kaza ta shiga, ta zauna. Daga can sai ga muzuru ya taho. Sai Gizo ya gaya wa muzuru cikin raɗa, ‘Maraba’. Shiga tana nan a ciki’. Shi ke nan sai muzuru ya shiga ya tasar wa kaza zai cinye ta. Ya cinye ta. Can kuma sai ga kare ya taho. Shi ma dai Gizo ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa muzuru. Sai shi ma karen ya cinye muzuru.

    Daga nan kuma sai ga kura. Ita ma ya gaya mata kamar yadda ya gaya wa kare da muzuru. Sai kura ta shiga ta cinye kare. Kura kuma tana zaune a cikin rumfa. Sai ga Zaki ya taho. shi ma Gizo ya gaya masa haka. Ya shiga ya cinye kura. Daga nan sai ga giwa da damisa sun jero sun taho. Sai Gizo ya ce, “To, ku shiga nan bukkar mana”. Daga shigar su, sai suka kaure da faɗa tun daga cikin rumfar har suka yiwo waje. Idonsu duk ya rufe, suna ta faɗa. Sai Gizo ya samo ganga, ya soma kiɗa yana waƙa:
    Zaki bari, damisa bari.
    Giwa bari.

    Faɗanku na manya,

    Wa yake shiga?
    Sai wawa, sai mahaukaci.
    Sai ko ni da ba ni da hankali.

    Suna ta faɗa, can da giwa ta ga abin ba dama, sai ta fito ta yi tafiyarta gida, ta bar zaki da damisa suna karawa. Sai Gizo ya ci gaba da yi musu waƙa. Ya yi ta yi, su kuma suna ta faɗa. Ashe Gizo da ma ya zo da yaji a ƙunshe. Sai ya ɗauko yajin nan ya barbaɗa musu a idanunsu. Sai fa faɗa ya rincaɓe, idanunsu suka rufe ruf. Daga can sai Gizo ya ɗauko wuƙa ya ce, “Yan banza. Ana so a ci nama an rasa yadda za a yi”. Sai ya kama yankan naman jikinsu yana tarawa, har ya kashe su duka. Sai ya jide naman ya kai gida aka soya masa, ya ci ya ƙoshi, ya ajiye sauran, yana ci lokaci-lokaci.

    Ƙurunƙus.

    Domin karanta Tatsuniyar Ɗankaɗafi danna nan.

    Domin karanta Tatsuniyar Gizo Da Giwa danna nan.

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Dawo Da Abin Da Aka Goge A Kan Komfiyuta

    Yadda Ake Dawo Da Abin Da Aka Goge A Kan Komfiyuta

    Mafi yawancin dukkanin wani abu da aka goge a kan komfiyuta ba wai an goge shi ne ba gaba ɗaya; mafi yawanci yana zuwa cikin wata ma’ajiyar datti ne; wanda ake kira da “recycle bin” a Turance; wani kuma ta wajen gogewa ake sa shi, a tsarin da idan an goge ba ya shiga wanann ma’ajiyar dattin (Recycle Bin).

    Shin ko ka taɓa goge wani abu daga komfiyutarka ba tare da kana son ka goge shi ba ? kuma kana bukatar ka dawo da shi, sannan kuma ba ka gan shi a cikin ma’ajiyar datti ba (recycle bin) wanda ta yiwu ka goge shi ne ta yin amfani da shift+delete ko kuma ka zazzage ma’ajiyar datti (emptied recycle bin) . Sabo da haka kada a damu, hakan yana iya yiwuwa domin ana dawo da irin wannan abin da aka goge.

    A wannan bayanin za a kawo yadda ake dawo da abubuwan da aka goge ta hanyar amfani da wasu massarafai da aka samar domin aiwatar da irin wannan aiki.

    Mafi yawanci duk wani file da aka goge a kan komfiyuta, ba wai ya goge daga kan kwakwalwar komfiyuta ba ne (hardrive) yana samun wani guri ne ya shiga, inda ba zai zama mai nauyi ba sabo da an nuna ba shi da muhimmanci, to zai je nan ya tsaya jiran ko za a iya dawo da shi, haka kuma zai ta zama ne har sai an sanya wani a madadin sa wanda zai cinye wannan guri da aka sanya wancan abin da aka goge na farko, a mafi yawancin kwakwalwar comoter ma ko an sanya wani ana iya dawo da shi.

    Akwai masarrafai (softwares) da yawa waɗanda ake amfani da su domin aiwatar da wanann aiki ga kaɗan daga cikin su:

    1. Tokiwa data recovery

    Wanna masarrafi bai wuce kimanin 200 kb ba, kusan ma shi ne masarrafi mafi ƙanƙanta/mafi ƙarancin nauyi wajen aiwatar da wannan aiki na dawo da abubuwan da aka goge, wanda yana ɗauko abubuwan da aka goge daga kan tsarin ƙwaƙwalwar da ke da FAT 12, FAT16, FAT32 da kuma NTFS file, haka kuma yana dawo da abin dake kan tsarin NTFS wanda aka yi compressed da kuma na kan EFS encrypted file. Haka kuma wannan masarrafi yana taimakawa wajen dawo da su ba tare da an sha wahala ba, haka kuma da wannan masarrafin za a iya goge abin da ba a buƙatar sa har abada.

    2. Pandora recovery

    Ita ma wannan wata massarrafar ce (software) dake bayar da damar yin wannan aiki da muka faɗa a baya, wanda a nan ita tana ba da cikakkiyar dama wajen gani ka nemi irin abin da kake so ka dawo da shi, ko kuma file na abin da kake son ka dawo da shi, haka kuma zai ba ka damar nemo wata hanyar amfani da sunan file naka da kake nema, musammam wanda ka san sunansa, ko kuma ranar da ka yi aikin,

    Haka kuma, yin amfani da wannan hanyar ba ya iya nuna maka asalin inda aikin yake, yana nuna maka aikin ne kawai da aka goge daga kan computer, musamamn daga inda ake ganin ya lalace , ko kuma ake ganin kamar ba zai dawo ba, ko kuma aka yi formated gaba ɗaya, haka kuma yin amfani da wannan hanya ba wai sai a kan ƙwaƙwalwar komfiyuta kaɗai yake aiki ba, za ka iya dawo da abin dake kan CDs da kuma DVDs.

    3. Recuva:

    Wannan ma wani masarrafi ne mai saukin aiki, wanda yake aiwatar da irin aikin da muka yi bayanai a baya , wanda shima yana ba ka damar ka yi serch ne na abin da kake son ka dawo da shi, ta yin amfani da sunan file misali, Waƙoƙi ne , hotuna, rubuce-rubuce ko kuma wasu abubuwa makamantan waɗannan kamar hoto mai motsi (vidios) haka kuma yana iya ba ka damar neman abin da ya daɗe , da gogewa, kamar yadda waɗanda suka gabata suke aiwatar da nasu aikin, haka kuma wannan masarrafin yana da versioin kala-kala sai wanda ka ga zai iya yi a kan computer naka, sannan za ka ɗauko domin amfani da shi.

    Haka kuma dukkanin waɗannan massarafi da ma wasu da ba aka kawo a nan ba, suna aiki ne wajen dawo da abin da aka goge daga kan memory na waya ko na kan computer , ko kan camera, ɗaukar hoto, haka kuma yana dawo da dukkanin hotuna, video, Waƙoƙi , rubutattun ayyuka daga kan tsarin FAT da kuma NTFS wanda aka yi formating , sanna kuma ana iya amfani da su a kan tsarin massarfin komfiyuta na win xp, win vista win 7,8,8.1 da kuma win 10.

    Hanyoyin Da Ya Kamata A Bi Wajen Samun Damar Dawo Da Abin Da Aka Goge

    1. Idan aka goge wani abu bisa rashin sani daga kan wata ma’ajiya, a tabbatar ba a sanya wani abu ba a kan inda aka goge wannan ma’ajiyar, misali abin da zai iya zama ya shige gurin da ka goge wancan bayanan, wanda in ya shiga gurin wanda aka goge hakan ba zai sami damar dawo da abin da aka goge ba kasancewar wanda aka sanya daga baya ya rufe gurin wancan da aka goge, hakan kuma zai iya hana dawo da wancan da aka goge.

    2. Idan ka yi ƙoƙarin dawo da abin da ka goge sai hakan ya gagara, hakan ba yana nuna abin ba zai yiwu ba ne, abin yi a nan shi ne, ka nemi wani kalar masarrafin wanda zai maka wannan aiki, ta yiwu wannan wanda kake da shi shi ne ba zai iya aiwatar da aikin ba.

    3. Idan ka goge abu a kan computer naka da kake aiki da shi, yi ƙoƙari kada ka sanya wani abu a kanta, sai dai kawai in kana da filin da za ka ɗauko ɗaya daga cikin massarrafan da suke taimakawa wajen dawo da abin da aka goge, sai ka ɗauko domin aiwatar da wannan aiki, bayan ka gama, sai ka kashe komfiyuta sannan ka kunna sai ka fara aiwatar da aikin dawo da abin da ka goge.

    Haka kuma yana da kyau ya zama kana da waɗannan masarrafan a cikin wata ma’ajiya taka ta musammamn “flash drive” , ko da za ka goge wani muhimmin abu bisa kuskure.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za Ka Dawo Da Martabar Batirin Wayarka danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Komfiyuta (Computer) danna nan.

  • Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai

    Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai

    Addu’o’in Tsari Daga Azzalumai; An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Radiyallahu Anhu) ya ce; Idan ɗayanku yana jin tsoron wani azzalumin shugaba sai ya ce:

    Allahumma rabbussamawatis sab’i, wa rabbul arshil azim, kun li jaran min wa atba’ihi min halƙika minal jinni wal insi an yafruɗa alayya ahadun minhum au an yaɗga, azza jaruka wa jalla sana’uka wa la’ilaha illan anta”.

    Asbahani ne ya ruwaito shi daga Ibn Mas’ud danganta maganar ba ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) (Mauƙuf).

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Idan ka je wurin wani shugaba mai kwarjini wanda kake jin tsoron zai afka maka sai ka ce:

    Allah Akbar Allah a’azzu min khalƙihi jami’an, Allahu a’azzu mimma akhafu wa ahzaru, a uzu billahillazi laa ilaaha illaa huwa almumsikus samawati an yaƙa’a na alal ardi illa bi iznihi min sharri abdika wa junudihi wa atba’ihi wa ashya’ihi minal jinni wal insi. Allahumma kun li jaaran min sharrihim jalla sana’uka wa azza jaruka wa tabarakas muka, wa laa ilaahha gairuka”(sau uku).

    Ibn Abi Shaiba ne ya ruwaito shi, daga Ibn Mas’ud.

    Ƙarin Bayani

    Wannan hadisi sahihi ne mauƙufan wato zuwa ga Ibn Mas’ud, amma bai inganta ba zuwa ga Annabi. Haka kuma addu’a ta biyu ta inganta daga Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu).
    Addu’o’i ne kyawawa da mutum zai iya yi duk lokacin da ya ji tsoron zaluncin wani azzalumin shugaba. A wurin da babu komai sai a faɗi sunan shugaban.

    Fassara

    Fassarar addu’a ta farko:

    Ya Allah Ubangijin sammai bakwai, Ubangijin Al’arshi; mai girma ka kare ni daga sharrin wane ɗan wane da dukkan mabiyansa daga halittunka aljanu da mutane; kada ka ba wa ɗaya daga cikinsu dama ya afka min ko ya yi min ta’addanci; kariyarka ta buwaya, yabonka ya girmama. Babu wanda ya cancanta a bautawa sai kai.

    Ita kuwa addu’a ta biyu ga fassararta:

    Allah shi ne mafi girma, Allah shi ne mafi buwaya daga halittunsa gaba ɗaya. Allah shi ne mafi buwaya daga abin da nake tsoro da fargaba. Ina neman tsari da Allah wanda babu wanda ya cancanta a bauta wa sai shi; wanda yake riƙe da sammai kada su faɗo kan ƙasa sai da izininsa. Ka kare ni daga sharrin bawanka wane da jami’an tsaronsa da mabiyansa da ma magoya bayansa mutane da aljanu.
    Ya Allah ka kasance mai kariya a gare ni daga sharrinsu, yabonka ya girmama, wanda ka baiwa kariya ya buwaya, sunanka ya yi albarka babu wanda ya cancanta a bautawa sai kai.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sahabban Da Suka Fi Kowa Rawaito Hadisai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Hadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni danna nan.