Ruɗani Game Da Hanyoyin Samun Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali.

0
495

1. Kuɗi

Waɗansu mutanen gani suke yi, ba mai more rayuwa a duniyar nan da samun natsuwa sai mai kuɗi. Shi ne kawai yake iya huce haushin duniya, ai in ka sami kuɗi ka sami komai, ka haye ka wuce tsara, ka fi ƙarfin raini, haka suke gani.

To amma shin kuwa abin haka yake mai kuɗi shi ne yake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali?

Bari mu ga waɗannan ‘yan misalai guda biyu:

Ƙaruna biloniyan biloniyoyin duniya.

Tun da Allah ya yi duniya ba a taɓa mutum mai mahaukaciyar dukiya ba irin Ƙaruna.

Alƙur’ani ma da kansa ya jinjina irin tarin dukiyar da Allah ya mallaka masa. Ya zama tauraron duniya son kowa ƙin wanda ya rasa. Duk inda ya yi, sai sha’awarsa ake yi, ana haɗiyar yawu, ana ina ma ni ne Ɗanƙaruna. Yana takawa ɗaiɗai, yana hura hanci yana ganin ya fi kowa, babu wanda ya isa sai shi.

Amma a ƙarshe kuɗinsa ne suka jawo masa halaka. Saboda irin girman kai da ɗagawa da ya rinƙa yi Allah ya halakar da shi da dukiyarsa. Karanta sura ta 28, suratul Ƙasas ka sha labari.

Christina Aunasis

Wata hamshaƙiyar biloniya ce yar ƙasar Jamus, wacce ta gaji dukiya ta fitar hankali daga iyayenta. Ubanta ya mutu ya bar mata tsabar kuɗi wuri na gugar wuri Dala miliyan dubu biyar da jiragen ruwa maka-maka, da na sama jibga-jibga, kai har tsibirai ubanta ya bar mata, ba a ma maganar gidaje gonaki da filaye. To shin wannan dukiya ta kawo mata zaman lafiya da kwanciyar hankali?

Ga taƙaitaccen labarinta. Uwarta dai ta mutu cikin baƙin ciki da mummunan yanayi, bayan ubanta ya wulaƙanta ta ya sake ta. Yayanta kuma jirginsa na sama ya hau yana ta wasan asha-ruwan-tsintsaye a kai, sai kawai ya rikito da shi ya mutu. Shi Kuma ubanta neman suna ne ya kai shi ya auri tsohuwar matar tsohon shugaban Amurka “John Kennedy”. Duk da ta kafa masa sharaɗin ba za ta yarda ya kwanta da ita ba, kuma ba wani umarni nasa da za ta ɗauka ga kuma miliyoyin daloli da ya kashe-kashe, amma ka san mai jan kunne da neman suna….. duk da haka zaman bai yi daɗi ba ya sake ta. Haka dai ya mace cikin damuwa da alhini.

Yanzu saura “Christina” ita kaɗai tare da ɗimbin dukiyarta. Da farko ta auri wani ɗan Amurka, amma ba a shekara ba ta sake shi. Sai ta tafi “Grecce” ta sake yin aure, shi ma abin bai yi daɗi ba, ta sallame shi.

Daga nan sai ta nufi Rasha Kasar gurguzu, inda ba a yarda mutum ya zamo mai kuɗi ba, duk da haka ta yarda ta auri wani ɗan Rasha ta zauna ita kaɗai, ko yar aiki ba ta da ita, da ‘yan jarida suka tambaye ta yaya haka kuma? Sai ta ce, “Lalube nake ko na sami kwanciyar hankali”. Shekararta ɗaya a Rasha ta saki wannan miji. Sai ta nufi Faransa.

A can ta auri wani Bafaranshe, aka yi gagarumin biki, ‘yan jarida suka tambaye ta game da dukiyarta sai ta ce: “Ni ce macen da ta fi kowa kuɗi a duniya, kuma ni ce macen da ta fi kowa hankali a duniya!”

Bayan sun haifi ‘ya mace da wannan bafaranshe sai ta sake shi. Kai a ƙarshe dai tsintar gawar ta aka yi a Ajantana har yau ba a san dalilin mutuwarta ba.

A gaskiya kuɗi dai shi kaɗai bai isa ya tabbatarwa da mutum zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Shi dai neman sa wahala, in an samu ba hutu, saboda tsoron kada su ƙare. Ga yawan tunani da damuwa. Ga tsoron ‘yan fashi ɓarayi da ‘yan ina-da- kisa, da zalunci a gwamnati, ba cikakken zama, ballantana isasshen barci, abinci ma ba shi da cikakken lokacinsa, ballantana iyali. Kai tashin hankalin yana da yawa. Allah ya kyauta, ya kuma ba mu na rufin asiri.

2. Suna

Waɗansu kuwa sukan ɗauka cewa kwanciyar hankali yana cikin yin suna. A ɓangaren wasan kwaikwayo da wasannin motsa jiki kamar ƙwallon ƙafa kokawa da sauransu. Masu irin wannan tunani za ka ga suna matuƙar sha’awar taurarin ‘yan wasa da shahararrun gwanaye a ɓangaren wasannin motsa jiki.

To amma masu wannan tunani sun tafka kuskure, saboda babu waɗanda suka fi taurarin ‘yan wasa tashin hankali da rashin zaman lafiya. Ka ɗauki ƙwallon ƙafa, misali irin faman wahala da suke sha wajen gwaji (training) da wulaƙanta da suke kafin su cancanci zama zakaru, ga rashin zama wuri ɗaya, da dama daga cikinsu sukan salwantar da karatunsu saboda ƙwallo. Sukan shiga halin tsoro da faɗuwar gaba duk lokacin da za su kara da wani kulob. Idan kuwa ba su yi nasara ba, ai sun shiga uku a wajen magoya bayansu, za su sha la’ana da zagi, wani lokacin ma har da duka.

Kuma ba wuya an mance da mutum, an koma kan wani gwarzon, shi kuma an jefa shi a kwandon shara. Daga nan sai ya shiga rayuwar takaici da ɓacin rai, musamman ganin ana yi babu shi. Haka dai zai ƙare ya mace a wulaƙance.

To don Allah ɗan uwa ina abin sha’awa a nan.

To in ka ɗauki ‘yan wasan kwaikwayo su ma haka suke, farkonsu shaye-shaye da lalata da rashin zama wuri ɗaya, rashin mutunci, rashin kunya ga zunubin ɓata tarbiyya, sannan kuma da tauraron mutum ya disashe, sai a tattara shi a koma wani. Ya mutu a banza ba addini ba adila. Shin yau ina su Pele James Brown, Amita, Dram, Danhaki, Gaso-rogo da sauransu?

To haka ma kwanan nan za ka daina jin su wane da wance, an koma gefe ana nadama marar amfani. A gaskiya babu wata nutsuwa da kwanciyar hankali cikin waɗannan wasanni. Allah ya ganar da mu amin.

3. Mulki

To ko a cikin mulki da riƙon muƙamai sirrin zaman lafiya yake?

Waɗansu da dama suna ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali na ga mulki, haka suke gani. Amma ga mai lura ya san abin ba haka ba ne. Ɗauki masu riƙe da muƙamin siyasa a yau, ga dai kuɗin kamar na Ƙaruna, ga su ɓulɓul da manyan riguna, gidaje da motoci da sauran kayan alatu. Amma shin suna iya watayawa cikin ‘yanci kamar kowa?

Ai ko wawa ya san wannan guje-guje da rundunar yaƙi da take biye da su, ba na lafiya ba ne. Kuma wace irin wahala ce ba a sha ba kafin a samu mulkin? Sannan in an samu, sai a kasa zaune a kasa tsaye ana tsoron sharrin ‘yan adawa da kuma gushewar mulkin. Daga nan sai cutar tazarce ta kama mai mulki.

Sai hauma-hauma da danniya ko ta-zarce ko ta-kauce. In ta-zarce ƙarin matsala in kuwa ta-kauce to sai dai a lallaɓa “Chairman” domin har hauka ta-kauce kan haifar, komai zai iya faruwa.

Akwai ɗimbin misalai a kan wannan batu nawa. Shin ina su Fir’auna da Hamana? Ina su Shah na Iran, Ferdinand Marcos na Filfin, da Mabutu na Zaire da Abacha na Nijeriya. To ai duk ba a nan take ba, in fa ba a shimfiɗa adalci ba, to tashin hankali sai an je lahira. Allah ya tsare mu. Amin.

To kaga dai zaman lafiya da kwanciyar hankali na gaskiya babu shi a cikin mulki sai in a lahira ga shugaban da ya yi adalci.

4. Wayewar kai da ci gaba

In haka ne za mu iya cewa wayayyun mutane waɗanda suka ci gaba suke da fasahar ƙere-ƙere da ƙirƙire-ƙirƙire su ne masu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wato dai kamar irin su Amerika da ƙasashen Turai da ‘yan boko-addini. To amma bari mu yi nazarın su, su ma mu gani.

A gaskiya duk ɗan boko da ya amsa sunansa ya san irin firgici da tashin hankali da Turawan yamma da na gabas suke ciki abin sai su. Tarbiyya ta daɗe da yin ƙaura daga wannan yanki har an mance da sunanta. Mutunci ba a yayin sa. Tuni mutanensa suka faku. Rayuwar ƙunci kuwa da fatara da rashin sanin inda aka dosa, sai wanda ya zauna da su ko yake karanta littattafai da mujallu da suke fitowa daga can.

Wannan shi ne ya sanya a koda yaushe suke kashe kansu ta hanyar rataye kai, ko shan guba ko kuma bindige kai, to don Allah ɗan uwa ina zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan rayuwa.

Mai karatu ruɗani game da hanyoyin samun nutsuwa yana da yawa ta yadda waɗansu Wawayen ma gani suke yi ta hanyar shaye-shaye da aikata miyagun laifuka kamar zina, liwaɗi, fashi da sauransu, wai ta waɗannan hanyoyi za su iya cimma burinsu. Amma ina! Sai ka ga waɗannan mutane su suka fi kowa shiga tasku cikin rayuwarsu. Haka nan sukan rayu cikin tsiya da wahalar zuciya kuma su yi mummunar mutuwa, su je su tarar da mummunar makoma.

Allah ya tsare mu.

To mai karatu tun da dai mun ga babu ci cikin waɗannan abubuwa to mene ne haƙiƙar abin da ya ke hana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali? Karanta waɗannan babi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Su Ke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ziyarar Mara Lafiya danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali; wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceZaman Lafiya Da Iyali
Labarin na GabaAbubuwan Da Suke Hana Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali