DUNIYA MAKARANTA!

0
647

Allah mai girma da ɗaukaka ya bayyana cewa: “Shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya gwada ku. Wane ne mafi kyawun aiki a cikin ku?”(Suratul Mulk: 2).

Kuma manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya siffanta Aljanna da haja. (Kayan sayarwa) mai tsada, ba a samunta a ɓagas kamar kifin gwangwani, sai an yi aiki mai tuƙuru, aiki na gari, sannan za a iya mallakar ta.

Don haka ne, Allah ya sauko da mutum a gidan duniya, sai ya jarrabe shi da Shaiɗan wanda kullum aikinsa shi ne;ya ɓatar da mutum, ya afka shi cikin saɓo. Wato ya sa shi ya faɗi a jarrabawar!
Bugu da ƙari, shi shaiɗan yana da mataimaka masu taya shi aikin ɓatar da mutum, waɗannan mataimaka suna da yawa, amma mafi hatsari a cikinsu sune: Son zuciya da ruɗin duniya. Saboda haka, idan mutum yana son ya ci jarrabawar Allah, ba shi da hanyar da ta wuce saɓawa waɗancan magauta guda uku.
• Shaiɗan;
• Son zuciya;
• Ruɗin zuciya

• Saɓa wa Shaiɗan: Kar mutum ya manta da ƙiyayyar da Shaiɗan yake yi masa, don haka ya kamata ya dauwama a kan nema tsari da shi, sannan ya riƙe koyarwar Musulunci sosai.
• Saɓawa Son Zuciya: Ta hanyar bin ƙa’ida, da riƙe gaskiya da tsarin amana, ko da ransa ba ya so.
• Saɓawa Ruɗin Duniya: Ta hanyar neman halal, da haƙuri da abin da ya samu ta hanyarsa, ka da ya yi garajen tara kayan more rayuwa ta hanyar sata da zamba.
Domin haka, mutum a gidan duniya kamar a filin kokawa yake, abokan karawar sa su ne shaiɗan da son zuciya da ruɗin duniya, wanda ya yi jarumta ya nana su da ƙasa, tabbas shi ne zai ci kambu kuma shi ne wanda zai zama jarumi, gwarzon maza (ko kuma jarumar mata!)
Domin haka ne Allah Ya aiko da Manzanni suka bayyana dokoki, suka ajiye ƙa’idoji, suka tsara hanyoyi, suka shata iyakoki. Mutumin da ya tsaya idan aka tsayar da shi, ya kuma nufi inda aka umarce shi,shi ne wanda ya kawar da waɗancan abokan kokawa nasa, kuma shi ne ya ci jarrabawa, don haka sakamakosa shi ne samun dacewa da yardar Allah. (Allah Ya sa mu dace).

Idan mutum ya yi tunani, zai gane cewa, yin haƙuri a cikin bin Allah, da kuma yin duniya wajen saɓawa son zuciya ba a cikin shari’ar addini kawai yake ba, a’a har ma cikin shari’ar rayuwa. Akwai abubuwa da ba ya so, amma haka yake haƙura ya tafi yadda ake tafi da shi a cikin su. Ba a komai ne zai gudanar da rayuwarsa yadda yake so ba, kamar tsufa da rashin lafiya da mutuwa waɗanda ba shi da tasiri a kansu. To, haka ma a cikin bin shari’ar addini, sai ya haƙura ya bi doka ko ta yi masa daɗin ko ba ta yi masa ba, kamar yadda ya saba yi, a shari’ar rayuwa. Abu dai mafi muhimmanci wanda yin tunani a kansa zai taimaka mana wajen ƙara yin haƙuri cikin bin Allah shi ne, duk abin da shari’a ta umarce shi da shi, to wannan abin amfani ne da alhari gare shi, a duniya da lahira, kuma duk abin da shari’a ta haramata masa, to sharri ne a gare shi da masifa da ƙangi da shiga halin ƙaƙa-naka-yi. Allah Ya kiyashe mu, ameen.
Duba ka gani; Allah Ya wajabta yin lmani da shi (Allah Shi kaɗai, wanda ba shi da abokin tarayya, mai iko ne bisa komai. wanda ya halacci dukkan halitta).kuma ya haramta imani da yin bauta ga wani wanda ba Shi ba, ko mutum ko aljan ko mala’ika ko tauraro ko rana ko wata ko dutse ko itace, da sauransu. Wanda yake dukkan su samar da su Allah ya yi,hasali ma gajiyayyu ne mubuƙata ne, ba su da ikon yin wani abu sai da izinin Allah.Ka ga a nan wanda ya yi aiki da umarnin Allah shi ne zai amfana, saboda zai samu nutsuwa a rayuwarsa. Wanda ya saɓa masa kuma shi ne zai cutu domin zai rayu cikin ruɗani, da damuwa.
Haka kuma, Allah Ya halatta madara da zuma, amma ya haramta giya, kuma ya halatta ciniki da saye da sayarwa na ƙa’ida, amma ya yi aure daga mace ɗaya zuwa huɗu, amma Ya haramta zina. Allah Ya halatta zaman lafiya,, zumunci, da mutunci, da alheri, da ƙaunar juna, amma Ya haramta gaba, da ƙullata, da kinibibi, da maunafunci, da ƙeta, da dai kowane mugun hali. Dukkan abin da Allah Ya halatta mana alheri ne garemu, kuma dukkan abin da ya haramta mana sharrine. Allah Ya sa mu gane, ameen.

Domin karanta cikakken bayani a kan Dabarun Yaƙi danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Yake Sonsa wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceDabarun Yaƙi.
Labarin na GabaCiwon Hanta (Hepatitis B)
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.