Kar Harshe Ya Gushe Ba Tare Da Ambaton Ubangiji Maɗaukaki Ba.

0
1068

Ambaton Allah

Kada Harshe Ya Gushe Ba Tare Da Ambaton Ubangiji Maɗaukaki Ba,domin ambaton Allah yana da muhimmanci ga duniya da kuma lahirar ɗan-Adam.

An karɓo hadisi daga Abdullahi bn Busrin cewa, wani mutum ya ce “Ya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) sharuɗan Musulunci sun yawaita daga gare ni don haka ka ba ni labarin wani abu da zan yi riƙo da shi”. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ce, “Kar harshenka ya gushe ɗanye daga ambaton Allah (Subahanuhu wata ala)”.
Babbar hanyar ribatar lokutan rayuwa ita ce, lazimtar ambaton Ubangiji.

Ambaton Ubangiji Kuwa ,ya ƙunshi karatun Alkur’ani da hailala da tasbihi da salatin Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) da yawan istigifari a aji ko a ma’aikata ko a kwance ko a tafe.
Na tabbata da ma’aikaci ko ɗan makaranta ko ɗan kasuwar da ma’aikatarsa ko makarantarsa ko kasuwarsa ke nisan mita (meter) dubu (1000) ko mita ɗari biyar (500), zai lazimta wa kansa wani zikiri tun daga fitowar sa daga gida, har ya kai inda za shi, to ba shakka zai iya samun adadi mai yawa na ladan zikiri, wanda mutane da yawa ba za su iya riskarsa a wata guda ba.

Babu shakka, Ubangiji Maɗaukaki na kwaɗaitar da mu yawan ambatonsa a zaune ko a kwance, ta yadda ɗan-Adam zai ci moriyar rayuwarsa. Ubangiji Maɗaukaki ya siffanta masu hankali cikin Alkur’ani da cewa su ne, “Waɗanda ke ambaton Allah (Maɗaukaki) a halin suna tsaye ko suna zaune ko kuma (kwance) bisa kuyabunsu”. Sura-Al’Imra aya ta 191

Ambaton Ubangiji mafi tsari shi ne wadda ake halarto da girmansa tare da jin tsoronsa cikin gaɓɓai da zuciya tamkar ana ganin sa.

Domin karanta cikakken bayani akan Ɗabi’ar lokaci saurin wucewa danna wannan koren rubutun.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Lokaci a Rayuwar Musulmi Tsakanin Riba da Asara. wanda Sunusi Iguda Ƙofar Nasarawa ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceNazarin Wasu Dokokin Tsarin Sautin Harshen Hausa
Labarin na GabaƘiyamul Laili (Tahajjud)