Jan Hankali Da Kuma Shawara Zuwa Ga ‘Yan Uwa Ƙananan Likitoci (Akan Infaction)

0
29
  • Shi fa vaginal infection ya kasu iri da yawa sannan akwai abubuwan da suke kawo shi da yawa misali akwai viral,bacterial,fungus da parasitic don haka wajibi ne kafin ka dora mutum akan magani kasan menene ya kawo infection din kansa  
  • Sannan ya kamata mu sani ba duk infection ne ake bada antibiotics ba,akwai infection din da idan kaba mace antibiotics to ka ƙara haukatashi ne.kuma ba daga ganin alamar cutar sanyi ka dauki antibiotics ka bayar kuskure.
  • Kuskure ne dora mutum akan babban antibiotics wato( broad spectrum antibiotics) akan karamin abin da bai kai ya kawo ba domin yin hakan yana jawowa jikin yayi developing antibiotics resistant ta yadda nan gaba zaiki aiki idan wata cutar ta samu saboda jikin ya saba da shi saboda haka (narrow spectrum ) sune first line ko yaushe na antibiotics 
  • Daga karshe yakamata jami’in lafiya ya san wacce irin tambayoyi ya dace yayi da kuma dalilin yinsu saboda wasu lokutan mace sai kaga ta zo masa da tambaya mai muhimmanci akan matsalar ta amma shi kuma sai yayi wata tambayar da bata ma shafi lafiyar ta ba ya kamata mu kula. 

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

labarin da ya wuceMenene Haila (Jinin Al’ada)
Labarin na GabaKadan Daga Cikin Cuttukan Da Ake Dauka Ta Hanyar Saduwa (Jima’i) (Sexually Transmitted Diseases