Tag: Jan Hankali

  • Jan Hankalin Matasa

    Jan Hankalin Matasa

    A matsayin ka na ɗan talaka idan ka kalli kanka ka san cewa kai ba kowa ba ne, iyayen ka ba masu kuɗi ko mulki ba ne, wajibi ne ka mayar da hankali akan karatun Al-Qur’ani, karatun Boko, Sana’a da kuma bautawa Allah don ka samu nasara ka zama abin nunawa a cikin iyali da ‘yan uwan ku.

    Ka tsaya ka kalli rayuwar yau, wataƙil kana da ƙanne da yawa, ana haifa maka su a yanzu, saboda wataƙil nan gaba mahaifin ku zai kwanta ya rasu, kai ne za ka ɗauki nauyin su, idan a yau ba ka yi karatu ba to idan lokacin ya zo ba za ka iya ɗaukan nauyin su ba.

    Idan a yau ba ka goge da karatun Al-Qur’ani ba nan gaba rayuwar za ta iya zuwa maka ba yadda kake so ba. Sannan dole ka tashi ka ka nemi kuɗi ta inda duk ya halatta gare ka, kuɗi ba sa yin yawa ga duk wanda yake da tun

    Wallahi yawan bacci da kasala da son kwalliya ko burge wa ba naka ba ne a yanzu, ka yi haƙuri zuwa lokacin da Allah zai sa ka tsallake ƙalubalen da suke gaban ka a yanzu.

    Sai dai kada ka sa a rai wani zai taimake ka bayan Ubangijin ka da iyayen ka, za ka ji zafi a zuciyar ka babu wanda yake taimakon ka kana makaranta, da ƙyar kake rayuwar za ka ga babu wanda zai kira yace turo account number ko ya ji yaya kake ciki don ya taimake ka, ka yi haƙuri haka ake girma, haka rayuwar ƙasar mu da al-ummar take.

    Kada ka yi sake carry over a makaranta ya hana ka cimma burin ka akan karatun, carry over kamar uniform ɗin ɗalibai ne ‘yan kaɗan ne ba su sanya shi a jikin su, kusan kowa sai ya saka kafin a gama karatun, wannan normal ne.

    Ka sadaukar da wasu shekaru domin gina kanka da ‘yan uwan ka da addinin ka, wata rana za ka zama abun nunawa in sha Allah. Sai dai in ba ka yi haƙuri ba dole za ka zo ka yi da-na-sani akan sakaci, son jiki, burgewa da son kwalliya ko hutawa a lokacin da bai kamata ka huta ba.

    Allah yasa mu dace…. Danna shuɗin rubutun nan don  karanta yadda aka samar da tsangayun gwaji na gwamnati

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Jan Hankali Da Kuma Shawara Zuwa Ga ‘Yan Uwa Ƙananan Likitoci (Akan Infaction)

    Jan Hankali Da Kuma Shawara Zuwa Ga ‘Yan Uwa Ƙananan Likitoci (Akan Infaction)

    • Shi fa vaginal infection ya kasu iri da yawa sannan akwai abubuwan da suke kawo shi da yawa misali akwai viral,bacterial,fungus da parasitic don haka wajibi ne kafin ka dora mutum akan magani kasan menene ya kawo infection din kansa  
    • Sannan ya kamata mu sani ba duk infection ne ake bada antibiotics ba,akwai infection din da idan kaba mace antibiotics to ka ƙara haukatashi ne.kuma ba daga ganin alamar cutar sanyi ka dauki antibiotics ka bayar kuskure.
    • Kuskure ne dora mutum akan babban antibiotics wato( broad spectrum antibiotics) akan karamin abin da bai kai ya kawo ba domin yin hakan yana jawowa jikin yayi developing antibiotics resistant ta yadda nan gaba zaiki aiki idan wata cutar ta samu saboda jikin ya saba da shi saboda haka (narrow spectrum ) sune first line ko yaushe na antibiotics 
    • Daga karshe yakamata jami’in lafiya ya san wacce irin tambayoyi ya dace yayi da kuma dalilin yinsu saboda wasu lokutan mace sai kaga ta zo masa da tambaya mai muhimmanci akan matsalar ta amma shi kuma sai yayi wata tambayar da bata ma shafi lafiyar ta ba ya kamata mu kula. 

    Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya