Jan Hankalin Matasa

0
38

A matsayin ka na ɗan talaka idan ka kalli kanka ka san cewa kai ba kowa ba ne, iyayen ka ba masu kuɗi ko mulki ba ne, wajibi ne ka mayar da hankali akan karatun Al-Qur’ani, karatun Boko, Sana’a da kuma bautawa Allah don ka samu nasara ka zama abin nunawa a cikin iyali da ‘yan uwan ku.

Ka tsaya ka kalli rayuwar yau, wataƙil kana da ƙanne da yawa, ana haifa maka su a yanzu, saboda wataƙil nan gaba mahaifin ku zai kwanta ya rasu, kai ne za ka ɗauki nauyin su, idan a yau ba ka yi karatu ba to idan lokacin ya zo ba za ka iya ɗaukan nauyin su ba.

Idan a yau ba ka goge da karatun Al-Qur’ani ba nan gaba rayuwar za ta iya zuwa maka ba yadda kake so ba. Sannan dole ka tashi ka ka nemi kuɗi ta inda duk ya halatta gare ka, kuɗi ba sa yin yawa ga duk wanda yake da tun

Wallahi yawan bacci da kasala da son kwalliya ko burge wa ba naka ba ne a yanzu, ka yi haƙuri zuwa lokacin da Allah zai sa ka tsallake ƙalubalen da suke gaban ka a yanzu.

Sai dai kada ka sa a rai wani zai taimake ka bayan Ubangijin ka da iyayen ka, za ka ji zafi a zuciyar ka babu wanda yake taimakon ka kana makaranta, da ƙyar kake rayuwar za ka ga babu wanda zai kira yace turo account number ko ya ji yaya kake ciki don ya taimake ka, ka yi haƙuri haka ake girma, haka rayuwar ƙasar mu da al-ummar take.

Kada ka yi sake carry over a makaranta ya hana ka cimma burin ka akan karatun, carry over kamar uniform ɗin ɗalibai ne ‘yan kaɗan ne ba su sanya shi a jikin su, kusan kowa sai ya saka kafin a gama karatun, wannan normal ne.

Ka sadaukar da wasu shekaru domin gina kanka da ‘yan uwan ka da addinin ka, wata rana za ka zama abun nunawa in sha Allah. Sai dai in ba ka yi haƙuri ba dole za ka zo ka yi da-na-sani akan sakaci, son jiki, burgewa da son kwalliya ko hutawa a lokacin da bai kamata ka huta ba.

Allah yasa mu dace…. Danna shuɗin rubutun nan don  karanta yadda aka samar da tsangayun gwaji na gwamnati

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceWaƙar yaƙin Korona
Labarin na GabaKo Ka San Cewa Idanun Sauro Sun Fi 100?