Gida Hukunci Hukuncin Rai Da Rai Shi Zai Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe

Hukuncin Rai Da Rai Shi Zai Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe

0
1

RAI DA RAI… SHI ZAI KAWO KARSHEN KASHE KASHE 

Whatsapp: 08039290267 

20th June, 2026 

“A cikin qisasi(kashe wanda ya yi kisa da gangan) akwai rayuwa” Qur`ani 2:179

SHIMFIƊA: 

Wannan hukunci na kashe duk wanda ya yi kisan kai, ba hukunci ne da addinin musulunci ya kaɗaita da shi ba, hukunci ne wanda duk sauran addininai da Allah SWT ya saukar daga sama suka yi umarni da shi. A aya ta arba’in da biyar cikin Suratul Ma’idah Allah SWT ya yi nuni da cewa, an wajabta a kan banu Isra`ila hukuncin kashe duk wanda ya yi kisan kai wato ƙisasi.

Banu Isra`ila ba su ɗau wannan hukuncin da muhimmanci ba, shi yasa kashe kashe ya yawaita a cikin su. kuma wannan shi ne dalilin da ya sa a wannan zamani ma kashe kashe ya yawaita a cikin wannan al’uma saboda rashin tsayar da wannan hukuncin.

MAUDU’I: KASHE KASHE A CIKIN MU 

A watan Nuwamban 2017 ne wata matashiya mai suna Maryam Sanda ta kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello a Abuja sakamkon wani rashin fahimta da ya shiga tsakaninsu. Shafukan jaridu, gidajen rediyo da dandalin sada zumunta duk sun karaɗe da wannan labarin. Wannan lamari ya tayar da hankalin mutane sosai, saboda abu ne da ba a saba ji ko gani ba, dan haka ya ɗau hankula sosai.

An kai ruwa rana sosai da taƙaddama a gaban kotu, bayan shekaru uku Alƙali Yusuf Halilu na kotun tarayya da ke Abuja ya yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya. A 2025 shugaban ƙasa Ahmed Tinubu ya yafe wa Maryam Sanda wannan hukuncin na kisa zuwa shekaru 12 a kurkuku.

Nan da nan kotun ƙoli ta ƙasa ta tabbatar da cewa fa wannan hukunci yana nan daram. Shugaban ƙasa da gwamnoni su ne suke da ikon bada umarnin aiwatar da hukuncin kisa. Kotu sai dai ta yanke hukuncin abinda za a yi kawai.

A shekarar 2021 ne aka wayi gari a unguwar Tudun Murtala a birnin Kano da wani labari mai tada hankali na wani mutum mai suna Abdulmalik Tanko wanda ya sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa kuma ya kashe ta. Babban abin tada hankalin shi ne, Abdulmalik malamin wannan yarinyar ne Hanifa, Abdulmalik ya sace Hanifa ne ranar 2 ga watan Desamba, 2021.

Bayan kwana biyu, ya tuntuɓi iyayenta da su bada Naira Miliyan Shida (N6,000,000). A ranar 18 ga watan Disamba, ya fahimci Hanifa ta gane shi saboda haka, idan an biya kudin ya sake ta, za ta faɗi wanda ya sace ta, don haka ya kashe ta, ya kuma binne ta a wani kango kusa da makaaranatar su.

Wannan labari ya tayar da hanlin mutane da dama, saboda cin amanar da wannan “malamin” ya yi ta hanyar amfani da damar da yake da ita a mtsayinsa na mai karantar da ita, sannan kuma rashin imani da ya nuna ta hanyar kashe Hanifa ‘yar shekara biyar ba tare da wani dalili ba.

An yi ta kiraye kiraye daban daban na a ɗau hukunci mai tsanini a kan Abdullmalik  da gaggawa, duk da shigar ƙungiyoyin kare haƙƙin yara amma dai ranar 24 ga watan Janairun 2022 ne wata babbar kotu a Kano ta yanke wa Abdulmalik da wani mai suna Hashimu hukuncin kisa. Amma har yau bayan shekaru huɗu Abdulmalik yana nan a raye a gidan gayaran hali ba a aiwatar da hukuncin ba.

Bayan kwana shida da aurensu kawai sai aka tashi da cewa Saudat Jibril ‘yar shekara 18 ta kashe mijinta mai suna Salisu Idris ranar 6 ga watan 5 2025. Wannan abu ya faru ne a unguwar Farawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. Ana raɗe-raɗin cewa auren dole aka yi mata da wannan miji na ta.

Bayan jami’an tsaro sun tafi da ita don bincike da neman sauran bayanai, daga nan dai labari ya ƙare. Kamar duk sauran kashe kashe da suke aukuwa, wannan yarinya za a yi ta zuwa kotu, karshe idan hujjoji sun tabbata, za a yanke mata hukuncin kisa, amma aiwatarwa ne ba lallai ba.

Da misalin 12 na ranar 17 ga watan janairun 2026 ne labari ya yaɗu cewa wasu sun shiga gidan wani mai suna Haruna a unguwar Chiranci da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano sun kashe wata matar aure mai suna Fatima Abubakar tare da ‘ya’yanta huɗu. Wannan labari ya karaɗe shafukan sada zumunta, gidajen radiyo da gidajen jaridu da majalisan hira da tattaunawa ba Kano kaɗai ba har wajen Najeriya.

Cikin gaggawa komishinan rudunar ‘yan sandan jihar Kano ya bada umarnin bincike da nemo waɗanda ake zargi da aikata wannan mummunar aika aikar. Nan da nan aka cika hanu da waɗanda ake zargi da wannan ɗanyan aikin. Sarkin Kano, Gwamnan Kano da sauran jama’a su jajanta wa Haruna wanda aka kashe masa mata da ‘ya’ya har kyututtuka don rarrashin sa da tausasa zuciyar sa Sarkin Kano da Gwamnan Kano suka yi masa.

Bayan cafke waɗanda ake zargi, an yi ta kiraye kirayen da a gaggauta yanke musu hukunci gani yadda abin ya ɗau hankali. Wannan kiraye kiraye kamar ya sami karɓuwa. A jawabin da ya fitar mai magana da yawun Gwamnan jihar Kano ya tabbatar da cewa za tabbatar waɗanda ake zargi an kai su gaban kuliya kuma an hukunta su.

Bayan wata shida da faruwan wannan abin, shiru kake ji daga lokacin da aka yi wannan rubutun, ko dai an yanke musu hukunci ko dai ana kan shari`a, amma dai gidan jiya za a koma, ko an yi hukunci, aiwatarwa shi ne jidali.

A unguwar Rimin Keɓe ƙaramar hukumar Nassarwa a jihar Kano wata mata mai suna Fatima ta kashe mijinta mai suna Auwalu a ranar 13 ga watan 6 na 2026.

RUFEWA DA SHAWARWARI: 

Kashe kashe sun yawaita a cikin al`umar mu musamman a wannan lokacin, waɗanda suka haɗa da kashe kashen faɗan daba, na ƙwacen waya, na masu satar mutane da sauransu, amma irin waɗannan da aka faɗa a sama ya fi tayar da hankula sosai saboda yanayinsu na cewa kashe kashe ne da ke faruwa a tsakanin iyali da makusantar juna.

Rashin ɗaukar mataki mai tsanani, da rashin aiwatar da hukuncin da kotu ta yanke shi ne maƙasudin ƙaruwar waɗannan aika aika. Allah SWT da ya halicci ɗan Adam, ya fi ɗan Adam son kansa, shi yasa ma ya hana kar mutum ya kashe kansa. Kuma ya sanya tsananin uquba ga duk mutumin da ya kashe kansa da kansa. Ƙari a kan wannan shi ne, Allah saboda ya san  ɗan Adam, toh sai ya sanya duk wanda ya kashe wani ba tare da wani dalili na shari`a ba, to a kashe shi.

Wannna hukunci ba tsanani ya yi ba, Allah ya yi haka ne don rayuwa ta inganta, ta zamo mai tsada, mai daraja, mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk wanda ya ga an kashe wani akan ya yi kisa, to zai shiga taitayinsa kuma ya razana tunda yana son rayuwa, sai ya haƙura da kisan da ya ke son yi.  Rashin yin wannan hukuncin ya kan sa rayuwa ta zama mai arha, rai ya zama ba a bakin komai yake ba, rai ya zama ba shi da wani kwarjini da daraja.

Wani lokaci kuma, rashin gaggauta yanke hukunci yakan sa zafin kisan da aka yi ya salance, mutane su manta kamar yadda aka manta kisan da ka yi wa Hanifa ‘yar shekara 5 da haihuwa. Wannan yana faruwa ne saboda dogon lokacin da ake ɗauka ana shari`a. Wasu shari`o`in suna kaiwa har kotun ƙoli kafin a yanke hukunci, wannan yana ɗaukan shekaru masu yawa. Sai dai  mai laifi ya yi ta zama a gidan gyaran hali har ta Allah ta yi, ko kuma a ma sake shi ta hanyar yafiya daga hukumomi, kamar yadda aka fara shirin yi wa Maryam Sanda.

Aiwatar da hukuncin kisa, musamman a dokar ƙasa, Shugaban ƙasa da Gwamna ne kawai ke da ikon aiwatar da wannan hukunci. Su kuma saboda tasirin siyasar duniya da tasirin ƙungiyioyin rajin kare hakkin ɗan Adam sai su zama suna tsaka mai wuya, ba sa iya zartar da wannan hukunci. Sai dai mai laifi ya yi ta zama a gidan gyaran hali ko kuma ce an mai da hukuncin zuwa ɗaurin rai da rai ko zuwa wasu shekaru.

Duk ƙasar da ake hukuncin kisa kan wani laifi, tabbas za ka ga wannan laifin ya yi ƙaranci sosai, saboda kowa yana son ransa ba zai yadda ya auka inda za a raba shi da duniya ba. Misali za ka daɗe ba ka ji an ce an yi kisan kai a ƙasar Saudiya ba, ko ƙasar Iran. Haka zaka daɗe baka ji an ce wani jami`in gwamnati ya wawure wasu maƙudan kuɗaɗe daga lalitar gwamnati ba a ƙasar Sin.

Saboda haka, lallai idan shugabanni suna son kawo ƙarshen kashe kashe da ba kangado, to, sai sun rufe ido sun ciza, an fara kashe waɗanda suka yi kisa na ganganci bayan an tabbatar kuma kotu ta yanke hukuncin kisa nan da nan. Yin wannan shi ne zai sa razani da firgici a zuciyar duk wani mai niyyar kashe wani ba da wani dalili ba ko akan wani abu da bai taka kara ya karya ba. Sannan kuma zai tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa da rayuwa mai cike da aminci, da kwanciyar hankali, ruyuka jama`a su zama masu daraja da ƙima.

Allah ya datar damu, Amin.

Danna nan don karanta Yadda Kunya Take

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru
Labarin na GabaTatsuniyar Sarki Mai Mata Ɗaya Da ’Ya Ɗaya
Rabiu Musa Adam
Sunana Rabiu Musa Adam, ni malami ne a sashen koyar da manya na cibiyar Al-Furqan, Kano.