Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take

    Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) yace: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Ku taru zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, sai waɗanda suka haɗu suka haɗu, Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fito sai ya karanta “Ƙulhuwallahu Ahad”.

    Sannan ya shiga gida, sai muka ce da junanmu mu zaton wahayi ne ya zo masa daga sama, shi ya sa ya shiga gida, sai ya fito ya ce haƙiƙa na ce da ku zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, ku faɗaka haƙika ita (ƙulhuwallahu tana daidai da ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani”. (Muslim 812)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Suratul Falaƙi Da Nasi Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Matakan da Iyaye Za Su Bi Don Kare Tarbiyyar ‘Ya’yansu A Intanet

    Matakan da Iyaye Za Su Bi Don Kare Tarbiyyar ‘Ya’yansu A Intanet

    Shin ka taɓa tsayawa ka lura ko ka tambayi kanka: “Me yasa yarona ba ya fita daga waya ko kwamfuta? Ko Kuma me yake yi da ita wanda ya kamata na sani?”

    A yau, duniya ta canza sosai. Wayoyin hannu, kwamfutoci da Intanet sun zama tamkar abinci da ruwa a rayuwarmu. Muna amfani da su wajen neman ilimi, kasuwanci, nishaɗi, da kuma sadarwa. Amma akwai wani ɓangare da yawancin iyaye ba sa kula da shi sosai :tasirin Intanet a rayuwar yara da tarbiyyarsu.

    Yaro na iya koyon alheri daga Intanet, amma kuma zai iya faɗawa cikin sharri idan ba a ja hankalinsa ko an sa ido ba. Akwai bidiyo marasa kyau, shafukan da ba su dace ba, sada zumunta da ba a san waye a can ba, da kuma labaran ƙarya da ke iya lalata tunaninsu.

    Abin da ya fi sa damuwa shi ne: yara suna da saurin koyo da kwaikwayo fiye da yadda iyaye ke zato. Wannan yasa wajibi iyaye su ɗauki matakai na kare tarbiyyar ‘ya’yansu online. Ga wasu matakai guda 5 masu sauƙi amma muhimmanci da kowanne uba ko uwa zai iya bi:

    1. Kasance Abokin Hira ga Yaronka – Ka Jawo hankalinsa da tausayi da shaƙuwa: Idan ba ka buɗe ƙofa ta tattaunawa da yaranka ba, to za su nemo bayanai daga waje. Kuma ka sani, Intanet tana da miliyoyin “malamai” waɗanda da dama daga cikinsu marasa gaskiya ne.

    Ka saba hira da yaranka game da abin da suke kallo, wasannin da suke yi, ko abokanen da suke chatting da su. Kada ka fara da tsawa ko zargi, sai su fara ɓoye maka gaskiya. Ka tambaye su cikin sauƙin hali:

    “Wani abu ne ya fi burgeka a wannan wasan?”

    “Wane aboki ne ka fi jin daɗin hira da shi?”

    Da haka za ka gina aminci, shaƙuwa da gaskiya da yaronka. Yaro idan ya yarda da kai, zai faɗa maka duk wani abu da ya gani a Intanet wanda ya dame shi.

    2. Sanya Dokoki da Iyakoki – Ka Nuna Kai ne Jagora. Yara suna buƙatar kulawa da Shata musu iyaka. Idan ka bar su da ‘yanci marar tsari, za su iya faɗawa cikin hatsari.

    • Kafa lokaci: Ka ƙayyade lokacin da yaro zai yi amfani da waya/Intanet. Misali: awa 1-2 a rana bayan makaranta.
    • Haramta wurare: Kar a yarda da waya ko kwamfuta a ɗakin bacci. Sai dai a ɗakin iyaye ko parlour inda ake gani.
    • Ƙa’ida: Idan an karya doka, sai a ɗauki matakin ladabtarwa mai ma’ana (kamar rage lokacin waya ko ɗauke ta na wasu kwanaki).

    Wannan yana koya musu yanda za su yi amfani da fasaha ta hanyar da ya dace.

    3. Yi Amfani da Parental Controls – Fasaha ta Kariya: Yawancin wayoyi, kwamfutoci da apps suna da Parental Control Settings. Wannan yana ba ka damar:

    Taƙaita shafukan da yaro zai iya ziyarta.

    Sa ido kan abinda yake yi online.

    Kariya daga shafukan batsa, tashin hankali da labaran ƙarya.

    Idan kai ba ka da ilimi sosai a kan wannan, ka tambayi wanda ya ke da sani a kai. Ko ka kalli bidiyon koyarwa a YouTube. Ka tuna, kariya ba ta nufin hana ilimi, sai dai nufin tsare tarbiyya.

    4. Ka Ilimantar da yaronka kan yanda zai amfani da intanet ta hanyar da ya dace.

    Idan muka koya wa yara karatu da rubutu, me yasa ba za mu koya musu yadda ake amfani da Intanet lafiya ba musanman a wannan zamani da muke ciki?

    Ka koyar da su cewa:

    • Ba a amincewa da duk wani abu da ake gani a Intanet. Akwai labaran ƙarya da yawa.
    • Kada su taɓa bayar da sirrinsu (password, adireshi, lambar waya) ga wanda ba su sani ba.
    • Kada su taɓa amincewa su haɗu da mutum daga online ba tare da sanin iyaye ba.
    • Su riƙa tambayar ka kafin su sauke app ko shiga wani sabon shafi.

    Wannan shi ake kira Digital Literacy da Safety – kuma yana daga cikin manyan ilimin da yara har ma da manya ke buƙata a wannan zamani.

    5. Ka Taimaka Wajen Nemo Abubuwan Alheri da za su amfane su – Ka Nuna Musu Hanyoyin Ilimi. Maimakon kawai a hana yara shiga Intanet, ka nuna musu madadin haka mai alheri:

    • Ka sa su dinga duba darussa a YouTube na ilimi (misali: lissafi, kimiyya, addini).
    • Ka koya musu amfani da apps masu amfani na koyar ilimin addini da na zamani.
    • Ka nuna musu shafukan labarai masu inganci na Hausa/English.
    • Ka tallafa musu wajen amfani da Intanet don yin binciken makaranta.

    Da haka za ka canza Intanet daga hatsari ko gurbacewar yaro zuwa makaranta.

    A ƙarshe, Iyaye sai Kun Tashi Tsaye. Intanet ba za ta tsaya ba, kuma yara ba za su daina sha’awarta ba. Amma iyaye na da iko sosai wajen shiryawa da kare tarbiyyar ‘ya’yansu.

    Ka tuna da Hadisin Manzon Allah (SAW):

    “Dukanku makiyaya ne, kuma kowane makiyayi za a tambaye shi kan abin da ya kiyayye.”

    Iyaye, ku kasance makiyaya na gaskiya – ku kula da amana.

    Kada mu bari Intanet ta yi mana hijira daga tarbiyyar Musulunci da al’adun Hausa. Mu amfani da ita a matsayin makamin cigaba, ba makamin lalacewa ba. Tambaya ta iyaye ce:

    Me kuka lura da shi game da yaranku da Intanet? Kuna ganin matsalar da ta fi yawa ko kuwa tana da alkhair mai yawa, ko kuma lokaci kawai ake ɓatawa?

    Ku rubuta a comments domin mu tattauna tare.

    Danna nan don karanta Tarbiyyar Yara

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Maguzawa Suke A Taƙaice

    Yadda Maguzawa Suke A Taƙaice

    SHIMFIƊA
    Hoton rayuwar wata al’umma takan fito cikin ayyukan adabi wanda adabin Hausa bai keɓanta ba. Hakan na faruwa ne idan marubuci ya taɓa jin labari, ko gani, ko karanta wani aiki da ya shafi wannan al’umma. Wani lokaci kuma zamantakewa ke kawo nason rayuwar wasu al’ummomi na kusa ko na nesa cikin aikin adabi.

    Idan kuwa ba haka ba, hoton rayuwar da aka gani wadda marubuci ke bayani; yana yiwuwa jinin marubuci ne da ke da asali tun daga iyaye da kakanni. Kenan asalin marubuci yana iya tasiri cikin rubutu har a ga hoton rayuwar magabata ta kusa ko nesa na mai rubutu, ya sani ko bai sani ba.

    MAGUZAWA

    Maguzawa Hausawa ne na asali da ke zaune a ƙasar Hausa tun da daɗewa. Tarihin Hausa da Hausawa ba zai kammalu ba sai an ambaci Maguzawa domin ba su da wani harshe sai Hausa.

    HALAYYA DA ƊABI’UN MAGUZAWA

    Wayo: Wayo yana ɗaya daga cikin ɗabi’ar Maguzawa (Abdullahi, 2008:4). Ana iya gane wayon Bamaguje idan aka yi mu’amala da shi, ko aka ji labarin wani abu da ya faru tsakaninsa da wani. A labarin Ɗan hakin da ka raina na cikin littafin Magana Jari Ce na uku, an nuna cewa Maguzawa mutane ne masu wayo. Ga dai abin da Anunu Mahauci da abokansa suke cewa:

    Suka hanga, guda ya ce , Bahaushe ina? Kuna ganin Bamaguje, ku dubi irin kayan gogan mana, iya magana yanzu nan ko ɗan Kano. Daga nan sai guda wanda ake kira Anunu ya ce : “Haba wane wayo ke ga Arne, daga dai an ƙyale su”. Guda ya ce: A! don wayo dai suna da shi. A nan Anunu da abokansa sun tabbatar da cewa duk wani Bamaguje yana da wayo. To amma dai haɗuwarsu a wannan wuri an yi wa Bamaguje hikima an cuce shi.

    Shi kuwa marubucin littafin Malam Inkuntum, ya nuna wayon Maguzawa ne a wurin da ya ambaci wani Arne da ke neman bawan Allah wanda zai ba ɗiyarsa a matsayin miji. Arnen ya gwada wayonsa ga wasu musulmi da cewa:

    Arne:Kai! Bawan Allah ne kai in kashe ka maimakon nawa da ya kashe jiya.
    Ladan : Lallai ni kam bawan Allah ne. In ka kashe ni ka kashe bawan Allah.
    Arne: Kashe ka fa zan yi yanzu, ko ƙyaftawa babu.
    Ladan: Ai ta samu gare ka. Allah ya ba mu cikawa da imani, mu tashi da imani, amin.
    Arne: (ya mai da gatarinsa a kafaɗa, ya kama hannun Ladan ) Zo mu je gidana , kuma kwantad da zuciyarka, ba kashe ka zan yi ba.

    Wannan misali ya nuna wayon da Arne ya yi amfani da shi domin ya tantance wanda zai ba ɗiyarsa aure. A ɓangaren su Anunu da Bamaguje kuwa, cutar da Anunu ya yi wa Bamaguje ya rama ta hanyar ɓad da kama kamar haka:

    To Bamagujen nan ya yi kamar ya ƙyale, sai da ya bari an yi kamar kwana ashirin har an bar wannan Magana, sai ran nan ya sami kayayyaki farare irin na Hausawa ya sa, ya nemi rawani ya bayar aka naɗa masa. Bamaguje ya nufi wajen Anunu ya tarad da shi da kan akuya yana sayarwa. Da zuwansa sai ya dafa kan Anunu, ya dubi kan akuya ya ce: “wannnan kan nawa ne?” Anunu ya ciro ido ya dube shi ya ce: “ Mene ne kuma na dafa mini kai? Ku dai Malamai kun raina mu..To ga shi nan faɗi abin da za ka biya.

    Nan ma wayo Bamaguje ya yi wa Anunu domin ya dafa kansa a matsayin kan akuyar da ake ciniki. A ƙarshen wannan ciniki dai sai da aka dangana da gaban alƙali. Ko da alƙali ya ji duk yadda aka yi tun lokacin da Anunu ya sayi San Bamaguje har ya zuwa cinikin kan akuya, ya san cewa, Bamaguje ya rama abin da aka yi masa ne. Ga shi kuma Bamaguje ke da gaskiya, don haka a ƙarshe dai Anunu ya yi hasara fiye da wadda Bamaguje ya yi lokacin da aka sayi Sansa.

    MUHALLIN MAGUZAWA

    A duk inda Maguzawa suke, sun fi son su zauna cikin daji, wato nesa da gari ba tare da mutane sun tsangwame su ba. Wannan ya sa suka ba noma muhimmanci a rayuwarsu fiye da duk wata sana’a. Cikin littafin ƙarshen Alewa Ƙasa marubucin ya yi bayanin muhallin Maguzawan Tsaunin Gwano da cewar:

    Wannan gari na Tsaunin Gwano yana da gidaje kamar guda ɗari biyu. A gefen garin akwai wani dogon tsauni wanda ta wajen ne garin ya sami suna. A da can ‘yan shekaru kaɗan da suka wuce dukkansu suna zaune a kan tsaunin nan ne. Wannan kuwa ya faru ne saboda tsoron masu harin bayi suna sayarwa. Nan ma nuni ne da muhallin Maguzawa tun lokacin da suke a saman duwatsu, har ya zuwa saukowarsu daga duwatsu, kuma a cikin daji.

    SANA’O’IN MAGUZAWA

    -Noma
    -Ƙira
    -Farauta

    NOMA

    Sana’ar da ta fi kowace muhimmanci wajen Maguzawa ita ce noma. Ita suka gada kaka da kakanni, da ita suke alfahari fiye da komi a duniya, (Abdullahi 2008). Ya ƙara da nuna baya ga noma Maguzawa suna da wasu sana’o’i irin su: ƙira, da farauta, da kiwo. Hoton sana’o’in waɗannan mutane sun fito cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa inda marubucin yake bayanin yekuwar farautar shekara da za a yi kamar haka :

    “Hyai, hyai! Ina mazajen Tsaunin Gwano, Sarkin Ƙira ya gaishe ku. Bayan gaisuwa ya ce a faɗa maku lokaci ya yi wanda duk mai ji da kanshi ya shirya….” Wani Saurayi wanda ake kira Mailoma yana zaune a kan wani buzu da aka yi da fatar biri ya miƙo hannu suka tafa. Sai ya yi wuf ya miƙe gaban hantsi yana gyaran lagen gwadonsa.

    Ya ce bara kuwa an yi farauta da sa’a. Ka tuna lokacin da muka darkaki ƙatuwar Barewar nan? Shi wannan ɗan tsoho sunansa Ci-wake. Duk garin Tsaunin Gwano da kewaye an san shi da yin jima. Wannan sana’a da yake yi ta sa a kullum ba ya rasa abin yin kayan miya.

    Waɗannan misalai sun kawo hoton sana’o’in Maguzawa da suka ƙunshi farauta, da jima. To amma ba waɗannan sana’o’in ba ne muhimman sana’arsu ba kamar yadda ya zo cikin littafin , noma shi ne babbar sana’arsu.

    Shi kuwa labarin Ɗan Hakin da ka Raina na cikin Magana Jari Ce ya nuna cewa noma da kiwo suna daga cikin sana’o’in Maguzawa. Farkon labarin ya fara ne da bayanin sana’ar Maguzawa kamar haka: Wata rana wani Bamaguje ya lafta wa takarkarinsa hatsi, ya kora zai kai kasuwa. Kasuwar da za shi kuwa ana ɗam mudu ƙwarai, don kullum in ya kai kayan takarkarin nan, daga ya sayar sule talatin sai ya sayar talatin da biyar.

    Haka ma a cikin littafin Malam Inkuntum, lokacin da Arne ya je neman bawan Allah, ya nuna cewa shi manomi ne inda ya ce:
    Arne:Kai tsaya tambayarka zan yi. Akwai mutane cikin akurkin nan naku?
    Malam Almu: Ai tukuna. Yanzu dai muke harama. Anjima kaɗan za a taru. Sallar za ka yi yau?
    Arne: Tir! Me ya kai ni wannan abin duƙe-duƙe ba wurin noma ba.
    Wannan Arne ya nuna babu wani abu da zai sa ya dinga wasu duƙe-duƙe in dai ba wurin noma ba. A ganinsa wurin noma ake yin duƙe-duƙe a nasa tunanin.

    SUNAYEN MAGUZAWA

    Suna shi ne kalmar da ake amfani da ita wajen kira ko ambato ko wani abu, (Ƙamusun Hausa 2006:401). Akwai abubuwa da dama da kan ba da haske wajen sa wa yaro ko yarinyar da aka haifa suna.

    Cikin irin waɗannan abubuwa akwai: yanayi, da halin haihuwa, da yanayin haihuwa, da siffar mutum , (Yahaya 1979:5-8). A wasu lokuta kuma, akan sa sunan wata dabbar daji ko ta ruwa a matsayin suna ga Maguzawa. Wasu daga cikin sunayen gargajiya da aka yi amfani da su cikin waɗannan littattafai guda uku su ne :

    Arne: Wanda ke yin tsafi, kuma ana kiran Maguzawa da wannan suna.
    Bamaguje: Suna ne na namiji tilo mai bin addinin gargajiya na Hausa.
    Dubu: Wadda aka haifa lokacin da ake yin bikin dubu da tambarci.
    Hantsi: Yaron da aka haifa lokacin da rana ta fito kafin ta kai tsakiya
    Juda: Suna ne na wata dabbar daji mai kama da Mage. Ana samun turare daga wasu sassa na wannan dabba.

    Maguzawa: Jam’i ne na kalmar Bamaguje
    Malka: Ita ce Yarinyar da aka haifa lokacin da ruwan damina ya kai tsakiya.
    Sarkin Arna: Shugaban Maguzawa kuma mai jagorancin bautar gargajiya.
    Sarkin Dodanni: Abin bautar gargajiya ne.
    Sarkin Noma: Mai yin jagoranci wajen harkokin noma.
    Sarkin Tsafi: Mai yin jagoranci wajen tsafi.
    Tayani: Sunan abin zama ne wanda aka saƙa da kaba tare da fatu, mata suke kaɗi kansa.
    Tamu: Suna ne da ake sa wa yaron da aka haifa shekarar da gyaɗa ba ta yi kyau ba.

    MAGUZANCI

    Maguzanci a Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa:
    Imani da tunanin Maguzawa na gargajiya shi ke jagoranci wajen tafiyar da harkokin rauwarsu. Wannan shi ne abin da ya bambanta Maguzawa da sauran ‘yan’uwansu Hausawa. Wannan fasali ya dubi wasu ɓangarori cikin imani da tunanin Maguzawa a gargajiyance da suka haɗa da bautar gargajiya, da cin mushe da sharholiya, da zagi da batsa da dai sauransu.

    Bautar Gargajiya:

    Bauta da abin bauta a wajen Maguzawa suna da muhimmancin gaske, don haka suke kiyayewa da mutunta duk wani abu da ya shafe su. A tsarin bautar Maguzawa, akwai abin da ake yi wa bauta, da wurin bauta, da hidima ga abin bauta, da kiyaye dokokin abin bauta, da kuma sakamakon da ake samu ida an saɓa ma abin bauta.

    Abin Bauta:

    Addinin Maguzawa addini ne na gargajiya ne da suka gada wajen iyaye da kakanni. Hanyoyin bautar Maguzawa su ne tsafi, da bori, da mu’amala da dodo. Abubuwan da suke bauta ma kuwa su ne Aljanu, da Dodanni, da wata dabba da sukan keɓe, ko wani itace. Aljanu su ne abubuwan da suka fito a matsayin abin bauta cikin wannan aiki.

    Misali, a rigimar Bamaguje da Anunu Bamagujen na cewa:
    Da ni dai na fi son kan da kome , don in kai wa gunkinmu ya sha jini.
    Bayanin wannan Bamaguje ya nuna cewar gunki yake bauta ma, amma ba gunkin ba ne aljani yake nufi domin gunki ba ya shan jini. Shi kuwa littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa Aljani ne aka ambata a matsayin abin da suke yi wa bauta.

    Kodayake an ce yakan fito cikin siffar maciji ko wani abin daban, amma dai Aljani ne. An bayyana shi da cewa:
    Wannan surin yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce …… Sarkin Arna da jama’arsa Talakawa sun yarda cewa wai a cikin wannan surin akwai wani tsohon Aljani. Shi wannan Aljani an san shi a cikin siffar maciji, ko da yake an ce kuma ba abin da ba ya rikiɗa.
    Shi ma wannan ya nuna babu tsayayyar sifar da abin bautar yake da ita, sai dai a iya cewa ya fi bayyana cikin sifar maciji.

    Ana iya samun jinsin mata cikin aljanun da ake yi wa bauta kamar yadda Arnen cikin littafin Malam Inkuntum ya ce:
    Ladan: Na ji na yarda, amma ina so a ɗaura aure.
    Arne: Ku yi can ruwa ga wuya, in ji mata. Ai ni tun da Uwar Dawa (aljana) ta yi mini izini, iyakar nawa ke nan. (arne ya koma gida).

    Wurin Bauta:

    Maguzawa ba kamar sauran mutane ba, sukan keɓe wani wuri na musamman domin yin bauta. Duk wurin da suka keɓe suna yin bauta nan ne mazaunin da abin bautar tasu yake. Suna kula da wurin fiye da makwancinsu ta fuskar tsaftacewa, da ba wurin kariyar da ta dace musamman ga wanda bai san darajar wurin ba. Irin wannan wuri na iya kasancewa ɗaki a cikin gida, ko bishiya a ƙofar gida ko bayan gari.

    Misali cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa an ambaci wurin bauta da cewa:
    Ita fadar Sarkin Dodanni wani irin wuri ne inda yake da wani irin babban shuri wanda girmansa ya kai tsawon mutum uku dogaye. Wannan shurin yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce, kuma a kowace rana Sarkin Arna yakan sanya yaran shi su share wurin nan fes. Lallai wannan wuri ya amsa sunansa wurin bautar gargajiya na Maguzawa kasancewarsa bayan gari, kuma ga shuri jikin bishiyar tsamiya. Wanda ake sharewa a duk safiya.

    Hidima ga Abin Bauta:

    A tsarin bautar gargajiya ana yin hidima ga abin da ake yi ma bauta. Hidimar da ake yi ta haɗa da tsaftace wurin, da yin yanka ga abin bauta, da sagale ƙasusuwan dabbar da aka farauto, da yin kyautar mutum ko dabba ga abin bauta. Cikin labarin Bamaguje da Anunu na Magana Jari Ce , an nuna inda Bamaguje ya so a bari ya yanki Anunu domin Gunkinsu ya sha jini. Bamagujen na cewa: Da ni dai na fi son kan da kome, don in kai wa gunkinmu ya sha jini.

    A littafi Ƙarshen Alewa Ƙasa kuwa, an yi bayanin hidimar da ake yi wa abin bauta kamar haka: A kowace shekara Sarkin Arna yakan zo ya yi sujada, kuma ya kawo wa Sarkin Dodanni ‘yar gaisuwarsu. Irin gaisuwar da Sarkin Arna ke kawo wa tana da nauyi ƙwarai. Wato kyautar da ake yi ita ce rai guda na mutum. Ita ma wannan hidima masu gudanar da bautar sun gaje ta ne tun iyaye da kakanni ba sai cikin wani labari ba.

    A wajen wasu Maguzawan kuwa, ba sa bayar da ran mutum sai na dabba. Bayanin Maguzawan garin Jinjin Wawa na cikin Ƙarshen Alewa Ƙasa ya tabbatar da haka:
    Jinjin Wawa wani gari ne wanda shi ma girmansa kamar na Tsaunin Gwano yake. Suna da Sarkinsu na tsafi, to amma shi ba a ba shi ran mutum sai na dabba.

    Sakamakon Saɓa Ma Abin Bauta:

    A duk lokacin da ake gudanar da bauta a Maguzance, ya zama wajibi a kiyaye tare da mutunta wannan abin bauta. Idan ba haka ba za a ga sakamako wanda ba daɗi. A lokacin da Mailoma ya yi karambanin zuwa fadar Sarkin dodanni ya aikata abin da ba a yi kamar haka:

    Da yake wannan yaro ba ya cikin hankalinsa, ko tufafinsa bai tuɓe ba. Da ya ji tarin ya ƙi tsakaitawa sai ya tura ɗan yatsa a maƙogwaro ya yiwo aman giya a kan shurin nan. Yace ma shuri, “sha mana” Ya sake kecewa da dariya. Wannan rashin kunya da Mailoma ya aikata ga Sarkin Dodanni na daga cikin abin da ba a yi a wurin tsafinsu. Yin haka kuwa kan haifar da mummunan sakamako ga wanda ya aikata.

    A dalilin wannan rashin kunya da Mailoma ya yi, wasu abubuwa sun faru da shi kamar haka: Ai wannan babu shakka cizon maciji ne, don kuwa ga alamar ɗan jini da kuma shaidar haƙora. Maciji? Aha ga amsa a fili. Nan take ya fusata ya yi ruri cikin dajin nan yana kira, MACIJI. MACIJI! SARKI. SARKI! Kai ne ka cinye Tayani.

    Zagi Da Batsa:

    Zagi shi ne faɗa wa mutum baƙar magana ko bacin iyayensa, (Ƙamusun Hausa 2006: 487). Zagi wani ɓangare ne cikin lafuzzan ɗaurin auren Maguzawa wanda a wasu lokuta yake zuwa surke da batsa. Maguzawa suna sanya zagi cikin lafuzzan ɗaurin aure domin wanda yake da niyyar ƙalubalantar ɗaurin aure idan ya tuna girman zagin, da kallon da jama’a za su yi masa ya fasa, (Abdullahi 2008: 5-7).

    Ko ba wurin ɗaurin aure ba Maguzawa sukan yi ashar cikin magana ta yau da kullum, ko da kuwa zagin surke yake da batsa. A irin wannan yanayi, ba sa jin nauyi ko kunyar wani don sun yi irin waɗannan kalamai. Misali an sami zagi cikin litttafin Ƙarshen Alewa Ƙasa a yayin da Mailoma yake yin kirari kamar haka:

    “Ni ne na bara ni ne na bana
    Mijin Tayani dogon yaro
    Samun irinku sai an tona
    Yaro ko kana musu in ci ubansa”.

    Haka kuma Mailoma ya sakeƙunduma wani ashar ɗin lokacin da matarsa ta sheda masa tana da juna biyu inda ya ce:
    “ Sai ni Arne tsaran manya na Chiwake da Tayani.
    Yaro ko kana shakka ne yanzu in ci ƙundun durin uwarka .

    Batsa ita ce maganar banza musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji. Ga Bamaguje, batsa ta zama jiki, domin tana cikin lafuzzan ɗaurin aurensu. A maganganun yau da kullum, al’ummar Maguzawa ba sa jin kunyar yin batsa. Haka ma a littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa batsa ta fito a wannan wurin kamar haka:
    Dutsen niƙa: Kakir-kakir
    Malka: “Ba ruwan ka da yaron kowa”
    Malka ta sake maimaitawa.
    “Ba ruwan ka da yaron kowa
    To, zagayo ka ci gutsu,
    A hankali ba da garaje ba”.

    Batsar da ke cikin wannan zance na Malka tana ƙunshe da kalmomi waɗanda idan ba Bamaguje ba, babu wanda ke iya faɗi ba tare da jin kunya ba. Dalili kuwa, an ambaci al’aurar mace ba tare da jin kunya ba.

    ABINCIN MAGUZAWA

    Cin Mushe:
    Hausawa na cewa: “kyawun Bamaguje ya ci mushe”. Mushe shi ne naman wata dabba ko tsuntsu da ya mutu ba tare da an yanka ba. A wurin Maguzawa dabba ko tsuntsu da ya yi mushe nama ne mai kyau. Wasu Maguzawa da aka kira da sunan Filani cikin littafin
    Malam Inkuntum, an nuna cewa sun ci mushen Biri a cikin daji kafin su iso gari.

    Marubucin na cewa:
    Ana ta rawa da waƙa sai ga waɗansu Filani su uku sun fito daga cikin daji. Ashe sa’ad da suke can daji yunwa ta kama su har sun tarad da gawar bika sun gasa namansa sun ci. Sun yi wa juna alƙawarin ba wanda zai faɗi wannan magana har abada. Ko kafin su iso nan ƙishirwa ta kama su ƙwarai da gaske. Sai kuma suka ji durin kiɗa ake yi, suka tona asirinsu.

    Bafillace na Farko: Ho ɗan kare da ba da ƙishirwa
    Bafillace na Biyu: Hala kana so ka faɗi.
    Bafillace na Uku: He, ku faɗi, mun ci biri, mun ci biri, mun ci biri.

    Shan giya

    Sharholiya ita ce yin abubuwa na jin daɗin rayuwa da nufin more rayuwa da shaƙatawa. Abubuwan sharholiya ga Bamaguje su ne shan giya, da wasanni, da auren mata da yawa, da yin bukukuwa, da sha’awar doki, (Abdullahi 2008:5) Daga cikin waɗannan ɗabi’un, giya ita ce ta mamaye littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa. A farkon littafin an fara zancen giya lokacin da ake sanarwa domin gayyatar farauta da cewa:

    Hantsi ya ajiye ƙoƙon da ya gama shan burkutu da shi, ya yi wata doguwar miƙa ya yi murmushi. Hantsi ya ƙara ciko ƙoƙonsa da giya ya ce: A wannan rana duk tsawon rai na ba zan iya mantawa da ita ba. Lallai da ban sa baki ba da ai da kun yi ɗanyen aiki, ya miƙo masa giya cikin ƙoƙo, Mailoma ya karɓa.

    Ko da yake yin wannan sanarwa, waɗannan samari suna cikin sharholiyarsu ne da giya. Wannan ya nuna cewa rayuwa ba ta gudana wurin Maguzawa sai da giya, kuma wa da ƙani suna iya haɗuwa su sha ba tare da sun ji komi ba. A lokacin da Mailoma ya je yi ma Juda gaisuwar ɗansa, an nuna cewa ko a nan sai da ya sha giya ya yi tatul har aka ba shi wadda ya yi guziri da ita. Juda ya fara bayani da cewa:

    Ku kawo masa giya nan, hankalin yaron nan ya tashi.” Ku yi sauri mana ku zubo, ka bar kukan nan.” Bayan an zubo giya a ƙoƙo sai aka miƙa wa Mailoma don ya sha. Ya karba.
    Bayan da Mailoma ya ƙare zaman gaisuwa, sai ya yi sallama da jama’a ya nufi ƙauyensu. Ko da yake dai shi ya yi sallama da mutane, amma a gaskiya bai san lokacin da ya yi ba.

    Giyar da ya ɗirka da kuma naman da ya ci duk sun yi masa babakere a ciki. Ga shi saboda buguwar da ya yi har da ƙyar yake iya takawa. Kuma tun lokacin da ya zauna gindin su Manje mai kukuma yake ɗaukar ƙoƙo bisa ƙoƙo na burkutu, wanda ma ba ya ko ɗan saurarawa domin ya huta. Ya tinkaro hanyar Tsaunin Gwano da wani goran giya mai girma a hannunsa.

    Wannan kyauta ce wadda Juda ya yi masa saboda ba a samu wani wanda ya kama ƙafansa wajen shan giya ba. Kusan kowane lungu da saƙo na rayuwar Maguzawa, giya ba ta rasa gurbi. Idan kuwa babu wata hidima, to haka nan ma sukan sha domin annashuwa.

    NAƊEWA

    Haƙiƙa adabi ba ƙaramin tanadi ya yi wa rayuwar Maguzawa ba, ya kuma haskaka mana rayuwar Maguzawa. Kenan hoton Maguzawa da Maguzanci cikin wasu littattafan adabi, rayuwa ce ta wata al’umma da wasu marubuta suka ƙyallaro cikin fasaharsu a rubuce.

    MANAZARTA

    Abdullahi, I.S.S. 2008. Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato..
    Abdullahi, I.S.S 2008. “Bamaguje da Ɗan Akuya: Rashin Ƙauna Ko Ƙiyayya?” Departmental Seminar Series, Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.
    Abdullahi, I.S.S 2012. “Falsafar Ɗaurin Auren Maguzawa”. Muƙalar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

    Karanta Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

    Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

    NAZARIN WASU DAGA CIKIN FINAFINANSA

    DAGA
    FATIMA ADAM ISAH
    adamisahfatima@gmail.com
    07015974659
    DA
    MUHAMMAD SAHAL ALIYU
    Sahalaliyu@gmail.com
    07065994177
    ƊALIBA A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA DA KIMIYYAR HARSHE,
    JAMI’AR JIHAR KADUNA, KADUNA

    Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron ƙara Wa Juna Sani Na ƙasa Da ƙasa Karo Na Biyar Mai Taken ‘Hausa Playwrights And Dramatists As Agents Of National Integration And Development’ In Commemoration Of Late Playwright, Alhaji Yusuf Ladan, Ɗan Iyan Zazzau, 2th-4th Dec 2021. Wanda Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe Jami’ar Jihar Kaduna Ta Shirya.

    DECEMBER, 2021.

    Tsakure
    Tun samuwar fina-finan Hausa a shekarun baya, harkar ta sami bunƙasa da haɓaka sosai wanda hakan ba ya rasa nasaba da yadda matasa da ‘yan kasuwa suka shigo cikin harkar shirya finafinai. Waɗannan fina-finai na Hausa idan aka masu fyaɗar kaɗanya, za a ga yawancin saƙonnin da ke ƙunshe a cikinsu ba ya wuce soyayya da matsalolin zamantakewar aure.

    Don haka ne ma wannan muƙalar za ta mayar da hankali a kan ɗaya daga cikin jigogi a harkar shirya fina-finan Hausa da ba da umurni wato Ali Gumzak tare da nazarin gudummuwarsa wurin samar da kuma haɓaka fina-finan Hausa. Daga ƙarshe, za a yi nazarin gundarin soƙonni da ke ƙunshe a wasu fina-finansa guda uku wato Burin Fatima da Izzatu da kuma Ƙawaye.

    Gabatarwa

    Ko shakka babu, finafinan Hausa ɓangare ne na adabi kuma fasaha ce ta al’umma da ke nuni da yanayi da tsarin rayuwar al’umma. Ta hanyar fina-finan Hausa za a iya ganin hoton rayuwar wata al’ummar da ta gabata, haka kuma za a iya fahimtar tsarin rayuwar waɗannan mutane da ɗabi’unsu da tattalin arziki da zamantakewarsu.

    Za a iya ganin hoton abin da ke faruwa a cikin al’umma, har ma wani lokaci a iya kirdaden abin da zai iya faruwa a cikin al’umma. Finafinan Hausa hanya ce ta bayyana tunanin mai shirya fim ɗin, ko marubuci, ko kuma irin falsafarsa game da rayuwa.

    Taƙaittaccen Tarihin Samuwar Fina-finan Hausa

    Fim abu ne mai gajeran tarihi idan aka kwatanta shi da sauran ɓangarori na adabin zamani. Misali waƙa da rubutun zube waɗanda tuni suka ci gaba ta fuskar nazari da aikace-aikacen masana da manazarta masu rubuta kundayen bincike don neman digiri na farko zuwa na uku.

    A wajen Hausawa wasan kwaikwayo shi ne tushen samuwar fina-finan bidiyo domin shi aka fara aiwatarwa a dandali kafin a samu na’urar ɗaukar hoto ta majigi wadda daga baya kuma aka sami gidajen talabijin da na’urar bidiyo da ake amfani da ita a yanzun.
    Dangane da wasannin kwaikwayon majigi, sun fara samuwa ne a wajen 1950 lokacin da ma’aikatar yada labarai ta Arewa (Ministry of Information Northern Nigeria) take ƙoƙarin wayar da kan ‘yan Arewa dangane da harkokin noma da wayar da kan su al’amuran da suka danganci rayuwar yau da kullum.

    To sai ma’aikatar ta zaɓi ta yi amfani da wasan kwaikwayon majigi domin shi ne hanya mafi sauƙi da za a jawo hankalin ‘yan Arewa a kan su noma abubuwan da gwamnati take buƙatar da su a kan yadda da wannan noma ta hanyar amfani da hanyoyin zamani. To gwamnatin wannan lokacin ta yi amfani da wasan kwaikwayon majigi domin gudanar ta hanyar amfani da mota wadda take ɗauke da na’urorin nuna majigi wato “Projector”.

    Ana amfani da wannan mota ne ta bin birane da ƙauyuka domin nuna wasannin domin ilimantar da su a wannan ɓangare na noma da kuma ɗebe masu ƙewa. Dangane da fim wanda aka fara aiwatarwa a harshen Hausa kuwa shi ne Baban Larai Mai Auduga a cewar Abdulkadir (1998:24) wanda aka aiwatar a shekarar 1948.

    Daga nan sai Ɗan Arewa a London, sai kuma fim ɗin Shaihu Umar a shekarar 1976 da sauran ɗimbin fina-finan da aka samar a wannan lokacin, sai dai akwai fina-finan masu yawa da wasu mutane ko jihohi suka shirya, to amma ba su zo ga jama’a ba saboda wasu dalilai.

    Akwai kuma fina-finan da tashoshin gidajen talabijin na ƙasa da suke jihohin Arewa suka gudanar don nuna wa jama’a. Misali Golobo daga Sakkwato da Karkuzu na Bodara daga Kano. Dukkan waɗannan shirye-shirye na NTA da suke a waɗannan jahohi. Har ila yau, kuma akwai Bakan-Gizo da Hadarin Kasa sa Hankaka na CTV 67 Kano (Gidan Dabino da Wani), a cikin Adamu da wasu, (2004:342).

    Fim na farko da ma’aikatar yaɗa labarai ta Arewa ta fara nuna wa jama’a sun haɗa da fim ɗin Baban Larai da Dan Arewa a London da Shaihu Umar da Kulɓa na Ɓarna da sauransu. Nuna fim babu ko shakka hanya ce mafi inganci ta yada al’ada. Ta wannan hanya ce al’adun ƙasar Indiya da Sin da Amurka su ka zo Nijeriya har ma wasunsu suka samu karɓuwa, aka kwaikwaiye su.

    Binciken da aka gudanar a 1970, a Arewa akwai gidajen silima ɗari huɗu(400) wato a cikin birnin Kano kawai, akwai guda shida (6) kuma kowannen su za su iya ɗaukar mutane fiye da dubu biyu(2000) a lokaci ɗaya. Sa’anan kuma akwai gidajen silima da dama a sauran ƙasashen Arewa, amma duk cikin su babu na ‘yan ƙasa, ƙwarori ne (Lebanese) ke da su. Saboda haka mutanen Arewa, ba su da zaɓin fim ɗin da za a nuna masu.

    Dangane da wannan dalilin, shi ya sa mutane suka shaƙu da kallon fina-finan Indiya, ga kaɗe-kaɗe da raye-raye. Ba abin mamaki ba ne a ƙasar Hausa ka ga wani magidanci na rera waƙar Indiya lokacin da yake nishaɗi ko kuma lokacin da yake gudanar da wani aiki. Su ma mata ba a bar su a baya ba, lokacin Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a 1974, lokacin da fito da wani fili na kaɗe-kaɗen Indiya da ake sawa, ba mamaki ka ji ana kiran mace Bahaushiya da sunan Hema ko Rani da dai sauran sunayen taurarin da suka yi fice a fina-finan Indiya.

    Kaunar da Hausawa ke wa labaran soyayya, shi yasa CTV 67 ke nuna wasu wasanni guda biyu wato Bakan Gizo da Hadarin Sama waɗanda suka sami nasara. An gina labaran ne kan soyayya irin ta Indiya (Salihu,2002).

    Bunƙasar Fina-Finan Hausa

    Sun fara samuwa ne tun kafin ‘yancin Nijeriya musamman bayan kammala yaƙin duniya na biyu. A wannan lokaci tattalin arziƙin Turai ya yi rauni ƙwarai tun ma ba na Ingila ba. Saboda haka ne Turawan mulkin mallaka suka taru don tattauna hanyoyi da za su fitar da ƙasashensu daga wannan ƙangi, inda suka shirya cewa a samu kaya da suka sarrafa a kasuwa.

    Nan take aka yanke shawarar cewa ƙasshen da ake wa mulkin mallaka ne za a iya matsawa su noma abubuwa da za a kawo nan ƙasar Ingila irin su gyaɗa da auduga maimakon kayan abinci, sa’annan kuma a yi wa jama’a farfaganda domin su yi amfani da kayayyakin da aka ƙera a ƙasashen wajen. Ta irin wannan hanyar ce sai su jama’a suka kashe kuɗaɗen da suka samu ta sayan kayayyaki daga waje.

    Me ya kamata a yi don a tura wa mutane wannan hanyar kashe kuɗi? Sai aka yanke shawarar yin fina-finai da Hausa domin ‘yan Arewa. Nan ne aka fi samun manoma sai aka shirya fim ɗin Baban Larai. Wanda aka nuna wani hamshaƙin manomi ne da ya bunƙasa wajen noman gyaɗa da auduga.

    Bayan samun ‘yancin kai an yi fina-finai don nuna muhimmancin haɗa kan ƙasa, da samun ‘yancin kai, da yadda ake gudanar da zaɓe. Haka kuma an yi fina-finai irin na Sir Ahmadu Bello da sauran mashahuran mutane da Jam’iyyar NEPU da NCNC mafi yawan waɗannan fina-finan Hukumar Talabijin ta Amurka ce ta yi su, inda aka yi fim mai suna Ɗan Arewa a Landon inda aka nuna Dr. Ibrahim Tahir a matsayin tauraro. An nuna yadda ɗan Arewa ya kamata ya gudanar da rayuwarsa a Landon.

    An fara yin fina-finan Hausa a 1960 lokacin da Adamu Halilu ya shirya fim ɗin Shehu Umar wanda aka gina kan littafin nan na Shehu Umar na Abubakar Tafawa Ɓalewa. Fim ɗin ya sami gagarumar nasara saboda abu biyu. Na ɗaya, ita ce a lokacin babu fim na Hausa tsantsa sai shi, na biyu kuma shi ne jigon labarin mai tsuma jiki ne wato soyayyar uwa zuwa ga ɗanta.

    A lokacin da aka nuna fim ɗin a silima ta ‘Plaza’ a Kano a 1976, duk wanda yake ganin ya shahara wajen zuwa silima ya je kallo. Bayan waɗannan fina-finai an yi waɗansu fina-finan da suke magana kan al’adun gargajiya na Hausawa waɗanda suka haɗa da “Auren Hausawa” da “Kano Heritage” da “Hawan Sallah” dukkansu na Alhaji Yahaya Imam.

    Dangane da bunƙasar fina-finan Hausa kuwa (Salihu, 2011) ya ce za a iya cewa sun yi tashin gwauron zabi ta yadda suka kai ga wani matsayi da za a iya kwatantawa da matsayin sana’ar kwatantawa da matsayin sana’ar acaɓa a ƙasar Hausa.

    Daga shekarar 1990 lokacin da aka fara gudanar da fim ɗin bidiyo na sayarwa zuwa yanzu an sami kamfanoni fiye da 121 da suka yi rijista da ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Jihar Kano, ban da waɗanda kuma suke gudanar da harkokinsu a ɓoye, sannan daga wannan lokaci zuwa yanzu an samar da fina-finan Hausa sama da guda dubu (1000).

    Muhimmancin Fina-Finan Hausa

    Fina-finan Hausa abubuwa ne masu matuƙar muhimmancin gaske ga al’ummar Hausawa, musamman domin ilmantarwa da faɗakarwa da ke tattare da irin waɗannan fina-finan. Maƙasudin shirya fim shi ne domin wayar da kai ko kuma maganin wata matsala da take tattare ga al’umma, wato ta yi wa al’umma dabaibayi. Ta harkar fim ake nuna wa jama’a wata matsala mai wuyar warkewa kuma a warwareta domin nuna wa jama’a ta yadda za su kuɓuta duk lokacin da suka ci karo da irin wannan matsala.

    Kuma ana shirya fim a kan kowace matsala ta rayuwa domin warware ta ko maganinta.
    Fim hanya ce ta faɗakar da al’umma, wato ana amfani da fim don ilimantar da mutane a kan wani abu da ya shige musu duhu ko kuma wani abu da ake so su yi ko su ɗauka.

    Misali, idan gwamnati tana so ta faɗakar da jama’a bisa ga muhimmancin ilimi za ta sa a shirya fim wanda wani ya shiga makaranta har ya gama ya samu aiki ya zama wani a al’umma ta yadda mutane za su kwaikwayi wannan mutum. Akwai fina-finan da aka shirya domin ilimantarwa waɗanda suka haɗa da Jahilci Ya Fi Hauka da Wuyar Magani Zato wanda yake ilimantarwa a kan yawan zage-zage da ke faruwa a ƙauyuka musamman a kan maganar maita da sauransu.

    TAKAITACCEN TARIHIN ALI GUMZAK

    An haifi Ali Gumzak a shekarar alif ɗari tara da saba’in da tara (1979), a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano. Asalin sunansa Aliyu Ibrahim Khalil. Ya yi karatun firamare a makarantar Makama Primary School, sannan ya yi karatun sakandire a wata makaranta da ake kira “Gwale Secondary School, sannan daga bisani ya tafi School of Management Studies, inda ya karanci Financial.

    A hirar da aka yi da shi, ya bayyana cewa abun da ya jawo shi shiga harkar fim shi ne sha’awa da kuma sana’a. Ya fara harkar fina-finai a shekarar dubu biyu da sha ɗaya inda ya shirya fim ɗinsa na farko mai suna Salma Hayat. Fim ne da ya ja hankalin mutane sosai saboda saƙon da yake cikin sa.

    Salma Hayat fim ne da aka yi shi domin jan kunne ko gargaɗi ga ‘yan mata masu wulaƙanta samari. Ali Gumzak ya ce ba zai iya tuna adadin fina-finan sa ba sai dai a ƙalla za su kai hamsin (50) ko fiye da hakan a halin yanzun’. Misalan wasu daga cikin wannan fina-finan sun haɗa da:

    1.Salma Hayat
    2.Baban Sadiq
    3.Manyan Gobe
    4.Sultan
    5.Zango
    6.Dawo Dawo
    7.Burin Fatima
    8.Jaruma
    9.Ka yi na yi
    10.Aliya
    11.Wata Ruga

    12.Ruma
    13.Meera
    14.Wasiya
    15.Haidar
    16.Maƙota
    17.Ƙawaye
    18.Sai da ke zan rayu
    19.Manyan Mata
    20.Ga Duhu Ga Haske
    21.Rumfar Shehu
    22.Karangiya

    DALILIN SAMUWAR SUNAN GUMZAK

    Ya samu wannan suna na Gumzak ne sanadiyar wani aiki da ya yi a ƙarkashin kamfanin wani mutum mai suna Hamza, Hamza ya haɗa sunan garin Mahaifinsa wato (Gumel) da kuma sunan garin Mahaifiyarsa (Zakirai) shi ne ya samar da Gumzak. Sanadiyar ficen da ya yi a wannan kamfanin ne ya sa ake kiran shi da wannan sunan.

    Ali Gumzak ya kara da cewa ba shi da wata gaɓa da ya fi karkata a kai, yana taɓa kowane sashe walau na barkwanci ne ko na soyayya da dai sauran irin nau’in fina-finai. Duk wanda ya kalli fim ɗin Rumfar Shehu ya san fim ne na barkwanci, fim din Dawo-Dawo fim ne na soyayya, fim ɗin Salma Hayat fim ne na jan hankali. Ya shirya fim ɗin da ya shafi addinin muslinci wato Ga Duhu ga Haske.

    ƘALUBALEN DA YA FUSKANTA A RAYUWARSA

    Kamar yadda muka sani duk wata ɗaukaka ta rayuwa sai an sami ƙalubale. Daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta su ne; Ba ya manta lokacin Gwamna Shekarau a Kano, shi da abokin sa Aminu Saira sai da suka bar garin Kano suka dawo garin Kaduna, a lokacin ko kuɗin da za su kama ɗaki ba su da shi. Sai daga baya suka samu wani ɗaki da ake biya a Arewa House.

    Ya ƙara da cewa wannan babban ƙalubale ne mutum ya tafi ya bar mahaifansa. Bayan haka ya ce kallon da mutane ke musu da cewa suna ba da gudunmawa wajen ƙara taɓarɓarewar tarbiyan yara, ya ce wannan ma wani babban ƙalubale ne’. Sannan yace satar fasaha ma ƙalubane ne, domin sai sun gama wahala ba su mai da kuɗinsu ba sai zauna gari su kwafe don su saida.

    NASARORIN DA YA SAMU A HARKAR FIM

    Yace nasarorin da ya samu sun fi kalubalen yawa, sanin da mutane suka mai a duniya yana ganin babban nasara ce a rayuwar shi. Da kuma tarin masoya da ya samu ya ce matuƙa wannan abun yana burge shi. Daga cikin nasarorin ya samu gidan zama na shin a kan shi sannan ya sai abun hawa, har ila yau ya yi aure duk ta sanadiyar wannan harka ta fim. Inda yace yanzun kam Alhamdulillah yaran sa biyu sannan yana da mata ɗaya kuma yana zama a garin kano .

    YADDA ALI GUMZAK YAKE KALLON HARKAR FIM

    Ya ce a ganinsa harkar fim hanya ce da ke gyara tarbiya, sai dai kowa akwai irin kallon da ya ke ma harkar. Yadda mutum ya ɗauke ta, haka zai amfana da ita, sai dai su suna yi ne don gyara da jan hankali da kuma gargaɗi ga masu irin halin walau mai kyau ko akasin hakan. Ko kuma ya za a yi a nuna ma al’umma dai dai da kuma akasin hakan. Ya ƙara da cewa jigon fim shi ne mutum ya gani ya yi koyi da mai kyau ko ya watsar da na banza.

    NAZARIN FIM ƊIN BURIN FATIMA

    Yan Wasa
    1.Adam.A.Zango
    2.Aisha Aliyu Tsamiya
    3.Maryam Booth
    4.Ummah Shehu
    5.Jamila Gwaska
    6.Jamilu Kochila
    7.Haj. Aisha Mahuta
    8.Tasiri Kaduna
    9.Asma’u Nass

    Shiryawa; Abubakar Bashir Maishadda
    Mataimakin mai shiryawa; Aisha Aliyu Tsamiya
    Umarni; Ali Gumzak
    Mataimakin mai shiryawa; Murtala Balala
    Shirin kamfanin Maishadda Investment Nig.Llimited
    Shekarar: 2017

    Da farko dai an nuna Fatima da ƙawayenata su biyu a cikin makaranta, suna Magana a kan auren da Fatima ta yi, suna ba ta shawarar cewa ya kamata ta yi irin tsarin nan na ma’aurata domin idan ta haihu hakan zai shafi karatun ta. Bayan Fatima ta ba wa mijin ta wannan shawarar sai ya yi fushi ya nuna mata baya so. Sannan ya faɗa mata cewa haihuwa ba ya hana karatu, ya kuma kawo mata misali da wata da ta zama Farfesa, kuma ta yi aure ne bayan ta kamala karatun sakandare.

    An nuna Fatima ta samu juna biyu bayan wani ɗan lokaci, Umar ya yi matuƙar murna da wannan labarin sai dai bayan ta je makaranta ne ƙawayenta su ka ga tana amai sai suka fara ba ta shawarar cire cikin, har suna ba ta misali da cewa cikin mai laulayi ne ga shi karon farko har ta rasa jarabawa na gwaji na makaranta.

    A haka Fatima ta biye wa shawarar ƙawayen ta aka zubar da wannan cikin, ta cewa mijin ta ta yi ɓari. Bayan kammala makarantar Fatima da ɗan wani lokaci ne sai ta fara son haihuwa, amma sai Umar mijin ta ya ce mata “haihuwa na Allah ne, in lokacin ya yi zai ba su”. Duk da haka Umar bai daina neman mata magani ba a duk inda ya samu labarin wani likita ko mai maganin gargjiya.

    Ana haka ne kwatsam Umar ya samu labarin wani ƙwararren likita sai ya ɗauki Fatima, ya kai ta wajen shi. Bayan gwaje- gwaje sai ya gano wannan zubar da cikin da tayi ne a baya ya haifar mata da wanann matsalan, bayan komawar su gida ne sai Umar ya yi fushi da Fatima har ta kai ga ya ƙarba shawarar da mahaifiyarsa ta daɗe tana ba shi a kan ya ƙara aure.

    Bayan Umar ya ƙara aure ne da ɗan wani lokaci sai wannan matar ta samu ciki, murna a wajan Umar da mahaifiyar sa ba kama hannun yaro, lokacin ne koma Fatima ta ci gaba da ganin bambamci a cikin gidan, wanda amaryan ta haihu a hakan ba abun da ba ta gani. Umar bai da lokacin Fatima sai daga ƙarshe da ta nuna za ta bar gidan sai ya ce mata ya yafe mata kuma zai cigaba da neman man mata magani har Allah ya sa a dace.

    JIGON FIM ƊIN BURIN FATIMA

    Kamar yadda muka sani jigo na nufin ginshiƙin abin da fim ya ƙunsa. Wato dalilin yin fim ɗin. Akwai masana da dama da suka yi magana a kan jigo. Sun haɗa da, Sarbi,(2007;71) in da ya ce jigo a fagen adabi na nufin manufar marubuci, wanda dukan bayanai suka dogara da ita.

    Jigon cikin wannan fim ɗin shi ne “Gargaɗi ko jan hankali ga masu bin shawarar ƙawaye”. Idan muka yi duba yadda mijin Fatima wato Umar ya nuna mata soyayya sannan ya nuna mata yana son haihuwa, amma ƙawayen ta suka zuga ta da cewa idan ta bari ta haihu za ta kasa karatunta na jami’a, tattaunawarsu da ƙawarta a cikin cikin makaranta ɗaya ga cikin ƙawayen ta ta ke ce mata:

    “Ni fa na san ba a iya haɗa aure da karatu, domin da zarar kin samu ciki za ki fara samun carryover, daga nan kuma sai spillover, daga nan kuma sai tafiya, ba ki ga Karima ba sai da aka kore ta.” Har ila yau, za mu ga tun daga nan ta fara haska mata irin matsaloli da za ta fuskanta idan har ta yadda ta ɗauki ciki, da kuma abin da zai biyo baya na samun cikas a a harkar karatu, tare da buga mata misali kan makomar ɗaya daga cikin ƙawayensu mai suna (Karima) ta shiga, suna dai ganin rashin cikin shi ne alheri a shawarar su.

    An kara nuna su tare, inda suke zuga Fatima domin ta zubar da cikin da ta samu, duk da cewa ta nuna musu tana jin tsoro amma a hakan suka dage suka cusa mata wannan ra’ayin a zuciyar ta har ta amince da wannan shawarar: “Fatima kin ga tun daga yanzun daga samun cikin, kin fara samun matsala ba ki da test ɗin da malam ya yi jiya, sannan ya ce ba zai yi ma kowa makeup ba, kin ga abun da muke guje miki ke nan tun farko, don haka ki zo mu je asibiti a markaɗe cikin.”

    Sai Fatima ta ce:To me zan ce wa Umar? Ba ku ga yadda yake son cikin nan ba.”
    Sai ƙawarta ta ce mata: “To ki faɗa mai za ki yi kin zubar da cikin, zuwa kawai za ki yi mu je wajen wani doctor na cikin sauƙi zai miki komai, shi dai kawai ya san kin fito makaranta idan an gama ki koma gida ki kira shi a waya ki sa kuka yana zuwa ya tambaye ki ki ce cikinki, kin yi ɓari, shi ke nan”

    Bayan Fatima ta amince ne sai suka je aka cire cikin kuma ta yi duk yadda suka tsara mata. Idan muka duba wannan maganan da ƙawar Fatima ta yi za mu ga cewa ta ɗora ta a kan turbar ƙin yi wa mijinta biyayya wanda hakan ne ya haifar mata da duk wata matsala da ta shiga ciki na rashin haihuwa. Fim ɗin Burin Fatima ya nuna mana ƙin aminta da ƙawayen banza da kuma ɗaukar shawararsu wacce idan mutum ya bi tabbas zai faɗa halaka.

    NAZARIN FIM ƊIN IZZATU

    Jaruman cikin shirin sun haɗa da:
    Ali Nuhu
    Abdul.M.Shareef
    Hadiza Muhammad
    Fatima Muhammad(Fandi)
    Abdussalam Imam
    Ladidi Fagge

    Shiryawa; Yakubu Inuwa qyari
    Umarni; Ali Gumzak Sak
    Kamafanin; Gumzak investment Nigeria Limited
    Shekarar; 2019

    An nuna yadda wata budurwa mai suna Izzatu da wani ɗan uwanta wanda yake tamkar aboki a gare ta duk inda za ta suna tare haka ma aikin gida ko saƙo duk tare suke yi. Har iyayen su suke tunanin haɗa su aure domin ana ganin soyayya suke yi, kwatsam Izzatu ta kawo mijin aure gida aka sa lokacin aure ana ta shirye-shiryen buki, kwanaki na ƙara ja har lokacin bukin nan ya zo.

    Suna cikin shagalin buki ne a dandali da daddare sai ga wani tsoho ya zo yana musu magana a kan su daina dare ya yi, sai Izzatu ta yi masa rashin kunya ta ce bai isa ya hana su yin rawar gaban hantsi ba, har tana cewa ji tsohon nan. Bayan ta koma gida ta kwanta bacci ne sai wasu irin ƙuraje suka fito mata a jiki, aka dinga neman magani amma ba a dace ba, kwatsam sai aka samu labarin wani mai magani.

    Bayan sun je wajen shi sai ya ce wannan mutumin aljani ne, sannan za a samu magani amma sai wani na jikin ta wato mahaifin ta ko ɗan uwan ta ko dai mijin ta su ne kaɗai za su iya zuwa wajan maganin. Babanta makaho ne ba zai iya zuwa ba, don haka sai aka ce mijin da ta aura shi ya ce. Kwatsam sai wannan mijin ya kawo mata takardan saki.

    Don haka wannan ɗan uwan nata shi ya tafi wajan samun maganin, dama kuma da sharaɗin wanda ya je sai ya dawo shi ma da wata kalar cutan. Cikin nasara ya samu mata magani ta samu lafiya sai dai ya samu irin ƙurajen a jikinshi da kuma ƙusinbi.
    Iyayen Izzatu sun yi tunanin haɗa Izzatu da wannan abokin nata aure amma ta yi butulci ta ƙi yarda.

    Mahaifiyarta ta yi Alawadai da halin ta har ta kai ga gudu ta bar gida. Garin guduwan ne sai mota ta bige ta har aka yanke mata ƙafa. Bayan dai wannan abun da faru da ita sai suka so haɗa ta aure da ɗansu, sai suka gano asalinta su ma suka yi tir da ita suka mai da ta gidan su, da ƙyar suka yafe mata dai a ƙarshe.

    JIGON FIM ƊIN IZZATU

    Kamar yadda aka ba da ma’anar jigo a baya, shi ne ginshiki na gina fim ɗin. Wannan fim na Izzatu jigon shi, shi ne Butulci. Butulci na nufin (yankakkiyar rashin godiyar Allah). Rashin nuna godiya ga wani mutum. Inda butulci ya fito a wannan fim din shi ne inda Izzatu ta ƙi ta aure wannan ɗan uwan nan ta har ta gudu ta bar gidan su sanadiyar hakan.

    Sannan butulci a karo na biyu shi ne inda mijin ya sake ta a lokacin da ta ke buƙatar shi, lokacin da ya kamata a ce ya tafi wajan neman mata magani, amma sai ya mata sakayya da takardan saki duk da irin soyayyan da aka nuna sun yi. Butulcin da Izzatu ta ma wannan ɗan uwan na ta har ta nuna tana ƙyamar shi sannan kamar ma ba ta san shi ba.

    Wannan shi ne abun da ya faru a cikin shirin izzatu, an yi ƙoƙarin jan hankalin ‘yan mata masu ma tsofaffi rashin kunya da rashin ladabi ga na gaba da su, sannan an ja kunne ga kyautata wa wanda ya kyautata maka a rayuwa.

    NAZARIN FIM ƊIN ƘAWAYE

    Jaruman cikin fim ɗin
    Ali Nuhu
    Sani Danja
    Hafsat Ɓarauniya
    Aisha Humaira
    Hajara Usman
    Rahama Hassan
    Da sauran su

    An nuna ƙawaye guda biyu Ruma da kuma Fatima a makaranta saboda tsabar ƙawancen su a ɗaki ɗaya suke kwana a makarantar babu abin da ɗaya za ta yi ɗaya ba ta sani ba. Sai dai halinsu ya sha bamban kamar yadda ma su iya Magana kan ce ”Sai hali ya zo ɗaya ake abota” Su kuma wajan su ba haka ba ne. Don ita Fatima tana da natsuwa akasin ƙawarta Ruma.

    Hakannan matsalar ɗaya ta ɗaya ce, haka kuma kowa da yake a makarantar ya san su tare don haka komai na su ɗaya su ke yi. Suna cikin hakan ne ita Ruma ta samu matsala da saurayin ta sanadiyyar halinta na bin maza. Bayan kodayaushe ƙawar tana nuna mata gaskiya da cewa iyayen su fa karatu suka turo su ba wasa ba, amma ta ƙi ji. Saurayin da ya gane sai ya dai na zuwa wajan ta ya kuma dai na kiran ta.

    Sanadiyar hakan Ruma ta ne ma ƙawarta ta raka ta Abuja wajen shi, amma sai ta umarci ƙawarta da tace mai ta zo biki ne, hakan kuma suka yi sai ya kama mata ɗaki ya kuma ba ta kuɗi bayan ta faɗa ma Ruma ne sai ta ce ai soyayya su ke yi ba ta yarda ba, cikin hakan ne ta kira mahaifiyarta a waya tace mata ga fa ƙawarta ta tafi Abuja bayan kuma ta hana ta tafiya, maman ta yi fushi ta kira ta a waya ta tambaye ta inda ta ke sai ta ce tana gidan yayarta.

    A haka dai har ta samu ta kira yayar ta mata bayani shi koma saurayin Ruman ya biya mata kuɗin jirgi don ta yi saurin dawowa. An nuna lokacin da za ta shiga otel ɗin da ya kama mata, mijin da za ta aura ya ganta daga nan ya je ya yi mata mummunan zato sannan ya fasa auren ta, ya aika gidan iyayen ta aka kwaso masa kayan auren shi.
    Haka ita ma Ruma saboda halinta wannan saurayin nata ya fasa auren ta, ya dawo ya aure wannan ƙawar tata wato Fatima mai natsuwa da kuma hankali.

    JIGON FIM ƊIN ƘAWAYE

    Jigon wannan fim ɗin ba ya wuce nunawa ‘yan mata muhimmancin kamun kai. Idan aka ce kamun kai ana nufin natsuwa da yin abun da ya kamata da kuma kama mutuncin kai.
    A wannan fin ɗin mun ga yadda ƙawar Ruma wato Fatima ta so ta sa ƙawarta a hanyar daidai amma ta ƙi, don akwai inda ta ke ce mata;

    “Wai ke Ruma ba za ki canza halinki ba? Kin ga irin abun da nake faɗa miki ko, ba kya jin magana wannan tsalle-tsallen da kike yi ya yi yawa, yau ke ce kwaso wannan gobe ki ɗakko wancan, me ye amfanin shi? Ya kamata ki zauna ki ma kanki karatun ta-natsu ki riƙe mutuncinki, ke fa mace ce aure za ki yi wata rana……….”
    An samu wuri da dama inda aka nuna tana zama domin yi mata faɗa a kan halayen ta amma ta ƙi.

    KAMMALAWA

    Kamar yadda muka ji ma’anar fina-finai daga bakin masana da kuma jigon fim da kuma tarihin ɗaya daga cikin masu bayar da umarni a harkar fim ɗin, sannan da yadda muka yi sharhi a wasu daga cikin fina-finan, wato Burin Fatima, da Izzatu, da Kawaye. Haka koma mun ga muhimmancin fina-finai da kuma yadda mai ba da umarnin yake kallon harkar fim ɗin.

    MANAZARTA

    Sadik, L.A (2021) “Karatun Jami’a A Fina Finan Hausa” :Nazari Daga Wasu Fina-Finan Hausa. Kundin Digiri Na Ɗaya Jami’ar Jahar Kaduna.
    G.P Bargery, (2016) “A Hausa-English Dictionary And Englsh-Hausa Vocabulary” Jami’ar Ahmadu Bello University Press Limited.
    Chamo I.Y (2016), Saƙo A Fina-Finan Hausa: Nazari Kan Jigo Da Rabe-Rabensa, Kundin Binciken Digirin Na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero Kano.
    Gidan Dabino, A.A da Wani (2004) “Matsaloli Da Nasarorin Masu Shirya Fina-Finan Hausa Musamman Na Kano” A Cikin Adamu da Wasu (Editoci). Gidan Dabino Publishers, Kano.
    Hira da Ali Gumzak Da Muka Yi A Ranar Laraba 27-10-2021, A Garin Kaduna.

    Don Karanta Adana Harshe (LANGUAGE PRESERVATION) danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

     

  • Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Wannan Shi ne Farfesa Da Ya Kafa Tarihi A Duk Faɗin Najeriya.

    Farfesa Abdallah Uba Adamu, ɗan asalin unguwar Daneji a Kano, da ya kafa Tarihin zama Farfesa na farko sau biyu a fannoni daban-daban a Najeriya a Jami’ar Bayero, Kano. Ya zama Farfesa na farko a Science Education a 1997, sannan a Media and Cultural Communication a 2012. Shi kaɗai ne a Arewacin Najeriya da ya sami wannan nasara, yayin da mutum uku kacal ne a Najeriya gaba ɗaya.

    Baya ga koyarwa da bincike, ya shahara wajen nazarin Hausa, Tarihi, Al’adu, fina-finai, da tasirin kafofin sada zumunta, har ma ya ƙirƙiri haruffan Hausa masu lanƙwasa (ɓ, Ɓ, ɗ, Ɗ, ƙ, Ƙ) a kwamfuta a shekarun 1990. Ya shugabanci National Open University of Nigeria (2016–2021) tare da kawo sauye-sauye a tsarin karatun nesa, ya gabatar da shahararren jawabin Sunset at Dawn, Darkness at Noon (2004), kuma ya koyar a jami’o’in ƙasashen waje ciki har da Poland, Amurka da California Berkeley.

    Duk da irin wannan manyan nasarori, Farfesa Adamu ya kasance mutum mai barkwanci, sauƙin kai, da shahara a kafofin sada zumunta.

    Karanta Sababbin Karin Maganar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Masu Rera Waƙa

    Masu Rera Waƙa

    Masu rera waƙar, su ne asalin mawaƙan, wato waɗanda suke zama su tsara waƙar ta hanyar amfani da basirarsu.

    Waɗannan su ne rukuni na farko, kuma su ne tushe; domin dalilinsu ne aka samar da dukkanin wani nau’in kayan kiɗa da tanadar dukkanin abin da zai kai ga rera waƙar; har ta kai ga yaɗuwa a tsakanin jama’a.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudumawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki; Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Takardun da Ake Saya Domin Rubuta waƙar danna nan

  • Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo

    Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo

    Abin Da Bincike Ya Gano Game Da Gudumawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki: Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo

    Dukkanin wani bincike da za a gudanar ko aka gudanar; za a iske akwai irin nasarar da aka ci a sakamakon yin sa; wanda hakan ya sanya aka gano wasu muhimman abubuwa.

    A wannan nazari kan waƙar baka, an gano wasu muhimman abubuwa da suke da amfani ga rayuwar al’ummar Hausa da ma ƙasa baki ɗaya.

    Cikin abubuwan da binciken ya gano akwai:

    i. Yadda aka sami bibiyar sawu ta fuskar sana’a a tsarin waƙa, daga waƙar baka ta gargajiya zuwa waƙoƙin baka na Situdiyo. Wato sai ya zama kamar abin da Bahaushe ke cewa, “Sawun da na gaba ya taka, na baya ma kan takawa” amma fa ta fuskar sana’a.

    ii. Yadda aka fahimci mamayar mutane a cikin sana’ar waƙoƙin Situdiyo.

    iii. Yadda aka ga tattalin arziki na bunƙasa a dalilin waƙoƙin Situdiyo.

    iv. An fahimce yadda gungun jama’a ke cin abinci a dalilin waƙoƙin Situdiyo na Hausa.

    v. An gano yadda waƙa ta zama wata babbar sana’a a Ƙasar Hausa tun daga jiya har zuwa yau.

    vi. Binciken ya binciko irin nau’o’in mutanen da suke jinginuwa da wannan sana’a ta waƙa a matsayin hanyar samun abin masarufin rayuwa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudumawar Adabin Baka Wajen Haɓaka Tattalin Arziki: Keɓantaccen Nazari Kan Waƙar Baka Ta Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

  • Fitattun Iyayen Gida Na Ɗanƙwairo A Kiɗan Fada

    Fitattun Iyayen Gida Na Ɗanƙwairo A Kiɗan Fada

    Bisa dukkan hasashe, ubangida a wajen Makaɗi yakan zama mutum wanda ya nuna damuwa a harkoki da al’amurran makaɗi; wataƙila kuma makaɗin nan ya fi daidaita tunaninsa da zubin waƙoƙin da yake yi masa.

    Ubangida yakan zama murabbi ta fuskar kyautata ayyukan makaɗa don su zama na ƙwarai.

    Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo tun a farko-farkon tsundumarsa a cikin waƙoƙin baka, Allahu ya hore masa irin waɗannan dattawan iyayengida.

    Muhimmai daga cikinsu sun haɗa da:

    a) Abubakar na Birnin Ƙaya a Gundumar Maradun
    b) ‘Yandoton Tsahe, Alhaji Aliyu II (1960-1991)
    c) Sardaunan Sakkwato, Firimiyar Jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello Sakkwato (1962-1966)
    d) Sarkin Maradun Alhaji Abubakar (1939-1964)
    e) Sarkin Maradun Muhammadu Tambari (1964-1981)

    f) Sarkin Maradun Ibrahim II, Maigandi (1981-2003)
    g) Sarkin Daura, Alhaji Muhammadu Bashar (1966-2007)
    h) Sarkin Sudan, Alhaji Shehu Malami Wurno
    i) Sarkin Das, Alhaji Bilyaminu Usman
    j) Da sauransu

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙungiyar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Ta Kiɗa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Waƙa A Matsayin Sana’a danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Sauran Waɗanda Suka Yi Shahada Tare Da Husaini (Radiyallahu Anhu)

    Sauran Waɗanda Suka Yi Shahada Tare Da Husaini (Radiyallahu Anhu)

    Wani abun jan hankali shi ne sunayen waɗansu daga cikin ‘ya’yan Husaini da ƙannansa waɗanda suka gamu da ajalinsu a wannan lokaci a Karbala.

    Waɗannan sunaye su ne:

    1-Abubakar ɗan Aliyu ɗan Abi Talib (Radiyallahu Anhuma)
    2-Umar ɗan Aliyu ɗan Abi Talib (Radiyallahu Anhuma)
    3-Usman ɗan Aliyu ɗan Abi Talib (Radiyallahu Anhuma)
    4-Abubakar ɗan Husaini ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma)
    5-Umar ɗan husaini ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma).

    Wannan yana nuna yadda Ahlul Baiti (Radiyallahu Anhuma) suke matuƙar ƙaunar waɗannan sahabbai har suke sanyawa ‘ya’yansu sunayensu, wannan bai tsaya kan sayyidina Au da Husaini ba, a a kusan dukkan Imamai sha ɗaya sun bi sahu.

    Ɗan uwa karanta waɗannan sunaye:

    1-Umar ɗan Aliyu ɗan Abu Ɗalib (Al-atraf)(Radiyallahu Anhuma)
    2-Umar ɗan Muhammad ɗan Umar ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma)
    3-Umar ɗan Husaini ɗan Au (Radiyallahu Anhuma)
    4-Umar ɗan Ali ɗan Husaini ɗan Ali (Al Ashraf)(Radiyallahu Anhuma)
    5-Umar ɗan Aliyu (Al-asgar) ɗan Umar (Al Ashraf) ɗan Aliyu zainul Abidina ɗan Husaini (Radiyallahu Anhuma)
    6-Umar ɗan Hasnul Aftus ɗan Aliyul Asgar ɗan Aliyu Zainul Abidin ɗan Husaini (Radiyallahu Anhuma)
    7-Umar ɗan Husaini ɗan Zaidu ɗan Aliyu ɗan Husaini ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma)
    8-Umar ɗan Musal Ƙasim ɗan Ja’afarus Sadik (Radiyallahu Anhuma)
    9-Umar ɗan Husaini Sibti ɗan Aliy ɗan Abu Talib (Radiyallahu Anhuma)
    10-Umar ɗan Ja’afar ɗan Muhammad ɗan Umar Al-traf ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma)

    11-Umar ɗan Muhammad ɗan Umar ɗan Aliyu ɗan Husaini Asshadi (Radiyallahu Anhuma)

    12-Umar ɗan Yahaya ɗan Husaini ɗan Zaid (Radiyallahu Anhuma)
    13-Umar ɗan Hasan ɗan Aliyu ɗan Husaini ɗan Aliyu Bin Abi Talib (Radiyallahu Anhuma).
    14-Abubakar ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (Radiyallahu Anhuma)
    15-Abubakar ɗan Husaini ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma)
    16- Abubakar ɗan Hasan ɗan Aliyu (Radiyallahu Anhuma)

    17-Abubakar ɗan Abdullahi ɗan Ja’afar ɗan Abu Talib (Radiyallahu Anhuma)
    18-Usman ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (Radiyallahu Anhuma)
    19-Usman ɗan Akilu ɗan Abi Talib (Radiyallahu Anhuma)
    20-Usman ɗan Akilu ɗan Abi Talib (Radiyallahu Anhuma)
    21-A’isha ‘yar Musal Ƙazim ɗan Ja’afarus Sadik (Radiyallahu Anha)
    22-A’isha ‘yar Aliyu Rida ɗan Musal Kazim (Radiyallahu Anha)
    23-A’isha ‘yar Aliyu Abul Hasan ɗan Muhammad Jawad ɗan Aliyu Rida (Radiyallahu Anhuma)
    24-Mu’awiyya ɗan Aliyu ɗan Ja’afar ɗan Abu Talib (Radiyallahu Anhuma)
    25-Ɗalha ɗan Hasan ɗan Aliyu ɗan Abu Talib (Radiyallahu Anhu)

    Ya ɗan uwa mai karatu ka dubi yadda waɗannan bayin Allah suka sanyawa ‘ya’yansu sunayen waɗannan manyan sahabbai musamman Umar domin su nunawa kowa cewa su fa ba sa gaba da su ko a kusa ko a nesa, saboda ai babu yadda za a yi mutum ya yi ta sanyawa ‘ya’yansa sunayen waɗanda yake ganinsu a matsayin maƙiya, koma munafikai ko kafirai.

    A nan na ƙara kira ga ‘yan uwa masu da’awar son da bin Ahlul Baiti da su yi koyi da su, su daina ƙin sahabbai, musamman Abubakar, Umar, Usman, A’isha, Ɗalha da Mu’awiya, su daina zaginsu da tsine musu, su daina yi musu ƙage, saboda su Ahlul Baitin (Radiyallahu Anhuma) ba su yi haka ba. Ya Allah ka ganar da mu ka bamu ikon bin gaskiya. Amin.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wa Ya Kashe Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Waiwaye Kan Tattalin Arzikin Hausawa Na Gargajiya

    Waiwaye Kan Tattalin Arzikin Hausawa Na Gargajiya

    TUNA BAYA SHI NE ROKO: WAIWAYE KAN TATTALIN ARZIKIN HAUSAWA NA GARGAJIYA

    DAGA

    Kabiru Abdulkarim

    Kabiruabdulkarim996@gmail.com  08034510967

    Da

    HauwaMuhammadMaikudi

    hawwammaikudi@gmail.com  08098191994

    School of Languages,

    Kano State College of Education and Preliminary Studies.

    Takardar da aka gabatar a Bikin Taron Ranar Hausa ta Duniya a Kwalejin Ilimi da Share Fagen Shiga Jami’a Ta Kanoa ranar Talata 26 ga Agusta, 2025.

     TSAKURE

    Hausawa kan ce “Waiwaye adon tafiya”. Wannan takarda ta yi waiwaye ne a kan tattalin arziƙin Hausawa na gargajiya domin abin nan da Bahaushe ke cewa “Tuna baya shi ne roƙo”. An yi nazarin sana’o’in gargajiya na Hausa, saboda su ne ginshiƙan rayuwa da tattalin arziƙin yau da kullum na Hausawa (Garba 1991:1).

    Takardar ta gano cewa watsi da aka yi da waɗannan sana’o’i  namu na gargajiya, shi ya jefa mu cikin wannan hali na ƙaƙa-ni-ka-yi da matsin tattalin arziki da muke fama da shi a halin yanzu. Sannan an kawo shawarwari da ake ganin za su iya taimakawa sosai wajen rage wannan raɗaɗi da ake ciki da kuma mawuyacin hali da matasannmu suka tsunduma kansu a ciki na shan miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya da kuma faɗan daba.

    Gabatarwa

    An shirya wannan takarda ne da nufin yin waiwaye kan tattalin arziƙin Hausawa na gargajiya, ba don komai ba sai don a waiwaya a kuma gyara halayyar da Hausawa suka ɗauka a halin yanzu na watsi da sana’o’inmu na gargajiya, muka koma bilayi da bilinbituwar neman arziƙi ta wasu hanyoyi da ba su dace da mu ba, sannan kuma suke wahalar da mu, har suka ke neman kai Hausawa ƙasa warwas.

    Bahaushe a da ba shi da wani abin da ya sanya a gaba sai sana’a, wato neman na kansa. Amma a halin yanzu an bar sana’a an koma neman wasu hanyoyi da za a azurta kai da gaggawa, kuma arziƙin ya ƙi samuwa. An koma ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko. Bahaushe yana cewa “Sana’a Sa’a, kuma rashin sana’a Sata” (Mu’azu da Satatima 2013:61).

    Daga nan za mu fahimci cewa lallai Hausawa na wannan zamani, musamman matasa an doshi hanyar rugujewar al’umma. Don haka,  ya zama wajibi a koma ga sana’o’inmu na gargajiya domin ita ce kaɗai hanya mai ɓillewa wadda kuma ba ta da tangarɗa.

    Wannan tattalin arziƙi da muke magana a gargajiyance ya ƙunshi hanyoyin da Hausawa suka bi a dauri, suka zauna cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali da wanzuwar arziƙi, har ya kasance sun zama abin koyi da kuma ban sha’awa a idon duniya.

    Hausawa dai su ne al’ummar nan waɗanda harshen Hausa shi ne harshensu, kuma al’adunsu da ɗabi’unsu suka yi kama da na addinin Musulunci (Zarruq 1992:2). Gargajiya kuma tana nufin hanyoyin da aka saba bi na rayuwa. A nan gargajiyar Bahaushe ta kasu gida biyu: (a) kafin zuwan Musulunci da kuma (b) bayan zuwan Musulunci.

    • Kafin zuwan Musulunci: A nan ana nufin duka abubuwan da Hausawa suka saba yi na rayuwa tun daga farkon samuwarsu , wato lokacin Maguzanci har zuwa lokacin da suka haɗu da Larabawa.
    • Bayan zuwan Musulunci: Addinin Musulunci ya zo ƙarsar Hausa a tsakiyar ƙarni na sha huɗu zamanin Sarkin Kano Aliyu Yaji (1349-80), (Maiyama 2008:40-41), kimanin shekaru 676 da suka gabata. Bayan zuwan Musulunci Hausawa sun karvi addinin hannu bi-biyu. Dukkanin wasu kyawawan halaye da ɗabi’u sai suka cigaba da su, amma duk wasu abubuwa da suka ci karo da koyarwa da tarbiyyar addinin Musulunci sai suka yi watsi da su. Dalilin daɗewar musuluncin a ƙasar Hausa, sai ya sanya su ma al’adun da aka samu daga Larabawa, sai suka zama gargajiyar Bahaushe.
    • Lokacin zuwan Turawa(zamani):Zuwan Turawa tare da mulkin mallaka shi ne ake kira zamani. Turawa sun karɓe ikon ƙasar Hausa a 1903. Don haka duk wani abu da ya samu bayan zuwan Turawa ƙasar Hausa, to shi ba gargajiyar Bahaushe ba ne ya zama na zamani ke nan.

    Togaciya: Wannan takarda ta yi togaciya kan abubuwa kamar haka:

    • Akwai sana’o’i da dama da takardar ba ta dube su ko nazarce su ba, domin an tsara wasu Makarantu ko Kwalejoji  za su gabatar da su a wannan taro na ranar Hausa ta Duniya. Sana’o’in sun haɗa da Saƙa, Sassaƙa, Koli, Ƙira (babbaƙu), Dillanci da sauransu.
    • Akwai wasu sana’o’in da ko dai Hausawa na tababarsu cikin sahihancinsu kamar roƙo da raraka da tsibbu da makamantansu, takardar ba ta dube su ba. Haka sana’ar ƙunshi da wasu ke kallonta a gargajiyance kamar ba sana’a ba ce wato kwalliya ce, daga baya ne zamani ya ba ta gurbi ta zama cikakkiyar sana’a kuma mai gwaɓi.
    • Sana’o’in da takardar ta yi bayani, ana so ne a kafa hujja ko buga misali da su, ba wai su kaɗai ne suka fi sauran muhimmanci ba.
    • Wasu sana’o’in kuma an haƙura ba a kawo su ba saboda yanayin lokaci da gudun ka da abin ya yi yawa wai “shege da hauka”, misali Arkomi,da Asako,da Kiri,da Bugu,daAikatau wato Dakau,da Sirfau,da Niƙau da makamantansu.

    SANA’A

    Garba (1991:1) ya dubi sana’a da cewar ita ce ginshiƙin rayuwa da tattalin arziƙin yau da kullum na Hausawa tare kuma da ɗaya daga cikin muhimman manyan hanyoyin gano martabar mutum da ƙasaitarsa da matsayinsa cikin al’umma. Watau ban da noma wadda take ruwan dare, Hausawa suna kuma ƙara wa kansu wata sana’a wadda da rani ana samun abinci ta hanyarta, har ma ko da daminar akan taɓa wasu sana’o’i ƙari a kan noma.

    Umar (1983) a cikin D/Iya (2006:1) ya bayyana sana’a da cewa; “wata hanya ce da ɗan Adam kan ta’allaƙa a kanta domin samin abin masarufi wadda ta shafi sha’anin kasuwanci, wato sha’ani na saye da sayarwa”. Ya ci gaba da cewa; “sana’o’in suna da babban matsayi a al’adun kowacce al’umma”. Ga Bahaushe su ne ƙashin bayan tattalin arziƙinsa.

    A nan sana’a ta zo da sigogin ma’ana, akwai zaɓaɓɓun lokuta da yanayi ke tabbatar da sana’a. Wannan ya yi dai dai da azancin da ke cewa lokacin abu a yi shi. Ma’ana kowace sana’a da lokacin yinta, wannan yana haska yadda Al’ummar Hausawa suke da abin yi rani da damina, dare da rana, mace da namiji, yaro da babba. Haka shi yake nuna ba sa zaman kashe wando  koyaushe akwai abin yi.

    Rabe-raben Sana’a

    Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ko tsara sana’o’in Hausawa bisa kashi-kashi dangane da ra’ayoyinsu da fahimtarsu.

    Yahya da Ɗangambo (1986:173-174) sun tsara rabon sana’o’i zuwa gida uku. Sana’ar noma, da sana’ar sarrafa wani abu domin samar da wani abu. Misali ƙarfe-ƙira; zare – saƙa; fata – dukanci; sai sana’ar sarrafa jari da ƙwarewa, misali, kasuwanci, da gini, da tallau, da sauransu.

    Haka kuma Yahya (1992:4) su ma a cikin littafin sun raba sana’o’i zuwa gida uku inda suka tsara sana’o’i na noma da kasuwanci da waɗanda suke dafe-dafe.

    Ragowar rabe-raben sana’o’in na Hausawa, su ne rabo ta ɓangaren jinsi, ma’ana an raba sana’o’in a ɓangaren jinsi zuwa gida uku, jinsin maza da jinsin mata da kuma na tarayya. Abin nufi a nan shi ne, bisa ƙa’idojin al’adun Hausawa, ba kowacce sana’a kowa yake yi ba, a a kowace da mai yinta, waɗansu na mata ne, waɗansu na maza ne, waɗansu kuma kowane jinsi na iya aiwatar da su. Misali:

    Na maza Na mata Na tarayya

    Ƙira (babbaƙu) kitso saƙa

    Dukanci sussuƙa ƙira (farfaro)

    Jima dafe-dafe d.s dillanci

    rini aikatau

    wanzanci, da makamantansu.

    Noma

    Noma tushen arziki,

    Noma na duƙe tsohon ciniki,

    kowa ya zo duniya kai ya tarar.

    A bisa tsarin gargajiya, noman nan shi ne tushen rayuwa, domin ta nan ne ake samar da abinci da kuma bunƙasar tattalin arzikin al’umma. Burin kowanne magidanci ne ya noma isassahen abincin da zai ci da iyalinsa tsawon shekara. Haka kuma dole ne akwai buƙatar a noma abin sayarwa irin su auduga da gyaɗa don samun ‘yan kuɗin biyan buƙatun rayuwa. Haka kuma sana’ar noma ta haifar da wasu sana’o’i musamman na abinci daban-daban.

    Al’adar sana’ar noma ta yi wa rayuwar Bahaushe riga da wando, har ma da hula da takalmi. Bayan wadatuwa da abinci da abin masarufi, noman nan ya hana Bahaushe ragwanci da zaman kashe–wando. Ya tsare masa gabas da yamma ta fuskar cikar mutunci da kwarjini da cancanta ta kowace fuska. Don haka sana’ar  noma ta haifar da wasu sana’o’i irin su kiwo da saƙa da kaɗi da akasari sana’ar abinci da mata kan aiwatar daga cikin gida.

    Fawa

    Maza na Sarkin fawa,

    Kuna yawa ana rage gona,

    Fawa ko ta kwana ta fi tallan ƙosai,

    Sarkin fawa rikici gado,

    Kaɗauki bashi ka biya bashi,

    Na Inna kashin shanu,

    Hankaka mai da ɗan wani naka,

    Bungare mai billen ‘yanci,

    Na kulluru mayen ɗanye,

    Maƙiyinki ya dama fura ya fasa.

    Fawa sana’a ce ta yanka dabba a feɗe ta, a yanka ta gunduwa-gunduwa, tsoka-tsoka domin sayarwa ta yadda za a iya amfani da naman yadda ake sonsa. Ana iya sayar da shi a ɗanyensa, ko a gasa, wato tsire ko balangu ko kilishi da makamantansu.

    Farauta

    Gwarzon daji,

    Mai tsare ƙauyuka,

    Barde mai tsaron daji,

    Wanda baya tsoron daji,

    Masanin dabarun naman daji,

    Kai ne mai kawo tsoron-tsoro.

    Farauta ita ce sana”a

    Su

    Mai su uwar ɗaka.

    Wanda ke kawo ɗanɗano ga abinci,

    Mai ba wa duniya ƙanshin ƙanshi,

    Ɗawisu na alheri,

    Mai zuba wa rayuwa ɗanɗano.

    Su sana’a ce ta kamun kifi, musamman ga waɗanda suke zaune a gefen ruwa. Sana’a ce da ake kama kifi don ci ko don sayarwa.

    Jima

    Romon Jaɓa,

    Mai yi wa saurayi aure,

    Mai sai wa saurayi wando,

    Mai kula da lafiyar mutane

    Jima hannun magani,

    Ka sha baƙar wahala don farar fata,

    Ka zama ma ji ɗaukar alhini.

    Jima sana’a ce da ake tusarrufi da fata. Jima dai ita ce sana’ar sulluɓe fata don fitar da gashin da ke jikinta (Alhassan da wasu,1980:43) Jima tsohuwar sana’a ce a ƙasar Hausa da har yau take cin ganiyarta. Kamar yadda Alhaji Sule Garo, shugaban masu Masana’antun jima na zamani, ya faɗa a wata hira da aka yi da shi (a Radiyo France International,R.F.I.ranar Litinin,17 ga watan Augusta,2009 da misalin ƙarfe 3:17 na yamma), cewa ya yi duk da shigowar zamani, har yanzu sana’ar jima ta gargajiya tana da tasiri. Domin kamar yadda ya faɗa, su kamfanonin sarrafa fatar sun fi buƙatar waɗanda aka jeme su a gargajiyance don haka ma sukan yi masu ƙima ta musamman wajen saya (Ɓatagarawa 2013: 328).

    Rini

    Baban dubu mai kamu,

    Kowane ganye ya ruɓe ya lalace,

    Amma ban da kai na Sarkin Marina,

    Katsi katse tsiya,

    Toka takore tsiya na Makaman Marina,

    Kowa ya bar ka gidansa a sha lami.

    Rini kuwa sana’a ce ta gargajiya da ta shafi canza launin tufa ko zare daga fari ya koma wata kala daban. Wajen rini ana amfani da abubuwa irin su muciya da kwatarniya da guga da itace da baba da katsi da shuni da tukunyar baba da ruwa da sauransu

    Rini, sana’a ce ta gargajiya da a waɗansu wurare a ƙasar Hausa, har yanzu ana ado da ita. Duk da cewa an sami hanyoyi da dama na zamani inda ake amfani da launuka iri daban–daban, amma duk da haka har yanzu ana ba wa sana’ar ƙima  daraja ta musamman.

    Wanzanci

    Kala-kala magani gizo Ɗan Wanzam,

    Aska na cikin kube tana cin gashi,

    Ka ci gashi ka sha jini na Magaji Aska,

    Kai wa Sarki rotse ka tashi da martaba.

    Wanzanci sana’a ce da ake yin amfani da aska da ƙaho da tankolo da ƙugiya wajen aiwatar da ita. Masu wannan sana’a wato wanzamai suna tallafa wa rayuwar al’umma ta fuskar aiwatar da abubuwa kamar aski da ƙaho da kaciya (shayi ko kugunu) da tsagar anfill da shasshawa da cire beli ko hakin wuya da makamantansu.

    Ɗinki

    Ɗinki sana’a ce da ake amfani da zare a samar da sutura ingantacciya, yalwatacciya kuma kyakkyawa. Ɗinki hikima ce ta yin amfani da sililin zare, tare da allura a riƙa haɗa geffan kyallayen yadudduka a samar da tufafi ga maza da mata. Ɗinki ya rabu gida biyu wato ɗinkin tufafi da kuma ɗinkin huluna.

    Ƙira

    Huntu ubangijin mai riga.

    Ƙira sana’a ce mai dangantaka da ma’adanai da tsirrai da dabbobi. Sana’a ce da ake sarrafa ƙarfe da itace don samar da ma’aikaci. Ita ma wannan sana’a a iya cewa tana daga cikin sana’o’in farko-farko ma’ana tun lokacin da ɗan Adam ya fara zama wuri ɗaya. Ƙira ta zama tamkar uwa ma ba da mama a wurin sauran sana’o’i domin maƙeri ne yake samar masu kayan aikin sana’ar su.

    Sana’ar ƙira ta kasu gida biyu. wato maƙeran fari, da kuma maƙeran baƙi. Maƙeran fari su ne masu ƙera abubuwa dangin farin ƙarfe da azurfa da zinare da makamantansu. Su kuma maƙera baƙi su ne suke sarrafa  baƙin ƙarfe  dangin tama da tagulla.

    Ta hanyar ƙira ake samar da abubuwan amfani (ma’aikaci) irin su wuƙaƙe da gatura da adduna da faretani, da kuma makamai irin su takubba da masu da da kibiyoyi da makamantansu. Ka ga wannan ba ƙaramin tasiri suke da shi ba ta fuskar tattalin arziki da kuma harkokin tsaro a gargajiyance.

    Fatauci

    Fatauci sana’a ce da ta danganci kasuwanci. Akan bar gari a tafi wani garin domin kai haja can, sannan kuma a sayo wata a kawo gida. Masu wannan sana’a ana kiransa fatake. Da wannan sana’a ta fatauci Hausawa suka shahara a idon duniya. Sukan ɗauki kaya (haja) kamar fata da gyaɗa da auduga su kai sauran sassa na kudancin ƙasar nan ko ƙasashen ƙetare su sayo wasu kayan da ba a samunsu a ƙasar Hausa.

    Sukan ya-da zango a wasu garuruwa. Wanda a halin yanzu waɗannan wurare suka zama mallakin Hausawa a wajen ƙasar Hausa misali Zango ta Gwanja a ƙasar Ghana in da daga nan ne ake kawo goro zuwa ƙasar Hausa.

    Gini

    Gini sana’a ceta sarrafa abubuwa don samar da muhalli, daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa. Hasali ma dai a iya cewa ga al’ada kowa magini ne. Ma’ana ko da dai ba a nuna ƙwarewa ba to a ƙalla kowa yana iya sarrafa ƙasa, ko laka don yin gini. Waɗanda suka ƙware, sukan maishe ta sana’a, kuma su ake cewa magina. Magina sun kasu kashi biyu, akwai magina na ƙasa ko laka (siminti a zamanance) da suke sarrafa ƙasa don samar da muhalli.

    A ɗaya ɓangaren kuma akwai magina na yumɓu, waɗanda suke sarrafa yumɓu su samar da abubuwa irin su tukwane da kasake da murahu (amare) da tuluna da asusu da butoci da mazubai iri daban-daban. Akwai ire-iren waɗannan magina masu tarin yawa a ƙasar Hausa, kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen baza harshe da al’adun Hausawa a wurare daban-daban ciki da wajen ƙasar Hausa. Adamu (1978:34).

    Matsayin Sana’a Wajen Bunƙasa Tattalin Arziƙin Hausawa:

    Ma’anar Tattalin Arziki

    Tattalin arziki shi ne yadda al’umma ke samar da abin da take buƙata da yadda take sarrafa shi, da amfani da albarkatun ƙasa domin samun ci gaba da walwala da biyan bukatunsu na yau da kullum.

    Ibrahim (2010) ya bayyana ma’anar tattalin arziki da cewa: “Tattalin arziki shi ne tsarin da al’umma ke bi wajen samar da abin da take buƙata daga albarkatun da ke hannunta da kuma yadda take sarrafa su.”

    Bunza (2002) ya bayyana cewa, “Tattalin arziki shi ne yadda al’umma ke tsara rayuwarta ta hanyar albarkatun da take da su, domin ci gaba, zaman lafiya da kuma walwala.”

     Bunƙasar Tattalin Arziƙin Hausawa

    Tattalin arzikin Hausawa ya bunƙasa sakamakon waɗannan sana’o’i da suke gudanarwa. Babu shakka Hausawa sun tsaya tare da jajircewa da bin wasu hanyoyi da ƙarfafa wa juna domin ganin tattalin arzikinsu ya bunƙasa daga waɗannan sana’o’i.

    Saboda irin jajircewar da suke yi a kan sana’o’insu har sai da ya zamo sun yi fice a fuskar noma ta inda suke noma, wannan ba ƙaramin bunƙasa tattalin arziƙinsu ya yi ba a wancan lokaci. Daga cikin hanyoyin da suka taimaka wajen bunƙasa wannan tattalin arziƙi sun haɗa da:

    Yadda wasu sana’o’in suke haifar da wasu sana’o’in: Ta hanyar haifuwar wasu sana’o’in a dalilin wasu, tattalin arzikin Hausawa ya bunƙasa matuƙa. Hakan na faruwa ne sakamakon duk lokacin da aka fari wani abu na sana’a to babu shakka za a samu majuɓunta a kan abin da suke samarwa.

    Wannan zai haifar da samun kuɗi ga masu wannan sana’a kai tsaye da ma sauran al’umma baki ɗaya. Misali Sana’ar noma, ta haifar da sa sana’o’i irin su kasuwanci, fatauci, ban gishiri na ba ka manda da nakamantansu.

    • Kiwo ya haifar da sana’ar fawa.
    • Fawa ta haifar da sana’ar jima.
    • Jima ta haifar da sana’ar dukanci.
    • Sana’ar kaɗi ta haifar da sana’ar saƙa da rini.
    • Saƙa ta haifar da sana’ar ɗinki.

    Bayan wannan akwai Sana’o’in da yawa da suka haifar da wasu sana’o’in, hakan ba ƙaramin bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa ya yi ba.

    Samar da kayayyakin da suke na buƙatu a matakin farko: Yawa-yawan kayan da Sana’o’in suke samarwa, kaya ne da ake buƙatar su ko ma a ce suka zama dole a mallake su. Hakan ya sa da zarar an samar da su da an saye su (ga waɗanda ake ƙirƙira ko samarwa) Haka abun yake ga sana’o’i na hidima irin su aski, kitso da makamantansu. Ƙarin bayani a nan, a zamanin da Hausawa ba su fiya ɗora kansu a sana’o’i na jin daɗin rayuwa ba da suke haifar da almubazzaranci da rashin adani ba.

    Hanyoyin Bunƙasa Tattalin Arziƙin Hausawa

    Akwai hanyoyi da dama waɗanda suke taimaka wa Hausawa wajen bunƙasar tattalin arziƙi. Kaɗan daga ciki sun hada da:

    Gado: A da mutane suna gadar sana’o’i da suke yi ne daga magabatansu (gida). Wannan ya sa da wuya ka samu wanda yake ba shi da sana’ar yi, don kuwa mutum tun yana ƙarami yake koyan sana’ar da ya gani ana yi a gidansu. Hakan kan sanya ƙwarewa da kishin sana’ar ga masu yin ta. A dalilin haka da wuya ka ga mai zaman banza a wancan lokaci. Wannan ya sa kowa yana da abin yi, kuma tattalin arziƙin al’umma ya daɗa bunƙasa.

    Ban gishiri na ba ka manda: Wannan wani kasuwanci ne da ake yi ba da kuɗi ba. Ana yin sa ne ta hanyar musaya na abubuwan buƙata. Misali manomi zai iya ɗaukar hatsinsa ya kai wa mai fawa don ya ba shi nama. Ko ya ba wa wanzami don ya yi masa aski. Wannan shi ake kira da ban gishiri na ba ka manda . Haƙiƙa wannan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa domin kuwa babu yadda za a yi kana da sana’ar ka ka rasa wani abu da kake buƙata ko da kuwa ba ka da kuɗin saye.

    Kiwo: Kiwo sana’a ce mai sirrin gaske ga al’ummar Hausawa. Ga mata har ma mazan a da ba a rasa su da yin kiwo. Idan biki ya taso ko haihuwa ko wata buƙata, mutum kan kama wata dabba tasa ya je ya sayar ya samu kuɗin biyan bukata nan take. Baya ga wannan, a lokacin da ake ciyar da dabbobi ciyawa akan zuba a ƙasa, to duk lokacin da dabbobin suka yi kashi, kashin kan haɗe da ragowar ciyawar da suka ci suka rage.

    Idan sun ruɓe sai su ba da takin noma. Irin wannan taki ya fi ba da albarkar noma da lafiya ga abin da aka shuka a gonar da aka zuba shi. Wannan ba ƙaramin kawo bunƙasar tattalin arziki ya yi ba a zamanin da, musamman idan an kwatanta shi da zamanin yanzu da ake sayen taki da tsada.

    Haɗin kai da tallafa wa juna: Yanayin yadda Hausawa suke aiwatar da sana’o’insu ya taimaka musu matuƙa wajen ƙara hada kawunansu. A sanadiyyar haka ya zamo akwai taimakon juna a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Misali ko ba ka da jari za ka samu aron kayan aiki daga ‘yan’uwa ko abokan arziƙi don gudanar da sana’arka. Wannan shi ma ba ƙaramin taimaka musu ya yi ba wajen bunƙasa tattalin arziƙinsu.

    Mafi yawan masu sana’oi’n nan, suna ba da taimakon magunguna a cikin sana’o’in nasu, wannan yana ƙara masu kuɗaɗen shiga, kuma ya ƙara bunƙasa tattalin arziƙinsu. Misali manoma ne ke bayar da maganin ciwon baya da maganin rana.

    Haka kuma maƙera ne suke ba da maganin ƙunar wuta. Su kuma marina ana samun maganin lalurar fata kamar ƙyasbi da  ƙurajen bar- ni-da-mugu da katsi ga masu juna-biyu. Masunta suke bayar da maganin sanyi da ƙayar kifi. Mahauta suke bayar da maganin kaifi da kuma tsini da sauransu.

    Shawarwari

    • Saka gasa a wajen samar da kayayyaki daga lokaci zuwa lokaci don bunƙasa sana’o’in kamar yadda Ƙungiyar Zauren Hausa Nijeriya ta ɗauki gaɓaren yi.
    • Hukumar ilimi ta sanya shi a manhajar makarantu domin sanya shi cikin manyan darussa koyarwa a matakai daban-daban na ilimi.
    • Masu riƙe da sarautun gargajiya lallai ne su zama sun yi kira da wayar wa da jama’a kai tare da cusa sha’awa don amfani da irin kayayyakin da sana’o’in na gargajiya suke samarwa.
    • Jama’ar gari su ma ba a bar su a baya ba, lallai ne sai sun dawo daga rakiyar da ba ta ƙarewa, wato sun yi riƙo  hannu bibiyu wajen rungumar kayayyakin da sana’o’in mu suke samarwa.
    • Ba da tallafi na kuɗi da kayan aiki ga masu sana’o’in da shawarwari da dabaru daga ƙwararru na masana iri daban-daban.
    • Hukumomi na gwamnati su dinga amfani a kayayyakin da ake samarwa ta fuskar sana’o’in Hausawa na gargajiya.

    Kammalawa

    Waiwaye a kan sana’o’in gargajiya na Hausawa ya nuna cewa jajircewa da tsayawa tsayin daka a kan wasu sirrika da taimakon juna su ne tushen tattalin arziki da ci gaban al’umma a wancan lokaci, kuma har yanzu suna da daraja wajen kare martabar al’adu da samar da ayyukan yi a cikin al’umma.

    Manazarta

    Adamu, M. (1978), The Hausa Factor In West African History. Zaria/Ibadan A.B.U. and Oxford,.

    Alhassan H. da wasu, (1980), Zaman Hausawa, Littafi Na Ɗaya  Zaria. .I.E.P.,A.B.U.

    Aliyu, U. (2015). Kasuwanci da Cigaban Al’umma. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    Aminu, K. (2000). “Saka Sana’ar Sarrafa Auduga a Kasar Hausa: Tasirinta da Muhimmancinta.” Kundin Degree na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Asiru, A. (2017). Sana’ar Dinki Da Ci Gabanta. Zaria: Amadu Bello University Press Limited.

    Bashir, I.S. (1990). “Take da Kirarin Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsu ga Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu. Jami’ar Bayero, Kano.

    Batagarawa , S.A.(2013). Nason Wasu Al’adu a Kan Sana’o’in  Gargajiya na Hausawa Mazauna Lokoja. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani na kasa da kasa mai taken “Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau” wanda Sashen Koyar da Harshunan Nijeriya  na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua tare da hadin gwiwar Hukumar Adana Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina a ranakun 25-26 ga watan Yuni, 2013.

    Dan’iya, M. A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. Kano: Kabs Print Services Nigeria.

    Garba, C. Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙasar Hausa. Ibadan: Spectrum Books Ltd.

    Ibrahim, M. (2010). Tattalin Arzikin Hausawa. Kano: Benchmark Publishers.

    Madabo, M.H. (1979). Ciniki da Sana’o’i a Kasar Hausa. Lagos: Nelson.

    Madauci, I. da wasu (1968). Hausa Customs. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Ltd.

    Maiyama, U.H. (2008): Sata A Zamantakewar Hausawa (Nazarin Waƙoƙin Barayi Na Muhammadu Gambo Fagada) Kundin Digiri Na Uku Da Aka Gabatar A sashen Nazrin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

    Mu’azu, A da Satatima,I.G. (2013). Kwaɗon Al’adun Hausawa da na Wasu Ƙabilu. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani na kasa da kasa mai taken “Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau” wanda Sashen Koyar da Harshunan Nijeriya  na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua tare da hadin gwiwar Hukumar Adana Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina a ranakun 25-26 ga watan Yuni, 2013.

    Sani, A. (2003). Hanyoyin Rayuwa da Aikin Yi a Najeriya. Kaduna: Fisbas Media.

    Smith, A. (1776). An Inquiry into the Nature and Causes of the Wealth of Nations. London: W. Strahan and T. Cadell.

    Yahya,  I.Y. da Ɗangambo, A. (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.

    Yahya, I. Y. da wasu (1992). Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan: University Presss Plc.

    Karanta Hanyoyin Zamantakewar Hausawa 

    Edita@rumasau-kallamu