Category: Addu’o’i

Mun samar da wannan ɓangaren ne, domin samar da Addu’o’i na addinin musulunci a harshen Hausa kuma a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hannu cikin sauƙi.

WikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara.

Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koyo ko koyarwa.

  • Addu’ar Mazaunin Gida Ga Matafiyi

    Addu’ar Mazaunin Gida Ga Matafiyi

    “Astaudi’ul laaha diinaka wa amaanataka, wa khawaatima amalika”. {Ina ba wa Allah ajiyar addininka, da amanarka, da ayyukan da ka ke cikawa a kan su}.

    “Zawwadakal laahut taƙ’waa, wa gafara zanbaka wa yassara lakal khaira haisu kunta”.

    {Allah ya yi maka guzurin taƙawa, ya gafarta maka zunubanka, ya sauƙaƙe alheri gare ka a duk inda kake}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Tafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Salatut Tasbihi danna nan.

  • Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare

    Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare

    Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; ‘Idan kuka ji haushin karnuka, da kukan jaki da daddare, to ku nemi tsarin Allah daga gare su; don kuwa su suna ganin abin da ba kwa gani’.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Yaɗa Sallama A Cikin Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Munafuntar Al’umma Da Rashin Fayyace Alƙibla danna nan.

    Don karanta Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan

  • Yadda Ake Addu’ar Shiga Da Fita Daga Banɗaki

    Yadda Ake Addu’ar Shiga Da Fita Daga Banɗaki

    “(Bismillahi) Allahumma inni a uzu bika minal khubusi wal khabaa’isi”.

    {(Da sunan Allah) Ya Allah ina neman tsarinka daga shaiɗanu maza da shaiɗanu mata}.

    Addu’ar Fita

    “Gufraanaka”

    {Ya Allah gafararka (nake nema)).

    Domin karanta cikakken bayani akan Zikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Alwala Da Falalarta danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar sanya sabon Kaya A Musulunci

    Addu’ar sanya sabon Kaya A Musulunci

    An rawaito daga Abu Sa’eed Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya yi sabon tufa ya kan kira shi da sunan shi sannan yace:

    اللَّهمَّ لك الحمدُ أنت كسوْتنِيهِ أسألُك من خيرِه وخيرِ ما صُنِعَ له ، وأعوذُ بك من شرِّهِ وشرِّ ما صُنِعَ له

    Allahumma lakal hamdu Anta kasautanihi, As’aluka min khairihi wa khairi ma suni’a lahu, wa A’uzu bika min sharrihi wa sharri ma suni’a lahu

    Abu dawud: 4020  Turmidhi: 1727

    Sharhin Addu’ar:

    Ubangijina ina maka godiya kai ne ka azurta ni da wannan tufafi, ba tare da iyawa ta ba, ina roƙon ka ka sanya wannan tufafi ya zamto mai taimako na wurin aikata alheri, Ka haɗa ni da alherinsa, ina kuma neman tsarinka daga sharrinsa sa: ka kiyaye ni kada ya zamto wannan tufafi ya zamto sanadiyyar saɓa maka.

  • Guraren Da Aljanu Suka Fi Zama

    Guraren Da Aljanu Suka Fi Zama

    A wajen zama mun bambanta, sai dai da yawan mu muna rushe musu wurin zamansu sannan mu gina namu, kuma muna sare musu wajen zamansu mu dasa namu.

    Aljanu sun fi zama a cikin daji, saman dutse, saman ɗaki, cikin bola, cikin garken raƙuma, jikin shuri da dai sauransu. Da yawa akwai hatsari da mutum ya ga an share fili a daji ya tsugunna ya yi fitsari ko kashi.

    Akasarin irin wajejen nan aljanu ne suka yi jinya suka warke suka tashi a wajen don haka sai a kiyaye. Akwai waɗanda suke mu’amalantar mu a cikin gida, waɗanda su suke zama a cikin gida kamar yadda muke zama, haka kuma wasu daga cikinsu a hanya muke gamuwa da su, su rako mu har gida. Shi yasa musulunci ya koyar da mu addu’ar da za mu yi in za mu shiga gida da in za mu fita. Ya kamata in za ka bar gida sai ka ce;

    “Bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala ƙuwwata illa billah, allahumma inni a’uzhu bika an adilla aw udilla, aw azilla aw uzalla, au azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya”

    Sannan in za ka shiga gida sai ka ce;

    “Bismillahi walajna, wa bismillahi kharajna wa’alal lahi rabbana tawakkalna”

    Amfanin addu’ar nan shi ne ko da aljanu sun biyo ka gida idan ka karanata wannan addu’ar za su ga babu ƙofa a gidanka, ba wurin zama sai su koma. Idan kuma ka yi sakaci wurin karanta ta, to za ka ga ka shiga gida cikin damuwa, da ƙunan rai da tashin hankali da jin haushin mutanen gidan. Daga lokacin shi kenan sun sami abinda suke so, ka yi ta faɗa da mutanen gida. Shi yasa musulunci ya koyar da mu hatta abinci in za ka ci ka ce bismillah, Allah ba zai ba su ikon su sa hannu su ci ba. In kuma ka gama cin abincin sai ka karanta wannan addu’ar;

    “Allahumma barik lana fi hi wa ta’amna khairan minhu”

    Idan ka yi wannan addu’ar Allah zai ba ka lada sannan kuma ya sa wa abincin da za ka ci albarka.

    Hatta kaya idan za ka cire, musulunci ya koyar da mu addu’a da ya kamata ka yi don ka samu kariya daga sharrin aljanu da sheɗanu. Don haka in za ka cire kayanka ka ce “bismillah” Allah zai rufe idanun aljanu ba za su ga tsiraicinka ba. Haka ɗakin da ya dade a rufe hatsari ne a shiga ba tare da an yi addu’a ba. Ko da shimfiɗa ce aka gyara ta domin a kwanta, musulunci ya koyar da mu ka karkadɗeta sau uku sannan ka yi addu’a ka kwanta. Kuma mu kiyaye zama a kofar ɗaki don wannan ma wurin zamansu ne.

    Sai a kiyayi zubar da ruwan zafi a makwarara, saboda nan ma wajen zamansu ne. Kuma a kiyayi zama a cikin ɗaki mai duhu da kuma yin surutu a bayi da zama kai ba ɗankwali da jiki a bude. Sai mu raba kanmu da yawan kalle-kalle marasa amfani ko jin kade-kade. Sannan uwar gida ki tattare kayanki da zarar magariba ta doso kai, ki killace yaranki, ki hana su zama ba riga, sannan a rufe kwanukan da aka ci abinci har dai za a bar su a waje. Wannan duk musulunci ya koyar da mu ne don kulawa da kanmu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Kalolin Aljanu Suke danna koren rubutun nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Kowane Irin Ciwo danna koren rubutun nan.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Yadda Alamomin Jinnu Yake

    Yadda Alamomin Jinnu Yake

    Za mu ɗauki kaɗan daga cikin jinnu mu bayyana alamominsa da kuma magungunansa.

    Jinnul Gawas

    Waɗannan jinnu sun yi zamani da Annabi Suleiman (Alaihis Salam). Kamar yadda Allah (Subahanahu Wata’ala) ya faɗa a cikin Al Ƙur’ani mai girma a cikin suratus Saad, aya ta 37:

    “Wash shayaɗina kulla banna’in  wa gawwas”

    Akasarin wannan aljanun suna daɗewa a duniya kuma akasarinsu musulmai ne amma duk da yake akwai kafirai a cikinsu kaɗan. Kuma akasarinsu sun fi rayuwa a cikin ruwa ko cikin tafki ko kuma rijiya. Kuma sukan yawan shiga jikin yara.

    Alamominsu Jinnul Gawas :

    Mutum zai ji yana yawan zama a cikin bayi shi kaɗai, ko ka ga yana yawan wasa da ruwa ko kuma ya yi alwala sau da yawa ya ɗauka duk alwalar ba ta yi ba. Ko da tsananin sanyi ake yi shi zai iya yin wasa da ruwa ba tare da ya samu wata matsalar ba. Zai so ya rinƙa jiƙa jikinsa kuma za ka ga yana yawan wasa da dabbobi, ko kuma ya rinƙa yawan ganinsu a cikin mafarkinsa sannan a cikin barci zai dinga firgita ko ya rinƙa yawaita mafarkin kifi. Sannan wani lokacin idan ya yi tsanani, yakan kai da mutum yarinƙa faɗuwa.

    Hanyar Da Ake Bi A Magance Su

    Akan samu ruwa mai kyau tsaftatacce ko ruwan sama ko na rijiya sai a karanta surorin nan kamar haka, kowacce ƙafa ɗaya sai a tofa a cikin ruwan. Ga surorin kamar haka;
    • Suratul baƙarah
    • Suratul Yunus
    • Suratu dukhan
    • Ayatul azab wal ƙahar
    • Ayatul garaƙ wal bahar
    Waɗannan su za a tofa a cikin ruwa a ba shi ya sha da safe da yamma. Sannan akan so a ɗebi ruwan da aka yi wannan addu’ar ana dafa masa kifi da shi har sai ya samu lafiya. Sannan a karanta waɗannan ayoyin a cikin muski yana shafawa a ƙirjinsa da kansa. In Sha Allah zai samu lafiya.

    Jinnul Ashiƙ

    Wannan jinnu ya fi takurawa mutane, musamman mata, ko matan aure, ko bazawara, ‘yan mata ya hanasu aure, matan aure ya raba musu aure kuma bazawara ya daƙile duk abinda zai sa su yi aure. Shi jinnu ne da yake auran mace ya zame mata tamkar mijinta, in kuma tana da miji ya haramta mata duk wani jin daɗin aure ta zama kurum gata nan kamar hoto a gidan mijin. Duk da ana samun jinnul ashiƙa ta auri mutum, namiji ko da yana da aure ta cire masa son matarsa; zai iya shafe shekara da shekaru suna kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya amma ba tare da ya yi sha’awarta ba. Amma da ya kwanta sai wannan aljanar ta rinƙa zuwar mishi a cikin bacci yana mu’amalantarta ta zama tamkar matarsa. In kuwa aka yi rashin sa’a ta auri wanda bai taɓa yin aure ba; to in ba an yi da gaske ba takan zama matarsa ce har lokacin da zai bar duniya. Ta cire masa duk ƙaunar aure ko kuma ƙaunar wata mace ya gwammace ya yi ta zama a haka har ya bar duniya; ba ya so wani ya yi masa maganan aure shi kuma ba zai yi ba.

    Alamomin Jinnul Ashiƙ

    Mace ta rinƙa yawan samun faɗuwar gaba, yawan fushi ba gaira babu dalili; mace ta ji ta tsani kowa ko mijinta ba ta son gani, ta rinƙa keɓe kanta daga cikin mutane ta ji ta fi so ta rinƙa zama ita kaɗai. Ta rinƙa jin wasi-wasi a cikin zuciyarta ana raɗa mata mutuwa za ta yi; mace ta rinƙa ji kamar ta bar gidan da take zaune ko ta ƙwalla ihu, wata ma haka kawai za ka ga tana hawaye ko tana kuka ba tare da an mata laifi ba, ga yawan mafarkai daban-daban. Kamar mafarkin saduwa ko mafarkin taron biki ko mafarkin kin ɗau ciki; ko kuma ki yi mafarkin kin haihu ko ki yi mafarkin ga ki kina shayarwa. Wata ma za ta ga mijin nata a mafarkin babanta ne wata kuma ta ga yayanta ko wani mutumin da take jin kunyarsa; sai ta gan shi yana saduwa da ita. Wata kuma sai ta ga ga mata ‘yan uwanta suna saduwa da junansu tana kallo tana jin daɗi; ko ta ga maza suna saduwa da junansu tana kallo tana jin daɗi. Za ta ji daɗi a mafarkin in ana saduwa da ita amma in mijinta ya zo kusa da ita, sai ta ji kamar an sa mata wuta ta ji kamar an aiko mata mala’ikan mutuwa; duk yadda mijinki zai faranta miki ba ya burgeki, za ki ji ba kya son sa kwata-kwata, ba kya san ganinsa ko kaɗan. Abin lura a nan shi ne duk mafarkin da kika yi a gurin gaskiya ne. Domin karanta cikakken bayani akan Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu

    Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu

    Akwai hanyoyi da yawa wajen rabuwa da irin waɗannan aljanu da ma wasu ba irin wannan ba. Ya zama duk inda aljani yake ajikin mutum sai ya gudu ya bar shi.

    Matakan Rabuwa Da Jinnu: Matakin farko akan so mara lafiya ta cire duk wani hoto a ɗakin da take kwana sannan ta kiyayi yawan kalle-kalle. Sannan ta sabarwa kanta kwanciya da alwala, idan za ta iya yi wa kanta ta yi da kanta, in kuma za ta sa ne a yi mata shi kenan, abinda dai ake so a yi shi yadda ya kamata. Duk lokacin da za ta kwanta bacci bayan ta yi alwala sai ta karanta waɗannan ayoyin kamar haka; 1. Aya ta ɗaya zuwa goma cikin suratul Kahf 2. Sai kuma ƙarshen suratul Mu’minun 3. Aya ta 54 zuwa ta 56 a cikin suratul A’araf Sannan ta karanta wannan addu’ar kamar haka;

    “Allahumma inni auzhubika min su’i ahlami, wa’astajiruka min talaubish shaidan fil yaƙzati wal manami”

    In kika karantata shi kenan sai ki yi baccinki. In Sha Allah muddin za ki kikayi wannan shawarar ba ki da matsala.

    Haɗin Turare

    Wannan turare aljani ba ya sonsa, duk inda ka turara aljani ba zai so wajenba In Sha Allah. Hannit Lubazzakar Habbatussaud Tafarnuwa Kajiji

    Waɗannan su ne za a haɗa su guri ɗaya sai a rinƙa turarawa. In kika yi haka ba ke ba aljanu In Sha Allah.

    Daddawar batso Habbatus sauda Kajiji Kustul hindi Al-mum Su ma turarawa za ayi da yardar Allah aljani zai bar jikin mutum da kuma gida. Sannan za a samu ruwa mai kyau, an fi son na zam-zam in ba a samu ba sai a yi amfani da ruwan rijiya ko kuma ruwan sama, ya zamo dai ruwan mai tsafta ne. Sai a yi alwala a nemi za’afaran mansa ko kuma garinsa sannan a samu ma’ul wardi sai kuma jan muski kaɗan sai kuma a samu ganyen magarya a niƙa shi a zuba kaɗan a ciki sannan a karanta wannan ayoyin kamar haka kowacce ƙafa bakwai ana yi ana tofawa cikin ruwa ko kuma numfashin na sauka cikin ruwan.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Suratul Fatiha Suratul Baƙarah aya ta 1-5 Suratul Baƙarah aya ta 101-102 Suratul Baƙarah aya ta 255-256 Ƙarshen Suratul Baƙarah aya ta 273-277 Suratul A’araf aya ta 54-56 Suratul Yunus aya ta 90-92 Suratul Isra’i aya ta 109-111 Suratul Mu’minun aya ta 113-118 Suratul Kahfi aya ta 1-10 Suratul Saffat aya ta 1-11 Suratul Mulk Suratul Jinn Suratul buruj aya ta 1-3 Suratul Kafirun Suratul Ikhlas Suratul Falaƙ Suratul Nas Waɗannan ayoyin su za a karanta a tofa a cikin ruwan sai a ba wa mara lafiya tasha da safe kafin ta ce komai, ta shafe kanta da ruwan kaɗan, sai kuma da daddare kafin ta kwanta bacci ya zama shi ne ƙarshen abin da za ta sha ta kuma shafe jikinta gaba ɗaya.

    Sannan waɗannan ayoyin za a karanta su kamar yadda suke, a samo mayuka kamar haka;

    Man habba Man kwakwa Man alayyadi Man zaitun Jan Muski (ɗan kaɗan) Man ridi A haɗe su wuri guda a karanta waɗannan ayoyin a tofa a ciki ta rinƙa shafawa a jikinta musamman in za ta kwanta bacci. Duk irin taurin kai da aljani yake da shi to zai bar jikinsa da yardar Allah. Domin karanta cikakken bayani akan Hanyar Ƙona Aljani Ajikin Mutum danna koren rubutu. Domin karanta bayani akan Addu’a A Lokacin Da Mutum Ya Fitinu Da Wasuwasi A Cikin Sallah danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Nau’ikan Sihiri

    a. Akwai kurciya

    b. Dan baka

    c. Sihirul firaƙ

    d. Sihirul muhabba

    e. Sihirul jini

    f. Sihirul tasrif

    g. Sihirul sariƙ

    Wannan su ne nau’i kaɗan daga cikin nau’ikan sihiri. Kowanne kuma da yadda ake yin sa. Ana yin sihiri mace ta saukar wa da ‘yar uwarta jini, ta rinƙa yin jini a duk lokacin da mijinta ke ɗakinta. Ana yin sihiri uba ya ji ya tsani ‘ya’yan wata sai na ɗaya. A na ma mutum sihiri ya ga duk abinda ya samu ya ruguje, ka ga kana samu amma kuma abun yana rushewa. Kuma ana iya yin sihiri a hana budurwa aure. Sannan ana iya yin sihiri mace ta rinƙa warin jaɓa, saurayi ya zo wajenta ya ji tana wari.

    Ana yi wa yaro sihiri dan a lalata rayuwarsa, ya zama ɓarawo, ɗan iska ko kuma ɗan shaye-shaye. Koma dai wane irin sihiri ne. Allah bai taɓa yin ciwo ba sai da maganinsa.

    Akwai matakai da ake bi domin a karya sihiri. Wani sihirin za a iya yi da an karya shi sai ya dawo, wani kuma da an karya shi yake tafiya. Sakamakon rashin kariya ne da tun farko ba a yi ba shi yasa da an karya zai iya dawowa.

    Da yawan waɗanda sihiri ke jikinsu ba su cika yadda da cewa sihirin ne ba. Gane sihiri aka yi maka, harka nemi maganin karya shi da na kariya shi ma arziki ne. Ga matakan da ya kamata ka ɗauka wajen maganin kariya yadda duk wani sihiri ba zai kamaka ba da kai da iyalanka, haka tsafin mai tsafi ba zai kamaka ba. Ko da mutum yana magana yana fitar da wuta a bakinsa saboda sihiri, to da yardar Allah ka fi ƙarfinsa. Sai dai a ganka ana faman duka amma ka kasa faɗuwa, ka zama shagwan mada. A kan yi amfani da ayoyi guda 33 a cikin Al-Ƙur’ani domin neman kariya daga sihiri.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Za ka karanta su ne bayan fatiha Suratul baƙarah aya ta 1-5 Ayatul kursiyyu aya ta 255 Amanar rasul zuwa ƙarshen surar Suratul A’araf aya ta 54-56

    Sannan ka karanta;

    “ƙulid’ullaha awid’ur rahman, ayyam ma tad’u falahul asma’ul husna, wala tajhar bi salatika wala tukhafit biha wabtagi baina zalika sabila”

    Har zuwa ƙarshen suratul Isra’i

    Da kuma suratus safat aya ta 1-11 Da suratur rahman aya ta 33-35

    Sannan ka karanta;

    “lau anzalna hazal ƙur’ani ala jabalin lara’aitahu khashi’an mutasaddi’an min khashyatillah, wa tilka amthalu nadribuha linnasi la’allahum yata fakkarun”

    Zuwa ƙarshen suratul hashri

    Da surar jinn aya ta 3-9 Sannan suratul buruj aya ta 20-22

    Waɗannan ayoyin akan samu ruwan rijiya ko na zam-zam ko ruwan sama a karanta su kowacce ƙafa bakwai a tofa a cikin ruwan, a sa za’afaran ko na mai, ko na gari, ko kuma na ciyawa. Sai a rinƙa ɗiba kaɗan ana sha da safe da kuma in za a kwanta. Za kuma a iya karanta su a tofa a cikin man zaitun da man habba da man kwa-kwa ko na riɗi, a rinƙa shafawa a jiki. Mutum zai iya shafawa da iyalansa gaba ɗaya. Muddin kai da iyalanka za ku rinƙa shafa wannan addu’ar, ba wani tsafin mai tsafi ko sihirin mai sihiri da zai yi tasiri a jikinka insha Allah. Sannan wannan addu’ar ka karanta ta a gidanka kullum da safe, Ubangiji zai ba iyalanka da gidanka kariya daga dukkan sharrin mutum da aljan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kariya Daga Hassada, Maita, Da Sharrin Aljanu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa

    Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa

    Wannan addu’ar mutum yakan yi ta idan ya shiga cikin damuwa ko ya shiga cikin wani hali, ko tashin hankali; ya rasa yadda zai yi sai ya lazimci karanta wanan addu’ar. Allah zai fidda shi daga cikin wannan tashin hankalin da damuwa.

    An ruwaito daga Imam Ali Hassan Shazah, yana koyawa almajirinsa wannan addu’ar. Ga ta kamar haka;

    “Ya wasi’u ya Aleem, ya zal fadlul azeem, wa in tamsasni bi durrin fala kashifa lahu illa anta, wa’in turidni bi khairin fala raadda bi fadlik, tusibu man tasha’u min ibadak wa antal gafurur rahim”

    Akan so duk lokacin da ka yi salla ko ka yi wani aikin alkhairi ka karanta wannan addu’ar, Ubangiji Allah zai yaye maka damuwarka In Sha Allah. Ansamo wannan addu’ar daga littafin MAFATIHUL FARAJ shafi na 110. Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kyautata Tsakanin Ka Da Ubangiji Da Neman Gafara dannna koren rubutu. Don karanta Addu’a Gatan Mumini danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Addu’o’in Tashi Daga Barci

    Addu’o’in Tashi Daga Barci

    “Alhamdu lillaahil- lazii ahyaana ba’ada maa amaatanaa wa’ilaihin nushuuru”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya ɗauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi yake}.

    Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya farka da daddare yace:

    “Laa’ilaha illallahu wahdahu la shariikalahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun. Subhanallahi wal hamdu lillaahi walaa ilaaha illallahu Allahu akbaru walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil laahil aliiyil aziimi, Rabbigfirlii”.

    {Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma shi Mai iko ne a bisa komai, Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, Maɗaukaki, mai girma Ya Ubangijina! Ka gafarta mini}.

    Wanda ya faɗi wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu’a za a amsa masa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a karɓi sallarsa.

    “Alhamdu lillaahil lazii afaani fii jasadii waradda alayya ruuhi wa’azina lii bi zikrihi”

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ba ni lafiya a jikina, kuma ya dawo min da raina, kuma ya ba ni izinin ambatonsa}.

    “Inna fii khalƙis- saamaawati wal ardhi wakhtilaafil laili wannahari la ayaatil li ulil albaab allaziina yazkurunallaaha ƙiyaaman waƙu’udan wa alaa junuubihim wayata fakkaruuna fii khalƙis- samaawati wal ardhi rabbanaa maa khalaƙta hazaa baaɗilan subhaanaka faƙinaa azaban naari rabbanaa innaka man tudkhilun nara faƙad akhzaitahu wamaa liz zaalimiina min ansaari rabbanaa innanaa sami’ina munaadiyan yunadii lil imani an aminuu bi rabbikum fa’amanna rabbanaa fagfirlanaa zunuubanaa wa kaffir annaa sayyi’ atinaa watawaffanaa ma’al abraar rabbanaa wa atinaa maa wa’adtanaa alaa rusulika walaa tukhzina yaumal ƙiyaamati innaka laa tukliful mii’ada fastajaaba lahum rabbuhum annii laa udhi’u amala amilin minkum min zakarin au ansaa ba’adhukum min ba’adhin fallaziina haajaruu wa ukhrijuu min diyaarihim wa uzuu fii sabiili waƙaataluu wa ƙutiluu la’ukaffiranna anhum sayyi’ atihim wala udkhilannahum jannatin tajrii min tahtihal anhaaru laziina kafaruu fil bilaadi mataa’un ƙaliilun summa ma’awaahum jahannamu wa bi’isal mihaadu laakinil laziina taƙau rabbahum lahum jannatun tajrii min tahtihal anhaaru khaalidiina fiihaa nuzulan min indil laahi khairun lil abraar wa’inna min ahlil kitaabi laman yu’uminu bil laahi wamaa unzila ilaikum wamaa unzila ilaihim khaashi’ina lillaahi laa yashtaruuna bi ayaatil laahi samanan ƙaliilan ulaa’ika lahum ajruhum inda rabbihim innal laaha sari’ul hisaabi yaa ayyuhal laziina aamanuus biruu wa saabiruu wa raabuɗuu Wattaƙullaaha la’allakum tuflihuuna”.

    (Ali imrana, aya ta 190 zuwa ƙarshen surar)

    {Haƙiƙa a cikin halittar sammai da ƙassai, da saɓawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma’abota hankula. (su ne) waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingiɗe, suke kuma tunani a kan halittar sammai da ƙassai (suna cewa):

    “Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa kai, duk wanda ka shigar da shi wuta, babu shakka ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu mataimaka. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa; ku yi imani da Ubangijinku. Sai muka yi imani.

    To ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun ayyukanmu, ka kuma karɓi rayukanmu tare da mutane nagari. Ya Ubangijinmu! Ka ba mu abin da ka yi mana alƙawari da shi a kan harshen manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alƙiyama. Haƙiƙa, kai ba ka saɓa alƙawari.

    Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa); Haƙiƙa, Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace sashinku daga sashi yake.

    To, waɗanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaƙi, kuma aka kashe su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah.

    Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai- koman waɗanda suka kafirta a cikin garuruwa ta ruɗe ka. Jin daɗi ne ɗan ƙanƙani; sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da wannan makwanta.

    Amma, waɗanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fi ga managarta, kuma haƙiƙa akwai daga ma’abota Littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar.

    Zuwa gare su, suna masu ƙanƙan da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da ɗan tamanni ƙanƙani. Waɗancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Haƙiƙa Allah mai hanzarta hisabi ne. Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi haƙuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin haƙuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta}.

    (Ali Imran, 190 zuwa ƙarshen surar).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.