Category: Addu’o’i

Mun samar da wannan ɓangaren ne, domin samar da Addu’o’i na addinin musulunci a harshen Hausa kuma a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hannu cikin sauƙi.

WikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara.

Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koyo ko koyarwa.

  • Addu’o’in Kiran Sallah

    Addu’o’in Kiran Sallah

    Wanda ya ji kiran sallah zai faɗi dukkan abin da ladanin yake faɗi, sai dai idan ya ce:

    “Hayya alas-salaati (da) Hayya alal falaahi”.

    {Ku taho ga sallah; ku taho ga babban rabo}.

    A maimakon haka sai shi ya ce:

    “Laa haula walaa ƙuwwata illaa bil-laahi.

    {Babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah}.

    Bayan ladanin ya yi kalmar shahada, sai shi kuma (mai sauraron) ya ce:

    “wa’ana Ashhadu an laa ilaaha illallaahu wahdahu laa shariika lahuu wa’anna Muhammadan abduhu warasuuluhu, radhiitu bil-laahi Rabban, wabi Muhammadin Rasuulan wabil Islaami diinan”.

    Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam). Sannan kuma sai ya ce:

    “Allaahumma Rabba haazihid da’awatit tammati was-salaatil ƙaa’imati ati Muhammadan wasiilata wal fadhilata wab’as’hu maƙaaman mahmuudal lazii wa’adtahu innaka laa tukhliful mii’adi”.

    {Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita, ka ba wa Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) wasila (matsayin kusanci a Aljanna), da Matsyin fifiko, kuma ka tashe shi a matsayin abin godewa, wannan wanda ka yi masa Alƙawarinsa. Lalle kai ba ka saɓa Alƙawari}.

    Sannan ya yi wa kansa addu’a a tsakanin kiran sallah da tayar da iƙama, domin addu’a a wannan lokaci ba a ƙin karɓar ta.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a A Yayin Sujjada danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya Yi Bayan Ya Tafi Sujudah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Lokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a

    Lokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a

    Yana cikin kamala da girman karamci da rahamar Allah ya sanya a kowanne lokaci dare da rana bawa ya fuskanci Allah yayi addu’a za’a amsa masa.

    Tare da akwai wasu lokuta da gurare waɗanda Allah jalla wa’alaa ya albarkacesu da daraja ta musamman, wanda addu’a acikinsu keda tasiri na musamman. Ga wasu daga ciki:

    1. Addu’a ranar Arafah.

    2. Addu’a a Lailatul ƙadr.

    3. Addu’a akashi daya cikin ukun karshen dare.

    4. Addu’a bayan tahiyar karshe.

    5. Addu’a a cikin sujjadah.

    6. Addu’a tsakanin kiran Sallah da Iƙama.

    7. Addu’a yayin saukar ruwan sama.

    8. Addu’a ranar juma’a.

    9. Addu’a yayin shan ruwan zam-zam.

    10. Addu’a yayin da ake kiran sallah

    11. Addu’a yayin tashi daga bacci.

    12. Addu’a a kwanaki goman farko na Dhul-hijjah.

    13 .Addu’a a cikin ka’abah.

    14. Addu’a yayin gama karatu ko karantarwa.

    15. Addu’a yayin da mayaƙa sukayi sahu.

    16. Addu’a a majalissan da ake ambaton Allah.

    17. Addu’a yayin da imani ya ƙaru a zuciya.

    18. Addu’a bayan zare ran mamaci.

    19. Addu’a yayin jifan jamraat.

    20. Addu’a akan dutsen safa.

    21. Addu’a akan dutsen marwa

    22. Addu’a a mash’aril haram.

    23. Addu’a yayin ziyarar marar lafiya.

    24. Addu’a gabannin sallar azzahar.

    25. Addu’a a watan Ramadhan.

    26. Addu’a yayin sahur ga mai azumi.

    27. Addu’a yayin buɗa-baki ga mai azumi.

    28. Addu’a yayin shiga tsanani, matsi da ƙunci.

    29. Addu’a da addu’ar zun-nun Alaihis salaam.

    30. Addu’a da Istirja’i.

    31. Addu’a a multazam.

    32. Addu’a a Makam Ibrahim.

    33. Addu’a yayin karatun suratul fatiha.

    34. Addu’a yayin ƙarfafuwar Mahabbah da Ikhlasi a zuciya.

    35. Addu’a yayin carar zakara.

    Duba:

    1. Du’aa na Dr. Yassir Qadhi

    2. Addu’a wa Manzilatahu Minal Aqidatil Islamiyyah na Dr. Jilan Alarusiy wanda rubuntunsa ne, na Masters Degree kulliyatud da’awah, Qismul Aqidah a Jami’atul Islamiyyah Madinatul Munawwarah a shekarar 1410A.H.

    3. Ahmiyyatud Du’a wa Kaifiyyatahu fis Sunnatin Nabawiyyah na Dr.Ibrahim al-Hamd.

    Domin karanta cikakken bayani akan Alkunyar Da Ake Wa Manzon Allah (S.A.W) danna koren rubutun nan.

  • Addu’a A Yayin Sujjada

    Addu’a A Yayin Sujjada

    “Subhaana Rabbiyal a’alaa”.

    {Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka}. Sau uku (3).

    “Subhaanakal laahumma rabbanaa wa bihamdika Allaahummagfir lii”.

    {Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu! Tare da godiya gare ka. Ya Allah! Ka gafarta mini }.

    “Subbuhun ƙuddusuun Rabbul Mala’ikati war ruuhi”.

    {(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kuɓuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala’iku da Jabrilu}.

    “Allaahumma laka sajadtu wa bika aamantu, walaka aslamtu sajada wajhii lillazii khalahu wa sauwarahu wa shaƙƙa sam’ahu wa basarahu tabaarakal laahu ahsanul khaaliƙiina”.

    {Ya Allah! Gare ka na yi sujada, kuma da kai na yi imani, kuma gare ka na miƙa wuya. Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta. Kuma ya yi mata sutura, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita}.

    “Subhaana zil jabaruuti, wal malakuuti, wal kibriyaa’i, wal azamati”.

    {Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da ƙasaitar ɗaukaka da girma}.

    “Allaahummagfil lii zanbii kullahu, diƙƙahu wa jillahu, wa auwalahu wa akhirahu wa alaaniyatahu wa sirrahu”.

    {Ya Allah! Ka gafarta min zunubaina dukkanninsu, ƙanananansu da manyansu, na farkonsu da na ƙarshensu, bayyanannunsu da ɓoyayyunsu}.

    “Allaahumma inni a’uzu bi ridhaaka min sakhaɗika, wabi mu’aafaatika min uƙuubatika wa a’uzu bika minka, laa uhsii sanaa’an alaika anta kamaa asnaita alaa nafsika”.

    {Ya Allah! Ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da kuma rangwamanka daga uƙubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare ka. Ban isa na tuƙe ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda ka yabi kanka ne}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Ruku’u danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a A Lokacin Da Mutum Zai Hau Abin Hawa

    Addu’a A Lokacin Da Mutum Zai Hau Abin Hawa

    Bismil laahi wal hamdu lil laahi subhaanal lazii sakkhara lanaa hazaa wamaa kunnaa lahu muƙriniina wa innaa ilaa rabbinaa lamunƙalibuuna, alhamdu lil laahi, alhamdu lil laahi, alhamdu lil laahi, Allaahu akbar, Allaahu akbar, Allaahu akbar, subhaanakal laahumma innii zalamtu nafsii fagfirlii fa’innahu laa yagfiruz zunaaba illaa anta”.

    {Da sunan Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Tsarki ya tabbata ga (Ubangiji) wanda ya hore mana wannan (abin hawa); ba mu kasance masu ikon sarrafa shi ba. Haƙiƙa mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Allah ne mafi girma. Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah! Haƙiƙa ni na zalunci kaina, ka gafarta min, domin babu wanda yake gafarta zunubai sai kai}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Idan Mutum Zai yi Tafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa danna nan.

    Edita; RMK

  • Yadda Ake Addu’ar Shiga Kasuwa

    Yadda Ake Addu’ar Shiga Kasuwa

    Addu’ar Shiga Kasuwa – “Laa ilaaha illallaahu wahdahu laa shariika lahu, lahul mulku walahul hamdu yuhyii wa yumiitu wahuwa hayyun laa yamuutu bi yadihil khairu wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun”.

    Fassarar addu’ar:

    {Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai; babu abokin tarayya a gare shi. Mulki nasa ne (shi kaɗai); Yana rayarwa, yana matarwa, kuma shi Rayayyene Wanda ba ya mutuwa. Dukkan alheri a Hannunsa yake, kuma shi Mai iko ne a kan komai}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Matafiyi Ga Mazaunin Gida danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan

  • Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi

    Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi

    “Alhamdu lil laahil lazii kasaani haaza (sauba) wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya tufatar da ni wannan (tufa); kuma ya azurta ni da ita; ba tare da wata dabara daga gare ni ba ko wani ƙarfi}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Da Ake Ma Wanda Ya Sanya Sabuwar Tufa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci

    Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci

    Allaahumma baarik lahum fimaa razaƙahum, wagfir lahum warhamhum”.

    {Ya Allah! Ka albarkance su a cikin abin da ka azurta su da shi, kuma ka gafarta musu, ka ji ƙansu}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Alhamdu lil laahil lazii aɗ’amanii hazaa wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da ni wannan (abincin); ya azurta ni da shi, ba tare da wata dabara ko ƙarfi daga gare ni ba}.

    Allamdu lil laahi hamdan kasiiran ɗayyiban mubaarakan fiihi gaira makfiyyi walaa muwadda’in walaa mustagnan anhu Rabbunaa“.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sanya albarka a cikin sa; (Allah) wanda ba a ɗauke masa azurta bayinsa, kuma ba a rabuwa da shi (a bar nema daga wurinsa), kuma ba a wadatuwa ga barinsa; shi ne Ubangijinmu}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Shiekh Sa’id Ibn Ali Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane

    Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane

    Afɗara indakum saa’imuuna wa akala ɗa’aamakum abraaru; wasallat alaikumul mala’ikatu“.

    {Allah ya sa masu azumi su yi buɗa baki a wajenku; kuma Allah ya sa nagartattun bayi su ci abincinku; kuma Allah ya sa Mala’iku su yi muku addu’a}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyar Da Mai Azumi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Da Ga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Zahabaz zama’u wabtallatil uruƙu, wa sabatal ajru in sha’allaahu”.

    {Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so}.

    Abdullah bin Amr bin Al- As ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Mai azumi yana da addu’a da ba a mayar da ita idan ya zo buɗe baki”. Abdullahi bin Amr ya kasance idan ya zo buɗa baki sai ya ce:

    Allaahumma innii as’aluka bi rahmatikal latii wasi’atu kulla shai’in an tagfiralii“.

    {Ya Allah! Ina roƙon ka saboda rahamarka da ta yalwaci komai, ka gafarta mini}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.