Author: Khadija Yusha’u (Amira)

  • Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi

    A yau za mu koyi yadda ake biskit cikin sauƙi

    Abubuwan da ake bukata

    1. Fulawa   2cups
    2. Bota  1/2cup
    3. Baking powder 1tspn
    4. Icing sugar 1,1/2
    5. Gishiri 1tspn
    6. Madara  1tspn
    Yadda ake haɗawa
    1. A tankaɗe fulawa a kwano daban
    2. Sai a zuba mata icing sugar a ciki
    3. Sannan a zuba gishiri da baking powder a ciki
    4. Sai a zuba bota a ciki, a juya su, har sai sun haɗe jikinsu
    5. Sai a zuba madara a kai, a ci gaba da cakuɗa su, har sai sun haɗe jikinsu.
    6. Sai a sa a kan faranti a bubbuɗa shi.
    7. Sannan a kawo abu mai faɗi, amman rawun dai-dai girman da ake so
    8.  A yayyanka sai a sa a tsinke (thooth pick) a ɓuɓɓula samansa, sannan a gasa.

    Domin karanta yadda ake yogurt ko ice cteam custard danna nan

  • Yadda Ake Yogurt

    Yadda Ake Yogurt

    Yogurt na ɗaya daga cikin abin sha mai lafiya kuma mai matuƙar amfani a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Madarar gari
    • Ruwa
    • Nono
    • Filebo
    Yadda ake haɗawa
    1. A ɗora ruwa a kan wuta ya tafasa
    2. Sai ki zuba madarar gari a kwano daban, ki zuba mata ruwa ki kwaɓata
    3. Sai  ki juye a kan tafashasshen ruwan dake kan wuta
    4. A bar shi ya yi kamar minti biyar a kan wutar yana tafasa
    5. Sanna a sauke a bar shi ya dan sha iska, sai a zuba nono cokali biyu a kai, amma kar a juya.
    6. A bar shi ya yi awa takwas a ajiye.

    Domin karanta yadda ake danbun shinkafa ko yadda ake kunun zaki

  • Yadda Ake Tuwon Shinkafa

    Yadda Ake Tuwon Shinkafa

    A yau za mu koyi yadda ake tuwon shinkafa.

    Tuwon shinkafa abinci ne da ake yin sa da shinkafa, wanda ya kasance abincin gargajiya na Bahaushe, wanda yake daɗi musamman ma idan aka tuƙa shi sosai.

    Abubuwan da ake buƙata:
    1-shinkafa ta tuwo(fara).
    2-ruwa.

    Yadda ake haɗawa

    • A wanke shinka fara, a zuba mata ruwa daidai wanda za ta shanye.
    • Sai a bar ta ta dahu, har sai ta shanye ruwan duka. Ta yi laushi sosai.
    • Sannan a tuƙa da muciya sosai. a mai da shi kan wuta, ya turara na ɗan wani lokaci, a sauke a malmala.
    Karin bayani.
    Idan ruwan ya yi kaɗan, kada a ƙara na sanyi. a sauke a ɗora wani ruwan, in ya tafasa, sai a ƙara a kai, a bar shi ya ɗan ƙara haɗuwa ko sannan a tuƙa.

    domin karanta yadda ake tuwon masara danna nan

  • Yadda Ake Ice Cream Custard

    Yadda Ake Ice Cream Custard

    Ice cream custard ya kasance abin sha mai daɗi, mai sauƙin sarrafawa, ba tare da shan wahala ba, mafi yawanci ice cream custard ya fi soyuwa a wajen yara ƙanana.

    Abubuwan da ake bukata
    1. custard,
    2. madara,
    3. vanilla flavour,
    4. sugar.
    Yadda ake haɗawa,
    1. ki dama custard da ruwan sanyi ki sheƙa ma da na zafi, ya yi kamar koko,
    2. ki sa madara mai yawa a kai, da filabo da sugar, ki juya su sosai, su haɗe jikinsu,
    3. ki bar shi ya huce, ki sa a fridge ki bar shi har dai ya yi ƙanƙara.

    Domin sanin yadda boga ko biredin kwakwa danna nan

  • Yadda Da Ake Stuffed Yam

    Yadda Da Ake Stuffed Yam

    A yau za mu koyi yadda ake stuffed yam. Stuffed yam abinci ne da  ake yin sa da doya, doya na ɗaya daga cikin abinci mai lafiya da gina jiki.

    Abubuwan buƙata,

    • Doya,
    • Niƙaƙƙen nama,
    • Albasa, koren tattasai, karas,
    • Ƙwai,
    • Mai
    • Maggi da kayan ƙamshi.

    Yadda ake haɗawa.

    1.  A soya albasa tare da mai, ki zuba mince meat, ki soya su tare da maggi da ɗan curry da thyme a ciki,
    2. Sai a zuba yankakken karas da green Korean tattasai a ciki,
    3.  Sai a fasa ƙwai guda ɗaya a kai, ki juya ya ɗan soyu kaɗan,
    4.  Sannan a kawo doyar da kika fere ki ka ƙwaƙule tsakiyarta,
    5.  Sai a ki zuba a cikin tsakiyar doyar ya cika. Ki sa wani siririn yankan doyar (slice) ki soka mata toothpick a jiki (amfanin toothpick a jiki  idan ta dahu kina ja zai cire, shi ne alamun dahuwar ta)
    6.  Sai ki turara ta kamar yadda ake turara dambu.
    7.  Idan ta yi sai a yanyanka.

    Domin karanta yadda ake sakwara ko boga

  • Yadda Ake Sakwara A Sauƙaƙe

    Yadda Ake Sakwara A Sauƙaƙe

    A yau za mu koyi yadda ake sakwara a sauƙaƙe.

    Sakwara abinci ne da ya samo asali  daga doya, doya na ɗaya daga cikin abincin da ke gina jiki.  Sakwara ta kasance mai daɗi, tana ɗauke da fibre da (starch) a  wanda ke ƙarawa jikin ɗan Adam kuzari.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Doya
    • Ruwan zafi

    Yadda ake haɗawa

    1.  A fere doya a yanka ta ƙanana, ki zuba ruwa kaɗan blending ɗinta,
    2.  Idan ta nuƙu sosai a ɗaura ta a kan wuta, tana dahuwa ana juya ta tare da muciya,
    3.  Har sai ta janye ruwan jikin ta, ta yi kamar tuwo, sai a ƙara ruwan zafi kaɗan a kuma tuƙawa.

    Domin karanta yadda ake Biredin kwakwa ko yadda ake tuwon masara

  • Yadda Ake Biredin Kwakwa (Coconut Bread Rolls)

    Yadda Ake Biredin Kwakwa (Coconut Bread Rolls)

    A yau za mu koyi yadda ake Biredin kwakwa (Coconut Bread Rolls), biredi ne wanda ake yin sa cikin sauƙi da kuma saurin haɗawa, kwakwa na ɗauke da sinadaran vitamins wanda ke ƙara kuzari da garkuwar jini a jikin ɗan Adam.

    • Yis
    • Siga
    • Coconut milk
    • Bota
    • Gishiri
    • Ƙwai
    • Madar gari
    • Fulawa
    • Ruwan ɗumi

    Yadda ake haɗawa:

    1. A hada yis da ruwan ɗumi kaɗan, a bar shi don tabbatar da kyan yis din.
    2. Sai a zuba coconut milk a kwano daban.
    3. A narka bota a zuba a kai, a zuba siga da ɗan gishiri kaɗan a juya su.
    4. Sannan a fasa ƙwai a kaɗa shi daban, a zuba a ciki.
    5. A ƙara madarar gari a kai, a juya.
    6. Sannan a tankaɗa fulawa a kai, a kwaɓa su, har su haɗe jikinsu, sai a kai rana a ajiye ya yi kamar minti goma sha biyar(15 mint)
    7. Sannan a ciro shi, ana gutsirar sa kaɗan-kaɗan, ana mulmula shi ya yi kamar ball.
    8. A shafa bota a saman shi don ya yi ƙyalli.
    9. Sai a gasa.

    Domin karanta yadda ake boga (Burger) ko tuwon masara

  • Yadda Ake Biredin Kwakwa (coconut Bread Rolls)

    Yadda Ake Biredin Kwakwa (coconut Bread Rolls)

    A yau zamu koyi yadda ake Biredin kwakwa(Coconut Bread Rolls) biredi ne wanda ake yinsa cikin sauki da kuma saurin hadawa, kwakwa na dauke da sinadaran vitamins wanda ke kara kuzari da garkuwar jini a jikin dan adam.

    Abubuwan da ake bukata

    1.       Yis
    2.       Siga
    3.       Coconut milk
    4.       Bota
    5.       Gishiri
    6.       Kwai
    7.       Madar gari
    8.       Fulawa
    9.       Ruwan dumi

    Yadda ake hadawa

     

    1.      A hada yis da ruwan dumi kadan a barshi don tabbatar da kyan yis din.

    2.      Sai a zuba coconut milk a kwano daban.

    3.      A narka bota a zuba a kai a zuba siga da dan gishiri kadan a juya su.
    4.      Sannan a fasa kwai a kadashi daban, a zuba a ciki.
    5.      A kara madarar gari akai a juya.
    6.      Sannan a tankada fulawa a kai a kwaba su har su hade jikin su, sai a kai rana a ajiye yayi kamar minti goma sha biyar(15 mint)
    7.      Sannan a ciro shi ana gutsirar sa kadan kadan, ana mulmula shi yayi kamar ball.
    8.      A shafa bota a saman shi don yayi kyalli.
    9.      Sai a gasa.
    Domin karanta yadda ake boga ko tuwon masara

     

  • Yadda Ake Boga (Burger)

    Yadda Ake Boga (Burger)

    Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girken mu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda ake burger.

    Abubuwan da ake buƙata:

    1.Fulawa
    2.Yeast
    3.Kwai
    4.Bota
    5.Dankalin Turawa
    6.Salad
    7.Ketchup
    8.Salad cream
    9.Nama
    10.Albasa
    11.Maggi
    12.Kayan ɗanɗano da kayan ƙamshi
    13.Tumatir

    Yadda ake haɗawa:

    • A hada fulawa da gishiri da yis, ki kwaɓa su da ruwan ɗumi,
    • Sai a kai shi  ƙarƙashin rana ya yi kamar minti ashirin,
    • Sannan a shafa wa gwangwanin gashin bota a jikinsa, sai a saka kwaɓin fulawar a ciki.
    • A gasa a abin gashi, ya gasu har dai bayan ya yi brown, a cire a raba shi biyu.
    • A dafa nama tare da albasa da maggi, a daka shi, sannan a soya shi sama-sama,
    • Za a yanka dankalin Turawa ƙanana, sai a dafa shi tare da ƙwai, a yanka ƙwan, amman a tsaitsaye,
    • Sai a ɗauko wannan biredin da aka gasa, a shafe shi da salad cream da ketchup, a ɗauko salad a sa a ɓari ɗaya na jiki, amma kar a yanka salad ɗin.
    • Sai a zuba nama, ƙwai, dankali da yankakken tumatir da albasa a kan salad ɗin nan, sai ki rufe da ɗaya ɓangaren.
    • Idan ana so, ana iya ƙara gasa shi sama-sama ko a ci a haka.
  • Yadda Ake Tuwon Masara

    Yadda Ake Tuwon Masara

    Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda ake tuwon masara.

    Masara na ɗaya daga cikin abincin Bahaushe, Wanda ake iya sarrafa ta ta hanyoyi da dama. Ta kasance abinci mai gina jiki da kuma ƙara lafiya. Masara na ɗauke da sinadaran daban-daban.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Masara
    • Ruwa.

    Yadda ake haɗawa:

    • Ki tafasa ruwa, ki kawo garin ki, kamar kimanin kashi ɗaya cikin uku na garin.
    • Sai ki zuba masa ruwan sanyi  ki juya, wannan shi ne rude.
    • Sannan kuma ki zuba cikin wannan tafashasshen ruwan ki juya.
    • ki bar shi ya dahu na kimanin mintuna sha biyar, sai ki tuƙa shi da sauran garin nan.