Author: Khadija Yusha’u (Amira)

  • Yadda Ake Miyar Alaiyahu Domin Ƙarin Lafiya

    Yadda Ake Miyar Alaiyahu Domin Ƙarin Lafiya

    Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girken WikiHausa. A yau za mu koyar da yadda ake miyar alaiyahu, kuma wannan miyar, za ki iya cin abubuwa da yawa da ita.

    Alaiyahu yana ɗaya daga cikin nau’in ganyayyaki girki, mai amfani da kuma lafiya a jikin ɗan Adam. yana da saurin narkewa a ciki kuma mai yawan cinsa yana hana kitse zama a ciki da kuma daidaituwar ƙiba a jiki.

    Abubuwan da ake buƙata
    1. Manja
    2. Albasa mai lawashi
    3. Kayan miya
    4. Naman rago
    5. Allayahu
    6. Kayan ɗanɗano
    7. Tafarnuwa
    8. Kayan ƙamshi
    Yadda ake haɗawa
    • Ki tafasa namanki tare da albasa, ki sanya kayan ɗanɗano.
    • Ki zuba manja a cikin tukunyar, sai ki yanka albasa, ki zuba naman ya soyu sama-sama, sannan ki zuba kayan miyan da ki ka niƙa.
    • Ki yi ta jujjuya shi, har sai ya soyu, saboda kar ya kama ƙasan tukunya, sannan ki zuba wannan ruwan tafashen naman a ciki.
    • Ki zuba kayan ɗanɗano. Sai ki yanka allayahu, Ki zuba allayahu ki juya idan ta dahu sai a sauke.
    Domin koyan Yadda ake dafa miyar agushi danna wannan koren rubutun.

     

  • Yadda Ake Haɗa Brownies Na Musamman.

    Yadda Ake Haɗa Brownies Na Musamman.

    Yadda ake haɗa brownies na musamman

    Abubuwan haɗawa
    1. Nutella
    2. Flour
    3. Kwai
    4. Melted chocolate
    Yadda ake haɗawa

    Farko za ki zuba cup flour a bowl, ki sa nutella ki fasa kwai 3, ki zuba ki yi mixing ki saka parchment paper, a kan baking tray sai ki zuba butter, ki gasa a oven for 5 minutes.

    Idan ya yi sai a bari ya sha iska.

    A yanka, a saka melted chocolate ko nutella lafiya.

    KU KARANTA Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo.

     

  • Yadda Ake Onion Sauce

    Yadda Ake Onion Sauce

    Abubuwan haɗawa

    1. Albasa
    2. Koren tattasai
    3. Taruhu
    4. Tattasai
    5. Kayan ƙamshi
    6. Maggi
    7. Kwakwamba (cucumber)
    8. Butter ko man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. Ki ɗauko albasa ki gyara, ki yanka ta ƙanana, sai ki wanke ki tsane shi a matsami. A ajiye a gefe, a ɗauko koren tattasai ki yanka, shi ma ajiye a gefe. A ɗauko taruhu, ki yanka ƙanana, a ajiye a gefe.
    1. Ki ɗaura non stick pan a kan wuta, ki sa butter, ki yanka albasarki, ki soya sama-sama; Sai ki ɗauko taruhu, ki sa ki soya sama-sama shi ma, sai ki ɗauko kayan ƙamshi ki sa, maggi (iya ɗanɗanon da zai miki). Sai ki ɗauko yankakken albasa (dama kin yanka ta da ɗan dama) ki sa.
    1. A nan, sai ki sa ruwan ɗumi kamar cokali 4 (tbsp) ki rufe na ɗan wani lokaci, har sai ruwan ya ragu.

    Sannan ki ɗauko koren tattasai da cucumber ki sa ki rufe, na ɗan wani lokaci har sai ruwan ya shanye sai ki sauke ki zuba a plate.

    Ku karanta Yadda Ake Vegetable Macaroni

  • Yadda Ake Miyar Agushi

    Yadda Ake Miyar Agushi

    A yau zamu koyi yadda ake miyar agushi

    Abubuwan da ake buƙata

    • Tumatir
    • Attaruhu
    • Tattasai
    • Albasa
    • Kayan ɗanɗano
    • Kayan ƙamshi
    • Nama
    • Agushi

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a wanke naman, a sa albasa da maggi a ɗora a wuta
    2. Idan ya yi, sai a kwashe a zuba mai da kayan miya da aka markaɗa a rufe.
    3. Sai a bar shi ya ɗan soyu, sai a zuba ruwan tafasashen nama a sa maggi, da gishiri,
    4. Da nama, da tafarnuwa, da agushi sai a rufe ya samu kamar minti biyar
    5. Idan ya yi, za a ji yana ƙamshi sai a sauke a ci da tuwon shinkafa
    6. A ci daɗi lafiya.

    Domin sanin yadda ake mini pizza danna nan

  • Yadda Ake Shinkafa Da Miyar Attaruhu

    Yadda Ake Shinkafa Da Miyar Attaruhu

    Shinkafa Da Miyar Attaruhu: Shinkafa da miyar attaruhu abinci ne da aka fi yawan cin sa da rana; musamman saboda gina jiki da kuma samar da kuzari…

    Kayan Haɗi:

    1. Shinkafa
    2. Attaruhu
    3. Albasa
    4. Koren tattasai
    5. Ƙwai
    6. Plantain
    7. Mangyaɗa

    Yadda Ake Haɗawa

    Da farko uwar gida za ki ɗora ruwa a wuta, idan ya tafasa sai ki zuba shinkafa. Idan ta yi rabin dahuwa, sai ki sauke ki wanke ta; ki tace ki mayar tukunya, kisa ruwa kaɗan yadda zai turara ta; amma fa kar ya yi yawa don ba a son shinkafar ta caɓe, sai ki rage wuta.

    Sai ki ɗauko attaruhu ki wanke ki jajjaga, sai ki sa albasa ita ma a yanka ta, yankan tsaye ki wanke ta; ki bar ta a kwando ta tsane, sannan ki ɗauko koren tattasai, ki yanka shi, ki ajiye a gefe.

    Sai ki ɗauko plantain ki ɓare, ki yanka ta, sai ki koma kan shinkafarki; idan ta turara sai ki sauke ki bar ta a tukunyar ta ɗan sha iska, kafin ki zuba a plaks,

    Sai ki ɗauko kasko ko tukunya ki zuba mai ki soya plantain ɗin nan ki ajiye a gefe. Sannan ki ɗauko tukunyar da za ki yi miyarki a ciki, ki zuba mai; idan ya yi zafi, sai ki sa albasa idan ta yi brown, sai ki zuba attaruhun da kika jajjaga da albasa da koren tattasan. Sai ki juya za ki iya sa farin maggi kaɗan idan kina so,

    Sai ki sa maggi mai star da sauran kalolin maggin da kike so, ki sa seasoning mai daɗi, sai ki zuba citta da kanunfari kadan; wanda dama already ana so mace ta dake citta, kanunfari, masoro, gyaɗar Yarbawa mai ƙamshi da tafurnuwa ta dake abinta, ta zuba a roba idan za ki yi jar miya ko jallop sai ki saka.

    To bayan kin zuba sai ki juya sosai, idan miyar ta soyu, sai ki rufe ki rage wutar ki bar shi zuwa minti ɗaya, da kin bude za ki ga miyar ta kwanta, kayan miyan sun haɗe jikinsu. Sai ki sauke ki ɗora ruwa, ki dafa ƙwai idan ya huce, sai ki ɓare shi, ki kwashe shinkafarki, sai ki zuba a plet; sai ki sa miyar a gefe ki zuba plantain ɗinma a gefe, sannan ki sa ƙwanki a gefe; ki ɗanyi musu decoration mai kyau. Shi kenan girkinki ya kammala sai ci.

    Domin karanta yadda ake Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal ko Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa danna nan.

  • Yadda Ake Scotch Egg

    Yadda Ake Scotch Egg

    Scotch egg abinci ne da ake yin sa daga ƙwai, yana da daɗin ci ga sauƙi wajen haɗawa, ƙwai na ɗaya daga cikin abincin dake ɗauke da sinadaran Vitamin D, leucine, isoleucine wanda ke taimakawa wajen gina jiki da ƙara ƙarfin ƙasusuwa.

    Abubuwan da ake buƙata

    Kwai
    Flower
    Baking powder
    Maggi
    Curry
    Gishiri
    Albasa
    Attaruhu
    Tattasai

    Yadda ake haɗawa

    1. Za a dafa ƙwai adadin yadda ake bukata
    2. sai a yanka albasa attarugu a sa maggi da gishiri a soya su sama-sama,
    3. sannan a kwaɓa fulawa da butter da ƙwai a murza da abin murza fulawa ko da abun murza taliya
    4. sannan a ɗauko ƙwan da aka dafa a yanka shi biyu da wuƙa
    5. sai a dinga yanka kwaɓaɓɓiyar fulawar nan, a dinga zuba soyayyen kayan miyanki a ciki sannan a naɗe da fulawa, bayan an naɗe, sai a kaɗa ƙwai a dinga ɗaukowa ana tsomawa a cikin ruwan ƙwai ana soyawa.
  • Yadda Ake Dashishi

    Yadda Ake Dashishi

    Dashishi abincin ne da ake yin sa daga alkama. Dashishi abincin gargajiya ne a Arewacin Nijeriya, yana da matuƙar lafiya a jiki, musamman ma a wajen masu ciwon siga kasancewar alkama na ɗaya daga cikin abincin masu ciwon siga.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Alkama
    • Gishiri
    • Mai
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A wanke alkama sosai, a fitar da dukkan harkakinta.
    2. Sai a surfa ta, watau a cire dusar alkamar, sai a bakace a wanke a sake shanyawa.
    3. Idan ta bushe sai a ɓarza ta, sai a ɗaura tukunya da madambaci sai a shimfiɗa buhu mai kyau, wanda aka wanke shi, amma fa buhun mai shara-shara.
    4. Wanke alkamar a tsane ta sosai, a zuba a cikin wannan buhun da aka shimfiɗa a cikin tukunyar.
    5. Sai a rufe da faifai a bar shi ya yi kamar 20mnts.
    6. Sai a sauke a wanke shi bayan an wanke, sai a yi mashi hadi a sa gishiri da albasa da mai idan dashishi da miya ce, sai a maida a tukunya ya ƙarasa dahuwa, za  a iya ƙara masa 15-20mnts za a ji ma yana ƙamshi, sai a sauke ya yi, sai ci.

    Domin karanta Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal danna nan.

  • Yadda Ake Koko

    Yadda Ake Koko

    Koko abinsha ne na karin kumallo na hausawa, wanda ake yin sa daga gero. Koko na da daɗin sha, ga matuƙar amfani a jiki.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    Gero
    Citta
    Barkono
    Kanunfari

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A jiƙa gero ya jiƙu sosai, sai a zuba citta, kanunfari da ɗan barkona kaɗan, sai a niƙa.

    2. Sai a tace shi da abin tata, a fitar da dusar da gasarar, sai a bar shi ya kwanta.

    3. A tafasa ruwa a kwano daban, kuma sai a ɗebi kwantacciyar gasarar nan, sai a ƙara mata ruwa a juya ta ɗan yi kauri kaɗan.

    4. Sai a sheƙa mata wannan tafashasshen ruwan zafin da sauri sai a motsa kaɗan.

    Domin sanin yadda ake burabusko danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Shayi Kala-Kala (TEA)

    Yadda Ake Shayi Kala-Kala (TEA)

    Yadda ake Shayin abarba

    Abarba
    bawon Abarba
    citta
    kaninfari
    ganyen shayi

    Yadda ake haɗawa:

    Ki ɓare abarbarki ki yanka kaɗan, ba da yawa ba, ki haɗa da ɓawon abarbarki, ki zuba a tukunya, bayan ya fi abarbar yawa, sai ki saka citta da kaninfarin da kika dɗan daddaka su ki saka Lipton, ki haɗa ki tafasa sosai, ki sa sugar sai sha.

    GORIBA TEA

    Goriba
    citta
    kaninfari
    ɓawon bayan lemon zaƙi
    Lipton

    Yadda ake haɗawa

    Za ki samu goriba irin ɓararriyar nan, wadda aka fidda ta daga jikin ƙwallonta, sai ki wanke ta, ki sa a tukunya, ki zuba citta Da kaninfari sannan ki samu ɓawon lemo, ki ɗan goga shi a ciki da abun goga carrot, amma fa kar ki cika da yawa, don ƙamshin muke buƙata kaɗan, sai ki saka Lipton Da dan sugar, ki barsu su yi ta dahuwa, sai ki bar shi ya dahu, sosai komai na jikin goribar ya futo sosai, wannan shayin na da daɗi sosai, kuma yana ƙara wa maza da mata lafiya ƙwarai da gaske.

    SHAYIN ƊANYAR CITTA DA LEMON TSAMI

    Danyar citta
    Lemon tsami
    Lemon grass
    kaninfari
    Na’ana,
    Lipton

    Yadda ake haɗawa

    Ki goga cittarki daidai misali ya danganta da yadda kike son yajinta, ki saka Lemon grass Da na’ana, ki yanka Lemon tsaminki gida biyu ki jefa a ciki, kisa Lipton da sugar ki tafasa sosai. In kina Da bukatar tsamin, kya iya matsa ruwan lemon tsamin in kin zo sha.

    CINNAMON AND HONEY TEA

    cinnamon (girfa)
    honey (zuma)
    citta
    kaninfari
    lemon grass

    yadda ake haɗawa:

    Ki zuba ruwa a tukunya ki zuba garin cinnamon ko wanda ba a niƙa ba, ki saka kaninfari Da citta Da Lemon grass, ki tafasa sosai, in ya dahu, ki zuba zuma ki bar shi ya yi ta tafasa, da ya tafasa sai ki sauke.
  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Kunun gyaɗa na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da amfani a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan da ake buƙata;

    Farar shinkafa

    Ɗanyar gyaɗa 

    Sugar daidai misali

    Yadda ake haɗawa

    A gyara farar shinkafa sai a wanke ta, a tsane tsaf. Bayan haka, a soya gyaɗa sama-sama a murje, bayan an bushe, sai a markaɗa, bayan an markaɗa a tace.

    Sai a zuba tataccen ruwan gyaɗar a tukunya, in ya tafasa, sai a ɗauko wanna shinkafar da aka wanke aka tsane, sai a zuba ta a ciki, su yi ta dahuwa har sai ta dahu sosai.

    Don gudun kada ya tsinke, za ki iya zuba ruwan lemon tsami kaɗan. Idan kuma an ga bai yi kauri ba, sai ki ɗan ɗibi gasarar koko a dama da ruwan sanyi sai a zuba a juya sosai zai yi kauri.

    Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa danna koren rubutun nan.