Author: Khadija Yusha’u (Amira)

  • Yadda Ake Yin Crepes Da Vegetable

    Yadda Ake Yin Crepes Da Vegetable

    A yau za mu koyi yadda ake crepes da vegetable. Crepes da vegetable abin ci ne da yake da matuƙar daɗi a wajen karin kumallo.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Fulawa
    • Ƙwai
    • Madara
    • Bakin powder
    • Maggi
    • Gishir
    • Cabbage
    • Carasrot
    • Koren tattasai
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A kwaɓa fulawa da ƙwai da butter da madara da baking powder, a sa maggi da gishiri kaɗan,
    2. A yi kwaɓin kamar za a yi wainar fulawa, amma kar ya yi ruwa kwaɓin
    3. Sannan a yanka vegetables a soya su a ajiye a gefe
    4. Sai a ɗora frying pan a sa mai kamar za a soya wainar fulawa, a zuba kwaɓin fulawar a ɗan rufe.
    5. Idan ya soyu a cire, sai a zuba kayan haɗin a ciki, a dinga naɗewa,

    Domin sanin yadda ake danbun nama danna nan

  • Yadda Ake Pancake

    Yadda Ake Pancake

    A yau za mu koyi yadda ake Pancake

    Abubuwan da ake buƙata

    flour kofi ɗaya
    •Sugar cokali 2
    •Baking powder babban 1
    •Ƙwai ɗaya
    •Madara ta ruwa ɗaya (ko ta gari ne za a iya saka 2-3 table spoon a dama da ruwa cikin gwangwanin madara ƙarami)
    •Butter/oil
    •Gishiri kaɗan

    1. Yadda ake haɗawa
      Cikin kwano mai faɗi, a haɗa tankaɗaɗɗen flour, sugar, bakin powder da gishiri.
    2. A fasa ƙwai cikin madara da cokali ɗaya na mai, a kaɗa a juye cikin flour, sai a dama shi.
    3. Idan ya yi ruwa sosai, sai a ƙara flour kaɗan, ana son kwaɓin ya fi na wainar fulawa/kalallaɓa kauri kaɗan.
    4. A saka cokali ɗaya na bota, a frying pan, in ya yi zafi, sai a ɗebe kwaɓin daidai misali a zuba, a yi faɗi da shi, kamar za a soya ƙwai, idan ya yi, sai a juya ɗayan ɓangaren.
    5. Haka za a yi ta ɗiba har ya ƙare.

    Domin sannin yadda ake danbun nama danna nan

  • Yadda Ake Dambun Nama

    Yadda Ake Dambun Nama

    A yau na zo mana da yadda ake haɗa dambun nama; na kaza ko dai na jan nama. Danbun nama na daga cikin abincin da ake samarwa daga nama. Yana da matuƙar daɗi.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Nama/kaza
    • Taruhu
    • Albasa
    • Tafarnuwa
    • Seasoning
    • Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a wanke nama, ko kaza, a zuba cikin tukunya, a zuba albasa da taruhu da tafarnuwa.
    2. A ɗora a wuta, a bar shi, ya yi ta dahuwa kamar awa 4/5 yana dahuwa.
    3. Idan an sauke, sai a raba shi da ƙashi da kitsensa, ko fata duka, a cire a mayar da tsokar a sa muciya a tuƙe shi, a sa seasoning da spices.
    4. Sai a zuba man gyaɗa har ya rufe naman a soya. Ba za a ɗaga ba, a na yi ana juya shi har ya yi.
    5. Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbatar ba sauran mai, sai a zuba cikin sieve ko colander. A ci lafiya

    Domin sanin Yadda Ake Egg Muffin danna nan

  • Yadda Ake Egg Muffin

    Yadda Ake Egg Muffin

    Egg muffins abinci ne da ake yin sa daga ƙwai; ƙwai na da matuƙar amfani. Egg muffin yana da daɗi a karin kumallo ko tarar baƙi.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Ƙwai Dafaffe
    • Dankali Turawa
    • Dafaffafen nama
    • Koren tattasai
    • Tarugu
    • Albasa
    • Maggi
    • Curry da thyme
    • Gishiri kaɗan
    • Butter Ko mai
    • Baking power

    Yanda ake haɗawa

    1. A yayyanka nama, albasa, taruhu da dafaffen ƙwan. Amma kar a sa dafaffen dankali
    2. A kawo Curry da thyme kaɗan a sa, A ɗauko Maggi na ruwa a sa (za a iya amfani da su ne normal Maggi). Sai a juye a ajiye a gefe
    3. A sami ƙaramin kwano a fasa kwai, a ciki sai a sa baking powder sai gishiri kaɗan Sai a kara juyashi
    4. A ɗauko muffin pan a shafa mishi mai ko butter
    5. Sannan ki ɗauko Dafaffen dankali (yankakke) kisa a ciki
    6. Sai a sa a cikin oven a gasa, har sai ya gasu (ya zama golden brown)
    7. Za a iya ci haka ko kuma a haɗa shi da soyayyen dankali Turawa. A ci daɗi lafiya

    Domin sanin yadda ake potato balls danna nan

  • Yadda Ake Potato Balls

    Yadda Ake Potato Balls

    Potato Balls abinci ne wanda a Hausance ake kiran sa da Ƙwallon dankali, wanda ake yin sa da dankalin Turawa. Yana da matuƙar daɗi musamman ma idan a karin kumallo za a ci shi.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Dankalin Turawa (irish)
    2. Taruhu
    3. Albasa
    4. Kayan Ɗanɗano
    5. Man gyaɗa
    6. Ƙwai
    7. Fulawa

    Yadda ake haɗawa

    1. Farko za a dafa dankali, har ya dahu sai a bari ya huce sannan a yi mashing ɗin shi, a kwashe.
    2. A daka taruhu da albasa a zuba, a saka spices da seasoning.
    3. A saka lawashi, sai a juya ko’ina ya haɗe. A dinga ɗiban wannan mixture ana yinsa kamar ƙwallo a hannun ana ajiyewa.
    4. Sannan a barbaɗa masa fulawa. Za a kaɗa ƙwai, a sa masa gishiri, a ɗaura tukunya, a zuba mai.
    5. Idan ya yi zafi, a na ɗauko wannan haɗin da aka mulmula kamar ball, a sa cikin mai, ana soyawa.

    A ci daɗi lafiya.

    Domin sanin yadda ake cabbege sauce danna nan

  • Yadda Ake Cabbage Sauce

    Yadda Ake Cabbage Sauce

    Cabbage sauce miya ce wadda ake yinta da kabeji da jajjagen kayan miya, tana da daɗi da lafiya a jiki musamman ma idan aka kula da tsabtace da kayan girkin.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Cabbage
    2. Green pepper
    3. Peas
    4. Green beans
    5. Taruhu
    6. Tattasai
    7. Seasoning
    8. Gishiri
    9. Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. Farko za a yi granding din taruhu da tattasai da albasa a yanka lawashi a ajiye a gefe.
    2. A yanka cabbage da green pepper su ma, a ajiye su gefe.
    3. Sannan a zuba man gyaɗa a tukunya, idan ya yi zafi, sai a zuba albasa a juya.
    4. A zuba taruhu da tattasai ana juyawa.
    5. Sai a ɗan rufe na mintina biyu sai a wanke veggies a zuba, amma ban da cabbage da albasa su ne na ƙarshe.
    6. A juya, a sa seasoning a sake rufewa.
    7. Za a buɗe idan ya dahu, sai a zuba cabbage da albasa.

    Ita wannan sauce ana ci da abubuwa da yawa, tun daga farar shinkafa, da chapati, Fateera, har ma su jollof rice.

    Domin sanin Yadda Ake Moi-moi danna nan

  • Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

    Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

    Moi moi wadda muka fi sani da alala a Hausance ana yinta ne daga wake, alala ta kasance ɗaya daga cikin abincin gargajiya na bahaushe.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Wake
    2. Taruhu da tattasai
    3. Albasa
    4. Maggi
    5. Tafarnuwa
    6. Manja
    7. Sausage
    8. Ƙwai
    9. Karas

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki wanke wake a surfa, sai a zuba taruhu da tattasai da albasa a niƙa shi ya yi laushi sosai.
    2. Sannan a zuba wannan haɗin a cikin bowl a sa manja, maggi, tafarnuwa, da curry, za a iya saka cray fish ma, a juya shi sosai komai ya haɗe.
    3. A saka mai kaɗan a kan kaskon, a sa sausage da karas a yi stir frying nasu, sai a sauke. A dafa ƙwai a ɓare shi a yanka slices. Shi ma a aje a gefe.
    4. Za a kunna oven 180° sai a ɗauko parchment paper a shimfiɗa ta a kan faranti na gashi, a zuba ƙullun a saka a oven.
    5. Bayan mintina 10 in ya fara yi, sai a sauko da shi a zuba fillings ko’ina, a mayar ya gama gasuwa.
    6. Idan ya yi, za a ji ƙamshin ya haɗe ko’ina a sa toothpick a duba.
    7. Don a tabbatar ya dahu, a sauke a naɗe kaman naɗin tabarma.

    A ɗan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya.

    Domin sanin Yadda Ake Zobo Na Cucumba dannan nan.

  • Yadda Ake Zoɓo Mai Cucumber

    Yadda Ake Zoɓo Mai Cucumber

    Zobo na ɗaya daga cikin abin sha wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci, sauko da hawan jini musamman ma idan aka haɗa shi da cucumber.

    Kayan da ake buƙata

    • Zoɓo
    • Cucumber
    • Bakin flavour
    • Kanunfari
    • Citta
    • Kimba
    • Sugar

     Yadda ake haɗawa

    1. A wanke zoɓon, sai a zuba ruwa a ɗora a wuta
    2. A zuba su cittar a gurza cucumber a zuba a ciki sai sun dahu sosai
    3. Sai ki sauke a tace, a zuba flavour masu daɗi da daɗin ƙamshi, in an ji zaƙin ya yi, to ba  sai an zuba suga ba.
    4. In kuma akwai bukatar a zuba, sai a zuba, sai a juya sosai, sai a ɗan ƙara ruwa daidai yadda ake so,
    5. A saka ƙanƙara a frige, sai a samu kofi mai ƙayatarwa a zuba.

    A sha lafiya.

    Domin karanta Yadda Ake Haɗa Lemon Tsamiya danna koren rubutu

  • Yadda Ake Banana Da Strawberry Smoothy

    Yadda Ake Banana Da Strawberry Smoothy

    A yau, za mu koyi yadda ake banana da strawberry smoothy.

    Banana da strawberry na ɗaya daga cikin ƴaƴan itatuwa masu lafiya a jikin ɗan Adam, suna ɗauke da vitamins da sinadaran pottasium, wanda suke tsarkake jini da ƙara kuzari a jikin mutum.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Ayaba
    • Strawberry
    • Ƙanƙara

    Yadda ake haɗawa

    1. A ɓare ayaba a yanka ta uku-uku,
    2. Sai a rarraba strawberry gida biyu,
    3. Sai a zuba a bilanda su nuku sosai.
    4.  A juye a kofi a sa ƙanƙara.

    Domin sanin yadda ake Egg French Toast danna koren rubutun nan

  • Yadda Ake Ice Cream Na Ayaba

    Yadda Ake Ice Cream Na Ayaba

    A yau za mu koyi yadda ake ice crem na ayaba.

    Ayaba na ɗaya daga cikin kayan marmari dake inganta lafiya, ayaba na ɗauke da sinadarin dake gina jiki na potassium.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Ayaba
    Chocolate syrup
    Madara ta ruwa
    Peanut

    YADDA AKE HAƊAWA

    A ɓare ayaba me kyau, a yanka ta daidai da daidai.
    Sai a zuba ta a bilanda, a zuba madarar, ruwa kaɗan ana nikawa
    Ana yi ana ƙara madarar kaɗan-kaɗan, har sai ta nuƙu sosai.
    Sai a kwashe a zuba a ɗan bowl, sai a yaryaɗa chocolate syrup a kai a zuba peanut.

    Domin sannain yadda ake yogurt ko biskit cikin sauki danna nan