Author: Khadija Yusha’u (Amira)

  • Yadda Ake Miyar Kuka

    Yadda Ake Miyar Kuka

    Ganyen kuka wanda da ita ake miyar kuka, na da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan Adam. Tana ɗauke da sinadarai da dama, waɗanda suka haɗa da ‘Vitamin C’, ‘Vitamin A’, ‘Beta Carotene’, ‘Potassium’, ‘Calcium’ da sauransu da dama.

    Waɗannan Sinadarai kuma na taimakawa wajen magance wasu matsaloli da cututuka kamar su tari, tsutsar ciki, ciwon ƙoda, ciwon asthma, sanyin dake taruwa a ƙirji da sauransu.

    Abubuwan da ake buƙata

    Kuka
    Attaruhu
    Daddawa
    Albasa
    Bandar kifi
    Nama
    Magi
    Man ja

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a ɗora ruwa a wanke nama, sai a yayyanka masa albasa da gishiri kadan. Sannan a rufe ya yi ta dahuwa har sai naman ya yi laushi sai a sauke a ajiye a gefe.

    2. A ƙara ruwa kaɗan a kan silalen romon naman, sannan a yayyanka albasa sai a daka daddawa a zuba da jajjagen attaruhu mai tafarnuwa.

    3. A wanke bandar kifi a zuba. Su yi ta tafasa har sai bandar ta dahu, sannan a zuba magi da manja a rufe su ƙara tafasa.

    4. Bayan haka, sai a zuba kuka kaɗan, a riƙa kaɗawa ko da maburgi ko cokali domin kada a samu gudaji a ciki. Sai a ɗan rufe bayan ya ɗan tafasa sai a sauke.

    Domin sanin Yadda Ake Fruit Salad danna nan

  • Yadda Ake Fruit Salad

    Yadda Ake Fruit Salad

    A yau za mu koyi yadda ake fruit salad; Fruit salad abin sha ne, da yake ɗauke da nau’ika daban-daban na kayan marmari. Yana da matuƙar amfani a lafiyar jikin ɗan Adam, ga daɗi wurin sha.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Ayaba
    2. Lemo
    3. Abarba
    4. Mangoro
    5. Sugar

    Yadda ake haɗawa

    Za a tsaftace kayan lambu a saka su a tire, sai a samu roba mai ɗan girma, a sa ruwa a ciki.

    Sannan a ɗauko wuƙa a fere ko a yanka kankana ƙanana. Sannan a ɗauko lemo a ɓare shi da wuƙa, a wanke shi. Sai a yanka kowane sala ana cire yayansa, da shi za a yi amfani.

    Sai a ɗauko sauran kayan fruits din su ma, a yanka su ƙanana, in an gama, sai a sa sugar a sa a fridge ya yi sanyi. In kuma ana da ƙanƙara sai a sa.

    Domin sanin Yadda Ake Prawn Cracker danna nan

  • Yadda Ake Colorful Prawn Crackers

    Yadda Ake Colorful Prawn Crackers

    A yau za mu koyi yadda ake Prawn cracker, Prawn cracker abinci ne da yara ke matuƙar so, yana da daɗin ci da sauƙin sarrafawa.

    Abubuwan da ake buƙata

    Mai
    Siga
    Madara

    Yadda ake haɗawa

    1- Da farko za a ɗora mai a kan wuta sai ya ɗau zafi sosai.
    2- Sai a ɗauko prawn crackers a buɗe, sai a dinga zubawa da kaɗan-kaɗan.
    3- Ana zubawa za a ga ya tashi fuuuu sai a kwashe a colander, sai a zuba sugar da madara.

    Domin sanin Yadda Ake Miyar Ƙoda danna nan

  • Yadda Ake Miyar Ƙoda

    Yadda Ake Miyar Ƙoda

    A yau za mu koyi yadda ake miyar ƙoda; Miyar ƙoda miya ce da ake iya cin shinkafa, taliya, da makamantansu. Ƙoda na da matuƙar amfani a jikin mutum.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Ƙoda
    • Mai
    • Maggi
    • Gishiri
    • Curry
    • Attaruhu da tattasai
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A zuba mai a tukunya kaɗan a saka albasa.
    2. A wanke ƙodar a zuba, sai a ɗan bar ta, ta yi ‘yan mintuna ruwanta su fito, sai a zuba maggi, curry.
    3. Idan ya tafaso sai a zuba yankakken karas da aka gyara, a bar shi ya dahu sai a sauke.

    Domin sanin Yadda Ake Kunun Aya danna nan

  • Yadda Ake Pride Gish & Irish potato

    Yadda Ake Pride Gish & Irish potato

    A yau za mu koyi yadda ake pride gish & irish potato,

    Abubuwan da ake haɗawa

    • Kifi
    • Dankali
    • Curry
    • Maggi
    • Mai
    • Attaruhu
    • Kayan ƙamshi
    • Kwai
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A fasa kwai a ajiye, sai a dafa dankali, in ya dahu sai a sauke, a ɗauko kifi da kayan ƙamshi da attaruhu, a daka su a turmi.
    2. Bayan an gama, sai a soya su a ɗauko wannan dankalin da aka dafa, a zuba a turmi a daddaka shi.
    3. Sai a zuba a wannan kwano da aka fasa ƙwai a ciki, a haɗa da wannan kifin da dankalin, a cakuɗa su, sai a ɗora mai a kan wuta, ki rinƙa mulmulawa ana soyawa har a gama.

    Domin sanin yadda kunun aya danna nan

     

  • Yadda Ake Kunun Kus-Kus

    Yadda Ake Kunun Kus-Kus

    A yau za mu koyi yadda ake kunun kus-kus, kunun kuskus na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da riƙon ciki. Kasancewar yana ɗauke da madara a cikinsa.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Couscous
    • Sikari ko zuma
    • Madara
    • Tufa
    • Ayaba
    • Flavour na banila

    Yadda ake haɗawa

    1. A sami madarar gari ko ta ruwa,
    2. Sai a kwaɓa ta da ruwa, ta yi tsululu sai a ɗora a kan wuta,
    3. Idan ta tafaso, sai a kawo kus-kus ɗin a zuba a ciki, a ringa juyawa domin kada ya dunƙule.
    4. Sannan idan an zuba, iya yawan da ake so, sai a ci gaba da juyawa har zuwa minti biyar.
    5. Idan ya dahu kuma, kaurin ya yi, sai a sauke daga kan wuta a zuba sikari,
    6. A yanka tufa da ayaba a saka sikari ko kuma zuma duk wanda ake so,
    7. Sannan a ƙara madara, a zuba flavour mai ƙamshin vanilla a juya.

    Domin sanin yadda ake kunun aya danna nan

  • Yadda Ake Kunun Aya

    Yadda Ake Kunun Aya

    Aya tana ƙara ƙarfin garkuwar jiki ga mai yawan amfani da ita. Aya tana inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita ƙuruciya, tana ƙarfafa yanayin gudanar jini, sannan tana ƙara kuzari na zahiri.

    Haka kuma Aya tana da amfani ga sha’anin da ya shafi ciki da hanji, tana ɗauke da sinadarin dake hana cushewar ciki da kuma kumburi. Har ila yau, tana taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral mara kyau a cikin jini.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Aya
    • Suga
    • Ɗanyar citta
    • Flavour
    • Kwakwa
    • Madarar ruwa
    • Dabino

    Yadda ake haɗawa

    1. A jiƙa aya ta jiƙu, a wanke ta, a saka kwakwa 1 da dabino kamar 7 ko 10, da citta ɗanya ko busasshiya, sai a niƙa.

    2. Sai a tace, a zuba madara a ciki, a sa suga da flavour a juya, a jefa ƙanƙara ko asa a fridge.

    Domin sanin Yadda Ake Spicy Meat danna nan

  • Yadda Ake Spicy Meat

    Yadda Ake Spicy Meat

    A yau za mu koyi yadda ake spicy meat. Spicy meat abin ci ne da ake yin yinsa da nama.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Nama
    • Mai
    • Tafarnuwa
    • Gishiri
    • Maggi
    • Curry
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa:

    1. A markaɗa ɗanyan nama mara kitse, tare da albasa curry maggi gishiri da tafarnuwa,
    2. Idan ana son attaruhu za a iya sawa, amma in ba a so ba dole ba ne.
    3. Sai zuzzuba a leda a ƙulle kamar alala, a zuba a tukunya a dafa idan ya yi kamar minti 30 a sauke.
    4. Sai a cire shi daga ledar, za a ga ya cure, sai a yi masa yankan da ake so, sai a fasa ƙwai a sa magi 4 a kaɗa, a dinga tsomawa a ƙwan, a na soyawa za iya ci da komai.

    Domin sanin Yadda Ake Alalan Shinkafa danna nan

  • Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa

    Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa

    A yau zamu koyi yadda ake alalan shinkafa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Shinkafa ta tuwo
    • Ƙwai
    • Nama
    • Hanta
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Magi
    • Gishiri
    • Curry
    • Main gyaɗa

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A wanke shinkafa a shanya ta, ta bushe a kai a niƙa ta.
    2. A tankaɗe a kwaɓa da ruwa kamar ƙullun alala, a jajjaga attaruhu a zuba a yanka albasa a zuba a yanka dafaffiyar hanta ƙanana a zuba, a daka dafaffen naman a zuba.
    3. A zuba dafaffen ƙwai da aka yanka, a zuba maggi da gishiri da curry a sa mai yadda zai yi.
    4. Sai a jujjuya a zuba a leda a dafa kamar alala, idan kuma na gwangwani za a yi, sai a zuba mai a jikin gwangwani a zuba ƙullun a turara shi, idan ya yi, sai a kwashe a zuba filas.

    Domin karanta Yadda Ake Faten Wake Da Doya ko Yadda Ake Tsaba Da Wake danna koren rubutu.

  • Yadda Ake Farfesun Dankalin Turawa Da Kaza

    Yadda Ake Farfesun Dankalin Turawa Da Kaza

    A yau za mu koyi yadda ake farfesun dankalin Turawa da kaza.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Kaza
    • Dankalin Turawa
    • Karas
    • Curry
    • Maggi,
    • Thyme
    • Tattasai
    • Tumatur

    Yadda ake haɗawa:

    1. A fere dankali a yanka ƙanana,
    2. Sai a wanke kaza a sulala ta da maggi, curry, gishiri, thyme, sai a jajjaga tattasai, da tumatur
    3. Idan ya sulala, sai a zuba yankakken karas, a zuba dankalin shi ma, a juya har zuwa lokacin da zai yi, Wannan girkin an fi yi da safe domin ai breakfast da shi.

    Domin sanin yadda ake creepes da vegitable danna nan