Adabi kalmar Larabci ce da ke nufin al’ada. Al’ada ta qunshi dukkan abubuwan da al’aumma ke yi waxanda suka haxa da ilimi, imani, fasaha, qere-qere, tarbiyya da sauran halayyen xan Adam (Talyor, 1871). Aristotle (384 – 322BC) al’ada madubin rayuwa ce.
Ubali (2021) Bahaushe na da al’adu ta jiyau da ganau. Jiyau ita ce al’adar da take cikin tunani, ko ake ji da kunne, kamar zumunci, kunya, faxa, kishi da sauransu. Ganau kuma ita al’adar da ake iya gani da ido, ko yi aikace da gavvan jiki, kamar tufafi, sa’ana, haihuwa da sauransu.
Domin Karanta Ma’anar Bahaushe Danna nan
Amma a nan, adabi ana nufi fasahar qirqira ta harshe cikin tsarin labari, waqe ko kwaikwayon rayuwar zahiri domin koyar da al’umma tsarin rayuwa mai kyau. Kafin zuwan rubutu suna adana adabinsu da baka, wannan dalili ya sa tarihi da adabin Bahaushe da yawa suka salwanta. Kafin zuwan rubutu qasar Hausa, Bahaushe na amfani da harshe wajen sadar da baka/ka (orature a Turance, oral + literature = ora(l litera)ture). Wasu kuma suna amfani da duma, fatun dabbobi, ko dutse, ko wata masaida a jikin mutum.
Amfanin adabin baka ga al’ummar Hausawa a wancan lokaci ana jiyar da yara tarihi, bada tarbiyya cikin labarun tatsuniyoyi, tarihi, tarihihi, hikaya, al’amara, karin magana, salon magana, take da qirari, zaurance, don yaxa martabar Hausa da xabi’unsu, ko wasa kwakwalwa da gagara gwari (tongue twister), nishaxi, gina tunani da falsafar rayuwar Hausawa duk da harshen Hausa (Xangambo, 2008).
Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan
Ta vangare waqa da kixa Bahaushe yana, mawaqa da makaxan fada (mis., Xankwairo), makaxan sana’a, makaxan jama’a (misali, Mamman Shata da Haruna Uji), makaxan maza (mis. Gambo Fagada), makaxan mata (mis. Barmana Coge da Mai Amada).
A wajen kixa Bahaushe na amfani da goge, kalangu, gurmi, kuntigi, garaya, tafi, qaho, jauje, gula, ganga, duman girke, kotso, tambari, kwarya, akayau da kayan bushe-bushe irin su algaita, qaho, kakaki, farai da sauransu (Gusau, 2008). Bahaushe yana da sauran waqoqi da yake a lokacin aikin gona, aikin gayya, yaqi, ko yara a wajen wasa, kamar ‘yargalala ta mata da sauransu. BAHAUSHE na amfani da kixi da waqa, ko waqe domin zuga, jinjina, qara qaimi, zambo, faxakarwa, ko isar da wani saqo.
Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan
Bahaushe yana wasan kwaiwayo na gauta da ake a fadar sarakuna, yana kwaikwayon hawan dokin kara, da tashe bayan zuwan addinin Musulunci don nishaxi da faxakarwa.