Miyar kayan ciki wadda aka fi sani da pepper soup; Wannan miya ana haɗa ta ne da kayan ciki kamar su hanji, hanta da dai sauransu.
Abubuwan Da Ake Buƙata Idan Za A Haɗa Miyar su ne:
- Tumbi
- Kitse
- Hanta
- Zuciya – huɗu
- Albasa
- Salt & maggi (abin ɗanɗano da gishiri)
- Markaɗe
- Tafarnuwa
- Masoro
- Girfa
- Habbahan
Kayan Aiki
- Murhu/Risho/Gas
- Tukunya
- Mazubi (mai tsafta)
- Cokali
- Abin daka
- Wuƙa
Yadda Ake Haɗawa
A sami tumbi da kitse da hanta da zuciya da huhu da kuma hanji, sai a sami ruwa a tafasa a ɗauko hanjin, sai a samu mutum biyu, ɗaya ya riƙe ɗayan gefen.
Sai a tsoma shi cikin ruwan zafi sai a sa wuƙa a kankare shi, sai ya yi haske, sai a yayyanka ƙanana, sai a wanke hanjin sosai a tabbatar ya wanku a tsane
Sannan a sa albasa da mai da gishiri da kuma maggi, za a ga ya yi ruwa, sai a sa markaɗe irin na farko, in ruwan ya yi kaɗan a ɗan ƙara a bar shi ya yi ɗan kauri
Daga ƙarshe, a ɗauko tafarnuwa a daka da masoro a jefa girfa a ciki da habbahan a juya in ta yi a sauke
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Miyar Agushi danna nan
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Haɗaɗɗiyar Miyar Gyaɗa. danna nan