Ga ta nan, ga ta nanku.
Kurege da Biri suka ga wata yarinya, kowannensu ya nuna yana son ta da aure. Sai kowannensu ya aika a tambayo masa izinin nemanta da aure. Iyayen yarinya suka ce duk wanda yake son ‘yarsu da aure sai ya kawo musu fatun namun daji. Da Kurege ya ji haka, sai ya je wurin Kaza ya ce da ita: “Ina gayyatar ki aiki a gonata gobe.”
Kaza na jin haka ta ce: “To, zan zo amma fa kada ka gaya wa Kyanwa.” Sai ya ce: “Haba me zai sa in gaya mata kuwa?” Daga gidan Kaza Kurege bai zame ko’ina ba sai gidan Mage, ya ce da ita: “Ina son za ki taya ni aiki a gona gobe.” Mage na ji sai ta yi farat ta ce: “To, amma fa kada ka gaya wa Kare, ka san idan ya gan ni a wurin zai cinye ni.”
Kurege ya ce da ita: “Haba, ai na san haka, wa zai gayyaci wannan a gonarsa?” Yana fita sai ya nufi gidan Kare, ya same shi ya ce da shi: “Ina so ka taya ni aiki a gona gobe.” Da gari ya waye, tun da sassafe Kurege da Kaza suka isa gona, suna cikin aiki sai ga Mage. Sai Kurege ya ce da Kaza: “Maza ki ɓuya a cikin ciyawa.”
Da Magenta isa kusa da Kurege sai ta ce: “Na ji kana magana kai da wane ne?” Sai Kurege ya ce: “Ni da Kaza ne, ga ta can a cikin ciyawa. Idan kin cinye namanta, ni ne da fata.” Nan da nan Kyanwa ta gano inda Kaza ta ɓuya. Tana ganin ta sai ta auka mata, ta murƙushe ta, ta kashe, ta cinye nama, ta ce da Kurege: “Ga fatar da ka ce kana so.”
Kurege da Mage suka ci gaba da aiki a gona. Jim kaɗan sai ga Kare, ya zo yana haki bayan ya yi gudun ceton rai, saboda yara sun bi shi za su kashe a hanya. Bayan Kurege ya yi wa Kare barka da zuwa, sai Kare ya ce: “Kurege kai da wane ne a gonar nan?” Sai Kurege ya matsa kusa da shi ya kashe murya ya ce: “Ni da Mage ne, tana can tana aiki.
Idan ka kashe ta, ka cinye naman, ka bar mini fatarta.” Kare ya yi godiya ya je ya shammaci Kyanwa ya turmushe ta, ya shaƙe wuyanta. Da ta mutu ya cinye naman, ya bar wa Kurege fatar. Sai Kare ya dubi Kurege ya ce da shi: “To amma fa ka san idan ka gaya wa Kura ba zan zo ba.” Kurege ya ce da shi, “Wa zai gaya wa Kura?
Me za a yi da wannan sarauniyar kwaɗayi?” Da Kurege ya fita bai tsaya ba sai a ƙofar ramin Kura. Bayan sun gaisa sai ya ce da ita: “Na zo gayyatar ki aiki ne a gonata gobe da safe.” Yana rufe baki sai Kura ta ce: “Kai ni gobe ba zan sami dama ba, zan je cin wani mushe da na gani jiya.”
Da Kurege ya ji haka sai ya ce da Kura: “Haba Kura, idan aka yi aikin gonata ba ki je ba, ai za a ce ni da ke mun ɓata. Kin san ke ce babbar ƙawata. Ki tuna fa mun sha yin abubuwa da yawa tare.” Wannan maganata Kurege ta yi wa Kura daɗi, sai ta dube shi ta ce: “To zan zo, amma fa kada ka gaya wa Damisa, ka san ta da nuna fin ƙarfi.”
Sai Kurege ya ce da Kura: “Me ya gama ni da Damisa kuma? Ban san inda take ba ma yanzu.” Da Kurege ya fita sai ya nufi dutsen da Damisa take tare da ‘ya’yanta. Bayan ya gayar da ita, sai ya ce mata: “Ranƙi ya daɗe, ina roƙon ki zo aiki a gonata gobe da safe, idan da hali. Kin san ku manya sai kun sami hali.”
Sai Damisa ta yi miƙa, ta buɗe bakinta, Kurege ya ga haƙoranta masu kaifi da tsini sai ta ce: “Kai Kurege wa ka gayyata bayan ni?” Sai Kurege ya yi durƙuson ban girma ya ce: “Kura dai tana ciki.” Da Damisa ta ji haka, sai ta ce: “Yawwa, ka kyauta yaron kirki, lallai zan zo.”
Kare da Kurege suka kama aiki, amma saboda Kare ya ƙoshi da naman Kyanwa sai ya kwanta a gindin wani ƙargo ya fara barci. Can sai ga Kura ta iso ta dubi Kurege ta ce: “Abokina yanzu ba wanda ya zo aikin nan sai ni?” Sai Kurege ya ce: “Ai ke ƙawata ce, kuma kina da kirki, amma Kare ya riga ki zuwa, ga shi can ma yana barci.
Idan kin cinye shi, ki bar mini fatar.” Da man Kura tana jin yunwa saboda Kurege ya sa ta haƙura da zuwa wurin mushen da ta gaya masa ta gani, sai ta ce: “Amma kuwa na gode.” Sai ta je ta kashe Kare a cikin ruwan sanyi saboda yana barci, ta cinye namansa ƙafaf saboda haɗama har ma ta fara cin fatar Kurege ya je ya fisge.
Daga nan Kura da Kurege suka kama aiki a gonar. Can sai ga Damisa ta tunkaro gonar. Shi Kurege da ma ya san haka, amma Kura ba ta sani ba. Da ya fara hango Damisa tana zuwa, sai ya ce da Kura: “Babbar ƙawata, ai ya kamata ki ɓuya ina gani kamar za mu yi manyan baƙi.”
A tsorace Kura ta sami gindin wata kuka ta raɓe. Da Damisa ta isa gonar sai Kurege ya ce: “Kai madalla, sannu da zuwa manyanmu.” Sai ta harare shi ta ce: “Ka ce Kura za ta zo, ko tana ina ne?” Sai Kurege ya nuna mata maɓoyar Kura sai ya ce da ita: “To, amma idan kin kashe ta, ina roƙo ki ba ni fatar.” Ta ce: “To na ji.”
Damisa na faɗin haka sai ta nufi inda Kura ta ɓuya. Kafin Kura ta san abin da ake ciki, tuni Damisa ta sa haƙoranta masu kaifi da tsini ta tsinke jijiyoyin wuyan Kura ko shurawa ba ta yi ba. Kafin wani lokaci Damisa ta yi kaca-kaca da ita, ta cinye ta. Sai fatar kawai ta bari da ƙoƙon kanta. Da ta gama, sai ta je wurin Kurege ta ce: “Ga fatar can.
Ka kuma gayyatar wata Kurar aiki a gonarka zan zo.” Kurege yana ƙyarma, ya ce da Damisa: “To, na gode, zan sanar da ke idan za a sake yin irin wannan aiki.” Cikin murna Kurege ya shiga tara fatun nan. A zuci ma ya riƙa cewa: “Yawwa, ni ne zan sami mata. Biri kam sai haƙuri.”
Da Biri ya ji labarin abin da Kurege ya aikata, kuma ya ji yana cewa shi ne zai auri yarinyar nan sai a zuciyarsa ya ce: “Haba Kurege, za ka ga tsiyata kuwa.” Biri kuwa ya je ya samo gyaɗa mai yawa, ya bi hanyar gidan iyayen yarinyar yana zubarwa, wato inda Kurege zai bi don ya kai musu fatun da suka nema.
Da Kurege ya kama hanya ya ga gyaɗa a warwatse sai ya fara tsinta yana cewa: “Yau daɗi goma, ga shi na samo fatu zan kai a ba ni mata, kuma ga ƙauyawa sun sayo gyaɗa daga kasuwa sun ajiye mini domin in ci in more.” Kurege na matsawa gaba, gyaɗar tana ƙara yawa, har dai ta kai shi bakin wani ƙasko wanda yake cike da gyaɗa.
Sai kawai ya tsuguna a kusa da ƙaskon, ya zubar da fatu gefe, ya duƙufa a kan cin gyaɗa. Shi kuma Biri sarkin wayo sai ya bi ta bayan Kurege yana sanɗa, ya kwashe fatun nan Kurege bai sani ba. Biri ya tafi da fatu ya kai wa iyayen yarinyar nan, suka amsa, aka ɗaura masa aure da ita.
Bayan Kurege ya ci gyaɗa ta yi masa karo, sai ya waiwaya zai ɗauki fatunsa, sai ya ga wayam, ba komai a wurin, sai ya ce: “Na tabbata Biri ne ya yi mini wannan aikin. Amma bari in kai musu ragowar gyaɗar wataƙila su yarda su ɗaura auren da ni.” Kurege na isa iyayen yarinya suka ce ai tuni Biri ya kawo fatu, har ma an ɗaura masa aure da yarinyar.
Da Kurege ya ji haka, sai ya ba su gyaɗar da ya je da ita, tare da igiyar da ya tanada wai ta ɗaurin aurensa da yarinya, ya ce: “Ga wannan igiya za ta yi muku amfani, gyaɗar kuma ku soya ku ci.” Suka karɓa ya tafi. Kurege bai tsaya ba sai a gidan Biri, sai ya tarar da wani tsohon Biri, watau kawun ango, ya ce da shi: “Ni abokin ango ne.”
Jin haka sai tsohon Birin ya ƙyale Kurege ya shiga inda ango ke barci. Da shigarsa sai ya sa wa Biri dafi a baki, wanda a ƙarshe ya kasa tashi daga wannan barcin, ya mutu. Sai nan da nan Kurege ya nemo garin dawa a gidan, ya cusa a bakin Biri, don a ce garin ne ya ci ya yi masa karo ya kashe shi.
Can sai amaryar Biri ta shigo ɗakin ta ce: “Yaya na ga ango yana barci, amma kuma ga shi kamar yana cin wani abu?” Da ta ɗan taɓa shi, sai ta gane dai ya mutu, sai ta fara kuka, shi ma Kurege ya shiga kuka. Da ya yi shiru, sai ya ce da matar Biri: “Akwai wani Dodo a daji, ya kamata mu je ya gaya mana abin da ya kashe miki miji.”
Da suka shiga dajin nan, sai Kurege ya ce ta jira shi yana zuwa. Nan da nan ya je ya zane jikinsa da gawayi, ya canza kamanninsa ya sha gabanta, ya tsaya kamar shi ne Dodon, sai ya ce: “Ke baƙuwata, ni ne Dodon baƙin daji, me ya kawo ki?” Ita kuma ba ta gane Kurege ba ne sai ta ce da shi: “Mijina ne ya mutu, ina son sanin wanda ya kashe shi.
Kuma ina son sanin wanda zan aura.” Sai Dodo ya ce: “Ai Kurege abokin Biri ne, kuma ƙanensa ne saboda Biri ya girme shi ko?” Sai matar Biri ta ce: “Ba shakka haka ne, ko shi zan aura?” Sai Dodo ya kaɗa kai domin nuna amincewa. Ta ƙara tambayar sa, har dai ta tambaya sau uku, duk yana nuna cewa ta auri Kurege.
Daga nan ya sallame ta, ta koma gidan Biri. Shi kuma Kurege ya je wani tafki ya yi wanka ya kama hanyar gidan Biri, ya tafi yana kuka. Da amaryar marigayi Biri ta ga Kurege yana kuka sai ta ce: “Mene ne kuma ya faru?” Sai Kurege ya ce: “Na tuna ɗan’uwana, kuma abokina ne.”
Da ta ji haka, sai ta dubi Kurege a cikin tausayi ta ce da shi: “Ai Dodo ya ce kai zan aura saboda haka ka daina kuka, ka zo mu je a ɗaura mana aure.” Sai Kurege ya daina kuka, suka kama hanyar gidan iyayenta inda za a ɗaura musu aure. Aka ɗaura musu aure suka zauna cikin jin daɗi lokaci mai tsawo. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Zamba da cin amana mai yin sa ba ya kai wa ga nasara.
- Komai za a yi ya kamata a yi shi cikin hikima da ƙwarewa, yin haka shi yake kawo samun biyan buƙata.
- Ƙarya fure take, ba ta ‘ya’ya.
- Matar mutum kabarinsa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar ‘Yar ‘auta Da Kogin Rantsuwa
Edita@rumasau-kallamu









